Haka muka yi tafiya mai nisa muka samu wani guri muka ɓuya .
Na dube su cikin ɓacin rai zanyi magana amma matarsa waca nake kyautata tunanin itace uwar yaran tace" kayi hakuri bawan Allah, mu ba macuta ba ne, mun taho da kai ne domin tabbas yadda kamanin ka suka nuna in har basu ganmu ba zasu kamaka suyi ma abinda zasuyi mana kaga munja maka".
Shiru nayi ina kallon su hankalinsa ya kasa kwanciya da su gaba ɗaya har muka nausa cikin dajii muka nemi taimakon wasu mutane makiyaya suka bamu gurin kwana .
Kwanan mu biyu. . .