Shahida suna tafiya wasu hawayen mamaki da al'ajabi suna zubo mata.Anisa tana kallonta amma tai mata shiru domin a ganinta abinda yayi shine dai-dai.Suna shiga gidan ta dubi Anisa ta ce " shi na gani kuwa Anisa? Naga kamar shi ko bai gane ni ba ne".Ajiyar zuciya tayi Anisa ta ce" shine mana Shahida, wataƙila ya ji faɗa ne ya daina kulaki saboda auran dake kanki"."Anisa ya daina kulani fa kika ce".Ta ce " eh mana Shahida ko kinga laifinsa, idan fa ya kulaki duk zunubi zaku samu".Murmushi tayi suka ƙarasa ciki jikinta ba. . .