Ba Shahida ba ko Abubakar ba, hatta Abban Amir da Abban Anisa firgita suka yi dajin kalaman Yaya Baba na karshe.
Abban Anisa ne yace" ku gafararce ni dan Allah zan shiga hurumin da ba nawa ba, amma wana irin matar wani ce me kake nufi kunyi mata aure ne ko kunyi alkawarin za a bawa wani ita?". Hajiya ce tace" bawan Allah tun Shahida na da shekara tara mahaifinta kafin ya rasu ya daura mata aure da amininsa wato Mujahid"
Cikin tashin hankali Shahida da Abubakar suka miƙe tsaye bakinsu na rawa.
Hajiya tace" mun zaɓi ɓoyewa. . .