Skip to content
Part 16 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Noted: Afuwan fan’s, mastayin Bunayd na Air Force ba CAS bane, wato Chief of the air staff, mastiyinsa ACM ne, Air Chief Marshal, a yi haƙuri da mistake ɗin, shi CAS a land army ne, ACM ne Air Force, kuma Bunayd Sojan sama ne Air Force kenan, abin ne da rikitarwa sorry for the mistake.

Driver na parking, Bunayd ya fito a rikice, amma idan ka kallesa ka ranste ma rigima yake ba’a cikin damuwa yake ba, amma kuma shi ya san damuwan da yake ciki na abinda ya samu Abeed, cikin hanzari suka shige ciki, sojan da ke tare da Abeed ne ya musu jagora har ɗakin da Abeed ke ciki, ya so shiga amma kuma aka tsayar da shi, sakamakon taimakon gaggawa da ake kan bai wa Abeed ɗin.

ACM Bunayd stayuwa yayi a bakin ƙofan ya na safa da Marwa, da ya kasa haƙuri sai ya juya kawai, dai-dai lokacin kuma ya samu kuma ana rikici tsakanin Nurses da wata kyakkyawar matashiyar budurwa, da ke rikice kaman wata mara ishashshen hankali, taɓe baki yayi zai fice sai idanuwansa suka sauƙa akan mara lafiyan da ke kwance a gadon ɗaukan marassa lafiya, ɓata rai yayi ya nufe su gadan-gadan.

Banafsha tun barowansu gida kuka take yi, Abbaa saboda ɓacin rai ko magana ya kasa yi, sai ya Sadeeq ne ke ƙoƙarin bata baki akan tayi haƙuri, amma ta ƙi shiru har suka isa General hospital ɗin.

Abbaa kuma layin babban yaya ya ƙira, yana ɗauka Abbaa bai tsaya amsa sallaman da yake masa ba ya ce, “kabeeru ka je gidan Mamin Banafsha ka ɗau uwarku, kuma kar ka kuskura ka shigar mini da ita gidana, idan ƙafanta ya taka gidana ko gawanta ne, to ban yafe maka ba, kuma kuna farfaɗo da ita ta kwana cikin shiri dan ƴan sanda suna hanya.”

Babban yaya cikin tashin hankali ya miƙe, daman yana wajan aikinsa ne, gareji yake yi, cewa yayi, “Abbaa me ya faru? Me ya kai Umma gidan Mami?”

Guntun tsaki Abbaa ya ja, ya ce, “kana tambayana ne, ni na san irin haukan da ke damun uwarku, to dai ka ji abinda na ce, mu yanzu haka ma muna general hospital”, Abbaa bai jira me babban yaya zai ƙara faɗa ba, kawai ya kashe wayansa yana yin ƙwafa kawai.

kusan tare motan su Abbaa suka iso da su Bunayd, Bunayd suna shigewa, su Abbaa kuma cikin gaggawa aka ɗauko gadon ɗaukan mara lafiya aka ɗaura Mami a kai, suna shiga ciki Nurse ɗin ta dube su ta ce, “kunsan ba’a attending irin waɗannan patient’s ɗin sai da police ko?”

Abbaa ya ce, “Ku yi haƙuri ku fara ceton rayuwanta baiwar Allah, police kam dama dole ne ku gan su, dole su shigo cikin lamarin nan.”

Ya Sadeeq dialing layin Ya Farooq yayi amma ba ya shiga, dan ya Farooq ma a general hospital ɗin yake aiki, Banafsha cikin shessheƙa ta ce, “Dan Allah dan Annabi ku taimaka ku fara bata agajin gaggawa tukunna, ai an ce muku police ɗin za su zo.”

Magiyan duniya su Banafsha sun yi, amma amsa guda Nurses ɗin ke basu, ba’a amsan irin wannan mastalan ba tare da police ba, domin yan da mace-mace ke yawa ana ɗaure likitoci basu ji ba kuma ba su gani ba to dole sai da shedan police, dan ko ma mene ya biyo baya to dai ba za’a ga laifin likita ba balle har a ɗaure sa, Abbaa ransa ne yayi mugun ɓaci, dan haka ya sa Ya Sadeeq ya dubo musu wani likita abokin ya Farooq, Abbaa kuma ya ɗau waya ya ƙira babban yaya ya kuma faɗa masa ya turo musu police tukunna.

Banafsha fa ta ƙulu ta kai wuya cikin karaji da masifa ta fara balbala bala’i, cewa take, “Amma dai wallahi ku kam an yi marassa imani, marassa tausayi, asararru kawai, daman dan uban me kuka yi karatun naku, kuma aka baku daman aiki a asibiti, gomnati ta gina asibiti kuma ta ɗauke ku aiki, take biyanku albashi, ba duk dan al’umma ba? To in Allah ya yarda Mamina ba abinda zai sameta, shegu, munafukai, marassa imani, ƴan uwan fir’auna kawai, kuma nima zan zama likitan nan, aka kawo mamanku duk ni da kai na zan ƙarisa su….” masifa kawai Banafsha ke yi, kaman wacce aka aiko daga sama, Abbaa sai tausanta yake amma ta ƙi yin shiru, kuma a dai-dai lokacin Bunayd da ya ga duk abinda ke faruwa, ya iso wajan rai a ɓace.

ACM Bunayd ko kallon inda Banafsha ke masifanta bai yi ba ya kalli Abbaa, a ɗan daƙile ya ce, “sorry Sir! Za’a dubata yanzu.”

Shi da kansa ya tura gadon Mami, sai sauran sojojin suka zo da gudu suka amshi gadon suka tura, likitan da ke duba Abeed ne ya fito, ganin su da wata patient ɗin, take ya saka aka kai ta ɗakin ba da agajin gaggawa ba tare da ya tambaya ba ko ya ce wani abu.

Abbaa kaman zai rungume Bunayd ya ce, “Allah maka albarka likita, mun gode, Allah saka da alkairi ya rufa asiri duniya da lahira, idan ana samun irinku a likitoci ai ba wanda zai mutu saboda irin haka, sai dai in lokacinsa ne yayi, Mun gode bawan Allah” Abbaa ya faɗa dan duk ɗaukan sa Bunayd irin likitoci masu taimako da tausayin nan ne.

Bunayd murmushin da ko leɓensa bai kai ba yayi ya ce, “Ba komai Sir, your welcome.”

Banafsha tun da aka yi gaba da gadon da Maminta ke kai sai ta kuma ƙaro sabon walaƙanci, duban Nurses ɗin ta yi ta ce, “Munafukan Allah to ahirr ɗin ku za’a duba Mamina, kuma ba ɗan banzan police ɗin da za mu ƙira balle kuma Soja, ƴan baƙin ciki kawai, so suke na zama marainiya gaba da baya ba uwa ba uba, to ta Allah ba ta ku ba…” Masifanta ta ci gaba da yi har ta ƙarisa wajan su Abbaa.

Duk abin da Banafsha ke faɗa a kunnen Bunayd yana ji, surutun nata bai dame sa ba tun da ya saba da na ƙannensa, amma maganganun nata ma dariya yake basa, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kai kaman bai kalleta ba yana yastina fiska, ba tare da ta masa godiya ba ta wuce su ta ƙarisa ƙofan ɗakin da ta ga an shigar da Maminta, bata hango kowa a ciki ba sai Maminta, juyawa ta yi kuma kaman za ta yi kuka ta ce, “Abbaa ka ga mugaye, su ma ba dan Allah suka karɓe ta ba, ga shi sun ajiye ta ita kaɗai, so suke ta mutu, wayyoo ba’a ƙaunata ana son Mamina ta mutu.”

Abbaa ƙarisowa yayi wajanta ya ce, “ki yi shiru Faɗima, wannan likita mai mutuncin ya sa za’a dubata kin ji.”

Banafsha kwaɓe fiska ta yi ta ce, “tun da dai ba zai duba Mamina da kan sa ba, to ba shi da wani mutunci shi ma, shi ɗin banza, to ya duba ta da kansa mana indai da gaske yake yana da imani kuma shi na gari ne ba kaman sauran ba, ni wallahi ba za’a yaudareni a banza ba a bar uwata ta mutu ba, aikin banza daga shi har sauran har Umma duk in Mamina ta mutu sai na yi Shari’a da su, ko kuma na bi rana na kashe su, bin dare ma ai storo ce, ni da ranan Allah ido na kallon ido zan ƙaddamar musu.”

Tana rufe baki sai ga likita ya iso wajan da sauri, bai shiga ɗakin da Mami ke ciki ba ya wuce inda zai kai sa ɗakin da Abeed ya ke, da sauri Bunayd ya stayar da shi, cikin turanci ya masa magana akan tun da sun yi aikin Abeed ɗin su duba matar mana kada a rasa ta.

Likita duban Bunayd yayi ya ce, “sorry Oga, an mata abinda ya kamata, raunin nata ba sosai bane, idan muka gama da shi za’a dubata.”

Kamun Bunayd ya buɗe bakin ba da amsa, tuni Banafsha ta diro a gaban likita idanuwanta rufe ta ce, “wallahi ƙarya kake, maƙaryacin likitan da bai san aikinsa ba, wuƙa aka yage Mamina da shi, kuma ka ce raunin ba sosai ba ne, kai kasan jinin da ya fita a jikinta ne ma, wa ma ya sani ko har kayan cikinta sun yanyanke, to nima ɗalibar malaman lafiya ce, ina College kuma ina last year, dan haka kada ka wani faɗa mana ƙarya mun san me ne a aikin muka, kuma ba inda za ka tafi idan ba ka shiga ɗakin da aka kwantar da Mamina ka duba ta ba.”

Daga likita har Bunayd baki suka sake suna kallon ikon Allah, ganin yanda budurwan ta dage da masifa iya ƙarfinta, likitan ya kasa haƙuri sai da ya dara ya ce, “To masifaffiyar likita, tun da kinsan komai kuma kin kusa gama College sai mu baki kayan aiki ki duba Momin taki ko.”

Banafsha sai kuma ta shagwaɓe ta ce, “dan Allah duba Mamina ka ƙyale wancan ɗin, ai shi ma ka duba sa, ka koyo adalci mana likita, ai in ba ka practicing to ba za ka iya riƙe mata biyu ba, kawai Mami ma s dubata tun da shi ma an duba sa.”

Bunayd bai kalli Banafsha ba, amma yana sauraranta, ji yake kaman ya kwanta a ƙasa ya ta dariya har cikinsa yayi ciwo, wai ai ta kusa gama College ita ma likita ce, murmushi yayi har sai da haƙoransa suka bayyana, sannan ya kuma magana da turanci ya ce, “ka turo wani likitan ya duba ta, please a yi a gama da Captain namu dan transfer muke so a mana zuwa Kano.”

Banafsha ma ta ƙi kallon Bunayd, likitan take kallo ta ce, “wallahi ban yarda ba, ni kai ka mini, kai nake so ka duba Mamina, wani likitan ya je ya duba Captain ɗin nasu, tun da ba mu na Captain namu bane, ni Mamina ce Captain tawa.”

Bunayd murmushi ya kuma yi tare da yi wa likitan magana da ido, sai ya juya wajan Abbaa da yayi poster yana ganin ikon Allah, Abbaa bai taɓa sanin haka Banafsha take ba sai yau, Bunayd murmushi yayi ya ce, “ina so za mu yi magana Sir.”

Abbaa gefe suna yi da Bunayd, ya ce, “Ina sauraranka likita.”

Bunayd kiston kan sa ya shafa ya ce, “Sir ni ba likita ba ne, ni Soja ne, muma mun kawo wani ɗan uwanmu ne ya samu hatsari.”

Abbaa baki ya buɗe ya ce, “Ai ko na ji, amma dai kai a sojojin ma daban kake, ai ko likitoci ka fi su imani da tausayi, Allah kuma ya basa lafiya, ka yi haƙuri da shirmen Faɗima, ba haka take ba kawai abinda ya samu mahaifiyarta ne ya rikita ta haka.”

Bunayd cewa yayi, “Ba komai..”, zai yi magana sai ƙira ya shigo wayan Abbaa, haƙuri Abbaa ya bai wa Bunayd sannan yayi picking, “ina cikin asibitin kuna ta ina?” Faɗin Abbaa da ke kare da waya a kunnensa.

Yaya babba ya ce, “Abba ka fito bamu san a ciki ta ina ba.”

Abbaa ya ce, “To ganinan”, yana faɗa ya kashe wayansa, sannan ya dubi Bunayd ya ce, “bawan Allah bari na zo, Yarona ya taho da polisawan ne.”

Bunayd gyaɗa kai kawai yayi ya juya wajan likitan.

Likita dan dolensa sai da ya shiga ɗakin da Mami ke kwance, sannan ya fito ya tafi ɗakin da Abeed ya ke, jaraban masifan Banafsha dariya ma yake basa, sai ya ji ta burgesa.

Bunayd bayan ya je office na likitan, bayani ya masa dangane da Abeed, akan sun yi duk abin da ya kamata, gobe ma za su iya ɗaukan sa su tafi Kano ɗin, harbin bai yi muni sosai ba a cinya ne kuma an cire alburushin, sai su ƙarisa jinyan a asibitin Kano, dan zai fi samun kulawa sosai ma, Bunayd hamdala yayi, sannan ya ce, “likita wannan matar fa?”

Murmushi likitan yayi ya ce, “Ni da farko na ɗauka ma ai duk tafiyanku guda, sai da masifaffiyar likita ta yi bayani” likita ya faɗa yana murmushi.

Bunayd murmushi shi ma yayi dan ya tuna kalaman Faɗima, kaman yan da ya ji sunanta a bakin dattijon ɗazu, cewa yayi, “likita, ita ya nata condition ɗin? Komai zai tafi dai-dai a nan ko ita ma a sanja mata asibiti, ko da a cikin Yola ne.”

Murmushi likitan yayi ya ce, “a’a Oga, ita matar fa kaman yan da na faɗa raunin nata da sauƙi, anyi niyan caka mata wuƙan a ƙirji ne, amma sai ya kauce ya kar ci cikinta, bai ma shiga sosai ba, sai dai daman abin da ya sa muke so a ce sun zo da police saboda maganin samun mastala ne, ya kamata wanda ya mata haka a hukunta sa, dan gaskiya kasheta aka yi niyan yi, amma aka bar ta a nan asibitin ma komai zai tafi dai-dai, in Allah ya yarda za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu muyi duk abinda ya kamata.”

Bunayd gyaɗa kai yayi ya ce, “good, Allah bata lafiya” yana gama magana ya sallami likitan ya fita, lokacin dare ta yi sosai-sosai.

Abbaa ma bayani ya yi wa polisawan, suka samu likitan shi ma ya musu bayani, sannan ya faɗa musu Soja ne ya shiga lamarin shiyasa ya amshe ta ma, samun Bunayd suka yi, cikin girmamawa suka gode masa, amma Bunayd gyaɗa musu kai kawai yayi bai ko kallesu ba, sannan a gadarance ya ce, “Ku tabbatar kun mata duk wani hukunci yan da ya kamata dai-dai, she attempt to commit a murder, dan haka idan na ji ba’a mata hukuncin da ya kamata ba, ku ne za ku yi facing na hukuncin” yana gama magana ya miƙe ya yi gaba.

Polisawan amsawa suka yi, sannan suka tafi, tare da yaya babba da Abbaa suka koma aka ɗau Umma da ta farka zuwa lokacin da mugun ciwon kai, daman tana gidan yaya babba ne, tana kallon su ta miƙe tana muzurai, Abbaa staki kawai ya ja, ya ce, “ki je na sake ki, kuma aure ki sani ba gudu ba ja da baya, ke kin fita a banza, ita kuma za ta shigo hankali kwance.”

Umma za ta yi magana, polisawa suka tisa ƙeyarta sun ƙi bata daman magana, yaya babba gaba-ɗaya yasan Umma bata kyauta ba, abin bai masa daɗi ba, amma dai uwa-uwa ce, sai ya ji ba daɗi sosai, har ya ji haushin Danish dan shi ya ja komai, ya stani yarinya kuma ya dawo ya ce yana son ta, bayan shi ya ƙara ingiza Umma har ta musu mugun stana, yanzu ga shi abinda ya faru.”

Abbaa gida ya koma, ya faɗa wa Ummu abin da ke faruwa, Ummu hankalinta yayi mugun tashi, Abbaa ya ƙira ya Sadeeq akan ya dawo da Banafsha gida, tun da dare ta yi, kuma ana kula da Mami, ya Sadeeq ya amsa.

Banafsha na tsugunne gaban ɗakin da Mami take, sai ga ya Sadeeq, yana zuwa ya ce, “sistor ki zo mu je gida ko, zuwa safiya sai mu dawo.”

Tura baki Banafsha ta yi ta ce, “Ni dai ina nan da Mamina ba in da zan je.”

Ya Sadeeq yayi-yayi ta ƙi, dan haka dan dole ya ƙyaleta, dan ko da ya faɗawa Abbaa ma cewa yayi a ƙyale ta.

Bunayd ma an yi da shi ya koma hotel tun da Abeed ɗin na huta wa, amma ya ce yana nan kawai, ba dan sojojin sun so ba, haka suka mara masa baya kwanan asibiti ya same su.

Bunayd shi ba kwanciya zai yi ba, dan haka zama yayi kawai a ɗakin da Abeed ɗin ya ke, idan ya gaji kuma ya tashi ya fito.

Banafsha kuma likita ya faɗa mata ta shiga ciki ta kwanta, tun da daman Mami ita kaɗai ce a ɗakin, yau Banafsha ta ga daren da bata taɓa gani ba a rayuwanta, don kuwa baccin ma gaba ɗaya ta kasa, ya ƙauracewa idanuwanta, haka ta dinga juyi, ƙarshe alwala ta ɗauro ta ta da sallah, sai da ta yi nafilfiulunta sannan ta miƙe ta fito.

Mutumin da Banafsha ta gani a tsaye shi ya storitata, za ta koma ciki sai ta jiyo daddaɗan muryansa na faɗin, “storita kika yi?”

Banafsha tana jin muryan ta gane mai yin turanci ɗazu ne, tura baki tayi ta ƙarisa fitowa ta zauna, Bunayd ma ya ƙariso wajan ya zauna ba tare da rata sosai stakaninsu ba, wayansa ya fidda yana lastawa ya ce, “scared girl.”

Cunna baki ta kuma yi ta ce, “Ni ba mastoraciya ba ce, ni bana storon kowa sai Allah, sai na yi kokawa da aljani ma lafiya lau, duk wanda ya mini rashin kirki nima masa zan yi ba storo.”

Taɓe baki Bunayd yayi ya ce, “Kuma kina gani aka yi wa Mom naki wannan abun ba ki ɗau mataki ba, ashe kina da kirki.”

Banafsha da ta tuno abinda Umma ta yi, ai a masifance ta ce, “wallahi na buga mata abu a kai ita ma sai da ta suma, sam-sam ban da kirki ban san shi ba, bani da mutunci idan aka mini rashin mutunci, ni sai na stigewa mutum gashin mugun waje ma ba ruwana.”

Murmushin gefen baki Bunayd yayi, bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da danna wayansa, Banafsha sai mita take ita ɗaya, da ya gaji sai ta ɗago ta leƙa fiskan Bunayd, zaro idanuwa Banafsha tayi tana faɗin, “Mutum ko aljan”, a ranta, ganin irin kyawun Bunayd.

Bunayd a jikinsa ya ji tana ƙare masa kallo, yastine fiska yayi kaman wanda ke yi wa General shagwaɓa, ya ce, “Bana son kallo da yawa.”

Banafsha banza ta yi da shi, tana ta satan kallonsa, ita ba ta shiga harkan maza, amma dai wannan ta kasa ɗaure masa fiska ma, ga shi kyakkyawa kaman Malam Abbonta.

Bunayd haɗe fiska yayi a zuciyansa ya furta, “wannan yarinya ta ci sa’an condition da nake ciki, if not da ita ma ta amshi nata rabon na abinda nake yi wa masu mini kallon ƙurilla, da masu taɓa ni babu sadaki” yana gama magana a zuciyansa ya ja guntun tsaki tare da miƙewa ya shige ɗakin da Abeed ya ke.

Banafsha taɓe baki tayi, ta ce, “Allah kai mu safiya za ka san ni ka ja wa tsaki”, tana gama faɗa ita ma ta miƙe ta shige ɗakin da Mami take, tana kwanciya kuma ba jimawa bacci yayi gaba da ita, a ɓangaren ACM Bunayd kuwa idanuwansa biyu haka ya kwana, dan ƙarshe ma alwala ya ɗaura yana ta nafilfiulunsa har asuba ta yi.

Su Umma a police station, tun cikin dare aka mata statement da komai na attempt to commit murder, da yake tana cikin haushi har lokacin tuni ta amsa musu ita ta yi kuma da saninta ta yi, duk da dai ta amsa amma ta jibgu, kamun aka bar ta sai gari ya waye.

Abbaa yan da ya ga safe haka ya ga dare, gaba-ɗaya abun ya damesa ba kaɗan ba, shi ji yake sakin da ya yi wa Umma bai wadatar ba, da ace ya sani da ya haɗa mata Juni da majina tukunna, ƙwafa kawai ya kwana yi, Ummu ta ba sa baki amma ya ƙi sauraranta ma, dan ko da ta nuna a bar maganan auren banafsha da Danish, Abbaa kaman zai dake ta haka ya hayayyaƙo mata, dole taja baki ta yi shiru tana faɗin Allah ya huci zuciyansa.

Umaima tun da ta ji labari hankalinta ya tashi, kwana ta yi tana kuka har ciwon kai mai stanani ya rufe ta, tausayin Banafsha da haushin halin Umma su suka dame ta, gaba-ɗaya ji take ina ma ana sanja uwa da wallahi sai ta sanja nata uwar, ita sai yanzu ma take ganin ƙoƙari da tawakkali irin na Banafsha, ashe haka ake ji idan mahaifiyar mutum na aikata ba dai-dai ba, ji take kaman ta kashe kanta ta huta, sai ɓarawon bacci ne ya samu nasaran yin gaba da ita, washe-gari kuma ko ta kan magana makaranta bata bi ba, tana taya Ummu aiki, ta shirya ita ma za ta je asibitin.

Abbaa da Ummu da Umaima suka kama hanyan asibiti, aka bar gida ba kowa, dan Nana bealkysou ta fi zama a gidan yaya babba ita kam yawanci, tana taya Hindatu aiki saboda cikin jikinta da ya girma.

Yaya babba sammako yayi a police station amma an ƙi barinsa ya kalli Umma, tun da ta amsa laifin ta shikkenan aka killace ta, dan gudun kada ta yi yunƙurin kashe wasu ma, yanzu haka ma shirye-shiryen kai ta prison suke kamun a fara shari’anta a yanke mata hukunci.

Ya Danish da yake can bai san wainar da ake toyawa ba, babu wanda ya ƙira sa, babban yaya na fushi, Abbaa kuma ba ya son ya sanar da shi dan kada ya ce ya fasa, saboda yanzu yan da Abbaa yake ji ko Danish ya fasa, muddim yarinyar ta amince to sai ya aureta ko zai mutu, dan yafi son ya nunawa Umma bata ita ba.

Da sassafe Bunayd ya sa aka yi arranging na komai yanda ya kamata dan da wuri yake son su wuce, amma so yake kamun ya tafi ya bar wa Faɗima rabonta, na kallon ƙurillan da ta masa jiya, shi ka’idansa ne, mace ba za ta kula stabgansa ba dai-dai da ƙwayan zarra.

Banafsha kuwa saboda ba ta yi bacci da wuri ba, sai da ta makara, gari yayi haske fayau ta tashi, lokacin shida da rabi ta yi ma, a gurguje tayi alwala ta yi sallah, azkar nata da komai, tana idarwa kuma su Umaima suka shigo, Umaima ƙarisawa tayi jikin Banafsha ta ce, “Dan Allah Masoyiya ki yi haƙuri, ni ma ban ji daɗin abinda Umma ta yi ba, amma tun da tana hannun hukuma da sauƙi, Allah bai wa Maminmu lafiya.”

Hawayen da ya zubo wa Banafsha ta share, tare da amsawa da Ameen, gaishe da Abbaa ta yi ya amsa cikin tausayinta, Ummu ma sai ɓoye nata hawayen ta yi, sannan ta amsa gaisuwan Banafsha ta ce, “zo ki ɗiba abinci ki ci ko yarinyar Maminta.”

Banafsha ɗan Murmushin yaƙe ta yi kawai, ta ce ba yanzu ba, suna zaune cikin jimami har sai wajan ƙarfe tara na safe sannan ta karya, bayan ta cika cikinta ta ja hannun Umaima suka fice a ɗakin.

Umaima dai bin Banafsha tayi har ta ga sun nufi wani ɗaki, dai-dai za su shiga sai ga likita nan ya fito ga Bunayd a bayansa, shi likitan yana kallon Banafsha sai ya murmusa ya ce, “good morning annoying doctor.”

Banafsha murmushi ta saki tare da amsawa, Umaima ma suka gaisa da likitan da fara’a.

Bunayd da ke bayan likitan, haɗe fiskansa yayi ya fidda wayarsa yana lastawa, Banafsha a yanayin rashin kirki ta ce, “Sannunka bawan Allah ya mai jiki?”

Banza da ita Bunayd yayi bai ce komai ba, ta kuma magana shiru bai ko ɗago ya kalleta ba, sai da ta yi na uku sannan ya ɗago rai a haɗe ya wasta mata kallon banza ya ja guntun tsaki, Banafsha idan ran ta yayi million to ya ɓaci, saboda masifa har vibrating take yi, Umaima na gefe na ganin ikon Allah ita da likita.

Banafsha a hasale ta ja staki ta ce, “aikin banza aikin wofi, dan ma ka ci albarkacin Allah da Manzonsa ana maka sannu ai da ko kallo ba ka ishe mu ba, Allah ne ya ce, yana farin ciki da kuma kyautan aljanna ga duk wan da idan ya haɗu da mutum zai yi gaggawan masa magana cikin aminci, kuma Annabi SAW ya ce mai zuwa gaishe da mara lafiya yana hanyan aljanna, dan haka ka ji duk ba dan kai na yi ba, kuma daga yau ka ji, ko na ganka a hanya na kula ka, to ba nice Faɗima ba, aikin banza kawai kana nuna kai ba na gari ba, to wani ya faɗa maka shi ma nagari ne ko yana da kirki, ni ɗin nan na fika iya rashin kirki da wulaƙanci ka gode wa Allah ma na kulaka.”

Umaima da mamaki take kallon Banafsha, take kuma maste dariyanta, Bunayd dai ko ɗagowa bai yi ba balle yasan da halittanta a wajan, abun ya kuma ƙara damun banafsha, dan haka a masife ta kalli likitan ta ce, “Kai kuma da ya ke ba za ka iya riƙe mata biyu ba, kai ba adali ba ne, shi ne har za ka fara zuwa duba mara lafiyansa ba za ka duba Mamina ba tukunna ka ji storon Allah.”

Likita maste dariyansa yayi ya ce, “Allah ya so ma mata ta ɗaya ce kuma ba kishiya zan mata ba, dan haka shi ya ce a zo a duba masa ɗan uwansa, ke kuma ba ki faɗa a zo a duba miki Maminki ba.”

Masifa Banafsha ta fara, ka ranste gaskiya ne da ita, Banafsha akwai ƙarfin hali da samun waje, dan ko ita da kanta mamakin abinda take tun da ta zo asibitin nan take.

Bunayd jin surutun nata yayi yawa ɗagowa yayi a gadarance ya ce, “Idiotttt!”” Yana faɗan haka ya juya ya koma ɗakin da Abeed yake, yana mai jin haushinta, dan kawai ya sake mata shi ne take son rena sa, tana ƙoƙarin haɗa kan ta da shi, mastalan yara kenan musamman mata, guntun tsaki ya ja, ya yi dialing na wani layi, da turanci yayi magana akan sun gama a zo a ɗauke su.

Likita kuma gaba yayi yana dariya, su Banafsha na bin sa a baya, Banafsha sai ƙarewa Bunayd tanadi take yi, ga shi ko sunansa bata sani ba, amma ta ce sunansa ba zai wuce Isa stoho ba ta sani, haka suna je likitan ya gaisa da su Abbaa sannan ya duba Mami, sai da ya gama sannan ya ce, Abbaa ya biyo sa office nasa, yana gama faɗa ya fice.

Abbaa ya ce, “Ni ko na ce, Faɗima ina labarin wannan soja mai mutuncin, ya nasa mara lafiyan?”

Taɓe baki Banafsha tayi ta ce, “Au! Wai daman Soja ne? Shiyasa mana yake jin wulaƙanci, bai san gidan rashin kirki ya zo ba, yana can da halinsa nai wari da muni ba kaman fiskansa ba.”

Umaima dariya ta fashe da shi ta ce, “Amma ki dinga jin tsoron Allah Banafsha, kina abu kaman wani ke ce da gaskiya, ko da ya ke samun waje ne yake damunki, irin wannan masifa haka, waɗanda ya kamata ki musu ba ki musu ba sai wan da ba ruwansa.”

Banafsha hararan Umaima ta yi, Ummu ta tambayi ba’a si, Umaima ta labarta mata, ita Ummu ma duk da damuwan da ke damunta sai da ta murmusa ta ce, “Allah shiryaki Banafsha.”

Abbaa ya ce, “Ai bansan yarinyar nan ta iya rikici ba sai jiya, gaba-ɗaya kaman an kunnata” ya faɗa yana dariya ya fice a ɗakin ya nufi office na likitan.

ACM Bunayd kuwa ba jimawa mota ya zo ya ɗauke su, bayan an saka Abeed a bayan motan, dan ya farka, amma an masa alluran bacci, haka suka yi gaba, sun sha tafiya kamun suka isa jimeta, suna zuwa dama already an gama komai, suka hau jirgi kuma sai Kanawan dabo, tumbin Giwa ko da me ka zo an fi ka.

Abbaa bayan likitan ya basa izinin shiga, sai yayi sallama sannan ya shiga, ya zauna a inda likitan ya nuna masa, ƙara gaisawa suka yi.

Likita numfasawa yayi ya ce, “am Alhaji, jikin Mami da sauƙi dan wuƙan bai wani shiga jikinta ba, yankanta yayi kaɗan kawai, to storitan da ta yi ne, shi ya jefata cikin wannan suman, duk da dai akwai allurorin da aka mata ne, amma da ta farka tun cikin dare, amma Insha Allah zuwa anjima za ta iya farkawa, kuma ba zai wuce kwanaki zuwa sati guda ba Insha Allah komai zai zama dai-dai.”

Abbaa murmushi yayi jin likitan ya ce Mami, dan yana da tabbacin a bakin Faɗima ya ji, hamdala yayi da dai jikin Mamin ba wani muni yayi ba, sannan ya ce, “Mun gode sosai likita, Allah saka da alheri, Allah ya ƙara muku ƙarfin zuciyan taimakon bayin Allah.”

Likitan murmushi yayi ya ce, “Ba komai Alhaji, a gode wa Allah da kuma wannan bawan Allahn na Soja, sannan kuma ku dai tabbatar kun yi abinda ya dace, domin kasheta wanda ya soka mata wuƙan yayi niya, kawai dai Allah ya taƙaita ne.”

Abbaa ajiyan zuciya kawai ya sauƙe, dan idan ya tuna ji yake kaman ya je ya kashe Umma shi ma ya huta, cewa yayi, “in Allah ya yarda za’a yi abinda ya dace, dan ma tana hannun hukuma, shi kuma wannan bawan Allah Sojan Allah ya masa albarka ya saka masa, yanzu ya maganan receipt na abubuwan da za mu biya, kamun a sallamemu.”

Murmushi likitan yayi ya ce, “Ai kar ku damu Alhaji, dan Soja ya biya komai da komai daga nan har ku tafi, ko wata guda za ku yi ba mastala, balle ma Insha Allahu bama fatan ta kai sati guda.”

Abbaa ji yake kaman yaya dan farin ciki, cewa yayi, “Shikkenan likita mun gode, a taya mu gode masa, yanzu bari naje na gode masa, daman ba mu haɗu ba tun da na zo.”

Likitan cewa yayi, “Ai kuma Alhaji bana tunanin yana nan zuwa yanzu, dan sun riga da sun karɓi transfer na abokin nasu zuwa Kano, yanzu haka ma wataƙila sun fita a Mubi.”

“Ashsha! To Allah saka masa a duk inda yake, Allah kuma ya stare sa da alkairinsa” Abbaa ya faɗa, tare da miƙewa, suka yi musabaha da likitan ya fice.

Abbaa yana komawa ɗakin ya ce, “Faɗima kin ji ikon Allah, wannan soja mai mutuncin har da kuɗin jinyan Maminku ya biya, gaskiya wannan Soja da kyakkyawan zuciya yake, Allah masa albarka.”

Ummu ta amsa da, “Ameen! Idan yana da mata Allah ƙara musu zaman lafiya ya kuma albarkaci zuri’ansu, idan kuma bai da ita, Allah basa ta gari.”(Hhhhh na ce Ummu da Bunayd na kusa da kin sha mamaki dan wannan mugun addu’a kika masa)

Banafsha a zuciyanta sosai ta ji daɗi ta kuma godewa Allah ta gode masa, a fili kuma ta ce, “Abbaa, wallahi ba wani na gari bane fa shi ɗin, bai da wani mutunci balle kirki, ai Umaima tana kallon abinda ya mana ɗazu.”

Umaima saurin girgiza kai tayi ta ce, “Haram! Ba da ni za’a yi wa bawan Allah sharri ba, ki faɗa gaskiya ke ce kika wani dage kaman shi sa’anki, dan haka komai yayi ke kika nema.”

Hararan Umaima Banafsha ta yi ta ce……

*****

<< Yar Karuwa 15Yar Karuwa 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×