Skip to content
Part 13 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Alhaji Sulaiman Ilyasu Kwalli!

Shi ne kakan Bunayd, Sulaiman kwalli wanda aka fi ƙira da Sule kwalli shi asalin ɗan jihar Sokoto ne, a ƙaramar hukumar Binji, su biyu iyayensu suka haifa shi da ƙanwarsa mai suna Rahama, Sule da Rahama sun taso cikin gata da soyayyar iyayensu, saboda iyayensu na da rufin asiri Masha Allah, su Hausa-Fulani ne, bayan kiwon dabbobi da mahaifinsu Ilyasu ke yi har da sana’ar hannu yana yi wacce ta danganci nau’in su kwalli, Sule da Rahama duk iyayensu sun saka su a makaranta ta muhammadiya da kuma ta ilimin zamani(boko), lokacin da Sule yayi nisa a karatu sai shi ma ya ɗau sawun babansu Ilyasu kwalli ya fara sana’a irin tasa, cikin ƙanƙanin lokaci da ikon Allah shi ma ya staya da ƙafansa, a lokacin ne kuma ya samu mata mai suna Hauwa’u ƴar gidan wani babban mutum ɗan siyasa a cikin birnin Sokoto.

Bayan neman da suka yi na ɗan lokaci sai aka yi auransu, bayan biki ba jimawa Sule kwalli ya samu haɗaɗɗen gidansa a cikin birnin Sokoto, nan ya nemi da su koma duka da iyayensa amma sai iyayensa suka ƙi su sun fi son zaman Binji, haka Sule ya tattara da Amaryarsa Hauwa’u suka koma cikin birnin Sokoto da zama, sai dai sa’i zuwa lokaci su dinga kai wa iyayensa ziyara, Hauwa’u matar Sule bafulatana ce gaba da baya, kuma kyakkyawa ce ta ƙarshe ma, dan haka suna zaune lafiya da mijinta, a sanda auransu ya cika shekara a lokacin ne kuma ta haihu ɗan ta namiji santale mai matuƙar kama da mahaifinsa Sule, ranar da ya cika kwana bakwai yaro ya ci sunansa Mukhtar, kuma a wannan lokacin Rahama ƙanwar Sule ta dawo gaban Sule da zama tana kan karatunta, saboda akwai ratan shekaru sosai stakaninta da yayan nata.

Mukhtar na da shekaru biyar a duniya sai Hauwa’u ta kuma haihuwan yaronta kyakkyawan gaske namiji mai matuƙar kama da ita, kaman kakinsa ta yi, ranan bakwai yaro ya ci sunansa Sufyan, zuwa wannan lokaci Ilyasu ya manyanta sosai kuma matarsa Salamatu na fama da cutan ajali, shi kuwa Sule ya zama mai kuɗin gaske, kullum sintirin asibitin neman magani suke da mahaifiyarsa amma kwana ya riga da ya ƙare babu dabara, haka saƙon mutuwanta ya riske su, a ranan suka tattara suka tafi Binji, bayan an yi bakwai suka tattaro suka dawo, sai da aka yi arba’in sannan Ilyasu ya yarda ya dawo gidan Sule da zama.

Bayan wasu shekaru biyar Hauwa’u ta kuma haifan yaranta ƴan biyu mata, aka sakawa ɗaya sunan kakansu da ta rasu, Salma ɗayan kuma Salima, bayan haihuwansu ba jimawa Rahama ta samu mijinta dan ita kam auren ya ɗan mata jinkiri ma, shekaranta biyu da aure ta haihu ƴar ta mace ranan suna ta ci sunanta Huraira, kuma a lokacin Hauwa’u ta ƙara haihuwan ɗa namiji mai suna muhammad, amma ita rahama tun da ta haihu ciwon ciki ke damunta, a ranan da suka yi kwana ishirin da haihuwa a ranan ta cika.

Rasuwan Rahama sosai ya taɓa ahalinta, musamman da ta bar jaririyan da ko wata bata yi ba a duniya, mijin Rahama ya bar Huraira a hannun kawunta Sule saboda kara, Hauwa’u ta nemi ta haɗa su ta shayar tare da muhammad amma Ilyasu ya hana, dan haka madara ake bata, tun su Huraira ba su shekara ba muhammad yaron Hauwa’u ya koma, a wannan lokaci kuwa Mukhtar da ƙaninsa Sufyan sun zama Samari dan Mukhtar yana da shekaru kusan goma sha bakwai, shi kuma Sufyan shekaru sha biyu garesa, twin’s kuma shekarunsu bakwai kuma duk suna nan lafiya-lafiya, Mukhtar ma yana karatu kuma yana kula da harkoki irin na mahaifinsa Sule kwalli, yayinda Sufyan ya dage shi Soja zai yi, kuma da yake ba rayuwan yau ba ne sai ya samu cikin ikon Allah.

Lokacin da Huraira ta yi shekaru biyar a duniya, lokacin Ilyasu ya buƙaci da su kai ziyara a Binji wa sauran ƴan uwa, Mukhtar da Sufyan duk suna makaranta ba sa gida, dan haka sai duk suka shirya da Sule da matarsa Hauwa’u da Ilyasu babansa da yaransa ƴan biyu, Salma da Salima da kuma Huraira, sun shirya sun kama hanya, lafiya-lafiya haka suka isa, suka zaga dangi suka musu alheri, kwanansu biyu suka tattaro dan su dawo gida, a hanya kuma suka haɗu da ƴan fashi, duk da sun samu abinda suke nema amma ba su bar kowa da rai ba haka suka kashe su suka yi gaba, labari na iske Mukhtar da Sufyan kaman za su yi hauka haka suka zo, sai dai wajan yi wa gawa sutura aka samu Huraira da ranta, storita da lamarin da ya faru ne ta yi dogon suma ba wai kasheta aka yi ba ita.

Wannan rashi kaman zai haukata Mukhtar da Sufyan, sannan Sufyan ya ɗau alwashin kama masu laifin sai ya ɗau fansan iyayensa da ƙannensa, Mukhtar kuwa sai dai ido kawai, Huraira haka ta zama shiru-shiru ita ma kaman mara ishashshen lafiyan ƙwaƙwalwa.

Malam Zahraddin mahaifin Huraira shi ya riƙe su Mukhtar tunda da girmansu ba buƙatan sai ya riƙe musu dukiya, kawai ya riƙe su ya zama kaman mahaifinsu ne dan saka halaccin iyayensu a garesa na riƙe masa ta shi yarinyar da kuma basa mata.

Shekaru sun ja, Mukhtar ya zama Alhaji kuma cikin ikon Allah tunda al’amuransa suka yawaita a Kano sai ya tattara su suka koma can, a Kano kuma ya samu matan aure Sa’adatu ƴar gidan wani kansila, tun da Alhaji Mukhtar yayi aure aka tura Sufyan aiki a Abuja, ita kuwa Sa’adatu wulaƙanci ne da ita ba kaɗan ba, haka ta ke yi wa Huraira da mahaifinta, Alhaji ya stawatar sosai, amma sai mahaifin Huraira ya ce za su je Sokoto ganin gida, duk saboda kada yana babba ya haddasa rashin zaman lafiya stakaninsa yaransa, haka ya tattara Huraira suka koma Sokoto a can kuma ta cigaba da karatu cikin kewan yayunta dan sosai Huraira ta saba da su Mukhtar.

Sufyan daga Abuja aka kuma shillasa Lagos, kuma tunda ya je Lagos ta masa daɗi ya zauna daram abinsa, ba batun aure a lissafinsa, sai dai ya kawo wa yayansa ziyara kwana ɗaya biyu ya koma, ya je Sokoto shi ma kwana ɗaya biyu ya koma Lagos, yana aikin Soja kuma yana da business wanda ya ɗaura masu kula masa da business ɗin, kuma a ɓangaren aikinsa ko da yaushe cikin ƙarin girma yake, inda yanzu yake mastayin General, kuma cikin ikon Allah da taimakon bincike, ya samu ya kama waɗanda suka kashe masa iyaye, hukuma ta yanke musu hukunci, saboda sun ishi al’umma daman.

Hajiya Sa’adatu ta haihu ɗan ta namiji mai shegen kyau mai kama da Sufyan kaman shi yayi kakinsa, idan ka ga yaron za ka ɗauka ɗan larabawa ne, yaro ya ci sunansa muhammad Bunayd, Sa’adatu ta ce ta daina haihuwa ita ba za ta iya ba ta stofe da wuri, ita ba son haihuwa take ba, kuma ko shayar da Bunayd bata yi sai Alhaji ya stawatar mata, amma duk da haka sam-sam Alhaji bai rageta da komai ba, domin da mahaifinta ya rasu aka raba gado aka bata nata, sai ya ƙara mata jari a kai ta fara business, wanda cikin ƙankanin lokaci kasuwancinta ya bunƙasa ta zama Hajiya ita ma, sai dai wulaƙanci ya ƙaru, kwata-kwata Hajiya Sa’adatu bata son kowa ya raɓe ta ko mijinta, hatta Sufyan da yake ƙanin Alhaji Mukhtar to ba ta ƙaunarsa, komai ita ɗaya haka take so, ko Alhaji zai yi yaya da ita yanzu bata yarda ta je Sokoto, sai dai ta kawo masa uzurin ƙarya.

Sufyan ya fi Alhaji Mukhtar ziyara sosai ba kaɗan ba, dan sai Sufyan ya je Sokoto sau biyar Alhaji Mukhtar bai wuce ya je sau biyu ko ɗaya ba, tunda Hajiya Sa’adatu ta haihu shikkenan kuma sintiri ya samu Sufyan Kano to Lagos, Allah ya ɗaurawa Sufyan stanstar ƙaunar Bunayd, dan ko da Bunayd yayi shekara biyu sai Sufyan ya ɗauke sa suka tafi Lagos, duk da ba shi da aure amma ya samu wata musulmar Yoruba tana kula masa da shi, kuma shi ma da kansa yana kula da Bunayd kaman shi ne mahaifiyarsa, kashinsa fistarinsa komai akan Bunayd ba abinda General Sufyan bai iya ba, kuma karatunsa Arabic da boko yana kula da shi, musamman abinda ya shafi Addini da kansa yake zama ya koya masa, baya taɓa yarda aiki ya sha kansa bai duba karatun Bunayd ba, gata kam iya gata Bunayd na samu a wajan General Sufyan, gatan da ko ɗan cikinsa ba lallai ya samu ba.

Alhaji Mukhtar kuwa ba abinda ya ce dan General Sufyan ya ɗau Bunayd, saboda shi hakan ma hankalinsa ya fi kwanciya, akan hali irin na matarsa, ita Hajiya Sa’adatu kuwa gaba-ɗaya hankalinta na kan business nata ko a jikinta, sai hamdala ma da tayi an rage mata aiki, dan ita ko haihuwan bata so ba balle yaro ya takura mata, kwata-kwata Bunayd bai san wani daɗin mahaifiyarsa ba, shiyasa shi ma a duniyansa komai nasa General ne, dan da shi yayi mugun sabo.

General Sufyan ko ina zai je ƙafansa ƙafan yaronsa Bunayd da ya zama kamar abokinsa, har Sokoto suke zuwa tare har wajan wani abokinsa Soja ɗan gidan wazirin Sarkin Sokoto, kuma Bunayd ya shaƙu da Huraira sosai, haka mahaifin Huraira ma sosai yake ƙaunar Bunayd, dan Bunayd yaro ne da duk wanda ya kallesa to sai ya shiga ransa, ba shi da ƙiriniya irin na sauran yara, kana ganinsa kaga zubin sadauki, yana da raha idan yayi niya musamman idan yana tare da General Sufyan ko Alhaji Mukhtar.

Bunayd na da shekaru sha uku mugun soyayya ya ƙullu stakanin General Sufyan da yarinyar Sultan na Sokoto, ta sanadin abokin General Sufyan, Major Ahmad wanda yake yaro a wajan wazirin Sarkin Sokoto, soyayyan General Sufyan sosai yayi nisa shi da Gimbiya Ramlat, ta san yana da yaya kuma tasan yana da yaro, wani stautsayi ne ya faru stakaninsu wanda yayi sanadin raba soyayyansu, damuwan da General Sufyan ya shiga shi ya sanya mahaifin Huraira ya basa auren Huraira tunda ba ta haramta a gare sa ba، duk kuma abinda ke faruwa Alhaji Mukhtar bai da labari dan yayi tafiya ƙasar waje.

Ba jimawa aka yi auren Huraira da General Sufyan, Bunayd sosai ya ji daɗin da Huraira ta dawo gidansu, kuma Huraira stakani da Allah take riƙe Bunayd da soyayya kaman ɗan cikinta, duk da ba wai ya cika zama bane, sakamakon makarantan sojojin sama da General ya saka shi, da farko Sojan ƙasa yayi niyan turasa amma sai Bunayd ya ce Air Force yake so, shi jirgi yake so.

Alhaji Mukhtar ya dawo ya samu labarin abinda ya faru nan ya bi su da addu’an Allah ya kyauta, a wannan lokacin ne kuma ciki ya bayyana jikin Hajiya Sa’adatu ba shiri ba sanarwa, duk ta gama sakankancewa ta daina haihuwa tunda ta yi planning, amma ikon Allah sai ga ciki, baƙin ciki kaman ta yi yaya, ta yi iya yinta amma ta kasa ɓarar da cikin, haka ta haƙura ba dan ta so ba sai dan ba yanda ta iya da nufin Allah, ciki na kai wata tara ta haifa yarinyarta santaleliya kyakkyawa mai sunan mahaifiyar su Alhaji Mukhtar, Hauwa’u amma suna ƙiranta Majeeder.

Huraira na cika shekara a gidan General Sufyan ta haifo yarinyarta mace kyakkyawa mai kama da Alhaji Mukhtar, yarinya ta ci suna Ramla, bayan shekara biyu ta kuma haihuwan ƴan biyu mace da namiji, Suhail da Suhaila, bayan wasu shekaru biyun ta kuma haihuwan ƴan biyu, Nabeel da Nabeela, bayan shekaru biyu ta haifi yaronta namiji amma ya koma, saboda wahalan da ta sha da cikin yaron sai General ya buƙaci da a stayar da haihuwan, Allah ya yiwa waɗanda suka haifa albarka.

Hajiya Sa’adatu tun da ta haifi Majeeder sai ta je asibiti a ɓoye aka cire mata mahaifa ba tare da sanin Alhaji Mukhtar ba, kuma har yau bai sani ba.

Yaran gidan General Sufyan sun taso cikin gata da soyayya na iyaye da kuma yayansu Bunayd, kaman yanda General ya kula da karatun Bunayd, haka shi ma yake kula da karatun ƙannensa, sosai yake ƙaunar ƙannensa, amma sam-sam ba ya shiri da Mom tasu Hajiya Sa’adatu.

Bunayd ya fara abota da Abeed ne tun san da ya shiga makarantar sojojin ƙasa da farko, sai ya zamana duk da ya koma air force school to ba su bar abota ba, shi ma Abeed ɗan Kano ne, mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, haka mahaifiyarsa ma tana nata business ɗin.

Malam Zahraddin mahaifin Huraira bai jima da rasuwa ba, sai bayan rasuwansa sannan suka ɗaga ƙafa da zuwa Sokoto.

Alhaji Mukhtar business yake sosai, kuma ya mallaki companies da dama, a Nigeria da ma ƙetaren Nigeria, shi ma General yana da nasa business ɗin kuma shi babba ne a sojoji.

Bunayd ma ba iya aikin Soja yake yi ba, domin daga General har Alhaji Mukhtar ba wanda bai ba sa jari ba, sannu a hankali ya fara business da kuɗaɗen, kuma shi da kansa yake kula da harkokinsa, sai dai kawai wakilai da yake da su, ya na da gidaje uku a cikin Lagos, sannan yana da gida a Kano, sai kuma ƙasashen waje da ya yawaita zuwa, duk inda business nasa ya yawaita a can yana da gida, ƙasashe shida duk ba inda bai da haɗaɗɗen gida a can, kuɗi CAS Bunayd yake da shi na fitan hankali wanda har ya ƙere iyayensa da suka basa jari, kuma shi ma duk ƙannensa maza ya basu jari duk da ƙananun shekarunsu, dan Suhaila shekarunsa 17 ne, amma shi ma yana da nasa Companyn a Turkish inda yake karatu, sannan yana zama a gidan Bunayd da ke can.

Nabeel mai shekaru 14 yana cikin na 15, shi ma Bunayd ya mallaka masa nasa rabon, yanzu haka dai rikice yake da General, shi Nabeel ya ce baya son aikin Soja, General kuma ya ce sai yayi.

Majeeder ta taso sai a hankali, amma da yake ita mace ce da sauƙi, Hajiya Sa’adatu na kula da ita ba kaman lokacin da ta haifi Bunayd ba, Alhaji ganin irin halin Hajiya sai shi da kansa ya ke duba duk abinda ya shafi Majeeder, tarbiyanta da komai nata, bai bari rashin kulawan mahaifiya ya sa yarinyarsa ta lalace ba, tana karatu boko da Arabic, bai jima ba da suka yi musabaƙa a cikin Kano kuma ta zo ta ɗaya, a boko kuwa tana matakin degree tana shekaranta na kusa da final year, inda take karantar Agriculture, a University na Kano.

Ramla tana karatu a babban Private University na Lagos, Anchor university, inda take karantar Education and computer science, sai kuma Suhaila da take nursing school a Lagos ɗin tana karantar midwifery, ita Nabeela kuma yanzu ne za ta tafi matakin gaba da secondary, ta dage University na Abuja za ta je, Bunayd kuma ya ce ba za ta yi zaman hostel ba, dole ita ma a Anchor university za’a nema mata admission ta karanci accounting, Suhail dai yana Turkish yana karantan abinda ya shafi business, shi ka Nabeel ya ce business administration zai karanta ko a Lagos ko kuma wata ƙasan, amma sam General ya ƙi.

Bunayd na da tarbiya dai-dai gwargwado dan sosai yake kula da abinda ya shafi addininsa, kuma yana da girmama manya, sai dai yana da abin dariya wani lokacin, kuma idan hali ya mosta to yana da miskilanci, bayan Abeed yana da wasu abokanan amma a wajan aiki, kawai ba wai ana together irin sosai ɗin nan ba ne kaman yanda yake da Abeed, kuma a wajan abokanansa ya koyi zuwa su club da sauransu, ba inda za’a je bai je ba amma kuma tunda ya ke bai taɓa kai abinda ya shafi giya ko kusa da bakinsa ba, kuma duk iya yanda sojoji ke harka da mata to shi babu shi a ciki, domin shi gani yake ko ashawo ba su gana waye wa ba, shi ya fi son ya samu wayayyiyar mace wacce bata da kunya ya aura, sam-sam baya son Ustaziyan mace, dan gani yake duk ustazan matan nan ba abinda suka sani sai ƙauyanci da kunya ba su iya soyayya ba, kwata-kwata bai taɓa yin ko budurwa ba a rayuwansa, duk da kuwa harin da mata ke kawo masa ta ko ina, ba ya wulaƙanta mace amma kuma yana koya mata tarbiya, dan idan mace ta dame sa da maganan banza sai ya koya mata hankali wai a kan me za ta taɓa sa bata biya sadaki ba, maganan iyayi kuwa akwai a bakin Bunayd sinƙi-sinƙi.

Bunayd ɗan shashu ne sosai, indai zai je club to ko mazari ne a wajan ba zai kai sa rawa ba, kuma tun tashuwansa ya ke ƙiran General Sufyan da General, Alhaji Mukhtar kuma ya ce masa Sir, har sai da aka haifi ƙannensa suka fara ƙiran Alhaji da Papi sannan wani lokacin yakan ce wa Alhaji Papi, General kam duk da ana ce masa Affa, to sai ranan da ya ga dama zai faɗi hakan.

Wannan shi ne asalin wannan tarihin wannan ahali a taƙaice, kowa kun ji halinsa saura kun ji a baya, sauran kuma za ku ji a gaba.

CI-GABAN LABARI

Upstairs na farko a gidan Papi shi ne sashinsa da matarsa Mom Hajiya Sa’adatu, ɗaya upstairs ɗin kuma shi ne na Affa General da Momsee Hajiya Huraira, sai haɗaɗdun flat ɗin kuma ɗaya na CAS Bunayd, ɗaya na Suhail da Nabeel.

Duk da Bunayd yana da part nasa a gidan, amma sai bai ko je ba ya tsaya a sashin Affa General, anan da masu aiki suka kawo abinci, Momsee ta saka su Ramla suka yi saving nasu, cikin nistuwa suka ci, sannan kowa ya shige ciki dan ya wasta ruwa, Bunayd na miƙewa Majeeder ta miƙe ta rufa masa baya, juyowa yayi ya kalleta ya ɗaga mata gira ɗaya ya ce, “Autan dole ya aka yi?”

Tura baki Majeeder tayi ta ce, “Ni dai ƙafanka ƙafa na, sai ka ƙara guduwa irin na lokacin kuma ka jima ba ka zo ba.”

Murmushi Bunayd yayi dan ya tuna wayon da ya yiwa Majeeder ya samu ya koma Lagos, last time da ya zo, bai ce komai ba ya riƙo hannunta ya ce, “To Autan dole muje sai ki bani labari ma, amma dai wanka zan yi, kuma nan gaba matata ta ga kina maƙale mini haka haushinki za ta dinga ji, ba ruwanta da ke ƙanwata ce.”

Majeeder maimakon ta ɓata rai sai ta yi dariya ta ce, “Yauwá sweet bro yaushe za ka yi aure? Ai na faɗawa Papi ya faɗa maka zan zauna a gidanka idan ka yi aure, sai shi kuma ya ce na faɗa maka ka yi aure.”

Bunayd darawa yayi ɗan dai-dai sannan ya ce, “Autan dole ba wayo, kar ki damu zan yi aure soon, yanzu dai ki taya ni nemo matan kin ga ban da budurwa.”

Majeeder har da stallenta an ce ta taya sa nemo mata, “Sweet bro ka yi wanka ka zo na shafa maka wani labari.”

Bunayd dariya yayi ya shige ɗakinsa da ke sashin Affa General, Majeeder kuwa ta zauna tana jiransa, tana ta danne danne a wayansa, photo’s take ta kallo, wani idan ta gani sai dai ta dara, har Bunayd ya gama wanka ya shirya, sannan ya mata magana ta shiga ɗakin ita ma, zama tayi a kan gadonsa ta ce, “Sweet bro ban ga photon kowa a wayanka ba balle na taya ka zaɓan matan.”

CAS ya ce, “Autan dole ai ke za ki nemo mini, amma fa bana son masu saka hijabin nan, wacce dai ta waye hakan nan, ta fi ki wayewa fa, dan ke nistasttiya ce.”

Majeeder dariya tayi ta ce, “sweet bro wasa kake mini ko.”

CAS Bunayd ya ce, “To bani labarin da kika ce za ki bani, tunda ba za’a barni na huta ba za’a cika ni da hira.”

Murmushi Majeeder tayi ta ce, “Da ɗumi-ɗuminta ai ta fi yaya, kar ta huce makwabta su ji baka ji ba, kuma kai ne baka zuwa shiyasa ba zan iya haƙura ba.”

“To nidai bani labarin dan bacci nake so nayi” CAS ya faɗa yana kwanciya a gadonsa.”

Majeeder ta ce, “albirshir yaya.”

“Goro fari tass kaman Suhaila ba kaman ke ba.”

Cunna baki Majeeder tayi, sai an ce bata da haske sosai ita, cewa tayi, “To Papi ne ya ce mini zai kawo mini Aunty kuma Mami zan dinga ce mata, kuma har da ƙawa za ta taho mini da ita, yanzu ai ba dan ƙawata ƙanwarka ba ce, da sai ka aureta, ni nasan mai kyau ce ita daga sunanta, Faɗima Banafshaaa, kuma fa ita ma wai a musabaƙansu ita ta zo ta ɗaya.”

Bunayd ɓata fiska yayi ya ce, “tashi ki tafi zan yi bacci.”

Majeeder sturut! Ta miƙe ta ce, “Na tafi da wayan sweet bro sai ka tashi.”

CAS idanuwansa a lumshe ya ce, “je ki da shi.”

Majeeder juyawa tayi ta fita da wayan, ita bata lura da yanayin Bunayd ma ya sauya ba akan magananta, shi kuma guntun tsaki ya ja ya ce, “To ban taɓa tsanan mutum ba, amma har kin saka naji haushin yarinya na staneta, ni ma haɗina da Ustaziya wacce har musabaƙa take yi” yana cikin magana sai ga kira ga shigo a ɗaya wayansa, yana mita ya ɗauka bai ma duba waye ba ne.

Maganan da aka yi a ɗaya ɓangaren ne ya sa shi dan taɓe baki, cikin yaren Yoruba yayi magana, ya ce, “aikinka ya jima da kammaluwa, mun yi magana da baturen, sun amshi contract ɗin.”

Mr Sonny Yoruba, a ɗaya ɓangaren cewa yayi cikin Yorubanci, “Ok nagode CAS, yaushe za ka shigo? Ko kuma ni yaushe kake free na shigo.”

Taɓe baki CAS yayi ya ce, “ina Kano kuma zan yi kwanaki, duk abinda ake ciki ka ƙira ni ko kuma ka mini magana ta WhatsApp kawai…”, Haka suka gama tattaunawa suka yi sallama.

Bunayd ya gyara zai yi bacci sai ga ƙiran Abeed, guntun tsaki ya ja ya ɗauka tare da karawa a kunne ya ce, “Jarababben Ango ya aka yi? Ka bi ka dameni da kira ina hutawa, idan kai maye ne fa ka kama kurwan mutum to sai ka kashe mutum zai samu sukuni.”

Abeeb taɓe baki yayi a nasa ɓangaren ya ce, “Da alaman dai wani ya taɓo ka, ba sallama sai surutu haka, duk da daman kai kanari ne, to faɗa mini me ya faru.”

CAS ajiyan zuciya ya yi sannan ya ce, “Yanzu Majeeder ke shirin ɓata mini rai wai ai Papi zai ƙara aure kuma za a taho mata da ƙawa.”

Dariya Abeed yayi ya ce, “Soyayyan Mom ta mosta kenan, shi ne kake taya ta kishi, dan za’a mata kishiya.”

Bunayd taɓe baki yayi ya ce, “Ina ruwana da Mom balle dan za’a mata kishiya ya dame ni, ni ai so nake mu yi maganan da Papi naji idan gaskiya ne to ni na ɗau nauyin kayan aure da sadaki da komai ni zan masa, Allah sa ya samu wacce ta fi Mom hali mai kyau.”

“To me damuwanka da ka ce Majeeder ce ta ɓata maka rai” faɗin Abeed yana murmushi.

CAS ya ce, “Wai ƙawar da za’a zo mata da ita ne take cewa da sai na auri yarinyar dan ita ma har musabaƙa suke kuma ta ɗaya ta zo, ni ina ruwana da Ustaziya, ai Ustaziya sai ustaz, mu dai da muke ƴan jagaliya sai mata ƴan irin mu.”

Dariya ishashshe Abeed yayi ya ce, “To me abin damuwa a nan? Ai naga kai ma ɗin haddan ƙur’ani ne a kanka, Kuma abin addini babu wanda ba ka ƙoƙari a kai, to kuma duk da hakan ga ka ɗan jagaliya, ja’iri ɗan gidan General ba, to dan tana da ilimin addini mai zai sa ta zama ba yanda kake so ba, ni har naji haka kawai ta shiga rai na, ba dan ina da tawa ba, ai da na yi wuff ta ita.”

Staki Bunayd ya ja, ya ce, “Sai kuma ka yi ai, ni dama ji nayi na staneta ma, dan haka sai ka yi ta biyu da ita.”

Dariya Abeed ya saka, Bunayd ya taɓe baki ya ce, “sunan wani wai sallau, wa ya ga saliha da ta zarce, ni wayayyiya nake so wacce dai ba jahila ba, amma dai addini bata mata overdose ba, dan haka idan ta so ma zan juye mata na kai na, kawai ta zama ba nistasttiya ba, kuma ba ta gari ba, ba saliha ba, kuma ba kamila ba, indai ita musulma ce mumina shikkenan, kai ni fa tun da Allah bai haramta auran ahlul kitab ba, to zan iya auren alhul kitab indai ta waye yanda ya kamata, kuma ta san rayuwa.”

Dariya Abeed yayi ya ce, “Gaskiya Musulmin ɗan jagaliya ɗan gidan General, kana abinda kake so, to wa ya ce maka yanzu akwai nagari? Ai kowa tafiya haka kawai yake kaman ɗan iska a gantale, ai duniyan yanzu ba’a niste take ba balle a samu wani na gari, kowa ɗan iskan kansa ne kawai shiru ake, yanda rayuwa ta zama ai kowa ba dan storon Allah ba sai ya koma bariki iskanci ba mai yin aure, ko kuwa a fara fashi da rana tsaka, kai dai addu’a za ka yi dan ba’a hijabi kamila take ba, sai ka dage baka son salihar mace kuma sai ka ga wacce ka samu ɗin duk da a zahiri ba saliha ba ce, amma ba lallai ta maka abinda kake so ɗin ba, kuma sai ka ga salihar ta maka dunuyancin da kake so.”

Bunayd murmushi yayi ya ce, “Na dai gane me kake nufi, wato dai so kake ka ce kamilarka tasan rayuwa, to ba dai zan sauya maganana ba, atou tantiriya nake so.”

Abeeb murmushi yayi ya ce, “Ko ma menene kai ka jiyo, ni dai na ce Allah baka mace tagari saliha mar’atussaliha” ya ƙarishe yana dariya.

Bunayd ya ce, “Ba Ameen ba dan uban mutum.”

“To yaushe za mu haɗu ne? Kada na zo ka ce kana hutawa na san ka da renin hankali” faɗin Abeed.

Bunayd ya ce, “Yau ba inda zan je kuma ba wanda zan saurara hutawa zan yi muna hiranmu da Majeeder, Papinmu zai ƙara aure, za’a yi wa Mom tamu kishiya ka ga sai mu fara shiri.”

Dariya Abeed yayi ya ce, “ka ji ɗan banza yaro mara taya mamansa kishi ba..”

Hiransu suka yi suna ta kwalala dariya, har suka yi sallama Bunayd ya kwanta baccinsa.

Kowa hutawa yayi ba wanda ya je ko ina, su Suhail da Nabeel suna sashinsu, Bunayd kuwa yana maƙale a sashin Affa General hankalinsa kwance, ko sashin Papi bai je ba, shi kuwa Papi ya bari su huta tukunna, bai je sashin Affa ba kuma bai nemi su zo ba, ita kuwa Hajiya Sa’adatu tana cike fam kaman za ta fashe, mutum da yaronsa an mallake masa shi, yaro yana Lagos yana wajansu, ya zo ma yana sashinsu, ko zuwa ya gaisheta bai yi ba balle ya nemi albarkan ta, sai mita kawai take yi, kuma ga Majeeder ma ta je wajansu ta maƙale, Papi kuwa ko ta kanta bai bi ba yana yin abinda ya damesa ne kawai, dan shi akan haka ba ya ganin laifin Bunayd, ko me yayi ita ta nema tunda tun farko ita ma bata sauƙe nata haƙƙin na mahaifiya ba.

Sai washe-gari bayan sun karya kowa ya yi wankansa ya ci kwalliya kaman masu zuwa dinner, sannan dukkansu suna nufi sashin Papi, CAS da farko ya ce ba inda zai je, sai da Affa General ya nuna za su ɓata sannan ya yarda zai je, amma dan Papi zai je ba dan Mom ba.

Bayan sun shiga kowa ya samu waje ya zauna, Papi sai murna yake ganin dukkansu da iyalansa ga su, sai yake ji a ransa ina ma har da Ramlatunsa da sai ya fi haka farinciki.

Mom sai wani shan ƙamshi take, tana kallon banza wa Momsee, ita dai Momsee ko a jikinta dan bata san ma tana yi ba.

Taro CAS Bunayd ya buɗe musu da addu’a, duk suka gaggaisa, shi ma ya gaishe da Mom, ta amsa a daƙile tana cewa, “tunda an mallakeka ai dole ka dinga gaishe ni kaman ba ni ce na stugunna nayi naƙudanka ba.”

CAS bai ce komai ba, kuma hakan ya yiwa Papi da Affa daɗi, Papi ne ya kalli Mom ya ce, “Sa’adatu ki iya bakinki.”

Mom kawar da kai tayi kawai.

Papi faɗa ya yiwa yaran sosai, ya musu nasiha, Affa General ya faɗa wa Papi abinda Suhail yayi na ƙin aikin soja, sannan ga Nabeel ma yana son bostarewa.

Murmushi Papi yayi ya ce, “Wannan ai stakaninsu da mara jin yayansu ne General ba sai ka sako ni ciki ba.”

General ya ce, “ai my Man ya musu magana sun ƙi ji.”

Bunayd shafa kai yayi yana kallon Papi yana danne dariyansa, su Nabeel kuma dariya suka yi dan sun san indai dan Affa General ya kare yayansu ne, to ba abinda ba zai ce ba.

Papi ya ce, “To Shikkenan tun da sun ƙi jin nasa maganan, sai a ƙyale su kawai su yi kasuwancin, shi Bunayd ɗin ai yayi soja ya gajeka sai ka godewa Allah, nima a bar mini yarana su yi kasuwanci irin nawa su gaje ni.”

General murmushi yayi ya ce, “Shikkenan ai tunda ka ce haka yaya, Allah taimaka ya basu sa’a.”

Duk suka amsa da Ameen, Nabeel farinciki kaman yayi stalle, ya ce, “Papi Allah bar mana kai.”

Affa General ya ce, “Ni kuma Allah ya kashe ni ku huta ko?”

Bunayd miƙewa yayi ya ce, “Ai General kai ne ma mai lasting ɗin, Allah bar mana ku ya ƙara girma ya saka muku da aljanna, Allah bar mana General da Momsee kawai, Papi kuma ni zan masa gudumawa” yana gama faɗa ya fice.

Papi dariya yayi, dan yasan ba zai wuce Majeeder ce ta shafawa yayan nata ba, su General dai dariya suka yi ba su gane nufin CAS ba, Mom kuwa ƙwafa tayi kawai, duk da bata shaƙu da Bunayd ba, amma yanzu ƙaunar yaronta take yi, bata jin za ta iya faɗan wani mugun abu a kansa balle ya shiga wani hali tunda ta haife sa komin yaya bakinta zai iya kamasa, sai dai idan mugun fata yake mata ba kishiya to zata nuna masa ita ce mahaifiyarsa tana da iko da shi kuma.

Wuni suka yi cikin nishaɗi, Papi da Affa sai ƙara tattaunawa suka yi akan abinda ya kamata.

Sai da su General suka yi sati guda, sannan suka tattara suka koma Lagos, Bunayd ma ya bi su dan sun gama maganan komai na bikin da Abeed, yanda komai zai tafi, dan a ranan da suka koma Lagos a ranan Abeed ma ya wuce Adamawa.

Papi sai sati na sama zai yi tafiya nasa, amma kuma busy ya ƙi barinsa ya je ya kalli masoyiyarsa kamun ya tafi tunda har wata biyu zai yi, sai waya kawai suka yi ya tura mata duk abinda ya kamata, kaman yanda ya faɗa dai bai ƙara mata maganan aure ba, sai dai ya mata faɗan ta kula.

Majeeder ta bi su Affa General sun koma tare, Hajiya Sa’adatu kaman za ta haɗiye rai dan masifa, Alhaji kuwa ya ce tunda yarinyar sa ce shi ya ga daman ta bi su, idan abun bai mata ba ta yi zuciya ta haiho wata yarinyar ko wani yaron, Hajiya cikin masifa ta ce ita ta gama haihuwa da shi idan ya ga dama ya sayar da yaran.

Papi ko sati guda bai yi ba saboda ɓaci ran da Hajiya ke cusa masa, haka ya tattara ya tafi tafiyansa abunsa, Suhail ma bai kai sati ba ya koma Turkish ɗin sa, Nabeel kuwa Bunayd ya masa komai da ya kamata a Spain ya ci-gaba da karatunsa a can, shi ma yana zaune a gidan Bunayd.

Rayuwa na tafiya ta ko wani ɓangare lafiya sai godiya ga Allah inda yanzu haka auren Abeed saura sati guda, kuma CAS Bunayd ya shirya tare da su Suhaila, Ramla, Majeeder da Nabeela duka ya taho da su, sun ce su ma za su zo da bikin.

Suna isowa yayi magana da Abeed ya kai su Majeeder gidan su Nusaiba Amarya, ta tarbe su hannu bibbiyu, duk anko da ake da komai Bunayd ya yi musu, ana fara shagalin biki kuwa kullum da kansa yake kai su wajan event ɗin da za’a yi kuma ya basu kuɗi a hannunsa, duk abinda ya ke yana zuwa da sauran abokanansu da suke gari, idan ka ga shungullan da Bunayd ke yi za ka ɗauka shi ne Angon, sosai Bunayd yake da kirki kuma ba shi da girman kai.

Yau take Thursday wanda a washe-gari juma’a za’a ɗaura aure, kuma sai washe-gari Ango zai zo, yana can Adamawa a wani daji gaba da Michika kamun a isa Mubi, shi da abokanan aikinsa suna fama da ƴan ta’adda masu addabar mutane sai dai mu ce Allah ya ɗaura su a kan su.

Ɓangaren Amare yau walima ake yi, Bunayd ya kai su Majeeder da suka sha Arabian gown’s suka shuka yi kyau Masha Allah, yana sauƙe su ya miƙa musu kuɗi ya ce, “Ku ji wa’azi mai kyau kuma ku yi aiki da shi.”

Suhaila ce ta yi dariya ta ce, “yaya dama ai indai ka ji wa’azi dole ka yi aiki da shi, musamman idan ka zo dan wa’azin ne.”

Bunayd girgiza kai yayi ya ce, “wa ya faɗa Miki? Ai da yawa mutane suna jin wa’azi ne kawai ba aiki suke da shi ba, a cikin malamai wasu masu yin ma ba wai suna yin abinda suke faɗan ba ne, shiyasa aka ce ka yi abinda Malam ya ce ba abinda ya yi ba, dan haka ku ɗauka kuma ku yi aiki da shi.”

Nabeela murmushi tayi ta ce, “Inshà Allah yaya za mu ɗauka mu yi aiki da shi.”

“Good! Nabeela my love” Bunayd ya faɗa yana murmushi.

Majeeder ta ce, “yaya ka zo da wuri ka kai mu yawo.”

Bunayd ya ce, “ku mastalanku kenan ba’a haɗa hanya da ku, yara sai son yawa, to driver ne ma zai zo ya ɗauke ku ba ni ba” yana faɗa ya yiwa motansa key ya tafi.

Duk tura baki suka yi suka shige, sannan suka samu waje suka zauna, wa’azi ne ake mai kyau mai kuma rasta jiki, wanda ba iya Amarya zai amfana ba, duk wata mace da ta ji ta yi aiki da shi to zai amfane ta duniya da lahira, dan misali ake mana da rayuwan da Nana Faɗima AS ta yi a gidan mijinta sayyadina Ali AS, dan haka mata wannan kyakkyawan tunatarwa ce gare mu, ki duba Allahn da ya ce a zauna a gidan miji a yi haƙuri, ki kuma aro halayyan Nana faɗima AS za ki ji daɗin zaman gidan miji, kuma za ki yi alfahari da hakan duniya da lahira, Allah ya sa mu dace, ya ƙara mana zaman lafiya a dakunanmu, ƙannenmu da yayunmu, da yaranmu, da iyayenmu marassa aure duk Allah ya haɗa su da na gari ya kuma ba su haƙurin zama.

Duk kwanakin nan da Bunayd yayi a gidansa na Kano yake kwana, iyakacinsa da gidan Papi idan ya zo ɗaukan ƙannensa ko ya dawo da su, Hajiya Sa’adatu ita haka ya mata ko babu komai tunda dai ya baro su General, bata san biki ne ma ya kawo sa ba, shi kuwa idan ya zo zai gaisheta zai mata ladabin da ya kamata, kawai dai baya sakewa da ita ne, dan Bunayd na da ilimi kuma yana aiki da iliminsa, ya san ita mahaifiya ce kuma yasan haƙƙinta da ke kansa, sannan ya san hannunka ba zai ruɓe ka yankesa ka yasar ba, uwa ta wuce wasa.

Bayan Bunayd ya baro wajan su Majeeder, yana cikin driving ƙira ya shigo wayansa, ganin layin Abeed sai ya ɗauka yana murmushi ya ce, “Palace is loading, Ango mai jiran gado, Dragon za’a sha aiki” ya ƙarishe yana dariya.

A maimakon ya ji muryan Abeed sai ya ji muryan wani daban, hankali a tashe yake magana ya ce, “Bunayd an samu mastala fa.”

Bunayd ya ce, “Me ya faru? Ina shi Captain Abeed ɗin?”

Wanda ke maganan ya ce, “Wallahi a tarzomansu da ƴan ta’adda shi ne aka samu akasi, duk da mun gama da su amma dai an harbesa, mummunan rauni ya samu kuma daman ya ce, duk abinda ya faru kai kaɗai za’a kira kar a faɗawa iyayensa.”

Hankali a tashe Bunayd ya ja wani wawan birki ya ce, “Yanzu kuna ina?”

“Muna babban asibitin cikin Mubi.”

Bunayd bai jira ƙara jin komai ba ya kashe wayansa ya juya sai airport, hankali tashe yayi duk abinda ya kamata, jirginsu ya ɗaga sai Adamawa, jirginsu na sauƙa daman ya riga ya gama magana da sauran abokanansa da ke nan a air force base na cikin jimeta, mota aka turo mata da drivern da zai kai sa har cikin Mubi, ba ɓata lokaci suka kama hanya, suna tafiya amma Bunayd gani yake basa isa da wuri, tun da yake bai taɓa wuce cikin Adamawa ba, ba local government da ya sani, bai san nisan Mubi ya kai haka ba, ji yake kaman ya fire ya gansa a gaban abokinsa.

*****

Yau Lahadi Banafsha ta warke daga cutan period ta yi rass abinta ta gama, wanka ta sha sharr da ita suna zaune da Mami suna hira kaman ba komai, sallama suka jiyo, wanda daga ji Banafsha ta gane muryan waye ne, zuciyanta ne ya stinke sai kuma ta saki murmushi lokaci guda, Mami dubanta tayi ta ce, “amsa sallaman mana, ki je ki duba waye ne.”

Miƙewa nayi na shige ɗakina na sako hijabi sannan na fito na wuce, kaman yanda na zatan kuwa shi ne, Malam Abbo ne, murmushi nayi tare da yin ƙasa da kai na tare da masa sannu da zuwa, amsawa yayi, na ce masa ina zuwa, sai na koma cikin gida na faɗawa Mamina Malam Abbo ne, murmushi tayi ta girgiza kai kawai ta ce, “Sai ki ce ya shigo ko.”

Komawa nayi na masa iso, muka shigo palourn lokacin Mamina ta riga da ta shige ɗakinta.

Malam Abbo zama yayi ni kuma na wuce na kawo masa ruwa da abinci duka, yau ma kaman ranan murmushi yayi ya ce, “Lallai ni ɗan gata ne kullum har da abinci, ki ce idan zan zo zance za daina cika cikina da tuwon Ummina.”

Murmushi nayi tare da yin ƙasa da kai na ban ce komai ba.

Ƙara gaisawa muka yi bayan ya sha ruwa, sannan na ce, “Malam a yi haƙuri wannan satin ban samu zuwa ba, na faɗawa Umaima ta faɗa banji daɗi ba ne.”

Murmushi Malam Abbo yayi ya ce, “To ai ni yanzu ba abinda ya shafi makaranta bane ya kawo ni, batu ne akan rayuwata, farincikinka, cikar burina, muradina, maganar soyayyata da ƙauna ce ta kawo ni Sayyadata Roohi ta.”

Wani kunya ne ya rufe Banafsha da ya sanyata kulle fiskanta da tafin hannunta, wani irin soyayyan Malam Abbo ne ya stirga mata duk wani sassa na jikinta lokaci guda ba zato ba tsammani, sai dai kaman daga sama take jin maganganun Maminta na dawo mata, sai kuma wani damuwa ya maye gurbin farincikin, wanda har Malam Abbo sai da yayi mamakin ganin yanayinta ya sauya sosai, ba tare da ya ankara ba ya kuma jin tana cewa, “Malam Abbo ka yi haƙuri, abinda na faɗa maka da farko shi ne har yanzu, ba zan iya aure da mugun tabon da ke tare da ni ba” ta na ƙarishe maganan kaman zan yi kuka, saboda ni da kai na ina jin ciwon abinda nake faɗa.

Malam Abbo murmushi yayi ya ce, “Ni ma kuma ina kan baka na, ina ƙaunarki har gobe, duk wannan amsa naki ban gamsu da su ba Roohi, amma zan yi abinda ya kamata, sai dai dan Allah ko ne na yi kada ki ga laifina soyayyanki ne ya ja.”

Shiru nayi ban ce komai ba, saboda kokawa nake da zuciyata na samu da rashi da nake gani a filin Allah.

Malam Abbo ba tare da damuwan komai ba ya ce, “kwana biyu Umaima ma bata ke makarantan ba, fatan dai lafiya?”

Cikin damuwa na ɗago kai na, amma muna haɗa ido sai naji wani iri, tuni nayi ƙasa da kai na na ce, “Amma bansan me ya sameta ba, bansan ko wani abun ya faru ba, dan nima yau ne naji daɗin jikin nawa, sai dai in Allah ya yarda gobe da safe zan shiga na dubata kamun mu wuce makaranta.”

Jinjina kai Malam Abbo yayi ya ce, “Hakan ma yayi Sayyadata, Allah ya yarda ya kuma nuna mana da rai da lafiya, sannan kuma Allah nuna mana bikinmu, ranar da Malama Faɗima za ta zama mallakin Aliyu bawan Allah.”

Shiru na yi ban kuma cewa komai ba, Malam Abbo dai sai hiransa yake mini na soyayya, duk da ina jin daɗi da kuma sanyi a rai na amma na kasa nuna hakan dan bana son na yaudari malam Abbo ko kaɗan, sai da lokaci ya ja idan yayi magana sai dai na ce Uhmn! Ko uhun!, Ganin dare na ƙoƙarin yi suka ya dube ni yana sakar mini murmushi wanda yake daga zuciyansa ya ce, “Nikam zan tafi Sayyadata sai na ƙara zuwa kuma.”

Ba tare da na kallesa ba na miƙe na ce, “Bari na ƙira Mamina ko gaisawa ba ku yi ba.”

Murmushi Malam Abbo yayi ya ce, “Umma ta zama surkuwata kunyarta nake ji, ki bari zan zo daga baya na gaisheta daban, yanzu kunya nake ji dan yau wajanki na zo.”

Abinda Malam Abbo ya faɗa dariya ya bani, dan haka murmusawa nayi, kawai muka yi sallama na rakasa har ƙofan gida, kallona yayi ya ce, “Ina matukar ƙaunarki Sayyadata.”

Kallon juna muka yi na ƴan second’s, inajin kaman na faɗa abinda ke rai na, amma ba dama, ganin kuka na neman zuwa mini sai na juya da sauri na kulle ƙofa na koma ciki.

Malam Abbo murmushi yayi dan shi ya riga ya sanya a ransa indai Faɗima rabonsa ce to zai sameta, yasan mai zai yi, in Allah ya yarda zai mallaketa.

Ni kuma ina share hawayena na shige ciki, kusan karo muka yi da Mamina, girgiza kai tayi.

Mamina ta ce, “lafiya kuwa? Me ya faru? Me ya sameki? Yanzu nake cewa bari na bi bayanki kin zauna a waje me ya faru?”

Share hawayena nayi na seta kai na, cikin dakewa na ce, “Ba komai Mami.”

Ganin dare yayi duk yin Mami, sai ta ƙyale kawai ta wuce ɗakinta na wuce nawa, ina addu’an Allah ya sa lafiya an ce Umaima ita ma kwana biyu ba ta je makaranta ba, da tunanin haka na kwana a rai na.

<< Yar Karuwa 12Yar Karuwa 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×