Yayi murmushin takaici yace” gaskiya ne”.
Mujahid gaban sa sai faɗuwa yake domin alamu sun nuna Hajiya bata karɓi Shahida ba tun batasan a wana matsayin ma take ba yanzu.
Haka Suraj ji yake dama shi aka ɗaurawa Shahida ba yayansa ba saboda yasan akwai matsalar da yarinyar zata fuskanta.
Hajiya ce ta kuma ƙosawa tace” wallahi ko ku fadamin ko kuma ku fitar min da ita wannan halita kamar diyar Mayu da Ido kwala-kwala”.
Baba zai magana Mujahid yayi saurin cewa” yarinyar Usmance Hajiya ya bani ita amana tunkan yarasu”.
Wani wawan. . .