Ruwa aka yayyafa mata ta miƙe a firgice tana kallon mutanan dake gurin kafin tace" ka cuce ni Mujahid Allah ya isa ban yafe ma ba, daman auranta zakayi shine ka hana kowa zuwa gurinta? Munafiki banza , mayaudari kuma azzalumi".
Baban Mujahid ne ya daka mata tsawa da faɗin" ki tsaida hankalin ki Maryama ; ki san agaban wa kike" nan da nan tayi tsit amma kukan nan sai zuba yake .
Yace" auran Mujahid ba jiya ko shekaran jiya aka ɗaura ba ; balle ki dinga iƙrarin ya cuce ki" .
Anan ya bata labarin yadda auran ya samu asali. . .