Shiru Abubakar yayi yana murmushi yace “ muje”.
Shahida na dariya tana duban Minal da suke musu da Anisa akan wani littafi na Ikram da Tsananin Rabo wai wallahi a yadda littafin ya nuna Widad yarinyar cikin Tsananin Rabo tafi Ikram kyau.
Ita kuwa dariya take tana cewa” duk suna da kyau ko”.
Anisa tace “ Ita fa Widad jinin Larabawa ce “.
Minal tace” ita kuma Ikram fa Bafulata ce fa Shahida”.
Zatai magana kawai sai ganin Amir da Abubakar sukai a gefan su ta gimtse maganar tayi gaba.
Anisa ma suka rufa mata baya, shi kuwa Abubakar ya bisu yana kiran. . .