Skip to content
Part 15 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Sai da na wasta ruwa nayi sallah sannan na fito, samun Mami nayi tana zaune har yanzu, abinci ta saka ni na ɗibo na ci, har na ci na gama shiru Mami bata ce mini komai ba.

Washe-gari asabar sai da muka shirya muka je tahfiz sannan da muka dawo muka wuce College, yau class ɗaya kawai muke da shi, dan haka da wuri muka dawo, duk da mun ji ka-ce-na-ce akan za’a manna result ranan, Umaima ta ce mu jira, ni ko na ce bata isa ba gida za mu dawo, haka ta biyoni muka nemi mashine muka nufo gida.

Muna tafiya a mashine na ce, “Masoyiya ban faɗa miki yanda muka yi da Malam Abbo ba.”

Umaima hararana tayi ta ce, “Daman ai iya gudun ruwanki na staya gani, za ki faɗa mini ne, ko har yanzu bata yi stami ba balle na ji.”

Murmushi nayi na ce, “faɗa miki ai kinsan dole ne, ni bana miki ɓoyel-ɓoyel…..” Nan na kwashe duk yanda muka yi da Malam Abbo na faɗa mata.

Umaima murmushi kawai ta yi ita ma, ta ce, “Yanzu haka kika ce masa masoyiya?”

Ɗaga kai nayi na ce, “eh ai gaskiya ce, ni ba maganan aure a gabana, haka kawai za’a aure ni a dinga faɗa mini magana ko miji ko ƴan uwansa, to ba zan ma fara ba, daman aka ce da gabar na bayar gwanda gabar na hana.”

Murmushi Umaima ta kuma yi ta ce, “To Allah ya kyauta, tun da dai bakyajin shawara ta Allah da Manzonsa, to ni ba abinda zan ce, Allah rufa mana asiri kawai, amma dai aure ai abin so ne, kuma mutunci ga ko wacce ƴa mace kema kin sani, to stakani da Allah ma wa ya ƙi ni’imar aure? Ai ko ba dan ci da sha ba kana samu a gidanku, to ko dan John-thomas ai ka yi, indai Allah ya nufa kuma ya kawo miji to aure shi ne rufin asirin ko wacce ɗiya mace, ni wani gulma na ji ma nake son miki ke ma, bansan ko kin ji ba dai.”

Yau ba mu ce mashine ya kai mu ƙofan gida ba, sauƙa muka yi muna tafiya muna kan hiranmu, cewa nayi, “Gulman menene haka?”

Umaima ta ce, “kinsan ashe dukan da Umma ta mini wai har da kishi, tana dukana tana surutu ni bana fahimta da yake na jibgu, sai ranan nake jin Abbaa na magana wai saboda ya ce zai auri Maminmu ne, kuma sai ya aure ta.”

Ajiyan zuciya na sauƙe dan na tuna abinda Mami ta yi ranan dan na mata wannan maganan, kallon Umaima nayi na ce, “To ke kina goyon bayan auren kuwa? Dan ni gaskiya ina jin ta Ummu kaman dai bai kamata ba, kar ta ce Mamina ta ci amanarta, dan nima na ji gulman.”

Murmushi Umaima ta yi ta ce, “chaɓ! Ai ba ki sani ba masoyiya, Ummu kam ta amince kuma kaman ma har da shawaranta, nidai wallahi zan so haka, shikkenan mu koma zama gida ɗaya, ba wanda zai hanani zuwa gidan Mami ko miki magana tun da mun zama ƴaran baba ɗaya, kin ga ko aurenmu ma sai Abbaa ya mana tare.”

Murmushi nayi na ce, “ta kwana gidan sauƙi, Allah taimaka ya tabbatar da alkairi, nima zan dage da damun Mamina ayi ma da wuri kowa ya huta.”

Dariya muka yi dukkanmu cikin farin ciki muka cigaba da tafiya, yau ma dai kaman jiya a ƙofan gida muka samu Ya Danish a zaune, ba tare da na kallesa ba na yiwa Umaima sallama na juya na wuce gidanmu, Umaima gaishesa ta yi a storace, amma sai ya amsa bakomai kaman bai ganta tare da ni ba, hamdala tayi ta shige gida.

Ya Danish ci-gaba yayi da kallona har na ɓacewa ganinsa, sannan ya sauƙe nauyayyan ajiyan zuciya a fili ya ce, “jarabawa kenan, ko iya haka Allah ya saka miki abubuwan da nake miki, tun da ga shi kin hanani sukuni kin hana zuciyata nustuwa.”

Ni kuwa ina shigewa gidanmu na samu ba kowa a palourn, ina ƙoƙarin shiga ɗakina aka yi sallama, juyawa nayi na amsa jin muryan namiji, wani ɗan matashi ne, a mutunce muka amsa sai na ce, “wa kake nema bawan Allah?”

Matashin yana murmushi ya ce, “Ko ke ce Hajiya Ramla?”

Kallonsa nayi da kyau, har zan ce a’a sai na ce,.”Eh! ni ce, na faɗa ina murmushi dan kada yayi kokonto.

Washe baki matashin yayi ya ce,.”Daman layinki aka bani, aka ce kina ji da al’amuran lalura tamu ta maza,. shiyasa na zo” ya faɗa yana murmushi.

Murmushi nayi inajin kaman na ɗura masa ashar, amma na haƙura dan naci riban zance, na ce, “To fatan da nauyinka ka zo, ina nufin maganan kuɗi.”

Matashin murmushi yayi ya ce, “Hajiya dubu goma ce da ni a taimaka mini.”

Wani irin gululun baƙin ciki ne ya turnuƙe ni, wani irin kallon banza na zabga masa, tare da fara zaginsa tass!tass!, haka na mishi na faɗa masa baƙaƙen maganganu sannan ba shiri ya juya, nima juyawa nayi ciki kaman taƙaici zai hallaka ni.

Wucewa ɗakina nayi da haushi kaman ya kashe ni, nasan da yasan ni yarinyarta ne, to da shima ƙira na da sunan da na tsana zai yi, duk wani mai zuwa wajan Mami nasan mai zan masa yanzu, dan insha Allah Mamina aure za ta yi.

Abubuwan da zan yi na yi na kwanta, dan haushi ko zuwa gaishe da Mami ban yi ba, balle kuma na kula abinci, baccina nayi ishashshe sai da lokaci ya tafi na tashi, alwala nayi tare da yin sallahn la’asar, fitowa nayi na samu Mami na aikinta, ina tura baki na mata sannu ta amsa.

Mami ta ga yanda nayi kicin-kicin da fiska, sanin halin rigima irin nawa sai bata ce mini komai ba tun da bata san abinda ya faru ba, haka ni kuma na gaji dan kai na naje na ɗiba abinci na ci, ina ci Mami ta murmusa ta ce, “yunwa ai ba pendon mutum ba ne ko gwaggonsa.”

Tura baki nayi ina gamawa na ce, “Mami, ashe Umaima bata da lafiya ne shiyasa bata je makarantar ba, kuma har kwanaki suka yi a asibiti.”

“Ashsha! Subhanallahi! Allah ya bata lafiya, ai ba mu da labari, in Allah ya yarda zan shiga na duba jikin nata, kwana biyu ma Ummunku bata leƙo ba, tun da ta zo ta duba jikinki” faɗin Mami tana aikinta.

“Ameeen Mamina, yauwa Mami mun ji labarin wai za’a manna mana result, a taya mu da addu’a Mami Allah sa mu ga alkairi, daman Alhaji ya ce zai mini kyauta ma” na faɗa ina murmushi dan jira nake kawai ya tambayi abin da nake so, ni kuma na faɗa masa abinda na jima da ƙudurcewa a rai na.

Mami ta ce, “To Allah ya sa ku ga alkairi, mu kuma Allah sa mu ji alkairi, Alhaji kam yana can wata ƙasar ma ai.”

Tura baki nayi na ce, “Ai dai zai dawo Mami, kuma nasan zai mini kyauta na.”

Murmushi Mami tayi ta ce, “To Allah dawo da shi lafiya.”

Da, “Ameen na amsa.”

Hira muka dinga yi da Mamina, amma ko sau ɗaya bata ambato Malam Abbo ba, balle na ji ko ya faɗa mata wani abun, ganin haka sai na share lamarin nima, sai da na taya Mami aiki sannan na shirya tafiya makarantar yamma.

Ɓangaren Ya Danish dai aiki ya kallesa, bai ankare ba sai ga shi wankin hula na neman kai sa dare, yanzu gaba-ɗaya baya da aikin da ya wuce zama a waje yana jiran ganin giftawan Banafsha, ga shi tun zuwansa bata je ko ƙofan gidan su ba balle kuma a kai ga ta shiga, shi abin ma damunsa yake yi, ga shi Abbaa ya tuna masa saura musu sati biyu su kawo mata su yake jira ko ya aura musu ko ma wacece, Umma tun zuwansa ta bi sa da maganan tun da yana da budurwa yayi magana sai a tura, ko kuma ya koma Camaroon ya dubo a cikin yaran yayyunta ko akwai wacce ta masa, amma nan ma Danish yayi shiru abinsa, shi damuwansa kawai rashin sukunin da zuciyansa ke ciki game da Banafsha.

Umaima ta fito a gida ta samu Ya Danish zaune a ƙofan gida, ganinsa sai ba ta yi gigin ko bin hanyan gidan su Banafsha ba, duk da bata kalli ta fito ba, ta juya za ta tafi sai ya ƙira ta, juyowa Umaima ta yi ta ce, “Ga ni yaya.”

Ya Danish ya ce, “Ita mara kunyar ƙawar taki ba za ta je makaranta ba ne?”

Umaima dai a storace ta ce, “Nima ban sani ba yaya.”

Staki Danish yayi, ya buɗe baki zai yi wani maganan sai ga Banafsha ta fito, a ɓoye kada Umaima ta gane ya sauƙe ajiyan zuciya tare da cewa, “To sai ki tashi ku tafi ai tun da ba kya ji, kuma ki tabbatar kin kula sosai.”

Umaima miƙewa tayi a storace ta bar wajan, suna tafiya da Banafsha ta sauƙe ajiyan zuciya ta ce, “Masoyiya ba za ki ce mini sannu ba.”

Taɓe baki nayi na ce, “akan me?”

Hararana Umaima tayi ta ce, “Ba ki ga ya Danish da ya stayar da ni bane, wai tambayana ya ke ba za ki je bane, na ce su ya Danish an fara dawowa hanya, ya fara gane Annabi ya kafu, yanzu zan samu peace of mind, dan yanzu ya zama miskilin dole ma.”

Kafaɗa na ɗage irin ko a jikina ɗin nan, na ce, “shi ya jiyo ” daga haka ban kuma cewa komai ba, har muka isa muka yi karatunmu muka dawo.

Mun dawo ma a ƙofa muka samu Ya Danish, nan kowa ya kama hanyan gidan su.

Da dare muna zaune muna kallo da Mamina sai ta dube ni ta ce, “Faɗima.”

Hankalina na kan kallo na ce, “na’am Mami.”

“Ina son ki bani hankalinki, za mu yi magana mai muhimmanci.”

Ɗauke idanuwana akan TV nayi, na ce, “Ina sauraranki Mamina.”

Gyaɗa kai tayi ba ko alaman murmushi a fiskanta ta ce, “Ina son ki faɗa mini ya kuka yi da malaminki, da ya faɗa miki tasa maganan ke me kika faɗa masa?”

Ni tun da naga Mami bata mini maganan Malam Abbo ba, tun jiya sai na mance da kashinsa ma, amma jin tambayan da ta mini yanzu sai na cunna baki na ce, “Ni ba abinda na ce masa.”

Ƙara tamke fiska Mami tayi ta ce, “Kinsan bana wasa da ke ko? To maza ina sauraranki faɗa mini abinda na tambayeki.”

Tura baki nayi cikin shagwaɓa na ce, “cewa yayi yana so na zai aure ni” ina faɗan haka sai nayi shiru.

“Da ya faɗa miki hakan, sai ke kuma kika ce masa me?” Mami ta tambaya tana jefa mini mugun kallo.

Kaman zan yi kuka na ce, “Mami Allah gaskiya na faɗa masa, ya ce yana so na zai aure ni, sai ni kuma na faɗa masa gaskiya ba aure zan yi ba, ai gaskiya ce Mami, ni ba zan yi aure ba, tun yanzu ana mayar da ni saniyar ware akan jarabawan da Allah ya mini, idan nayi aure dangin miji da miji su dinga gallazawa rayuwata kenan su ma..”

Wani mugun stawan da Mami ta buga mini, shi ya sanya ni yin shiru na haɗiye sauran maganata, cikin tsawa ta ce, “Idan ba ki yi aure ba dan ƙaniyanki me za ki yi? Banafsha ki fita a idona na rufe, kada ki bari rai na ya ɓaci fa zan saɓa miki, idan ba ki yi auren ba so kike na saka ki a gaba kaman television ina kallonki ko kuwa na kwaɗaki a tire kaman kwaɗo na cinye? To ki mai da hankalinki.”

Tura baki nayi, ciki-ciki na ce, “Ni dai ba auren da zan yi, haka kawai a dinga ce mini ƴar mace, a ce mini ƴar karuwa, ni rayuwata gaba-ɗaya ba wani farin ciki kenan.”

Mami ta ce, “Banafsha kinsan Allah zan saɓa miki a kan wannan maganan, ke baki san cewa Allah ma da kansa yana tausayawa duk budurwa ko saurayin da suka mutu ba aure, kuma sun kai yin auren ba, idan ba ki yi auren ba me za ki yi? Me damuwanki da maganan mutane? Banason shashanci da rashin hankalinkin nan.”

Tura baki nayi na ce, “Ni dai ba wani auren da zan yi, aka masta mini kuma shikkenan sai na shiga duniya, daman gado ba karambani ba.”

Ranƙwashi Mami ta mini mai kyau ma kuwa, sannan ta ce, “To zan gani cikinmu wa ya isa da wani, tun da har kin yi girman da ina faɗa kina faɗa, kuma ki tabbatar Inshà Allah tun yanzu za ki fara shirin aure, muddin ya ce yanzu za’a yi auren, to ko bokon ma stayar da ita za’a yi, aure zan miki.”

Kuka kawai na saka ina bubbuga ƙafa, cewa nake, “nidai ba auren da zan yi sai an kai ni wajan dangin babana, su za su aurar da ni, kawai in ana so naji magana nayi biyayya a kai ni wajan dangin babana, ai ba’a jikin bishiya aka ɓanɓaro ni ba, nidai dangin babana.”

Mami ikon Allah ta staya gani, saboda Banafsha dagewa tayi ita sai dangin babanta za’a kai ta sannan ya yarda ta yi aure, numfasawa Mami tayi ta ce, “Banafsha ko kina so ko bakya so za ki yi aure Insha Allah, indai ni ce mahaifiyarki kuma na isa da ke, dangin ubanki kuma kibar maganansu idan ba haka ba zan saɓa miki, zan yi shawara da wanda ya kamata a je neman aurenki wajansa, ke kuma ki saurari Malam Aliyu, idan ba haka ba ni da ke ne, sai na niƙa ki a gidan nan.”

Tura baki nayi na ce, “nidai ko dole za’a mini to a haɗa ni da dangin ubana tukunna, sai an mini abinda nake so sai na yarda, kuma idan ba haka ba sai dai ke ma Mami ki yi haƙuri ki yi abinda kike so nayi.”

Mami wani kallo ta aika mini da shi ta ce, “tashi ki bani waje kamun na karyaki, ai kin girma yanzu wuyanki ya kai yanka, duk maganan da kike so faɗa mini kike yi.”

Miƙewa nayi sumui-sumui na wuce ɗakina, ina shiga na saki murmushi, domin ni ko kaɗan maganan auren Malam Abbo ba baƙin ciki ba ne gare ni, maganan auren Malam Abbo alkairi ne gare ni, domin da wannan batu zan yi ƙoƙari wajan gani lamuran Mamina sun saitu, alhamdulillahi! Daman Allah subhanahu wata’ala ya ce, FA’INNA MA’AL USRI YUSRAH, duk wani tsanani na tare da sauƙi, to yanzu ina ganin na fara tinkaro stanin sauƙi da kuma farin ciki na rayuwata, a haka ina zancen-zuci ina murmushi ban ankare ba, har ɓarawon bacci yayi gaba da ni.

Washegari Lahadi muka je makaranta safe da yamma duka tare da Umaima muka dawo, kuma duk ya Danish na nan yana kallonmu bai ce mata komai ba, ni kuma ko gigin shiga gidan su ban yi ba dan bana ko ƙaunar kallonsa balle haɗa inuwa da shi, stakanina da Mamina kuma bata ƙara mini maganan Malam Abbo ba, illa iyaka da ta ce mini na sauraresa.

Wannan karon Ya Danish bai koma ba har sai washegari Litinin, a hakan ma wai dan Umma tana surutun bata gane ma abinda ke damunsa shiyasa ya shirya zai koma, dai-dai lokacin da muka fito tafiya College shi ma ya fito, ni da Umaima tafiyanmu muka yi za ku nemi mashine, amma sai ya tsaya a gabanmu ba tare da ya juyo ya kalle mu ba ya ce, “ku shigo.”

Kallon sama da ƙasa na yi wa motar sannan na kawar da kai, Umaima jin ya ƙara magana sai ta riƙo hannuna ta ce, “masoyiya ki yi haƙuri mu shiga ya sauƙe mu.”

Hararanta nayi ban ce komai ba, na sake hannunta na yi gaba, Umaima kaman za ta yi kuka, ta kalli Ya Danish ta kalleni, Ya Danish kwallon Umaima yayi tare da yin ƙwafa ya ce, “Sai ku taka da ƙafanku ai” yana gama faɗa yayi gaba da mugun gudu, yana wuce inda nake na ja staki tare da hararansa shi da motan nasa.

Umaima da ɗan sauri ta iskoni tana faɗin, “Masoyiya mu godewa Allah yanzu ya sha nistojin ya daina bala’i, idan ba haka ba ai da tuni ya shuka mana, ke ma me ya sa za ki ƙi shiga?”

Hararan Umaima nayi na ce, “banason magana ki ƙyale ni, tun da dai naga ban hanaki shiga ba ke da motan yayanki, aikin banza aikin wofi, kina wani cewa na shiga sai ka ce baki san irin abinda yake mini ba, ko da ya ke ba laifinki ba ne, daman aka ce naka sai naka, ni bare ce stakaninku.”

Umaima dariya tayi sosai ta ce, “rai na bai ɓaci ba sai ki fama, anji ɗin ke bare ce, mutum sai ka ce kububuwa, rashin kirkin naki yau ni za ki yi wa kenan? To Allah huci zuciyanki.”

Hararanta nayi na ce, “oho muku ke da yayanki, kuma dan ki ji mun ɓata ma kowa yayi hanyansa.”

Murmushi Umaima ta yi ta ce, “Daman wallahi kaman kin san zaman lafiyanmu yayi yawa, ana ƙawance ana ɓatawa ya fi daɗi da ƙargo, amma kullum ni baki haƙuri, ke kuma yin haƙuri, ya kamata ai ko casuwa mu dinga yi, ko da yake ai ma Ummu ta ce mun yi dambe da muke yara, amma ni nake saka ki kuka.”

Dariya maganan Umaima ya bani, dan haka na dara muka tari mashine muka wuce makarantar, muna zuwa muka ci karo da kyakkyawan labari, an manna dodon bango, Umaima ta damu mu je mu gani, amma na ce ta bari ba yanzu ba, tasan yanda muke ƴan sturut ɗin nan sai a maste mu ko a cika mana ciki da warin hammata, ga kuma wani na stamin zafin da ake yi.

Sai da aka tashi sannan muka samu ganin result namu, amma duk da haka ba mu muka duba ba, dan duba mana aka yi, alhamdulillahi dukkanmu result yayi kyau yanda ake so Masha Allah.

Muna komawa kowa yayi gidansu, da farin ciki na faɗawa Mami, har da ɗagani Mami tayi dan farin ciki, saboda result yayi yanda ake so, sai godiya ga Allah.

Haka muka cinye wannan satin ma cikin farin cikin kyawun result namu, sannan a hadda an fara bitan karatun musabaƙan da za mu yi a cikin jimeta da sauran makarantu na local government’s ɗin Adamawa State, tsakanina da Malam Abbo kuwa yanzu ina sauraransa amma dai bana sake jiki da shi sosai, dan har yanzu ina kan bakana kar abu ta kwaɓe gaba ya ce na cutar da zuciyarsa ko kuma na yaudaresa, akwai abu guda da ke burgeni da Malam Abbo, sam-sam a makaranta baya nuna ma akwai wani alaƙa na daban stakaninmu, Malami da ɗalibarsa kaman baya haka muke, kuma ba ya zuwa zance sai ranan Lahadi ko kuma Alhamis, da yake ba mu zuwa makaranta ran Alhamis, sam-sam ba ya takura mini, tun da ba ni da waya, ta nan ɓangaren ma ba ya takura mini.

Tun da na fara sauraran Malam Abbo, sai kuma wani shaƙuwan ta shiga tsakanimu, mastayinsa da kiman da nake basa kullum ƙaruwa yake yi, Malam Abbo ya iya soyayya yan da ko wacce mace za ta buƙata, kuma yana ƙoƙarin mini nasiha da tunatar da ni rayuwa, alhamdulillahi sai fatan alkairi stakaninmu.

Har aka cinye wannan hutun ƙarshen makon Ya Danish bai zo weekend ba, muka shiga wani satin wanda a wannan weekend ɗin wa’adin da Abbaa ya ba su zai cika, da kuma wa’adin da ya bai wa Mamina na ta yi tunani, har juma’a ta yi ba Ya Danish ba alamansa, dan haka Abbaa waya ya ɗaga ya ƙirasa, sai da ya sollesa tass sannan ya faɗa masa ya zo ko ransa yayi mugun ɓacuwa, ba shiri ya Danish ya shirya ya kamo hanyan zuwa.

Da ya ke Umaima ta yi zazzaɓi kwana biyu, sai Mami ta shirya da yamma bayan an yi la’asar ta shiga gidan su Ummu, da sallama ta shigo gidan, ta samu Ummu zaune a palour tare da Ya Farooq, cikin fara’a ya Farooq ya gaishe da Mami ta amsa, sannan suka gaisa da Ummu, tana murmushi ta ce, “Mamin yara sai yau aka samu daman leƙo gidan namu.”

Murmushi Mami ma tayi ta ce, “ai gidan naku ne yana neman fin ƙarfin shiga na, yanzu ma dai yarinyata na zo dubawa da jiki shiyasa.”

Dariya Ummu ta yi ta ce, “Mu da muke addu’an a shigo din-din-din, ina wanda ya isa ya ce ba za ki shigo ba.”

Yaƙe kawai Mami tayi ta ce, “Ina yarinyar tawa?”

Ummu ta ce, “ai Umaima ta ji sauƙi Mamin yara, ina ga tana sallah ne ma, da yanzu kin gan ta…” Ummu bata gama rufe baki ba sai ga Umaima ta fito tana murmushi, ta buɗe baki ta ce, “Mamina ayoyoo, sannu da shigowa…”

Umaima bata gama magana ba, ta stinkayo muryan Umma na faɗin, “kika ƙara faɗan wani kalma ran ki zai ɓaci, wuce ki koma ciki, shashashan yarinya kawai.

Daga Ummu har Mami da Ya Farooq duk da kallo suka bi Umma, Umaima rau-rau ta yi da idanuwanta kaman za ta yi kuka, wani kallon Umma ta jefe ta da shi ta ce, “koma ciki na ce.”

Umaima juyawa tayi ta koma ciki, Ya Farooq dai da mamaki yake kallon Umma, ƙarshe tashuwa yayi ya fice dan baison ganin abin kunya.

Mami murmushi tayi kaman ba komai ta ce, “Umma Kabeer barka da yamma, ya jikin Umaiman?”

Wani irin kallon banza, kallon stana Umma ya jefawa Mami tare da sakin dogon tsaki ta ce, “Munafuka kawai, wato kin biyo mu har gida ki ƙwace mijin namu, amma tun da yake ke ɗin ƴar bariki ce dole ki lauye da duba yarinyata, to ba’a buƙatan gaisuwan an yafe miki, tashi ki fice mana a gida, ƴar ƙwace kawai.”

Mami murmushi ta kuma yi ta miƙe tare da kallon Ummu ta ce, “Ummun su sai anjimanku, Allah ƙara sauƙi.”

Ummu nauyayyan ajiyan zuciya ta sauƙe ta ce, “ki yi haƙuri Mamin yara, ke kuma Maman Kabeer gaskiya abin da kike yi bai kamata ba.”

Umma a hasale ta hayayyaƙo wa Ummu ta ce, “To babbar munafuka algunguma, an faɗa miki duk abinda ke faruwa ban sani ba ne? Wallahi can ya ƙare miki a maste-mastinki, ƙarya kike a auro wata balle ki samu daman haɗe kai da wata a gidan nan.”

Murmushi Ummu ta yi ta girgiza kai tare da cewa, “shi dai kishi ba hauka ba ne, dan haka kisan me ke fita a bakinki, kada ki ga ina miki shiru, ba storonki nake ji ba, gudun tashin hankali nake yi, kuma Insha Allah sai ya aurota.”

Umma na ƙoƙarin yin magana sai Mami ta yi saurin taran numfashinta ta ce, “Dan Allah kuyi haƙuri dukanku, in Allah ya yarda ma ba abin da zai haɗa ni da mijinku balle wannan tashin hankali ta faru, kuma ni ban shigo dan haɗa ku faɗa ba, dubiya na zo yi kuma na yi zan tafi Allah ƙara sauki” Mami na gama magana ta juya ta fice a gidan, cikin damuwa, ita ko ta rasa mijin aure me ya kai ta haɗa hanya da Umma, balle har su haɗa miji, ita auren da ma gaba-ɗaya babu shi a lissafinta.

Umma kuwa da harara ta bi Mami da shi har ya fice a gidan, sannan ta juyo ga Ummu ta ja staki tare da cewa, “aikin banza aikin wofi, kuma wallahi dan ki ji ba gwaninta kika yi ba, tunda abin ba ni kaɗai ta shafa ba, miji nawa ne kuma naki.”

Ummu murmushi tayi ba tare da ta tankawa Umma ba ta shige ɗakinta, tana koɗa halin kishi irin na Umma.

Mamina ko da ta koma gida, ɓoye damuwanta ta yi, ban ga alama ba kuma bata sanar da ni ba, ɓangaren su Ummu ma ba wanda ya yiwa Abbaa maganan abin da ya faru, Umaima dai ba yanda ta iya da halin Umma, ko mene mahaifiya ce dole ta ji magananta.

Washegari asabar sai ga ya Danish da sassafe, sai da Abbaa ya dawo sannan suka zauna shi da Ya Danish, Ya Farooq da kuma babban yaya.

Abbaa ne ya fara magana ya ce, “Farooq da Danish na baku lokaci, kuma ga shi lokacin kun cinye sa murƙus, ba wanda ya bani amsa mai kyau a cikinku, hukuncin nawa kuke so na zartar ko?”

Danish ƙasa yayi da kansa yana sosa ƙeya, shi kuma Farooq murmushi yayi, sai yaya babba ya ce, “A yi haƙuri a ƙara musu lokaci Abbaa, kasan yanzun lamarin daga matan har mazan sai a hankali.”

Wani kallo Abbaa ya yiwa yaya babba ya ce, “To ubana ba zan ƙara musu lokaci ba, kai da kake da mata yanzu baka jin ka cika mutum, baka jin wani nustuwa ta daban? Ai duk namijin da ya kai riƙe mata muka ba shi da ita, to ba’a niste yake ba, kawai a gansa haka ne a ƙyalesa, an faɗa maka gauranci daɗi ne da ita? Balle kuma ga wanda ke ƙoƙarin ƙewata ƴar mutane mutunci, to ba lokacin da zan ƙara musu, ko su fidda mata aje a tambayo musu ko kuwa ni da kai na nayi musu matan, idan ma idanuwansu sun makance ne, to nawa a buɗe suke tarr! Ai duk cikinsu ba wanda zai ce ba shi da budurwa, to ba za’a yaudari yaran mutane da ni ba dan haka kun ji me na faɗa ai, babu ɗaga ƙafa.”

Ya Farooq ƙasa yayi da kai ya ce, “Abbaa ni dai ina jira ne daman ka ƙira mu, amma mun gama magana da wacce nake nema, iyayenta kuma sun ce na turo manyana daman.”

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce,”To ka taimaki kan ka, inba haka ba kuwa za ka ga yanda ake yiwa namiji auren dole, to kai kuma Malam Danish ina sauraranka ya muke ciki? Ka samu ne ko na bada sadakanka?”

Daga Abbaa da yayi maganan, har su yaya babba ba wanda maganan bai sa dariya ba, ya Danish sosa ƙeya yayi ya ce, “Abbaa nima dai na ba da kai na sadaka wa wata.”

“To Masha Allah! Duk Allah ya muku albarka, kun taimaki kan ku” Abbaa ya faɗa yana murmushi.

Yaya babba ya ce, “To sai ku faɗa mana yaran gidan waye ne, dan a shirya maganan zuwa magana da iyayensu.”

Ya Farooq ya ce, “Sunanta Ruƙayya gidansu na anguwan Kaban.”

Abbaa jinjina kai yayi ya ce, “Madalla! Allah tabbatar da alkairi, kai kuma Danish fa.”

Danish sosa kai ya fara yi, yana in-ina, “uhmñ…umn..am..dama…daman ba..am Abbaa dama dai ni ba wai mun dai-daita da ita ba ne, izini za’a nema mini tukunna.”

Kallonsa Abbaa yayi ya ce, “To malam Danish, masu bin starin addini yanda ya kamata, hakan ma yayi ai Allah muku albarka, wacece, in ya so gobe ko jibi sai a tambayo maka.”

Danish ƙasa yayi da kai ya ce, “am Faɗima ce, ina…ina..ina nufin Banafsha.”

Ba iya Abbaa ke kallon Danish da mamaki ba, hatta ya Farooq da babban yaya kallon mamaki suke bin Danish da shi, gani suke dai kaman bai san abinda yake faɗa ba, kamun Abbaa yayi magana tuni yaya babba ya ce, “Amma dai Danish baka san sunan wa ka ƙira ba ko? Banafsha dai kake nufi ƙawar Umaima, yarinyar Mami?”

Abbaa ya ɗaura da cewa, “Banafsha da ka mayar da ita kuran wasanka ƴar gidan amaryan da zan aura Ramla, ita kake nufi ko wata daban?”

Maganan Abbaa duk dariya ya basu wai ƴar gidan Amaryan da zai aura, amma suka maste kawai suna sauraran Danish, shi kuma cikin tabbatarwa ya ce, “Ita dai Abbaa, ka yi haƙuri, wlh ita nake so.”

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce, “riƙe haƙurinka idan ka je wajanta zai maka amfani, ni ai mai farin ciki da hakan ne, zan yi addu’an Allah tabbatar da alkairi, Uba ya auri uwa, ɗan sa ya auri yarinya, Masha Allah, in Allah ya yarda zan yi magana da ita idan na je zance.”

Ya Danish murmushi yayi yana addu’an komai ya zo da sauƙi, shi ya rasa irin Soyayyan Banafsha da ya mara diran mikiya, ya Farooq dai mamaki yake har yanzu, yana kuma tunanin yanda za’a kaya da Umma idan ta ji wannan magana, yaya babba kuma dai kallon Danish bai san abinda yake ba yake masa, saboda ko shi da yake namiji idan aka ce shi ne suka wannan ƴar stama da mutum to ba zai yarda ya so shi ba balle aure, lallai akwai aiki a gaban Danish, haka zaman nasu ya waste bayan sun ɗan tattauna abubuwan da ya kamata.

Ya Danish washe-gari da sassafe ya bar gari baya son ma ya haɗa ko ido da Umma, dan yasan idan ta ji labari to akwai yin ta, amma bai da mastala tun da Abbaa ya yarda kuma zai tsaya masa, yanzu a yanda yake ji ba abinda ba zai iya yi ba akan soyayyan Banafsha, Allah-Allah yake a tambayo masa ya fara zuwa ya samu ya kori wannan saurayin nata, shi ana tambayo masa to kusan kullum sai an gansa a Mubi.

Ranan Lahadi kaman kullum Malam Abbo ya zo muka sha hiranmu, ya ce zai turo amma na ce masa ya dakata tukunna, haka ya haƙura ba dan ya so ba, Mami ta ƙira mini Alhaji mun gaisa na faɗa masa result na yayi kyau, ya tambayi abinda nake so, amma na ce sai ya dawo, idan ya zo zan faɗa masa, haka muka yi sallama akan ba zai wuce wata guda ba zai dawo, Mamina kuwa ko da ta ƙara mini maganan aure to abin da na faɗa mata ranan shi na maimaita, sai kuma ta koma lallashina ganin na dage.

Mun ci-gaba da zuwa makaranta boko da tahfiz tare da Umaima har yau da ta kama Alhamis, da yake ba mu da class da safe, to ba mu je da wuri ba, sai wajan ƙarfe goma muka bar gida muka tafi College.

Abbaa ya ƙara wa Mami sati guda akan watan da ya bata, to yau Alhamis ya yanke ranan juma’a zai je wajan Mami, sai ya ce bari ya sanar da su Umma maganan auren Danish dan su san da shi, don abun ya yiwa Abbaa daɗi ko ba komai hakan ma zai ƙara nistar da Umma.

Ƙiran Umma da Ummu Abbaa yayi, gyaran murya yayi ya ce, “Sai ku fara shirin da ya kamata, na tarban abokiyar zamanku, da kuma matan yaranku, zan faɗa muku ne na fita haƙƙinku ba wai dan dole ne sai na faɗa muku ba, Farooq ya samo mata a nan anguwan Kaban, sai kuma Danish a nan gida ya samu tasa matar, Faɗima yake so, kun ga abu ya zo gidan sauƙi, tuwo na mai na, ni ina son uwa, yarona kuma yana son yarinyar, dan haka ina gargaɗan ku da yin tashin hankali, Sabeera wancan karon ki daka mini yarinya akan kishinki na hauka, kina ga na zuba miki ido ban ɗau mataki ba, kin ɗauka banza kika daka ba, to zan ɗau mataki, kuma kika yi wannan karon to matakin da zan ɗauka zai baki mamakin da ba ki taɓa zato ba, aure ba gudu ba ja da baya daga ni har Danish Insha Allahu, indai Allah ya nufa to sai mun aure su.”

Ummu da mamaki take kallon Abbaa, ta ce, “Danish dai ke son Banafsha? Anya ka ji da kyau?”

Abbaa jinjina kai kawai yayi bai ce uffan ba.

Umma kuwa saboda haushi ma ta kasa cewa komai, miƙewa tayi ta fice, Abbaa kuma taɓe baki yayi bai ko stayar da ita ba, dan yanzu halin Umma ya fara gimsarshi, Ummu kallon Abbaa tayi ta ce, “kana ganin hakan ya dace? Ba za’a ja wa yarinyar nan mastala sosai a rayuwanta ba, a yanzu ma kusan kullum cikin kuka take da damuwa da mahaifiyarta, idan aka mata irin wannan auren kana ga yayi? Ni bana tunanin ma daga ita har mahaifiyarta za su amince da wannan batun, duk da babu wanda yasan abinda ya faru ranan.”

Abbaa murmushi yayi ya ce, “ke dai ki ce Allah tabbatar da abinda ya ke alkairi.”

Ajiyan zuciya Ummu ta sauƙe, ta ce, “Ameen summa Ameen.”

Umma tana shiga gida ta shige ɗakinta, gabas da yamma kudu da arewa ta rasa me za ta yi ta huce, ta rasa wani mataki za ta ɗauka, wai yau Danish da ke goyon bayanta ne ya kwaye mata zani a kasuwa, ya rasa wa zai so sai fistararriyar yarinyar nan, tana fama da Umaima ta raba su, sai kuma shi ya kawo magana mai gaba-ɗaya, maganan aure, to ba zai saɓu ba, dole ta ɗau mummunan mataki, wayanta ta ɗauka ta dannawa layin Danish flashing, saboda cherge’s na international call to sai dai ta yi flashing ba daman ƙira.

Ya Danish a nasa ɓangaren daman ya jima yana stumayen ƙiran Umma, dan haka yana ganin flashing nata ya biyo ƙiran, Umma na ɗauka bata saurari ko sallaman da yake yi ba ta ce, “Danish ni za ka tozarta? Ni za ka nunawa kai ɗan yau ne? To wallahi idan kaga ka auri yarinyar nan to ko bayan rai na ban amince ba, sai dai ka mutu babu aure.”

Danish ajiyan zuciya ya sauƙe ya buɗe baki zai yi magana, sai Umma ta dakatar da shi ta ce, “Idan ka kuskura ka ce mini wani abu, to wa billahil Azeem ranka zai ɓaci, kai ka san halina fiye da kowa, to kada ka yarda rai na ya ɓaci..”, Umma na gama masifanta ta kashe wayanta tana huci.

Haka Umma ta wuni da bala’i da masifa, abin na cin ta kwata-kwata ta kasa haƙuri ta kasa nistuwa, har yamma ta yi ta kasa haƙuri, wani abu ke ingiza ƙeyanta zuwa gidan Mami.

Yau har ƙarfe shida ta same mu a makaranta, sai da ta ɗora da mintuna sannan aka tashe mu, muka kamo hanya muka dawo gida, Umaima ta wuce nasu nima na wuce namu gidan.

Muna zaune da Mamina bayan sallahn isha’i sai kawai ganin mutum muka yi a kan mu ba ko sallama, daga ni har Mamina da mamaki muke kallon Umma Sabeera, dan nidai a iya sanina ban taɓa ganin ta shigo gidan mu ba.

Kamun Mami ta yi wani yunƙurin buɗe baki tayi magana sai gani muka yi Umma Sabeera ta fito da wuƙa, ta yi kan Mamina gadan-gadan, ihu na stala na yi kan Umma ina faɗin, “Me muka miki? Kashe mu za ki yi Umma? Dan Allah ki yi haƙuri.”

Umma tureni gefe tayi tana faɗin, “Wallahi idan ke mayya ce yau sai na kashe ki kowa ya huta, idan ya so nima a kashe ni, haba dan Allah kin dameni kin addabeni kin staya mini a maƙoshi, abun ya wuce na aure mini miji da za ki yi, ya koma har yarona kuka lashewa zuciya yana son yarinyarki, to indai ina raye ko aure ɗaya ba zai ƙullu ba, wallahi ba za mu haɗa jini da karuwa kuma mayya ba.”

Mami ƙoƙarin kare kanta take yi, amma Umma ta zuciya sosai, ƙoƙarin caka mata wuƙan take a ƙirji, suna kokowa har dai Allah ya bawa Umma nasaran caka wa Mami wuƙa a ciki, ihun da Mami ta yi shi ya tattaro mini sauran ƙarfin jikina, da kumburarren goshi na mike, na rarumi tire a gefe ba ƙwalawa Umma a kai, faɗuwa ta yi, ga Mami a kwance cikin jini ga kuma Umma a kwance a sume, ihu na kuma saki na fice a gidan da mugun gudu, cikin anguwa na yi ba hijabi ganin ba mutane sai na juya gidan su Umaima, a bakin ƙofa na ci karo da Abbaa da ya fito saboda ihuna da yake jiyowa.

Kasa magana nayi sai kawai nuna masa gidanmu nake ina faɗin Mamina, ina kuka, Abbaa bai tsaya tambaya na ba yayi gidanmu, muna shiga ya ga halin da Umma da Mami ke ciki, bai tsaya tambayan ba’a si ba ya fice, tare da ya Sadeeq suka shigo, Mami kawai suka saka a mota, nima Ya Sadeeq ya ja hannuna na shiga muka nufi asibiti, Abbaa ran sa a ɓace ko kallon Umma bai yi ba, General hospital Mubi muka nufa.

*****

CAS Bunayd suna tafiya yana jan staki ganin irin lokacin da suke ci, tafiya ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, har sai bayan isha’i suka shigo mubi, hamdala yayi, sannan aka wuce da shi direct General hospital na mubi.

<< Yar Karuwa 14Yar Karuwa 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×