Fita tayi da gudu tana kiran Abdul suka shigo a tare suna rige-rige.
Wani ƙarin tashin hankalin duk inda kurjin ya fito sai ya kumbura .
Dan haka daga ugunta zuwa karatunta sun kumbura suntum.
Abdul da Na'ima kuka suka fashe dashi suna kiranta sun ma rasa me zasuyi.
Mujahid da shigowarsa kenan yaji ihu da kuka yayi saurin yin hanar ɗakin Maryama.
Abunda ya tarar ne yasa shi jin wata juwa, cikin ƙanƙanin lokaci Maryama ta tasauya kamar ba ita ba.
Duk rashin imanin mutum ya kalleta sai yaji tausayinta.
Fita yayi domin bazai iya tsayuwa ba, dole. . .