Hajiya ta mike a firgice amma kuma sai ta yanke jiki ta fadi.
Ruwa Maryama ta dauko tana ihu ta watsa mata.
Hajiya ta buɗe ido tana duban Maryama sai kuma ta fashe da dariya .
Maryama ta ce" Hajiya ki tashi muje gurin Malam a fada masa ya baki abinda zaki sha tunda anyi kuskure".
Wani wawan ihu Hajiya ta saki tana dariya tare mikewa tana ture Maryama ta fita a guje alamar kai ya samu matsala.
Ihu Maryama ta saki tabi bayan Hajiya amma ina! Hajiya tayi mata nisa kuma an kasa riƙota .
Ganin haka yasa Maryama. . .