Alhaji Muddasir, Alhaji Muhammad da sauran mutane da suka biyo su, suna tsaye a tsakar asibiti, kowa cikin tsoro da damuwa.
Bayan lokaci mai tsawo, wani likita ya fito ya ce “Alhamdulillah, mun samu mun tsayar da jinin.
Amma har yanzu tana cikin hadari saboda asarar jini mai yawa. Ku cigaba da yi mata addu’a.”
Cikin sanyin jiki Alhaji Muddasir ya ɗaga hannunsa sama yana cewe “Ya Allah ka raya ta, ka bamu damar gyara wannan rayuwar tata , domin alamun sun nuna cewa tana da damuwa”.
Alhaji Muhammad ya ce“Wannan yarinyar tana buƙatar kulawa da gata, za mu. . .