Hajiya da kawu gombo a tare suka furta Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.
Wanda ya janyo hankalin Shahida ta dago tana duban Abban nata wanda tuni rai yayi halinsa.
Mujahid kuka ya saki me karfi yana rufe idon Usman din yana furta "Allah ya karbi bakuncin ka Usman , Allah ya gafarta ma" .
Wani gigitacan ihun Shahida ne yaja hankalinsu wanda a take ta fadi a sume.
Duk hankalinsu yayo kanta aka yayyafa mata ruwa ta fara kuka mai tsima zuciya , babu wanda yayi ƙoƙarin hanata domin kuwa ya cancanta tayi ta samu sanyi a ranta.
Wannan mutuwar ba. . .