Skip to content
Part 14 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Washegari da safe na shirya tafiya College da wuri, bayan na gaishe da Mamina ta amsa, sai na ce, “Mami zan bi gidan su Umaima kamun na wuce, Malam Abbo ya ce mini ita ma kwana biyu ba ta je makaranta ba, bansan ko me ya sameta ba.”

Mami ta ce, “To a dawo lafiya, ki gaishe su, sannan ki kula sosai ko.”

Ɗaga kai na nayi alaman na ji, sannan na mata sai na dawo na fice, ina ƙoƙarin shiga gidan su Umaima sai ga ta ita ma ta fito da shirin zuwa College, murmushi muka sakarwa juna, na ce, “Umaimatyna.”

Murmushi Umaima ta mini wanda hankalina bai kwanta da shi ba, ina tunanin ma na ƙarfin hali ne, bata ce mini komai ba kawai ta riƙe hannuna muka yi gaba, ni bin ta nake kaman mara lafiya dan jikina yayi sanyi, bansan me yasa tayi haka ba, amma dai na yi shiru, muka nemi mashine muka tafi College.

Mun wuni a makaranta muna ta lecture’s, amma kwata-kwata na kasa ganewa Umaima, gaba ɗaya bata son yin magana sosai, ƴar rigiman da muke yi da stokanan juna duk yau babu, sai dai murmushi kawai take mini idan na yi magana, kasa jurewa nayi da hakan, ana tashinmu muna tafiya kan mu samu mashine na ce, “Umaima me ya faru? Me na miki? Ko ba ki da lafiya ne?”

Mashine ta tare mana muka shiga, ƙara kallonta nayi na ce, “masoyiya me ke faruwa dan Allah?”

Umaima murmushi ta sakar mini ta ce, “Me ne kika damu kanki haka Banafshaty, lafiya fa ba komai.”

Kallon Umaima kawai nake yi ba dan na yarda da abin da ta faɗa ba, numfasawa nayi na ce, “To me ya hanaki zuwa makarantan tahfiz kwana biyu?”

Nan ma shiru Umaima tayi bata ce komai ba har muka isa gida, mashine na ajiye mu ta kalleni da murmushin ƙarfin halin da take mini tun safe ta ce, “Banafshaty ki gaisar mini da Mami”, ta faɗa tare da yin gaba ta shige gidansu.

Haka Umaima ta tafi ta barni a staye a gantale ta shige gidansu, sai da na gaji da tsayuwa sannan na numfasa na juya cikin damuwa na shige namu gidan.

Mamina na samu zaune a palourn tana waya, jakana na ajiye a kan kujera na shige jikin Mamina na lafe, ba tare da na ankare na bacci ya fara yin gaba da ni, sai da Mamina ta gama wayan da take yi sannan ta shafa kai na ta ce, “Fatu kulen Maminta, shugabar masu son jiki tashi kada ki karya ni.”

Ni kuwa tuni na fara bacci ban ma ji me Mamina ke faɗa ba.

Mami sunkuyawa tayi ta kalli fiskana, ganin bacci na fara sai ta murmusa ta girgiza kai kawai, a hankali ta bubbuga bayana ta ce, “tashi kije ki cire kayan makarantan, idan kin wasta ruwa sai ki kwanta ki yi baccin, dan da alama yau kin ajiye wanda zai je miki tahfiz ɗin.”

Cunna baki nayi, cikin shwagaɓa na ce, “Mami jikinki ne daɗin kwanciya shiyasa na ji bacci.”

Murmushi Mami tayi ta ɗaga ni, amma na koma na lafe na ce, “Mami yau bansan me ya samu Umaima ba, magana ma da ƙyar take mini.”

“Ba sai ki tambayeta ko wani abun ya faru ba Banafsha” faɗin Mami tana ɗaga ni.

Zama nayi sannan na ce, “Mami wallahi na tambayeta, da farko ta yi shiru, daga baya ta ce ba komai.”

“To wataƙila ko bata jin daɗine, ko kuma wani abun daban, amma ki bata kwans biyi idan ma bata da lafiyane Inshà Allah za ta ji sauƙi, kuma za ta faɗa miki, kada ki damu kanki kinji ƙawar Umaima.”

“Uhmñ!” Kawai na faɗa na miƙe na ɗau jakana na shige ɗakina, sai da na cire uniform na watsa ruwa, sannan na fito na ɗau abinci na cika cikina, sai na koma na kwanta, kamun lokacin tahfiz yayi.

Yamma na yi na tashi na shirya, nan ma a ƙofan gida muka haɗu da Umaima, yanzu ma yanayinta kaman ɗazu da safe, haka har muka isa tahfiz, mun yi karatu har aka tashemu, sannan muka kamo hanyan gida, muna tafiya sai ga Malam Abbo, ba daman na ɓata rai ko wani abu, murmushi ya sakar mini ya ce, “Sayyadata ina zuwa anjuma.”

Tura baki nayi na ce, “ka yi haƙuri Malam zan yi aiki.”

Ba tare da damuwan komai ba Malam Abbo ya amsa da shikkenan ba mastala, ya juya abinsa, mu ma muka yi gaba, Umaima murmushi tayi ta ce, “Sayyadar Malam Haidar.”

Taɓe baki nayi na harare ta na ce, “Tun da kin ƙi faɗa mini abinda ke faruwa, ba ruwana da ke kada ki mini wani magana “

Murmushi ta kuma yi ta ce, “To Allah ya sanya alkairi Banafshaty, Allah kuma ya tabbatar da alkairi, ashe da tabbata gaskiya ne hasashen ɗalibai.”

Ban ce mata komai ba, muka cigaba da tafiya har muka isa gida, Umaima ta shige gidansu, nima na shige gidanmu.

Haka muka kwashe kwanaki har muka cinye wannan satin yanayin Umaima ya ƙi sauyawa, kuma ta ƙi faɗa mini abinda ke faruwa, sannan a gefe guda kuma Malam Abbo kullum sai ya takura akan zai zo, ni kuma sai na dinga kawo masa uzurina duk saboda bana son ya zo, ni bana buƙatar shaƙuwa sosai ya shiga tsakaninmu, dan kada ma gaba idan na nuna bansan zancen ba, shi kuma ya ce na yaudaresa.

Yau da yake Friday ne muna da class na ƙarfe bakwai, da wuri na shirya, muka haɗu da Umaima a ƙofa yanda muka saba haɗuwa kwanannan, mashine muka shiga ya kai mu makaranta, mun yi lecture’s har lokacin sallahn juma’a yayi aka fita kamun a sauƙo juma’a kuma.

Ni da Umaima daman ba damuwa muka yi da zuwa masallacin school ba, dan haka alwalanmu muka yi, muka yi sallahnmu a ƙasan wani bishiya mai inuwa inda muke zama, sai da muka idar sannan na kalli Umaima cikin damuwa na ce, “masoyiya dan girman Allah dan darajan Annabi ki faɗa mini abinda ke faruwa, idan ma wani laifi na miki ai sai na baki haƙuri, idan wani abun ne ai gwanda na sani zai fi, masoyiya ki tuna fa, duk abinda ke faruwa da ni kin sani, wanda ba ki sani ba ma ina sanar da ke, mastayin Aminiyata na baki, banda wacce zan nuna na ce ƙawata ce sai ke, masoyiya da ke nake shawara, ke ce abokiyar kukana kuma abokiyar dariyana, to me ya sa abu zai faru ke ba za ki faɗa mini ba, sai ki dinga shashshareni, ko dai ke ba ki bani mastayin da na baki ba ne?” Na ƙarishe maganan ina kallon cikin idanuwanta.

Umaima murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi, bata ce mini komai ba sai hijabinta da ta ɗaga ta nuna mini dansten hannunta, ban dawo daga duniyan da nake ba ta kuma nuna mini gadon bayanta, cikin damuwa na ce, “Umaimaaaa!! Me ya same ki? Wannan shatin bulala ne fa, wa ya miki wannan duka? Naga dai banji mostin Ya Danish ba wannan weekend ɗin, dan Allah me ya sameki Umaima” na faɗa kaman zan yi kuka.

Murmushin Umaima ta kuma yi, ta buɗe baki za ta yi magana kuma sai ga hawaye, ganin kukanta nima sai hankalina ya tashi, ga shi dai-dai lokacin malamai sun sauƙo juma’a, an koma mana aji, haka na lallasheta muka koma class.

Sai wajan ƙarfe biyar aka tashemu, muna fitowa class Umaima ta labarta mini abinda ya faru har kwanciya a asibiti da ta yi, tana bani labarin har muka samu mashine muka shiga, ni kuwa cikin tausayi da damuwa nake sauraranta, uwa dai uwa ce amma wani abun sai a hankali, lallai dole Allah ya ce a duk halin da kake ka gode masa, kuma kowa da tasa jarabawan da Allah ke jarabtansa, ga ni dai mahaifiyata tana rayuwan da ba kyau har ana ƙirana ƴar karuwa, ina damun kai na bayan wannan shi ne jarabawana, indai Mami ta sa hannunta a jikina to fa ni ce na nema, garin faɗa mata gaskiya na faɗa mata maganan da bai mata ba, amma bayan haka Mami ko hararana bata yi, to ga Umaima wacce mahaifiyarta ba ta da wani mugun tabo, tana da mutuncinta a gidan aurenta, amma akan abinda bai kai ko stawa a yiwa mutum ba, Umma ta mata wannan mugun duka, to Allah kyauta ya raba mu da iyayenmu lafiya.

Mashine na sauƙe mu, muka fara tozali da Ya Danish zaune a bayan motansa idanuwansa a kan hanya kaman mai jiran isowan wani abu, ina ganinsa na ji gabana ya faɗi haushi ya turnuƙe ni, tuni na haɗa fiska ko kallonsa ban yi ba muka yi sallama da Umaima na shige gidanmu, ita ma ta shige nasu gidan bayan ta gaishe da Ya Danish da idanuwansa ke kai na.

Malam Abbo da ya gaji da bin Banafsha zai zo zance, ta ƙi basa dama sai abin ya damesa, dan haka daman yana da shirin yi wa Mami magana akan Banafsha, sai ya shirya staff abinsa, yana dawowa sallahn juma’a ya nufi gidan Mami, cikin takunsa na nistuwa yake tafiya har ya isa, da kansa ya shiga gidan yayi sallama.

Mami da ke zaune a palour ta sha wankan juma’an ta, amsa sallaman ta yi ta yafo mayafinta ta leƙo, ganin Malam Abbo ne tana murmushi ta ce, “Kai ne Malam Haidar.”

Malam Abbo da fara’a yana sunkuyar da kai ya ce, “Nine Umma, barka da gida.”

Mami ta ce, “ka iso ko.”

Malam Abbo bayan Mami ya bi ya shiga palourn, stugunnawa yayi zai gaisheta sai Mami ta ce ya zauna bari ta kawo masa ruwa, yana cewa da ta bari, amma Mami ko nuna ta ji bata yi ba ta wuce, ta kawo masa abun sha, sannan ta zauna, Malam Abbo durƙusawa yayi ya gaisheta.

Mami ta amsa tana murmushi ta ce, “Sannunka da zuwa Malam Haidar, ya kuma haƙuri da su Faɗima.”

Malam Abbo baki kaman zai yage dan murmushi, sai sunkuyar da kai yake yi irin ana gaban surkuwan nan, cewa

yayi, “Ba komai Umma, Allah ne da haƙuri da mu, Malama Faɗima yanzu kam Masha Allah, kwana biyu da bata zo ba ma, Malama Ummu-khultum ta faɗa mini cewa bata ji dad’i ba ne, fatan jikin da sauƙi?”

“Da sauƙi sosaima Malam Haidar, dan yanzu haka ma suna boko, mun gode sosai-sosai fa, Allah yayi albarka Allah ya taimaka, dama ita Faɗima indai makaranta ce to sai ciwo ke hanata zuwa, shiyasa wancan lokacin ma na je makarantar naku da kai na dan ka zo ka mata faɗa, bata taɓa irin haka ba sai hankalina ya tashi sosai.”

“To Allah ya kiyaye na gaba Umma, Allah ƙara mata lafiya Alfarman Annabi SAW.”

“Sallallahu Alaihi Wasallam, Ameen Malam Haidar, ga shi kun yi saɓani bata nan” faɗin Mami tana murmushi dan ta jima da fahimtan akwai abu tsakanin Banafsha da malaminta.

Malam Abbo ƙara duƙar da kai yayi ya ce, “Umma daman wajanku na zo, ita kam mun gama magana da ita.”

Mami ganin bai sha ruwan ba yana jin kunyanta, sai ta miƙe ta ce, “To ka sha ruwa bari na zo” tana gama faɗa ta shige ɗakinta, tana shiga ta saki murmushi tare da ɗaga hannu sama ta ce, “Allah ka tabbatar mana da alkairi.”

Malam Abbo Mami na tafiya, ya buɗe ruwa ya kwankwaɗa dan kada ta ce ya ƙi sha, kuma saboda ya samu ƙwarin guiwan faɗa mata komai, yana zaune ba jimawa Mami ta dawo ta samu waje ta zauna, sannu da fitowa ya mata ta amsa.

Mami ta ce, “yauwa Malam Haidar ina sauraranka.”

Malam Abbo ƙasa yayi da kansa cikin kunya ya labartawa Mami yanda suka yi da Banafsha, duk abinda ya kamata ya faɗa mata ya faɗa, kansa a ƙasa sosai ya ɗaura da cewa, “Umma ki yi haƙuri, amma ni ina son Faɗima a ko yaya take, amma ta dage da faɗa mini ba za ta yi aure ba, dan Allah Umma a taimaka mini a saka mana baki.”

Murmushi Mami tayi, wanda kana ganinsa kasan na tsantsan farinciki ne da take ciki, hamdala take kawai a zuciyanta, abinda take hasashen ya tabbata, kuma tasan in Allah ya yarda Banafsha ta samu miji wanda zai nusar da ita duniya da lahira, tana kan murmushin ta ce, “Masha Allah! Tunaninka na ka zo da kanka ka same ni yayi sosai Malam Aliyu, kuma ba komai Insha Allah zan yi magana da ita Faɗima ɗin, sannan ka yi haƙuri da abubuwan da ta faɗa maka, Faɗima ta girma ne kawai amma babu wayo, yaranta har yanzu yana damunta sai a hankali, in Allah ya yarda in har ita rabonka ce to za ka sameta.”

Malam Abbo ya kasa ɓoye farincikinsa, shi daman ya sani indai ya yiwa Umma magana, to Insha Allahu in ba dai akwai wanda aka bawa ita ba ne, to zai sameta, cikin farin ciki ya ce, “Nagode! Nagode! Nagode! Umma, Allah ya ƙara girma, Allah ya saka da alheri Umma, Allah ya ja kwana ya ƙara girma, Allah ya saka muku da aljanna mafificiya, in Allah ya yarda zan yi wa manyana magana, daman ina son idan muka dai-daita ne ba wani ja’inja a ciki sai na sanar musu.”

Mami ta ce, “shikkenan ba mastala, zan yi waa wanda za ku nema auran nata a wajansa magana, duk abinda ake ciki za ta faɗa maka, kar ka damu, Insha Allah Faɗima matarka ce.”

Malam Abbo saboda farinciki ji yake kaman ya tashi ya sha juyinsa a gaban Mami, amma kunyan surkarsa yake, sai dai dole ya ɗebowa Sayyada Roohinsa shoki akan wannan abun murna da farin cikin.

Malam Abbo sallama ya yi wa Mami ya tashi ya fice q palourn, ba abinda yake yi sai aikin washe baki, kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki, kaman wanda aka ce masa anɗaura an kai masa Banafsha ɗakinsa.

Banafsha na ƙoƙarin shiga gidan, shi kuma Malam Abbo na ƙoƙarin fitowa, saura kaɗan su yi karo ya masta da sauri yana faɗin, “subhanallah! Sayyadata afuwa.”

Ni kuwa baya nayi ban shiga cikin gidan ba, sai da na kalli ƙofan gidan su Umaima da gefen ido, na tabbatar Ya Danish na wajan kuma da alama idanuwansa a kai na suke, murmushi na sakarwa Malam Abbo na ce, “Ba komai Sayyadi.”

Malam Abbo ƙara washe baki yayi ya fito gabaɗaya ya ce, “Sannu da dawowa Sayyadata, a je a huta nima bari na wuce gida daman na zo gaishe da Umma ne.”

Murmushi na kuma yi na rausayar da kai na ce, “To nima a gaishe mini da su Umma.”

Murmushi tayi cikin nisto a kogin ƙaunar Banafsha ya ce, “Za su ji” yana faɗa ya wuce yana sakin murmushi.

Ni kuwa sai da na kuma satan kallon ya Danish, sannan na ja staki na taɓe baki na shige gida da sallama.

Ya Danish tunda suka yi magana da Abbaa shikkenan ya kasa gane wa tunaninsa, yarinyar da yake da burin aure yanzu haka kawai ta fice masa a rai, tun da Abbaa ya masa magana in har zai yi tunanin matan aure to Banafsha ke faɗo masa a rai, ko weekend ɗin da bai zo last ba ma abinda ya hana shi zuwa kenan, zuciyansa ke dage masa akan tana son kallon Banafsha, amma shi sai yana yaƙi da hakan, wannan karon ya kasa haƙura shiyasa da sassafe ya baro Camaroon, dan isowansa bai jima ba aka yi sallahn juma’a, kuma tun da yayi sallahn la’asar yake zaune a ƙofa, zaman jiran yaushe su Banafsha za su dawo, a kan idonsa Malam Abbo ya shiga gidan su Banafsha, da yake kuma ya ganesa, tun da ya ga shigansa sai haushi ya rufe sa.

Haka dawowan su Banafsha ma a kan idonsa, tun da ya kalleta kuma ya ji wani irin yanayi mai kama da nustuwa ya lulluɓesa, kaman jinjirin da ya wuni bai samu nono ba sai yanzu, haka ya ji da ya ganta, duk da haka kokuwa yake da zuciyansa yana son ya ƙalubalanci wannan abun da yake ji a kan ta, amma bai tabbatar da ba zai iya hana zuciyansa wannan tunanin ba sai da ya ga murmushin da take yiwa wani daban ba shi ba, ji yayi ina ma shi take yi wa wannan murmushim.

Ya Danish kaman ya kamo Malam Abbo ya shaƙesa haka yake ji, har ya wuce abinsa, ajiyan zuciya Ya Danish ya sauƙe, a fili ya furta, “Allah kar ka ɗaura mini son yarinyar nan, ni da kai na nasan na ci mata mutunci, Allah idan ka jarrabeni da soyayyanta nasan wahala zan sha, Allah ka hanani son ta, ka sa ba son ta nake yi ba.”

Ya IB da isowansa kenan, da mamaki yake kallon Danish ya ce, “Kai kuma tun ɗazu kana ta sumbatu kai kaɗai lafiya kuwa? Wacece ta taɓo ka haka da kake wannan addu’an Allah ya sa kada ka so ta, wacece za ta zarar mana da kai.”

Hararan Ya IB yayi ya ce, “kai dai da son gulma kake kaman wani mace.”

Murmushi Ya IB yayi ya ce, “Idan ta yi stami za mu ji, kuma dai in baka da labari ka sani yau, gulma ya jima da kauracewa mata ya koma kan maza, dan mata yanzu ba sa raya sa da kyau, gulma sai maza alaji je majalisa ka ga yanda ake baza hajar mutane kaman shinkafa da kaza a tire, Allah kyauta kawai, yanzu ma kamata yayi ace sheɗan ya fara storon maza ba iya mata ba.”

Danish abinda ya damesa shi ne damuwansa, ko ta maganan Ya IB ba ya yi.

Banafsha na shiga gida ta samu Mami na ɗage ruwan da ta kawo wa Malam Abbo, ganin Banafsha sai ta murmusa tare da amsa sallaman ta ce, “ƴammatan Mami an dawo.”

Jinjina kai na nayi, ina murmushi na amsawa tare da gaishe da Mami, ta amsa, sai na ce, “Yanzu na haɗu da Malam Abbo ma a ƙofa.”

“Eh! Daman nima nayi tunanin kun haɗu a waje ai” faɗin Mami tana zama.

“Mami wai gaishe ki ya zo yi in ji sa, haka ne?” Na faɗa ina rausayar da kai.

Mami dafe goshi tayi ta ce, “Allah shiryaki Banafsha, ki bari idan kin huta sai ki zo ki mini wannan tambayan, tun da shi da ya faɗa miki ba ki yarda ba.”

Tura baki nayi na wuce ɗakina, ni dai jikina bai bani gaishe da Mami kaɗai ya zo yi ba, addu’a nake Allah ya sa ba maganana ya mata ba, kuma ko maganan nawa ne to ba zan yi aure ba inhar Mamina bata yi ba.

*****

<< Yar Karuwa 13Yar Karuwa 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×