Mujahid ransa ya ɓaci ya ce" in ni baki sani ba amma kin san wannan ko?" Yana nuna Abubakar.
Ta dubi inda ya nuna Abubakar ta ce" ni ban ma taɓa ganin wannan fuskar a rayuwata ba".
Abubakar kasa tsayuwa yayi , kafuwansa suka kasa ɗaukarsa yana cewa" karkiyi haka Shahida dan Allah.
Mune fa , ga ni ga Anisa ga Uncle Mujahid ga Hajiya ga Abban Amir da Aunty Salma".
Lumshe ido tayi , ta zame ta juya musu baya .
Kowa mamakin abinda ta aikata yake , wasu kuma gani suke kanta ne ya tabu.
Baban Mujahid shi har ga Allah cewa. . .
