Abubakar tuƙa Napep din yake cikin sauri -sauri su fita daga unguwar kar wani ya gamsu .
Ita kuwa Shahida jikinta yayi sanyi , sai yanzu take ji kamar tayi kuskuran biyo shi .
Zuciyarta tace " anya kinyiwa Uncle Mujahid adalci? Mutumin da ya maida ke ƴa a gareshi? Ki gudu kibi saurayi anya baki rashin tunani ba?".
Cikin karfin hali ta dago tace " Yaya " ya juyo yace" ki bari mufita kar wani ya gan mu" tace" wai ina zamu ?".
Sai yayi saurin jan burki yana tunanin, shi kansa sai yanzu ya gane yayi kuskure .
Abu ɗaya yayi kawai aron keke napep a. . .