Ta dubi Maryam tace” ki sallami Hanne ga sabuwar ƴar aiki nan ki horar da ita kamar Jakar da tafito daga daji, kinji ko?”.
Ta daga kai tana murna da jin daɗin abunda aka kai mata.
Shikuwa uffan bai ce ba , domin yasan maganarsa wani kwaɓar zata jayo.
Haka yanaji yana gani suka fito da Shahida suna marinta , tare da haɗa ta da Hanne ta nuna mata komai gudin kartayi musu ɓarna.
Ba wani fahimta take ba amma haka dole ta daure tana kuka .
A ranar suka tasa ƙyeyar Hanne zuwa gidan su Maryama inda zata cigaba. . .