Cikin tashin hankali duk suka miƙe amma kafin suyi wani yunƙuri Suraj daya shigo daga waje domin kiran Shahida . Da Abdul ya faɗa masa ta shigo,yayi saurin kinkimarta cikin ruɗewa a tunanin sa dukan da akace Mujahid yayi mata ne yasa ta faɗuwa.Asibiti maifi kusa yayi da ita dan shi ko tunanin ya tsaya a watsa mata ruwa baiba.Yayin da tya bar su Abubakar da Anisa da Maman Anisa da Abbanta cikin ruɗani ko kyakkyawan motsi sun kasa balle su bi shi.Alhaji Mujitafa ne ya katse shirin da cewa" Allah ya farfaɗo da ita lafiya , ni. . .