Skip to content
Part 11 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Majeeder girgiza kai tayi ta ce, “A’a Papi.”

Alhaji ya ce, “Sunan Maminki ke da ƙawarki ne Ramla, dan haka ki daina ƙiran sunan kinji.”

Jinjina kai Majeeder tayi, tana murmushi ta ce ta daina, Alhaji ya ce, “good girl, kuma su General ɗin ma suna zuwa in Allah ya yarda nan da next week, inyaso idan kuna hutu a school ba lectures sai ki je can ki yi hutunki, saboda nima zan yi tafiya kuma zan iya kai 2 month’s kamun na dawo.”

Majeeder washe baki tayi ta ce, “Allah ya kai mu lafiya, Allah kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah kawo su yaya lafiya, finally zan ga yaya Bunayd bayan stawon lokaci, gaskiya ni Papi ka faɗawa yaya idan yayi aure ni gidansa zan koma da zama” ta ƙarishe maganan kaman za ta yi kuka.

Alhaji murmushi yayi ya ce, “Idan kika koma gidansa ke kuma wa zai zauna miki a naki gidan? Maman babanta.”

Majeeder tura baki tayi ta ce, “Ni dai Papi sai na koma gidan yaya da zama.”

Alhaji ya ce, “Shikkenan Allah basa mace tagari, sai kuma ki masa magana ki ce yayi aure, ni kuma sai ma faɗa masa za ki koma gidansa da zama ko?”

Majeeder na murmushi ta gyaɗa kai, hira Alhaji ya dinga janta da shi har bacci ya ɗauketa a wajan, tashuwa yayi ya gyara mata kwanciyanta, sannan ya ci-gaba da aikinsa hankali kwance, cike da kewar Ramlatunsa.

*****

CAS Bunayd mancewa yayi da maganan zuwa Kano, ya shirya ya bar Nigeria, daman shi kaman network haka yake ba tabbatas, yau yana Nigeria gobe kuma yana wata ƙasar, musamman ma da yake Sojan sama, kuma yawancin ƙasashen da yake zuwa yana da gida a can, kuɗin gaske Bunayd yake da shi, ko iyayensa ba su kai sa kuɗi ba.

Yau kuma a ƙasar Spain ya sauƙe zangonsa, jirginsa na sauƙa drivernsa ya zo ya ɗauke sa, a gaban wani tankamemen gida motan nasu ya staya, da wani button ake buɗe gate na gidan, ana buɗe musu suka shiga, mota na parking Bunayd ya buɗe da kansa ya fito, cikin takunsa na isa ya ƙarisa bakin ƙofan shiga gidan, ƙofa ne mai amfani da numbobi (password) wajan buɗewa, sai da ya saka sannan wani murya kaman na yara ya ce, “welcome” ƙofan ya buɗe ya shige.

Subhanallahi! Gida ne na gani na faɗa, stayawa faɗan staruwan gidan da haɗuwansa ma ɓata baki ne, direct ɗakinsa ya wuce ya wasta ruwa ya sauya wasu haɗaɗdun kayan sannan ya fito, a babban palourn ya samu wata dattijuwar baturiya ɗauke da tray, cikin turanci ta gaidasa, Bunayd ya amsa mata ba yabo ba fallasa, faɗa masa tayi ga abinci, lumshe ido yayi kawai bai ce komai ba, saboda ya sha faɗa mata tabar wahalar da kanta masa girki ko ya zo, indai yana buƙatan abu zai mata magana, amma dattijuwar muddin ya zo ƙasan to sai ta masa abinci, faɗa mata yayi ya ƙoshi sai ya dawo zai ci, yana gama faɗa yayi gaba, a wata haɗaɗɗiyar mota baturen drivern nasa ya ja sa suka tafi inda ya faɗa masa.

Wani irin haɗaɗɗen wajan shaƙatawa ne, ba abin da babu a wajan, gefen eatery, club, bar, hotel, swimming pool etc.

Bunayd wajan pool ɗin ya nufa, irin kujera mai kama da resting chair haka nan ya samu ya zauna, matan turawa sai zirga-zirga suke, daga masu swimming-wear sai masu pant da bra kawai, Bunayd kallon ma na rigima da isa yake yi, idan ya kalli wannan ya taɓe baki, idan ya kalli wannan ya runste ido, idan ya kalli wannan ya yi murmushi kawai, wayansa ya ciro tare da dialing layin general, a ɓangaren General daman ya gama gwada layin Bunayd na Nigeria bai shiga ba, rasa layin wacce ƙasa zai fara ƙira yayi, sai kuma ga ƙiran Bunayd ɗin ya shigo, amsawa yayi yana murmushi ya ce, “ɗan halak ya ƙi ambato.”

Murmushi ƙayatacce Bunayd yayi ya ce, “Affa Barka da gida.”

General ma murmushin yayi ya ce, “Yau kuma kai ne da ƙiran Affa? To ban amsa ba ka faɗa General ya fi daɗi, Affa haka kaman wani stoho, General ya fi ana ji ansan matashi ne ni ba stoho ba.”

Bunayd murmushi yayi sosai har sai da fararan haƙoransa suka bayyana, dimples nasa suka losta, cewa yayi, “Affa ai daman kai ba stoho bane, Sir ne dai stoho.”

General ya ce, “Yaya dai ya ce ka daina ce masa Sir, yauwa daman yanzu nake ƙiran layinka naji shiru na ce ka tafi kuma.”

“Eh amma 2 day’s kawai zan yi na dawo, akwai abinda na zo yi ne mai muhimmanci.”

General ya ce, “ai ko yawonka ma mai muhimmanci ne kai kam my Man, yanzu dai ka tabbatar ka dawo nan da kwana biyun saboda tare nake so muje Kano dukanmu.”

Dafe kai Bunayd yayi ya ce, “Ni na manta ma ai General, amma dai gobe zan dawo in Allah ya yarda, daman auren Abeed ma ya kusa may be na zauna har a yi bikinsa.”

“Ok! Allah dawo da kai lafiya Man, daman nasan yawo ka je ba aiki ba, kai ai ko stunstu ya ganka haka ya ƙyaleka, Allah ya sa ka haɗu da taka matar a wajan auren Abeed ɗin.”

Murmushi kawai Bunayd yayi bai ce komai ba, ci-gaba da wayansu suka yi kaman abokanaye ba uba da ɗa ba, sai da suka gama suka yi sallama ya kashe wayansa, wata baturiya ne ta zo wajan tare da miƙa masa sabbin kaya a ledansu, amsa yayi ya je ya sauya ya zo ya shige ruwan shi ma, tunda ya shiga ƴammatayen ciki suka fara yiwa wa kansa, Bunayd murmushin mugunta kawai ya yi dan shi kaɗai yasan abinda zai yi, wayansa da ke wajan kujera ne ya ɗau suwwa, drivernsa da ke staye a gefe shi ya miƙo masa, kara wayan yayi a kunnensa ya ce, “ina pool Abeed, idan na gama zan ƙiraka.”

Dariya Abeed yayi ya ce, “CAS ka ce kaje bawa idonka abinci, musulmin ɗan jagaliya ba, kai daga can sai can, kuma duk ka gama yawo ka dawo ka ce matan ba su gama sanin duniya ba, to nidai maganan serious ne kawai mu yi ta yanzu ba wani sai ka gama, inba dai Chaji kake yi ba.”

Ɓata rai Bunayd yayi ya ce, “Amma dai ka gama da ni wallahi, yanzu har akwai macen da za ta iya mini Chaji a Spain? Ƴan banzan da duk Palace nasu yake a salafce ba ɗumi, zan je ina Chaji ina gane akwai mutane a duniya ne, ai full definition of Chaji shi ne wanda kana yi baka sanin kowa yana existing, duka matan Spain ƙauyawa ne, yanzu ma so nake na ɗura wa wata ruwa.”

Dariya Abeed yayi sosai ya ce, “To ko ba Palace kake Chaji ba nasan ko kana taɓa biyu kyauta milkies.”

Guntun tsaki Bunayd ya ja ya ce, “Duka matan Spain ƙwailaye ne, ba wacce milkieynta yayi girman da zai ishi CAS Bunayd, wasunsu ƙirjin ma kaman an shafe sa, abu kaman ƙwallon cashew, da dai akwai mai kaman Mango ko Orange ai na iya lallaɓawa, amma duk abu ba kyawun gani, kuma fa yanda suke yawo hakan nan gani suke sun ƙure adaka suna da kaya load-load back an front, kai Allah mun gode maka, kuma mun tuba, Alhamdulillahi da ba mu fito a cikin turawa ba, haba dan Allah sai kaga mace kaman boss a dire kawai ba shape, baya ba tudu ƙirji ba tudu, daga kyawun fiska har na sura ana cire matan larabawa da na indiyawa to sai matan Africa, ni kwata-kwata turawannan ba burgeni suke ba, ƙauyanci ya musu yawa basu waye yanda ya kamata ba, bari na ɗurawa wata ruwa zan ƙiraka” Bunayd ya faɗa lokacin da ya ji wata na shafasa.

Abeed dariya yayi ishashshe ya ce, “Baka da kirki, nasan ba zai wuce an ɗan rungumeka ka ji ɗumi ba, ka ci-gaba da dannawa beb’s na mutane ruwa a pool, wataran sai ka kashe wata saurayinta ya ɗaureka, bar ganin kai Soja ne, law’s na ƙasashen turawan nan sam bai da daɗi, ba tausayi ba sassauci mugaye ne.”

Taɓe baki Bunayd yayi ya kaste ƙiran, Abeed a nasa ɓangaren dariya ya dinga sha, ya zauna jiran Bunayd ya gama muguntansa su yi waya ya faɗa masa abinda ake ciki.

Bunayd juyawa yayi ga baturiyan da ke shafa sa, murmushin mugunta yayi a zuciyansa ganin wata guzuma ce fiska ko kyan gani babu, a fili kuwa stadadden murmushinsa mai rikata mata ya sakar mata, tuni baturiya ta susuce tana ta shafa jikin Bunayd, cikin turancinta ta ce, “tattoo naka yayi kyau handsome.”

Lumshe narkakkun idanuwansa yayi, sannan ya buɗe su kaman mai jin bacci ko mugun feelings, a hankali ya mosta bakinsa ya ce, “thanks.”

Baturiyan kuwa ƙara matowa tayi akan Bunayd tuni ta rungume sa, Bunayd ganin tana ƙoƙarin taɓa masa Dragon ɗin sa, tuni yayi cikin ruwa da ita, Bunayd mayen ruwa ne, sosai ya iya ruwa kaman ba sojan sama ba, baturiya duk iya ruwanta sai ga ta kaman za ta mutu dan haɗiyan ruwa, saboda Bunayd yi yayi kaman shafata yake amma danneta yayi a cikin ruwan kuma bai bari ta ɗago ba, sai da ya ga tana ƙoƙarin mutuwa sannan ya saketa yayi gaba, a mugun haukace ta ɗago ta fice a ruwan tana ƙaƙarin amai.

Bunayd kaman ba shi yayi wannan ƙetan ba ya juya ya cigaba da swimming nasa, kuma duk macen da ta taɓa sa, in dai ya kulata to sai ta sha ruwa dai-dai gwargwado, kuma yana gamawa zai yi gaba, sai da ya gama iyayinsa sannan ya fice ya amshi towel ya goge jikinsa, kayansa ya mayar suka yi gaba, suna komawa gida ya taba girkin dattijuwar kaɗan ya haura sama ɗakinsa, yan shiga ya faɗa kan gado yana sakin dariyan mugunta, kar ku so ganin irin kyawun da dariyan ya yiwa Bunayd, a fili ya ce, “Ai ba mai taɓa jikin CAS Bunayd a bati sai mai Palace da ɗumi, mai isassun milkies.”

Yana gama dariyansa ya ƙira Abeed, tunda Abeed ya ji muryan Bunayd ya tabbatar ya aikata muguntan nasa, shi ma dariyan yayi ya ce, “kama tu dini tu dana, kana wahalar da budurwayen wasu, kai ma Insha Allah wani na can yana wujijjiga matar da za ka aura, may be ma har Palace ɗin ya leƙa.”

Taɓe baki Bunayd yayi ya ce, “So what!? Ai ni banda mastala da virginityn mace, abinda nake buƙata kawai mace wacce tasan rayuwa, idan wani ya leƙa Palace ɗin ma aiki ya rage mini no delay, Palace na isowa gare ni kullum Chaji available, kullum full cherge kawai, mace nistasttiya ba ta cikin tsarina, so ban saka virginity a starina ba, i want and love her, not her virginity, idan kai ma dan budurcin za ka auri salihar taka tun wuri ka sanja mind, Allah na iya jarabtan mutum duk kamewansa sai ya auri mace ba kamammiya ba, idan ka saka virginity a ranka to idan baka samu ba hakan na nufin auren ba lasting zai yi ba, dan haka tun wuri ka gyara niyanka akan maganan aure, ni shiyasa na jima da saka wa rai na, ƴar jagaliya iri na zan aura, ko wacce ma ta fi ni shaƙiyanci, ba zan auri kamila na cuceta ba, nafi son tantiriya-tantiriya haka yanda nake a gantale ita ma ta zama dai gantalalliya-gantalalliya sai mu zauna normal, wasu mata ba sex ke sa su rasa virginity nasu ba, akwai hanyoyi da yawa da suke rasa virginity ɗin su ta shi wanda wasu ba su sani ba ko kuma ba da son ransu ba, wasu situation na rayuwa ko kuma iyayensu basu da hali, musamman masu ɗaukan abu mai nauyi, sannan ga wannan bala’i da ke damun mutane na infection, shi ma idan ya yiwa mace yawa ai ya isa yayi disvirging nata musamman yaran talakawa masu using local toilet, so ka gyara niyanka.”

Abeeb murmushi yayi tare da yin kabbara ya ce, “Allahu Akbar! Sheikh CAS Bunayd bin Mukhtar sule kwalli.”

Bunayd da har yanzu fiska ba’a sake ba ya ce, “Me yasa ka ƙirani dama?”

Abeeb murmushi yayi dan yasan abokin nasa kuma yayi fushi, maste dariyansa yayi ya ce, “auren ne an dawo da shi baya, 3 week’s wai, and next week zan tafi Adamawa za’a tura mu wani local government Michika, kuma ina tunanin za mu iya kai 2 to 3 week’s a can, so za ka yi handling na abubuwan da ya shafi bikin ne, sai ka shigo Kano da wuri.”

CAS Bunayd ya ce, “All the best! Za mu shigo next week da su General duka, dama na faɗa masa zan zauna har bikinka, so idan busy ya bar ni ba mastala komai normal, ango na saliha kamila, Captain Abeed ya kusa dangawa ga Palace, Dragon za’a sha Chaji.”

Dariya Abeed ya fashe da shi bai shirya ba ya ce, “ɗan iskan abokina, Allah nuna mini taka matar, tun a waje zan faɗa mata gaskiya kada mu munafurceta, kai iskancinka har da na sayarwa kuma dai da alama kai jarababbe ne.”

Murmusawa Bunayd yayi ya ce, “Ko banda jaraba ai sadaki ya fi kuɗin da ake bawa ashawo, idan ban da shi ma zan koyo.”

Waya suka yi har suka yi sallama kaman ba komai, dan Bunayd duk fushinsa yana da saurin sauƙa kuma bai da riƙo.

Abubuwan da ya kamata yake yi har dare tayi, nan ma ya shirya driver ya ja sa sai club, Bunayd fiska a haɗe ya shige, duk wata mace da ta tinkaro sa to tana kallon fiskanta take shan jinin jikinta, Bunayd ya iya rawa na fitan hankali, tunda ya hau step na guy’s ɗin, to duk wani mai rawa tsayawa yake kallon na Bunayd, mata sai gani sai hange daga nesa dan fiskan nan a haɗe ba alaman rahama, gaba-ɗaya wajen tafi ya ɗauka, wasu mazan turawan kuwa kishi suke suna haushi a banza, saboda Bunayd bai san suna yi ba ko a kwalansa, sai da ya gama shashewansa sannan ya samu waje ya zauna, abubuwan sha aka kawo masa, duk wine sun fi yawa, taɓe baki yayi saboda shi ko non-alcoholic wine ba ya sha, drivernsa ya turawa text ya ɗauko masa energy drink a mota ya kawo masa, sai da ya kwankwaɗa ya ɗan ƙara cashewa sannan suka koma gida lokacin kusan 12 na dare agogon Spain.

Suna komawa ya wasta ruwa tare da ɗaura alwala, dama Bunayd ibada ba ya wuce sa, mayen ibada ne sosai-sosai, ko me yake lokacin sallah na yi zai yi, kuma nafilfilu ma haka yake yin su kaman wani babban Malami, yanzu ma sai da ya gabatar da nafilfiulunsa har 1 da mintuna na dare, sannan ya bi lafiya haɗaɗɗen gadonsa ya kwanta.

Washe-gari da wuri ya shirya cikin court nasa arsh color, ba ƙaramin kyau kayan ya masa ba, ka ce ma’aikacin banki ne, yana fitowa dirver ya ja su, motoci uku ne, ɗaya na guard’s nasa a gaba sai wanda yake ciki a tsakiya sai kuma wani a baya, a gaban wani kantamemen building mai hawa-hawan gaske suka yi parking, guard’s ne suka buɗe masa ƙofa ya fito yana takunsa na sadaukan maza, wani ɗan ƙaramin brief case ne a hannunsa ya shige ciki, lifter ya hau ya kai sa step da zai je, a wani haɗaɗɗen office ya tsaya aka basa izinin shiga.

Office na wani babban ɗan kasuwan Bature ne, bayan Bunayd ya zauna ya zaro wasu peppers ya miƙawa Baturen, sosai suka tattauna kuma da alama dai kaman contract na wani aiki ne, sai da suka gama ya fice, bayan sun koma gida ya shirya sai airport, daganan sai Nigeria, ko da ya dawo sai da ya huta sannan ya tattara komai da zai buƙata sojojin suka shigo suka ɗauka suka fice.

Yau ma da jerin motoci kaman kullum haka suka fice a gidan da mugun gudu suka yi Victoria Island, suna isa aka buɗe masa ƙofan motan, yana ƙoƙarin fitowa sai ga wani kyakkyawan yaro wanda ba zai wuce 14 year’s ba ya zo yayi hugging nasa, Bunayd na murmushi ya ce, “Nabeel kai ne ka girma haka?”

Nabeel murmushi yayi kawai ya amshi kayakin Bunayd da ke hannun sojojinsa, suna tafiya suna hira, Nabeel ya ce, “Yaya zama Soja is not easy gaskiya, ni kawai ka yiwa General magana nima a barni na tafi ko Spain ɗin ne ko Turkish nima na karanto wani abun.”

Bunayd murmushi yayi dai-dai sun shiga palourn gidan, wani corridor suka bi sai ga su gaban wani parta haɗaɗɗe, shigewa suka yi Nabeel ya dire kayakin a palourn ya ce, “Yaya CAS ɗan gidan General ya dawo, nidai ka taimaka ka masa magana, nasan idan kai ne ka yi magana zai yarda.”

Bunayd ya ce, “tunda ka dawo za mu yi magana letter, yanzu dai bari na huta, sai ka faɗawa su Suhaila su shirya tafiya Kano, kai ma har da kai, General ya ce duka gida za’a je, ina tunanin Suhail ma may be zuwa gobe yana hanya.”

Sanin Bunayd baya son hayaniya idan ya ce zai huta, sai Nabeel ya fice salun alun, dan ba laifi idan Bunayd ya so surutu to ko menene biye musu yake yi, Nabeel na ficewa Bunayd ya rage kayan jikinsa a nan palourn ya kwant dan ya huta, baccin ne bai ɗauke sa da wuri ba, can yayi ɗan guntun staki a fili ya ce, “Kowa yayi sa’an Mom amma ban da mu, na stani zuwa Kano ba dan kowa ba sai dan ke Mom..” haka ya dinga mitan surutu shi kaɗai har bacci yayi gaba da shi, Bunayd fa da alaman birgima ne da shi dan kaman zai faɗo daga kujeran haka yake baccin.

*****

Banafsha da Maminta suna zaune a palournsu suna hira, sai Banafsha ta dubi Mami ta ce, “Mamina tunda ba ki saya mini waya ba ki saya mini system to.”

Murmushi Mami tayi ta shafa kai na ta ce, “shalelen Mami kada ki damu ko, Allah ya kawo kuɗi Mami za ta saya miki abinda ya fi system ma balle ƙaramin alhaƙi waya, duk abinda nake yi dan ke nake yi, neman kuɗi da komai faɗi tashi duk saboda gudalliyan Maminta nake yi, Faɗima ƴar albarka.”

Tura baki nayi jin wai Mamina dan ni take komai, yanzu ba abun na ce idan saboda ni take wannan rayuwa mara fa’idan to ta bari na yafe ba, amma nasan sai ma Mami ta dakani duk da banda lafiya, jan bakina nayi tare da yin shiru, can na miƙe na ce, “Mami bari na sauya pad.”

“To ammatan Maminta a fito lafiya”, Mamina ta faɗa tana murmushi, ni kuma na shige ɗakina cikin jin kunya.

Banafsha na shiga ɗaki bai jima ba sai ga sallaman Abbaa, Mami da fara’a ta amsa tare da masa iso, wucewa ɗaki tayi ta sako mayafi sannan ta dawo suka gaisa cikin mutunta juna, Abbaa ya tambayi jikin Banafsha, Mami tana murmushi ta ce, “Da sauƙi sosai ma, yanzu ta tashi ta shiga ɗaki.”

Abbaa yana murmushi ya ce, “To Masha Allah! haka ake so.”

Palourn sai ya ɗau shiru na mintuna daga Abbaa har Mami ba mai magana,can Mami sai ta miƙe tare da cewa, “Bari na ƙira maka Faɗiman tunda ta shiga ɗaki ta zauna shiru.”

Abbaa na maza yayi ya daure saboda Mami sosai ta masa kwarjini, cikin jarumta ta ce, “A’a ƙyaleta ta huta, daman dai wajanki na zo.”

Mami murmushi tayi tare da komawa ta zauna, bata kawo komai a ranta ba ta ce, “Allah ya sa dai ba laifi na yi ba.”

Abbaa murmushi yayi ya ce, “ai kuwa laifi kika yi, irin gungumemen laifin nan, dan ko a kotu ya wuce civil case sai dai a ƙira sa da criminal case.”

Mami ɗan waro ido tayi ta ce, “ahh! Ba sai an kai ga kotu ba ma, haƙuri zan bada, yanzu dai a faɗa mini laifin nawa na ji sai na bada haƙuri yanda ya kamata” ta faɗa tana murmushi.

Abbaa gyara zama yayi tare da gyaran murya ya ce, “Ai haƙuri ba zai goge wannan laifin ba, saboda criminal issue ne, sata kika mini irin babban satan nan da idan aka riga aka maka shi sai abinda Allah yayi kawai.”

Mami da bata harbo jirgin abinda Abbaa ke nufi ba, da mamaki ta ce, “haƙuri kuwa ya zama dole na bada, Allah baka haƙuri Abbaansu, me na sace haka nayi gaggawan dawo da shi?”

Abbaa murmusawa yayi ya ce, “ai sacewan shi ne dai-dai Mamin yara, idan an sace ba’a dawo da shi sai dai a riƙe da kyau, Mamin yara maganan gaskiya da gaske nake kuma da gaske nazo sannan a shirye, a taimaka wa bawan Allah a kula mini da zuciyata da aka sace, tun ranan farko da na fara ganinki naji kin kwanta mini a rai kin mini, kin tafi da imanina, na daure na kusan shekaru goma sha, amma yanzu abin ya fi ƙarfi na a taimaka mini a tausaya mini, da gaske kuma na zo idan kin amince ko juma’an nan ban ƙi a kawo mini ke gidana ba, kuma kada ki yi tunanin alaƙanki da Ummul-khultum, domin ban zo ba sai da duk suka amince suka kuma yarda, dan Allah ki taimaki marayan Allah mai mata biyu, na jima ina dakon soyayyanki Hajiya Ramla.”

Mami tunda Abbaa ya fara magana ta ɗauke wuta na ƴan mintuna, zamowa tayi kaman photo kawai tana kallonsa ta rasa ma me za ta ce ko me za ta yi, mamaki kawai ya tafi da ita a zaune, kallonsa take kuma ba ta ko kiftawa, har ya gama magana bata iya mosta laɓɓanta ba balle ta ce wani abu, dan bata san ma me za ta ce ba.

Abbaa murmushi ya sakarwa Mami ganin ta kafesa da kallo, a hankali ya ce, “Hajiya Ramla ke na ke saurare.”

Mami wani irin dogon ajiyan zuciya ta sauƙe, sai sannan ta kawar da idonta a kan Abbaa, wani irin murmushi ta saki tare da buɗe baki ta ce…

<< Yar Karuwa 10Yar Karuwa 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×