Maryama ce cikin farin ciki yau tun bayan kwanakin da tayi na kunci akan batun Shahida da mijinta.
Amma ga dukkanin alamu sun nuna akwai abunda take shiryawa kuma yau saura kwanaki kadan na tarewar Shahida a matsayin ta na matarsa .
Uncle Mujahid ne ya sako yayi hanyar ɗakin Shahida domin yau fita zai yi da wuri
Tana zaune tana aikin da ta saba wato tunani.
Ya dube ta bayan ya zauna a gefan katifar da take kwance yayi magana da ƙarfi domin yasan ko yayi a hankali ba ji zata yi ba.
Ta ɗago. . .