Mami ta ce, “Alhaji abinda kunnuwana ke jiye mini kana faɗa haka ne ko kuwa mafarki nake?”
Abbaa yana murmushin ya samu karɓuwa ya ce, “ba mafarki kike ba Mamin yara haka abin yake, nine dai na ce a taimaka mini a tausaya mini kar na mutu da soyayyanki, kuma ko nan da sati kika buƙaci ayi biki to a shirye nake.”
Mami murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo tayi sannan ta ce, “ka yi haƙuri Alhaji ba wai na ƙi ka bane, a’a aure ne kawai ba ya gabana har yanzu, wanda nayi a baya ya isheni.”
Abbaa cikin damuwa yake kallon Mami ya ce, “Me yasa Hajiya Ramla? Ki faɗa mini gaskiya idan nine ban miki ba ko kina tunanin wani abu ne akan mata na.”
Girgiza kai Mami tayi tana mai iya ƙoƙarinta wajan ganin wannan magana bai sa ta yiwa Abbaa rashin mutunci ba ta ce, “Ko ɗaya Alhaji, nice kawai ba aure a gabana.”
Abbaa ya ce, “Duk ɗan sunna ai ba ya ƙin aure Mamin yara, nasan dole dai kina da wani dalilin naki, Allah huci zuciyanki amma dai ina sonki, kuma zan baki lokaci dan jiran amsar da za ki bani, yanzu ban ɗauki wannan a matsayin amsa ba, daganan har wata guda na baki duk ki yi shawara ki yi tunani, duk abinda kika yanke ki sanar da ni, musamman in maganan bikin ne to sati guda kawai za’a yi Insha Allah sai ki fara shiri tun kamun ki gama tunanin” Abbaa ya faɗa yana sakar wa Mami murmushi ƙayatacce.
Gululun baƙin ciki ne ya tokare Mami, amma da yake bata son dogon magana sai bata ce wa Abbaa komai ba, har ya gama iya surutunsa ya fice, sai sannan ta ja wani dogon tsaki a fili ta ce, “Matarka bata ƙyaleni ba kuma ba ta ƙyale yarinyata ba a haka zan aure ka? Ai ko auren zan yi ina da wanda nake ƙauna, shi ma ban amince masa ba balle kai, saboda ba auren bane a gabana yanzu, kuma iya shekarun da ka ɗauka kana dakon soyayyata haka Alhaji Mukhtar ya ɗauka ko na ce fiye da haka, dan tun Banafsha bata yi wayo ba ga shi har ta zama budurwa, wa ma ya san ko kai naka na yaudara ne kawai, ni yanzu ba aure ne a gabana ba, aurar da Faɗimatu na shi ne a gabana, Allah kuma ya bata miji nagari…” Haka Mami ta dinga mita da surutu ita kaɗai kaman wacce ke yi da mutum a gefenta, ko kuma wacce aka kunnata, hhh ko da yake Abbaa ne ya kunnata tunda ya taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi.
Banafsha da ta shiga ɗaki sanya pad, tun shigowan Abbaa ta ji, da har tana niyan fitowa amma tun daga kalman Abbaa na Mami ta masa laifi har ya ce criminal case ne, sata ta masa tuni Banafsha ta fahimci me Abbaa ke nufi, mamaki ne da kuma farinciki suka kuma kama Banafsha san da Abbaa ya furta abinda ke zuciyansa, duk da a wani gefe tana tuna Umma da Ya Danish, amma abin ba ƙaramin daɗi ya mata ba, kuma ya ƙara wa Abbaa kima a idonta, Abbaa shekara da shekaru yake maƙwabtaka da Maminta, yasan abinda take aikatawa amma duk da haka yana sonta, kuma bai yi ƙasa a guiwa ba yau ya sanar mata sannan a shirye yake da ya aure Mami akan lokaci, su Abbaa na hiransu amma Banafsha ke musu murmushi ita ɗaya kaman ta buga tsalle, saboda haka kawai ita ta ji Abbaa ya fi kwanta mata akan Alhaji, musamman da za su zama so close again da Umaimatynta, kuma tunda su Ummu sun amince su shikkenan ba komai Allah ya sa Mami ma ta amince…
Tunanin Banafsha na Allah sa Maminta ta amince ne ya staya, sakamakon jin amsan da Mami ke bawa Abbaa, saurin runste ido Banafsha tayi tana jin kaman ita ake sokawa wani abu mara daɗi a kirjinta, gaskiyan Abbaa ne da ya ce duk ɗan Sunna ba ya ƙin aure, kuma a ganin Banafsha ko yana da dalili duk da haka ƙin aure bai kamace sa ba, saboda yanda aka same shi ta Sunna, to bai kamata a ce shi ma bai da wannan burin na samar da wasu ta Sunna ba, menene mastalan Mami kam? Allah ya hore mata baiwan kyawun jiki, fiska, hali da na zuciya, sannan uwa uba abinda wasu sai sun haɗa da boka da malam suke samu, to ita Allah ya hore mata a sauƙi wato farinjini, Mami na da jama’a sosai-sosai, amma Banafsha har yau ta rasa ne ya sa mahaifiyarta ta zaɓi wannan rayuwan, dole tana buƙatan amsa, dole tana buƙatan jin labarin wacece Maminta, asalinta, ƴan uwanta, mijin da take ikirarin ta yi auren farko ta gama, da duk komai ma dangance da tarihin rayuwan baya na Mami, a hankali Banafsha ta lumshe ido ta ce, “Duk a ina zan samo waɗannan amsoshin ya Rabbi, ka iya mini da kanka ya Hayyu ya Ƙayyum” ta faɗa kaman za ta fashe da kuka(ni uwar batoorl na ce ni ke da amsoshin Banafshaty, ki biya kiji komai a_z).
Banafsha dai-daita nistuwanta tayi yanda Mami ba za ta gane ta ji abinda suka tattauna da Abbaa ba, ta shiga palourn da sallama, jikin Mami ta koma ta kwanta tana cewa, “Mamina kaman muryan mutun na ji, amma kamun na fito ban ga kowa ba ke ɗaya.”
Mami taɓe baki tayi ta ce, “Eh! Abbanku ne ya zo tambayan ya jikinki, na faɗa masa da sauƙi, zan ƙira ki kuma ya ce sauri yake, idan kin ji sauƙi sai ki shiga gidan ki gaishe sa ko.”
Jinjina kai na yi a zahiri, a zuciyata kuwa mamakin Mamina nake, mamakin gaske ma kuwa, wato Mami ba za ta ma faɗa mini ba, ana cewa yaran fari abokanan shawara ne kuma ƙawaye amma banda Mamina, musamman a irin wannan magana, uhmn to Alhamdulillahi!, Duk da nasan maganan da ta yi ɗazu da ɗan gaskiyanta na Umma bata ƙyaleta ba kuma ba ta ƙyale ni ba, amma wannan ba hujja ba ne, ko ni da ya Danish yayi ƙoƙarin ƙeta mini mutunci na so mata auren Abbaa balle ita da bata san da wannan ba ma, kuma Mami in za ta duba da kyau ni a ganina auren Abbaa ya fi mata auran Alhaji, tana son Alhaji kam amma wani lokacin abinda muke so ba shi ne alkairi a gare mu ba, sannan tana maganan aurar da ni, a muna zaune haka ba namiji shi ne take tunanin wasu za su zo neman aurena wajanta tana mace? Ai babu mai aurar mara uba, ana dai auran wacce/wanda ba su da uwa amma banda marassa uba, saboda da uba ake ado ba rigar aro ba, ni sai yanzu ma Malam Abbo ya faɗo mini a rai, Mamina bata nadama a irin wannan rayuwan ina na isa na yi maganan aure, shiyasa ma ni ban saka wa rai na zan yi aure ba, tunda haka Mamina ta zaɓa sai mu zauna duka haka, niyan nayi shiru nayi mu je a haka a bansan abinda ke tafiya ba, amma zuciyata ta ƙi ƙyaleni nayi shiru, numfasa nayi a hankali kaman munafuka na ce, “Mamina me yasa kike yi yin haka?” Na faɗa kaman zan yi kuka.
Mami kallona tayi ta ce, “Me nayi Banafshan Mami?”
Gyara kwanciya nayi a cinyan Mamina na ce, “Dan Allah ki yi haƙuri Mami idan abinda zan faɗa zai ɓata miki rai, gaskiya ce komin ɗacinta faɗansa yana da kyau, Mami me ya sa za ki ce ba aure a gabanki? Mami me yasa kike nunawa mahaliccinki ba za ki cika sunnan ma’aikinsa Annabi SAW ba, Mami duk mace ko namiji da suka kai aure suka mutu ba aure fa Allah ma tausayinsu yake, Mamina nasan kin sani aure ni’ima ne kuma rahama ne, Mami Allah ya azurtaki da farinjini wanda wasu ma sai sun nema da kuɗi sun saɓa ma Allah sannan suke samu, Mami har yanzu taurarinki suna haskawa ba su disashe ba, me yasa ba za ki yi aure ba tun yana binki, kamun ya zo yana guje miki kina bin sa, Mami a haka akwai mai aure na ban da uba ina ƴar mace? Mami….” Maganan baki nane ya maƙale sakamakon wani irin stawan da Mamina ta daka mini, wanda ya sa na miƙe zaune babu shiri a rikice.
“Banafshaaaa!!!!” Haka Mamina ta ƙira sunana a stawa ce.
Tura baki nayi tare da runste ido na inma duka na Mami za tayi sai dai ta kashe ni, amma sai na faɗa mata gaskiya, ci-gaba nayi da magana ba ruwana da hucin da Mamina take yi, cewa nayi, “Mami ranan Alhaji ya ce miki Amaryansa kika ɓata rai, ya ce za ki haifa mini ƙanne kika yi fushi, Mami yau ina ji Abbaanmu ya ce zai aure ki nan ma kika ce ke ba aure bane a gabanki, Mami menene damuwanki dan Allah? Mami ya kike so a miki, duk da Alhaji mutum ne da yake rayuwan da bai dace da ke ba amma ya nuna yana ƙaunanki a haka, kuma zai aure ki, akwai soyayyan da ta fi wannan? Abbaa ya san ki shekara da shekaru, ya san duk abinda kike da wanda kike aikatawa na ba dai-dai ba amma hakan bai dame sa ba, bai hana sa ƙaunanki ba, yana sonki ya danne zuciyarsa, yanzu ya kasa haƙuri kuma ya furta miki kin ce ba haka ba ya kike so Mami? Wani irin masoyi kike son samu sai ki kawo maganan aure a starinki? Mami kina tuna mutuwa kuwa? Kina tuna za mu mutu ba tare da mun san yanzu ne ko anjuma ko kuma yaushe ba? Mami ita fa mutuwa ba ta alert a ko wane yanayi za ta ɗauke ka idan lokacinka yayi, Mamina kowa burinsa da fatansa ƙarshensa ya fi farkonsa kyau ya kuma gama da duniya lafiya yana mai imani mumini amintacce, Mami ke me yasa bakya fatan hakan? Mami dan Allah ki yi aure, wallahi idan ba za ki yi aure ba to kibar cewa aurar da ni ne damuwanki kuma burinki, sabida babu mai aure na a wajan mace, kuma ko akwai ma to ba auran zan yi ba, ba zan jure a goranta mini ina gidan mahaifiyata a ƙira ni da ƴar karuwa, sannan a ce nayi aure a goranta mini a ƙira ni da ƴar mace ba, Mami kina da dangi, kuma nasan ina da uba tunda mutum ba ya haifan yaro shi ɗaya, amma duk kin rabamu da su kin guje su kin wastar da su saboda me Mami? Ni Ko da mahaifina na raye ko ba ya raye ai ya kamata ki haɗa ni da danginsa saboda su ne gata na, kuma su za su shiga tsakanina da masu yi mini gori, Mami wallahi ko shegiya kika haife ni to haɗa ni da mahaifina ya fi wannan hukuncin naki kamata, kuma ni na yafe muku ina ƙaunarki a haka ke da mahaifi na, in ma ba ta hanyan da ya dace kuka same ni ba, na ɗauki ƙaddarata ta zamowa ƴar shege…”
Tasss! Tasss!! Tasss!!!, Shi kawai kake ji Mami ta kwashe Banafsha da wasu mahaukatan maruka, idanuwan Mami jajazir kaman garwashin wuta ta ce, “Banafsha ni kike wastawa wannan kalaman? Banafsha har ni za ki saka a gaba kina mini magana kaman ƴar cikinki? To wallahi kin ji na rantse ranki zai yi mugun ɓacuwa akan rashin kunyan da kike mini, har kina ƙiran kanki shegiya kina faɗa mini kenan me nayi na haifeki? Banafsha….” Maganan bakin Mami ne ya sarƙe sai ga hawaye a idanuwanta, saurin juyawa tayi dan kar Banafsha ta gani, abinda bata sani ba kuwa duk da yanayin da nake ciki naga zubowan hawayenta.
Mami juyawa tayi tana ƙoƙarin danne hawayenta amma ina sun ƙi stayawa, ɗakinta ta shige kawai ta kulle, kan gado Mami ta faɗa tare da sakin sabon kuka tana jin duk abinda ya faru shekaru ishirin baya yana dawo mata sabo dall kaman yau abin ya faru, cikin kuka ta ce, “Duk wanda ya aikata wannan mummunan tabo gareni in har da son ransa ban yafe masa ba duniya da lahira, in kuma shi ma bai yi da niya ba na yafe masa, amma duk mai hannu a faruwan wannan mummunan ƙaddara gare ni Allah zai saka mini, ban yafe ba, ban yafe ba, ban yafe ma ko waye ne ba, astagfirullah Ya Rabbi!…” Haka Mami ta dinga sumbatu tana kuka, saboda duk maganan da Banafsha take faɗa mata baya damunta sosai, amma maganganun yau ya soketa sosai, ya tuna mata da abinda bata son tunawa a rayuwanta, ya tuna mata da lissafin da ta jima da cire shi a rayuwanta, ta stani baya bata son tuna baya domin bata ji daɗin baya ba, haka Mami ta dinga kuka har sai da kanta ya fara mata mugun ciwo.
Banafsha kuwa Mami na barin wajan ita ma ta ɓarke da nata kukan mai cin rai, ga ciwo a zuciyanta ga ciwon mara, ita ji take ma ta Mami ta bugeta har ta kasheta da ya fi mata daɗi, ko kaɗan bata ji zafi ko raɗaɗin marukan da Mami ta mata ba, kuka take kaman ranta zai fita, gaskiya ce ta faɗa wa mahaifiyarta, amma kuma ba wai dan ta sanya ta a damuwa ta saka ta zubar da hawayenta ba, lallaɓawa Banafsha tayi a dudduƙe ta ja jikinta ta ƙarisa ƙofan ɗakin Mami, tana turawa ta ji a kulle, a hankali da muryan kuka ta ce, “ki yi haƙuri Mamina, Allah ya huci zuciyanki, ba niya na saka ki a damuwa ba, niyana tunatar da ke da kuma baki shawara a mastayina na ƴar ki, Mami auren Abbaa Insha Allah alkairi ne gare ki Mamina, ki yi haƙuri ki auri Abbaa, shi cikakken me ƙaunaki ne Mami, wallahi ni nasan Abbaa zai fi Alhaji riƙe ki da amana, ki yi haƙuri Mami.”
Mami bata yi niyan yin magana ba, amma jin abinda Banafsha ke faɗa sai wani abun ya ƙara tokareta, stawa ta daka mata ta ce, “Banafshaaa! Ki ɓace mini a ƙofa kamun na fito na saɓa miki, shashashan yarinya wacce bata gudun ɓacin ran mahaifiyarta, duk haƙurin da nake akan rashin kunyan da kike mini, ke burinki kawai ki sa na miki baki ko? To ki cigaba kada ki dena zan miki bakin da kike so na miki, ɓace ki bani waje.”
Na buɗe baki zan bai wa Mami haƙuri, ta kuma sake mini wani gigitaccen stawan da ya saka ni barin ƙofan ɗakinta ban shirya ba, marana mugun murɗa mini yake ga kukan da nayi, tuni zazzaɓi yake son mini mugun kamu.
Umaima bayan ta je tahfiz an tashi, Malam Abbo ya ƙara ba da saƙon gaisuwa zuwa ga masoyiyarsa Banafsha, Umaima ko da ta dawo bata shiga gidansu ba sai ta yi hanyan gidan su Banafsha, kuma dai-dai lokacin Umma ta fito a gida kenan, wani irin mugun kallo Umma ta bi Umaima da shi, tuni Umaima ta sha jinin jikinta tare da fara yarfe hannu dan tasan yau sai dai ɗan buzunta, Umma fasa fita tayi ta juya cikin gida, Umaima haka ta bi bayan Umma tana faɗin, “Ƙulya ƙulle bakin Ummana”.
Ummu tana zaune a palour, tunda ta ga yanda Umma ta shigo sai ta girgiza kai kawai dan bata san me kuma ya faru ba, Umma dakinta ta shige tana ƙwafa dan yau ba mai hanata daka Umaima sai ikon Allah.
Umaima haka ta shigo tana raɓe-raɓe kaman wacce ta yiwa sarki sata, Ummu tana ganin Umaima tasan to da wani abun, kamun Ummu ta buɗe baki Umaima ta ce, “Ummu ki bawa Umma haƙuri kada ta dake ni, wallahi saƙo na je kai mata malaminmu ne ya aike ni wajanta.”
Ummu da ba ta gane ba ta ce, “Wajan waye kuma aka aike ki, kin dawo makaranta ba za ki taho gida ba, ina kika bi har Ummanki ta haɗu da ke a can.”
Umaima kaman za ta yi kuka ta ce, “Ummu wallahi ba inda na je, gidan su Banafsha ne kawai, kuma ban shiga ba da naga Umma.”
Ummu shiru tayi kawai ta rasa me za ta ce, dan tasan muddim Umma za ta daki yaranta, to bata isa ta ce ƙala ba, in ma ta saka baki to yanzu kuma faɗan zai dawo kanta.
Umaima ta yi rau-rau da ido ta ce, “Dan Allah ki bata haƙuri Ummu.”
Ummu ta buɗe baki za ta yi magana sai suka jiyo muryan Umma tana faɗin, “Dan ubanki, kin staya a wajan uwarki ta biyu ko ba za ki zo ba ina jiranki.”
Umaima baya-baya ta fara za ta juya, sai Ummu ta girgiza mata kai ta ce, “a’a kar ki gudu Umaima, kije ki bata haƙuri, babban budurwa da ke Ummanki ba za ta dake ki ba, faɗa za ta miki kuma ko me ta ce ki bata haƙuri, ki ce kin ji kin daina.”
Umaima ɗaga kai tayi tana tafiya a hankali kaman wanda ƙwai ya fashewa a jiki, har ta shiga ɗakin Umma da sallamanta, Umma kuwa ko amsawa bata yi ba ta miƙe ta saka wa ƙofanta sakata, mugun kallo ta jefawa Umaima ta ce, “Me na ce miki ranan? Wato sai dai na stine miki ki lalace nine da asara ba uwar kowa ba ko? To kuwa ko ban stine miki ba zan daka ki sai na sauya miki kamanni, idan tare aka haifo ku da ita za ki faɗa mini yau.”
Umaima ta buɗe baki za ta bawa Umma haƙuri, amma ina sai sauƙan bulala ta ji a jikinta ko ta ina, Umaima na ihu, Umma na dukanta kaman an aiko ta bata fasa ba.
Ummu na zaune a palour, tana jin ihun Umaima ta taho da sauri duk da bata shiga ɗakin Umma, amma ta tura ƙofan da niyan shiga, sai ta ji da gam a garƙame da sakata, magana take tana faɗin, “Dan Allah dan Annabi SAW ki ƙyaleta ki yi haƙuri Maman Kabeer, ki bar dukanta haka nan….” Magiya Ummu ta dinga yi amma Umma ko jin ta bata yi ba, balle ma ta saurareta kawai jibgan Umaima take yi.
Umaima tun tana kuka da ƙarfi har ta zube a waje guda muryanta ya dishe, ba abinda take faɗi sai, “ki yafe ni Umma, ki yi haƙuri ba zan ƙara ba, wallahi Abbaa ne ya ce muje, ki yi haƙuri Umma ki mini rai, zan mutu, wayyoooo! Ummuna!!!” Umaima na faɗan haka ta sume.
Umma duk da Umaima ta sume amma dukanta take zuciyanta kaman zai faso ƙirjinta ya fito, magana take kaman zararriya, “Ni za ki mayar ƴar iska bansan me nake yi ba, wato kin faɗawa ubanki sai ya saka ki gaba kuka je, ban isa da ke ba, to gwanda ma na kashe ki na huta da ki kasheni da naki takaicin, har da ke ubanki zai je zance, duk munafurcinku ne ya ja in ba haka ba, me za’a yi da karuwa a kishiya, ai sai ta addabi kowa ta ishi kowa ta nemi ɗaga mutum akan yaransa…” Umma tana magana tana dukan Umaima tana haƙi, har sai da ta ji kaman za ta sume ita ɗin ma, sannan ta jefar da bulalan ta jawo ruwa ta kwankwaɗa ta wastawa Umaima, wani wawan ajiyan zuciya Umaima ta sauƙe tare da sakin marayan kuka tana numfashi a hankali-hankali.
Ummu kuwa da ta gaji da magiyan, ficewa tayi ko ta duba samarin gidan amma ba kowa, Abbaa ma bai dawo ba, haka ta dawo cikin gidan lokacin Umma ta gama jibgan Umaima, Ummu kaman za ta yi kuka haka ta koma ƙofan ɗakin Umma, amma har lokacin bata buɗe ƙofan ba, ƙarshe Ummu ɗakinta ta koma.
Umaima na zube a wajan, Umma ko ta kanta bata bi ba, ta shige bayi ta wasta ruwa, ƙwafa tayi tare da kallon Umaima ta ce, “tashi ki fice mini a ɗaki, idan kin so gobe na hanaki yin abu ki yi, idan yayanki ya dawo kuma na faɗa masa ya ƙara miki, kinsan dukansa kuma sarai.”
Umaima ko yastanta ta mosta raɗaɗi take ji, dan ta daku sosai ba ƙarya, Umma tsawa ta mata, dan dole Umaima ta ja jikinta tana kuka ta shige ɗakinsu, ga shi Ummu bata san ta fito a ɗakin Umma ba, haka ta zube a stakar ɗakinsu tana kuka har baccin wahala yayi gaba da ita.
Ummu kuwa tana ɗakinta, bata san Umaima ta fito ba, har Abbaa ya dawo a palourn sa na cikin gida ya gama komai ya tafi wajan Mami, har ya dawo duk bai san wainar da ake toyawa ba a cikin gidan, sai da ya shigo ciki ya ji gidan shiru kaman ba kowa, ɗakin Umma ya fara shiga sai ya sameta tana sallah, juyawa yayi ɗakin Ummu, samunta yayi ta haɗa hannayenta ta tallafe kuncinta, Abba ƙarisawa yayi wajanta ya zauna tare da cire mata tagumin da ta yi, Ummu ɗagowa tayi ta kalli Abba sai kawai ta faɗa jikinsa tana faɗin, “Dan Allah kabar maganan auren Mamin Banafsha, ka yi haƙuri, kuma ka ce Umaima ta bar shiga gidan, komai ya wuce, zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki.”
Abbaa kallonta yayi ya ce, “Me ya faru? Me yasa kika ce haka? Bayan ke kika kawo shawaran kuma na amsa, meyasa?”
Ummu kaman za ta yi kuka ta ce, “nidai dan Allah ka bari, nasan ni na bada shawara amma kuskure nayi, dan Allah ka mance da batun ka ji Alhaji.”
Abbaa miƙewa yayi ya ce, “Ba zan zamo mutumin banza ko kuwa mijin da ake juyasa ba, ke kika yi magana ba ni na ce ba, dan haka bakin alƙalami ya riga da ya bushe, na samu Ramla na faɗa mata abinda ake ciki, yanzu haka amsanta nake jira, kuma ina da tabbacin amsan nata eh ne” yana gama faɗa ya nufi hanyan waje fiska ba sassauci, ta ya za ta ce abu kuma yanzu ta ce a’a idan ba ta renasa ba, to shi ya riga da ya sakawa zuciyansa son Mamin Faɗima, kuma idan har bai aureta ba Allah ne kawai bai nufa ba.
Ummu jiki a sanyaye ta ce, “ka yi haƙuri Abbaansu ba nufi na kishi nake yi ba, duk da nasan kishi dole na yi sa tunda ina ƙaunanka, amma ba hakan bane dalilin maganana, ka je ɗakin Maman Kabeer ka duba halin da Umaima ke ciki, na tabbata kai ma za ka fahimci janye maganan nan shi ne alkairi da zaman lafiya.”
Abbaa bai kuma cewa da Ummu komai ba ya fice a ɗakin, ɗakin Umma ya koma lokacin ta idar da sallah, ba murmushi ba komai kaman an mata dole ta ce, “Sannu da dawowa.”
Abbaa ko ta sannunta baya yi ya ce, “Ina Umaima?”
Umma taɓe baki tayi ta ce, “tana ɗakin su.”
Abbaa bai ce komai ba ya juya, da sallama ya shiga ɗakin su Umaima, bai ma kula da ita a stakar ɗakin ba, sai da ya ga bata kan gadonsu sannan idanuwansa ya sauƙa a stakar ɗakin, da mugun sauri Abbaa ya nufe ta a rikice yana faɗin, “Ummu-khultum lafiya?”
Umaima ta jima da tashuwa daga baccin wahala, amma zuwa lokacin jikinta yayi stananin stami, ba abinda take sai aikin nishi, ko da taji Abbaa na ƙiran sunanta ba daman amsawa, sai kuka ta sanya wanda idan ba kana kallonta ba, ba za ka ji sautin kukan ba saboda yanda muryanta ya dishe.
Abba yana taɓa jikinta yaji yayi zafi sosai, ya juyo da ita kuwa ya ga fiskan a kumbure alaman ta sha kuka, kallonta yayi cikin damuwa ya ce, “Me ke damunki Umaiman Abbaa?”
A hankali take mosta laɓɓanta tana jan zuciya ta ce, “Umma ceeeee” ta ƙarishe maganan kaman za ta sume.
Abbaa ficewa yayi ya nufi ɗakin Umma, amma ya samu ta kulle ƙofa, bugawa yayi taƙi buɗewa, ɗakin Ummu ya koma ya ƙirata, tana shigowa ta kalli Umaima sai ta fara hawaye tana mata sannu, Umaima lumshe ido tayi cikin azaban da jikinta ke mata, Abbaa ya ce, “Khultum shiryata mu tafi asibiti” yana faɗa ya fice.
Ummu haka ta ƙoƙarta ta ɗaga Umaima ta ja ta banɗakinsu da ke cikin ɗaki, ruwan zafi ta koma ta ɗauko a ɗakinta ta zo ta haɗa ruwa, kamawa Umaima jikinta tayi, ta mata wanka ta shiryata sannan ta yiwa Abbaa magana akan ta gama.
Abbaa da kansa ya ɗauki Umaima suka fice a gidan, asibiti ya kai ta a cikin gari, sai dai an kama su a gado, dole Ummu ta kwana a asibiti, shi kuma Abbaa ya koma gida, bai bi ta kan Umma ba dan tabbas zai yi abinda ba dai-dai ba, mataki ne kuma ya ɗauka, in Allah ya yarda zai auri Mamin Faɗima ya ga ta ƙarshen rashin mutuncin ta.
Ɓangaren Mami da Banafsha haka suka kwana, ba wanda ya fito balle ya sa wani abu a cikinsa, Mami sai da dare tayi sosai sannan ta fito ta zo ɗakin Banafsha, samu tayi tana bacci jikinta da zafi, kayan jikinta ta rage mata ta share mata jiki da towel mai sanyi, sannan ta tofa mata addu’a ta ja mata ƙofa ta koma nata ɗakin, alwala Mami ta ɗaura ta dinga sallah, har sai da ta ji ƙiran assalatu, bayan tayi sallahn asuba tayi ayyukanta ta gyara gidan staff, ɗakin Banafsha ta shiga ta sameta ta fito wanka kenan, Mami murmushi ta sakar wa Banafsha ta ce, “shalelen Mami har an tashi, fatan jikin da sauƙi?”
Banafsha wani abu ne ya soki zuciyanta, sai take jin sam-sam bata kyauta ba duk da gaskiya ce, amma Mami bata chanchanci haka daga gare ta ba, hugging na Mami ta yi ta amsa da sauƙi, ta gaisheta ta amsa, Banafsha ta ce, “ki yi haƙuri Mamina.”
Murmushi Mami tayi ta ce, “ya wuce Allah miki albarka, Allah shirya mini ke.”
“Ameen Mamina” na amsa ina murmushi, haka na gama shiri muka fice da Mami muka karya, yau ma ba iya zuwa makaranta zan yi ba Mami ta ce na bari sai wani Monday kawai, muka zauna muna hira Mami na ƙara mini faɗa.
Haka rayuwa ta dinga tafiya har aka cinye wannan sati Banafsha bata je makaranta ba, kuma sai da ta cika kwana bakwai ciff sannan ta samu sauƙi ranan Lahadi, Umaima ma duk sauran kwanakin bata je makaranta ba, kwanan su kusan huɗu a asibiti sannan aka sallamesu, har Ya Mus’ab ya zo shi ma daga Camaroon duba jikin Umaima, Ya Kabeer su ya Sadeeq su ya Farooq duka, kowa duk ya ji abinda Umma ta yi amma ba daman magana sai ido, Abbaa ma idon ya zuba dan shi ya gama ɗaukan nasa matakin, Ummu kuwa bata da bakin magana tunda gori Umma ke mata ko ta yi magana ta ce ai ba ƴar ta ba ce, haka ta dinga jinyan Umaima har ta warke, ya Danish ne kawai bai zo ba kwata-kwata ga shi har weekend ya ƙare yau Lahadi.
Ɓangaren Malam Abbo kuwa ganin Umaima ma ta daina zuwa makaranta kwana biyu ba ya jin halin da masoyiyarsa ke ciki, tuni hankalinsa ya tashi, haka a daddafe ya daure har sati ya cika, ranan Lahadi da yamma ya sha wankansa ya chakare ya shirya rass ya nufi gidan su Banafsha, farinciki kawai yake ciki da ɗauki gani yake ba ya isa da wuri saboda yanda yake ɗaukin son ganin abar ƙaunarsa, Sayyadarsa, Malama Faɗima.
*****
Bunayd hutawa yayi sosai ba wanda ya san yana sashinsa a gidan, sai da General ya ƙirasa a waya sannan ya faɗa masa ai yana cikin gida ma tun da ya dawo ya taho gidan, General mayar da wuƙan yayi ya kashe wayan yana sakawa Man nasa albarka.
General layin Suhail ya kuma ƙira yana ɗauka ya rufe shi da faɗa ya ce, “Suhail ina ce dai ba gidan ubanka ba ne a Turkish ɗin nan ko? To idan ka kuskura gobe ba ka dawo ba sai na ƙwace har jarin da yayan naka ya baka, sai naga ta inda za ka zauna a ƙasar mutane babu kuɗi.”
Suhail murmushi yayi da haɗaɗfiyar muryansa ya ce, “sorry General! Na gama shirin komai jirginmu da asuba zai tashi.”
Ƙwafa General yayi ya ce, “Idan ma baka dawo ba kasan abinda zan iya yi, dama har yanzu ban huce da ƙin aikin soja da ka yi ba, kuma ka zo kana zuga mini yarona Nabeel.”
Suhail dariya yayi ya ce, “Ni kuma ka yafe ni ne General? Ko da yake ni da nake da yaya CAS Bunayd ko General ya yafeni normal ne, daman ni yaya ne babana.”
General murmushi yayi ya ce, “Za ka dawo ka same ni, daman shi yake ɗaure muku wajan zama.”
General haka yake da yaransa maza kaman abokanayensa, musamman CAS Bunayd, kwata-kwata General ba shi da zafi, kuma haka matar sa Hajiya Huraira.
Momsee da ke zaune a gefe dariya tayi ta ce, “Dear gaskiya yarannan su maida ka kaka.”
General kansa ya shafa ya ce, “Alhamdulillahi kawai za mu ce, yara arziƙi ne tunda Allah ya bamu, dole mu jawo su jiki dan mu ji daɗin nuna musu dai-dai da ba dai-dai ba, yiwa yara zafi bai da wani fa’ida, illa ya saka yaro ba zai sake da kai ba balle kasan damuwansa, ko yayi shawara da kai, Allah dai ya musu albarka ya kare su a duk inda suke.”
Da, “Ameen” Momsee ta amsa, suka cigaba da hiransu.
Bunayd yau daurewa yayi bai je ko ina ba, ba dan yaso ba sai dan General bai cika son yawan fitansa da dare sosai ba, idan ba kamawa tayi ba, amma idan ba saboda General ba sam-sam Bunayd baya son zama, shi zuwa wajan chasu a jininsa yake, ko da ba zai yi komai ba sai dai ya bawa idonsa abinci yayi catching fun’s, sai da ya gama hutawansa sannan ya shigo palourn nasu na ƙasa, su Suhaila suna ganinsa suka fara washe baki, shi kuma haɗe fiska yayi dan ya san ba zai wuce su ce yawo da daren nan ba, fiska ba Rahama ya ce, “Ku kawo ƙur’anan ku.”
Stuttt! Duk suka miƙe suka je suka ɗauko, General da isowansa palourn kenan murmushi yayi ya ce, “Kaman haɗa fiskan da gaske ne, ai ina ga yaran nan sun gama lashe maka zuciya, musamman Suhaila da Nabeela.”
Bunayd shafa kiston kansa yayi bai ce komai ba, ya fara sauraran karatun ƙannensa sai ga Nabeel ya shigo, kallo ɗaya Bunayd ya masa tuni ya gane nufinsa, shi ma ɗauko nasa ƙur’anin yayi da littafin da suke yi na addini, Bunayd sai da ya duba karatun ƙannensa duka ya musu ƙari, sannan ya kuma suka zauna hira ana raha, bai cika magana sosai ba amma idan da ƙannensa ne kuma yana mood to duk shirmen su yana biye musu.
Da dare ya ja sosai sai General ya kora su kowa ya kwanta, da safe a fara shiri sai Kano in Allah ya yarda.
Bunayd yana komawa sashinsa sai ga ƙira, ganin mai ƙiran sai ya taɓe baki, a fili ya ce, “Yoruba people akwai reni, to nima ba zan yi attending naka ba sai gobe.” Yana gama mitansa ya kashe wayansa ya kwanta.
Cikin dare ya tashi yayi nafilfiulunsa yanda ya saba, sannan ya koma ya kwanta.
Washe-gari Suhail da wuri ya iso, lokacin kuma kowa ya gama shiryawa, ba jimawa suka kamo hanyan Kano amma ta Flight, jirginsu na sauƙa motoci uku suka zo ɗaukansu daga gidan Alhaji.
Shigan su Bunayd gidan yayi dai-dai da shigowan motan Hajiya Sa’adatu da sai yau ta dawo daga inda ta je, su Suhaila duk da ba wani sake musu Hajiya Sa’adatu ke yi ba amma duk sun yi hugging nata, a yastine ta amsa, General da Momsee duk sai su suka ɗaga mata gaisuwa, sannan ta amsa a gadarance, da yake General ma da nasa part ɗin a gidan, sai suka wuce duka can, Majeeder tunda ta ji zuwansu ta fito ta rungume sister’s nata mata, da kuma General da Momsee, tunda ta maƙale wa Bunayd ko mostawa zai yi tana riƙe da shi, ba ƙarya Bunayd ma yayi mugun kewan ƙanwar tasa dan ya kwana biyu bai zo ba.
Alhaji da kansa ya saka masu aiki suka kai wa su General abinci, sannan da waɗanda za su musu aiki har su koma.
Hajiya Sa’adatu tunda ta shige ko leƙowa bata kuma yi ba, sai kawai cin magani take yi kaman ba ɗan uwan mijinta da yaransa ba ne suka zo, kaman wasu bare daban.
SU WAYE WANNAN AHALI?
MENENE FARKON LABARINSU?