Skip to content
Part 1 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

  اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Matashiyar yarinya ce zuƙeƙiya fara, farinta daidai, ‘yar kimanin shekaru 20 da haihuwa, durƙushe take akan guiwowinta ta yi kneel-down a gaban wata mata wacce ko ba’a faɗa ba kasan mahaifiyarta ce duba da kaman da suke yi da kuma maganganun da matashiyar budurwan ke yi.

Cikin tsananin kuka mai nuni da stagwaran taƙaici da kuma tsaban damuwan da take ke ciki ta ce, “Haba Mami na, Mami dan Allah dan Annabi ba dan ni ba, kuma ba dan halina ba ki bar wannan rayuwa, Mami kina zubar da mutuncin kanki kina zubar da na ‘yar ki, Mami da girmanki kina rayuwa irin ta yara ƙanana marassa tunani ko mafaɗi, Mami ke fa ya kamata ki stawatar mini idan kinga ina ƙoƙarin sanya kai na a irin wannan lalatacciyar rayuwan, amma fa Mami ke da kanki kike yi ba ma ni ɗin ba, haba Mami na ina iliminki da tunaninki kika zaɓa mana wannan rayuwa irin ta jahilai…”

Maganan dake baki na ne ya maƙale a maƙoshi na, sakamakon wani azababben marin da Mami na ta kifa mini, miƙewa tayi tsaye tana huci ranta a ɓace kaman ko da yaushe idan hakan ya faru tsakaninmu, idanuwanta ta zuba mini tare da cewa,  “Banafsha har rashin kunyar ki da fistaranki sun kai haka? Ina mahaifiyarki kina sokamun baƙaƙen magana, ni kike faɗawa ina rayuwa irin ta jahilai? Ni kike ƙira jahila Banafsha? Irin tarbiyyan da na miki kenan ki nunawa duniya ni ma kin renani balle wasu? Banafsha ni kike faɗa wa haka?” Mami ta ƙarishe maganan cikin stananin ɓacin ran da har idonta na ƙoƙarin sauya kala.

Cikin kukan da ya zamo mini jiki dan in da sabo na saba, sai na ce, “Allah ya huci zuciyanki Mami na, amma wuyana bai yi ƙwarin da zai sa nayi suɓutan harshe a kan mahaifiya ta ba, koma menene ke ɗin uwa ce a gare ni kuma ko ya kike ke mahaifiyata ce, amma ina mai haɗa ki da Allah da Manzon sa Mami kiji tausayin rayuwata kibar wannan lalatacciyar rayuwan, munanan maganganun da mutane ke jifa na da shi tun baya damuna har ya fara mini ciwo, Mamina dan Allah kiji tausayin maraici na ki daina wannan rayuwan ko dan ni Mami, wallahi duk inda naje suna ɗaya ake qira na da shi manya da yara, duk inda na wuce sai ace ga ‘YAR KARUWA! Mami tun ana faɗa a ɓoye har takai mutum zai staya a gabana ya ce mini hakan kuma ba ni da yacce zan yi, dan girman Allah Mami kiji tausayi na kibar wannan rayuwa mai cike da kunyan duniya da lahira, Mami ki tuna fa akwai mutuwa fa, kuma ba mu san yaushe, a ina, a wanne hali, ta yaya za ta riske mu ba, dan Allah Mamina ki daina kinji” na ƙarishe maganana cikin sigan tausayi ina share hawaye mai ɗumin gaske da ke bin kunci na.Mamina zama tayi ta dubeni tare da cewa, “Maganar da nake faɗa miki a kullum ita ce zan ci-gaba da faɗa miki Banafsha,  ni ba karuwanci nake yi ba sana’a nake yi, wanda kuma da wannan sana’a na siya gida na kai ki makaranta, cinki, shanki, suturanki, maganinki, da komai naki har kika kawo i zuwa yanzu da kuɗin sana’ar nan nake miki, me yasa kema za ki bi ta faɗin jama’a ba za ki fahimci mahaifiyarki ba? In na zauna bana komai kina ga akwai mai kula da mu? Akwai mai ɗaukan nauyin karantunki, cinki ko shanki ko suturanki? Ko da ace aikatau muka je gidan mutane to tabbas nasan za’a nemi lalata mini ke ko wulaƙanta mu, wanda ni kuma ba zan jure hakan ba, akan abu ya same ki gwanda ko duniya ne su taru a kaina su ce komai ma sannan sunan da ake ce miki ‘YAR KARUWA ya bar damunki in baki fahimci mahaifiyarki ba babu mai fahimtarta Banafsha, ki dubi rayuwan yanzu da idon basira da kyau, ko bara na ce zan yi dan na kula da ke to fa tabbas za’a nemi lalata miki rayuwa ko kuma ni ɗin, Banafsha duk da ke yarinya ce, amma a wannan shekarun naki ya kamata ki fahimci rayuwa da kyau.”

Kallon Mamina nayi da idanuwana da kullum cikin zubar hawaye suke na ce, “Wallahil Azeem Mami na gwammaci muyi rayuwan aikatau akan irin wannan rayuwa, na kuma zaɓi muyi rayuwan bara akan wannan rayuwa, Mamina gwanda na zama ‘yar talla mu yi sana’anmu ko na rufawa kai asiri ne ya fi mini akan wannan rayuwan, sannan lalata rayuwata ba wanda yake da ikon hakan in har Allah bai ƙaddara hakan ba to babu wanda ya isa tunda kina min addu’a, kuma Allah zai kare ni dan addu’an bakin mahaifiya ba a maida shi, dan Allah Mamina ki daina, wallahi Mami akwai mutane na gari da yawa a rayuwa masu yi dan Allah ba tare da zalunci ba, nifa Mami ko baran kika turani zanyi na nemo mana abinda za muci karatu ko wani sutura na haƙura da su, mutuncinki da nawa su ne abun da nafi buƙata, wannan suna da ake faɗa mini yana sa zuciyata tana mini zafi sosai-sosai Mamina, dan Allah inma ba za mu yi wani aikin ba mubar garin nan mu koma wajan ‘yan uwanki ko na mahaifi na ne kinji…..”,   wannan karon ba mari ne ya maƙalar da sauran maganan dake baki na ba domin kuwa Mamina rufe ni tayi da duka ko ta ina kaman an aiko ta, da ƙyar aka shigo aka karɓe ni.

Maman ƙawata Umaima ce ta shigo ta karɓe ni ta riƙe hannuna muka tafi gidanta wanda ya ke gidan su babbar ƙawata kuma Aminiyata wacce banda kamarta.

Matar da ta shigo ta karɓeni wacce muke ƙira da Ummu, kallona tayi ta ce “Banafsha wai me yasa kike son yawan yin sa’insa da Maminki ne da har yake kai da ga miki irin wannan dukan ne? Yanzu ba dan Allah yayi fitowa na ba kin san halinta za ta iya miki rauni, Banafsha kin girma fa yanzu ba da bane kin zama budurwa duka bai kama ce ki ba kiwa mahaifiyarki biyayya ki kuma yi haƙuri komai zai wuce kiyi ta addu’a.”

Cikin tsananin kuka da ciwon da jikina ke mun na dukan da Mamina ta mini ina sheshsheqa da muryana da ta fara dishewa na ce, “Um..mu yaa..yaa.. yaya zan.. yi? Ummu, Maa..mi na, Ummu me yasa sai ni? Wan…..nann ra..yuwa..n akwai…ciwo mahaifiyar mutum ta dinga kule-kulen mazaje daban-daban, Ummu kiji fa sunan da ake qira na da shi a anguwan nan ‘YAR KARUWA! Ummu hakan akwai daɗi?  Ummu ya zanyi da rayuwa ta? Ya ake so nayi? ina ake son na saka kai na? Ko sai na mutu kowa hankalinsa zai kwanta?” Na faɗa ina ƙara fashewa da mastanancin kukan da zuwa yanzu sautin ma ba ya fita.

Ummu kallona tayi cikin sigan rarràshi ta ce, “komai na duniya mai wucewa ne Banafsha, ke dai ki ci-gaba da addu’an Allah ya kawo miki miji na gari kiyi aurenki wanda nake fata zuwa wannan lokacin Allah yasa komai ya wuce.”

Cikin kuka na ce, “Ummu wa zai yi aure? Wa zai aure ni? Ina ‘YAR KARUWA wa zai auri yarinyar da uwarta ke lalatacciyar rayuwa? A’a Ummu karki faɗa min abinda ni da kai na nasan ba zai taɓa faruwa ba, kuma nima ba zan yaudari kai na ba, nasani ni da aure har na mutu sai dai a lahira idan ana yi, zan zauna da Mamina na dinga addu’an Allah gyara mana rayuwanmu ya shirya min uwata, amma ba zan taɓa yin aure ba dan nasan ba mai aure na, kuma ko an aure ni za’a goranta mini.”

Ummu murmushi tayi wanda hakan ya ɗan sauƙaƙa mini abinda ke damuna a zuciyata, dan sosai nake jin Ummu a rai tamkar mahaifiya ta, Ummu ta ce, “Banafsha ki rubuta ki ajiye ni Ummul-khultum na ce za kiyi aure in Allah ya yarda, kuma aure ne irin wanda ba ko wacce yarinya ke dacen yi ba sai wacce Allah ya ƙaddarawa hakan, za kiyi aure in Allah ya yarda wanda mijinki na tabbata zai sanya ki mance kin ma taɓa shiga wannan halin quncin rayuwa, duk bawan da ƙaddara ta stananta a rayuwarsa to tabbas gaba kaɗan idan da rayuwa zai riske alkairi mara misaltuwa, to ina so kema ki ɗauka hakan, duk da akan jarabawan rayuwa da wani ke ciki to naki ba komai bane, kuma bawan da Allah ke jarraba shi Allah ke so, kibar wannan tunanin in Allah ya yarda za ki yi aure.”

Kallon Ummu nayi idanuwana har yanzun da burbushin ƙwalla na ce, “Ummu nasan da haka, amma babu mai aure na ina ‘YAR KARUWA! sannan ko da nayi auren to Ummu tabbas wulaƙantaccen rayuwa zan yi dan kuwa zan zama tamkar mujiya ko saniyar ware yacce ake nuni dani yanzu haka can ma za’a yi, za’a dinga gorantamini a ce ni Ƴar karuwa ce a dinga wulaƙantani, Ummu ni ko kaɗan ma bana ƙaunar maza, Ummu na tsani maza gani nake kowa irin halin sa kenan bin mata.”

Cigaba da rarrashina Ummu tayi har
Ƙawata Umaima ta shigo ta same mu a haka, ganina kawai da tayi ta fahimci me ke faruwa dan ta sani tabbas labarin gizo baya wuce na ƙoƙi, dan kusan aikin kenan kullum ni da Mamina, idan ba’a yi da safe ba za’a yi da yamma.

Cikin yanayi na rarràshi ta ƙira sunana ta ce, “Masoyiya Banafshaty.”

Jin sunan da ta qira ni da shi sai da na ɗan murmusa dan kuwa Allah ya gani ni da Umaima ba ƙaramin ƙaunar junan mu muke ba, duk irin halayyan mahaifiyata da yacce ake yama-ɗiɗi da ni a gari hakan bai dame ta ba ko kaɗan dan Allah take ƙaunata nima dan Allah nake ƙaunarta, duk gidansu suna ƙaunata illa iyaka yayansu ɗaya da ko giftawa nayi sai yaja staki in kuma ya ganni da Umaima to ranan sai tasha na jaki idan dai ba wai Ummu na gida bane ta gani ta hanasa, gaba ɗaya ya staneni shi da mahaifiyarsa, ba iya su ba kowa a anguwar kallona yake da laifin mahaifiyata kowa ɗauramun laifin da ban taɓa kusantan shi ba yake yi, in ka cire wannan gida to ba gidan da nake shiga a anguwan mu, kuma bayan Umaima ba ni da wata ƙawa ko a makaranta.

Cikin sigan wasa na harari Umaima na ce “Ba wata Masoyiya atou kar ki yaudare ni, kin tashi kin kama hanya kin tafi aiken Ummu ke kaɗai wato salon asa miki albarkan ke kaɗai ba, irin ba amanan nan, shi ne za ki wani ce mini masoyiya to na ƙi”, na juya ga Ummu nace “Ummuna ai dai tare za ki raba mana albarkan ko?”

Ummu na murmushi ta ce, “Daidai wa dai-da ma kuwa Banafsha ‘yar Ummu.”

Murmushi nayi, ƙawata Umaima ta riƙe hannuna ta jani har cikin ɗakin su ta zaunar da ni a bakin gado ta ta ce, “Wai yanzu ke ni za ki cewa yaudara amma dai kinsan ƙaunar da nake miki na amanane ko?”

Kukan da nake dannewa ne ya samu nasaran kuɓucemun, sai kawai na rungume Umaima ina kuka mai cin zuciya. Hankalinta ya tashi ita ma a take idanuwanta suka kawo ruwa sai hawaye kuma, bubbuga bayana take yi cikin sigan rarrashi ta ke cewa “Kiyi haƙuri haka dan Allah masoyiya, kukan da kike yi yana yawa ko so kike hawayenki ya ƙare ne? dan Allah kibar kukan nan bana so please Banafshaty.”

Cikin kukan na ce, “Umaima ya zan yi da rayuwa ta? Ya ake so nayi ne? Ni ji nake mutuwa ma tafi mini wannan ƙazantaccen rayuwan, dan Allah ace uwarka ta rasa abun yi sai karuwanci kuma a haka Mami ke cewa sana’a ce wai dama karuwanci sana’a ne? Mami ta ce bata so aci mutunci na ko a lalata mini tarbiya shi ya hanata zama haka ta kama wannan sana’a dan Allah wannan shi ne soyayya Umaima? Ta kwaɓar da mutuncinta sannan ta kwaɓar da nawa, shi fa mutunci Madara ne, a abinda Mamina ke yi wa zai ganta da mutunci idan ba ni da ya zamo mini dole ba?” duk cikin mastanancin kuka nake wannan magana wanda i zuwa yanzu kai na mugun sara mini yake yi kaman na cire kan na huta.

Umaima ta ce “Banafshaty dan Allah ki yi haƙuri haka nan, ni dai mu ci gaba da addu’a komai zai wuce kin ji, kuma Mami na sonki fiye da yanda take faɗa ma dan Allah kiyi haƙuri kina addu’a kina kau da kai kinji” ta faɗa tana sharemun hawayena.

Lumshe ido nayi nace “Umaima in dai wannan ce soyayya to tirr! da soyayya, Allah wadaran soyayya, bana son soyayya, bana ƙaunar soyayya, na tsani soyayyan, Umaima ko na kau da kai kan baya kauduwa domin muddin ina gida wani zai zo wajanta to sai naji zuciyata na tafarfasa zuciya ta kaman ana wastamun ruwan zafi zuciyata kaman ana ƙonemun ita, ji nake kaman na kashe kaina na huta, wallahi ba dan kisan kai zunubi ne babba ba da na jima da kashe kai na dan da wannan rayuwa gwanda na mutu na huta, Umaima imagine wai har YA DANISH shiima zai ce mun ‘YAR KARUWA, stana da cin mutuncin ya wuce mutanen waje ya koma har kan mutanen gida suna min wannan wacce iriyar rayuwa ce?”

Fashewa nayi da kuka mai ciwo tuno abinda ya faru ɗazu sai na ce, “Umaima kinsan me ya faru ɗazu?”

Girgiza kai tayi tana hawaye dan maganan ya Danish ya mata ciwo ita ma sai ta ce, “Banafshaty kar ma ki faɗa min me ya faru kinji, yacce kike shanyewa ki shanye kawai, saboda ciki ba dan tuwo kawai aka yi sa ba ki yi haƙuri za ki ga riban haƙurin da muke cewa kiyi kullum da yardan Allah, babu jimawa za ki ga sakamakon Ubangiji akan jarabtar da ya miki.”

Hannunta na riƙo ina hawaye na ce “A’a Umaima, ko kaɗan wani abun ba zai riƙu a ciki ba dan riƙuwan sa tabbas masifa ne, haɗiye wani abun to barazana ce ga lafiyan mutum, kaman kai ne ka samu guba ka cusa a cikinka kuma ka ƙi zuwa asibiti a baka taimako, Umaima idan ban faɗa miki ba bazan ji sanyi a rai na ba wallahi ba abinda zan ɓoye miki a rayuwata indai bai kauce sirrin da Allah ya ce ya zama sirri na ba, wanda wannan nasan babu shi a kai na nikam, Umaima wai ɗazu fa ina kwance a ɗaki na ina bita haddan da ya rage mana kawai naga mutum ya faɗo mini ɗaki daga shi sai ɗan gajeren wando, wai yana tambaya ta ina Mami na ta tafi a hannu yake sauri yake” kuka nake sosai nace “Umaima kiji fa wai har ni ya ke gayawa wannan magana, to wallahi idan ita Uwata na haƙura ban ɗau mataki ba dan Uwata ce to su na kusa fara ɗaukan mataki a kansu in ta kama in kashe mutum in yaso nima a kashe ni, yaro ya zo babba ya zo dattijo ya zo stoho ya zo, Mami har da wanda ta kusa haifa take kulawa wannan wacce rayuwa ce? Haka da safe wani saurayi ya fito ɗakinta ina stugunne ina aiki kawai naji an zame mini ɗan-kwali ɗan iska wai gashina na burgesa irin na mamata”, kuka nake sosai idan na tuna wasu abubuwan.

Ƙawata Umaima rarràshi na ta ci-gaba da yi kawai dan ita ma abun sosai yake damun ta, ba ɓata lokaci zazzaɓi ya rufe ni ruf-ruf nan take na fara tari wanda nake ji tamkar zuciyata zan amayo dan azaban da nake ji a ƙirji na, hawaye nake ina tarin, wanda hakan ya storita Umaima, cikin ruɗewa ta fice ta ƙira Ummu suka shigo tare, Ummu ma ta ruɗe amma duk da haka ta mini faɗa na daina saka damuwa a rai na, sai da ta gyara mini kwanciyana ta lulluɓe ni sannan ta fice dan ta ɗauko mini magani, Umaima kuma tana zaune a gefe na tana aikin jero mini sannu tana hawaye.

Ganin tarin yaƙi stayawa sai Umaima ta dube ni cikin tsananin kuka ta ce, “Banafshaty wallahi idan kika ja abu ya same ki ba zan taɓa yafe miki ba” tana gama faɗa kawai ta fashe da kuka mai nuni da tausayina da take ji, ta rungumeni nima kukan nake jikina sai rawa yake yi ga kuma ya ɗau wani azababben zafi kaman garwashi.

Yar Karuwa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×