Skip to content
Part 17 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Banafsha hararan Umaima tayi ta ce, “Anji ɗin.”

Abbaa ba jimawa ya fita ya tafi wajan aikinsa, tun da ga Ummu da yaranta a kan Mamin, bayan tafiyan Abbaa sai Ummu ta ce su je gida su ma, amma bata musu maganan boko ba dan ta san ba yarda za su yi, su je ba.

Da ƙyar Banafsha ta yarda, amma tana tura baki, haka suka fice suka tafi, saboda haushi ma ko duba Bunayd bata yi ba, ta bari akan sai sun dawo ta duba sa, dan bata san da ya tafi ba, so take ta rama idiot ɗin da ya ce mata ɗazu, dan ita ta rasa ma gaba-ɗaya mai ya taɓa tunaninta da ta yi behaving haka, ko me ya kai ta shiga stabgan sa ma oho ta rasa.

Suna komawa suka fara zuwa gidan su Umaima, sai da suka gyara gidan, sannan suka tafi gidan Mami, nan ma gyarawa suka yi ko ina ya ɗau ƙamshi, suka ɗaura girki, bayan sun gama suka ci nasu, suka saka na kai wa asibiti, sannan suka saka wa Abbaa suka kai masa gida.

Wanka Umaima ta fara shiga, sai da ta fito sannan Banafsha ma shiga, shiryawa suka yi cikin kayan su iri ɗaya da Mami ta ɗinka musu ba jimawa.

Masha Allah! Kar ku ga kyawun da Banafsha da Umaimatynta suka yi, kaman ka sace su ka gudu, sai da suka gama komai suka yi sallah, lokacin ma har an sauƙo juma’a, sannan suka koma asibitin.

A asibiti kuma, bayan tafiyan su Banafsha ba jimawa Mami ta farka, lokacin ana ƙoƙarin shiga sallahn juma’a, Ummu da kanta ta ƙira Nurse, da yake likita ya tafi masallaci dan haka Nurse ɗin tayi abinda ya kamata.

Isowan su Banafsha yayi dai-dai da lokacin da likita ma ya iso, tare suka shiga ɗakin, likitan ya duba Mami babu wani mastala, sai ɗan abin da ba za’a rasa ba, Banafsha kaman za ta yi yaya dan farincikin ganin Maminta ta farka, lafiya-lafiya.

Umaima da Banafsha duk suka gaishe da Mami ta amsa da kai kawai, likita ya hanata cin abu mai nauyi, dan haka Banafsha gida suka koma suka kuma kawowa Mami abu mai dama-dama wan da za ta iya ci.

Bunayd sun isa Kano da wuri wajajen ƙarfe biyu na rana, komai da yake ready sun wuce asibitin da shi, kuma an ƙara yi masa abin da ya kamata, sannan Bunayd ya bar asibitin ya koma gidansa dan shirin zuwa ɗaurin aure.

Babban gidansa da ke anguwan Dala GRA ya nufa, gida ne haɗaɗɗe har ya gaji da haɗuwa fan’s, wanka yayi da wur-wuri ya shirya cikin manyan kayansa, idan ka kallesa ka ɗauka shi ne angon ma, masallacin da za’a ɗaura auren a can ya nufa, yana zuwa kuwa ana idar da sallah aka gabatar da ɗaurin aure, da yake ya faɗawa iyayen Abeed, kuma su ma sun yi wa iyayen Nusaiba bayani, duk an amince ba komai tun da kowa yasan ƙaddara, balle ma ga soja, kuma yarinya ta ce tana son mijinta a haka.

An ɗaura auren CAPTAIN ABEED TASI’U ADAMU & NUSAIBA YAKUBU NASHE akan sadaki Naira dubu ɗari biyu, bayan ɗaurin aure kuma, Bunayd da sauran abokanaye duk suka yi abinda ya kamata.

Abeed kuwa a asibiti ana gama ɗaurin aure ya farka, ko da Bunayd ya zo wajansa sai da ya saka shi ya kira masa Amaryansa Nusaiba, Bunayd dariya ya dinga yi wa Abeed ya ce, “stautsayi ta rista da Ango mai jiran Palace, sorry Captain Abeed, amma kai ma ai da nine kai ba zan je wannan aikin ba atou, haka kawai ga shi an maka baƙin cikin yin mopping na Palace from corner to corner, kai gaskiya ma dole kamilarka ta renaka, yo baka goge mata hadda a take ba ai ba wani suna mai daɗi da za’a ƙara maka, kai in kana son ganin asalin soyayya da girma a wajan Amarya to a ranan da aka kai ta, kada ka bari ta kwana lafiya, balle ma ta kai Sunday, a ranan Friday ka sha hidima ka yi disko, ka kwaso shoki, ka yi har da Apro dance duka a Palace, nan za ka ga wani irin ruwan ƙauna, ai ba abinda ke saita mace ka ga ta ji duniya babu ya kai irin Dragon, ka bata blessfull milk ka kwashi gifted water, ni ana fara maganan aure na ko nan da can ba zan je ba, ƙarshe ma General ne zai je ya ɗauro auren a kawo mini Amaryata, yanzu dai dole ku cinye wata guda babu ko romancigin, ai hidiman cherge a Palace ta wuce Friday to duk buge ce, dan a ranar ma ake son ka jefa ƙwallo a raga, za ka ga albarkataccen baby da za’a haifa maka, wanda ya amsa sunan sa ɗan halak, ranan da aka biya sadaki da ɗuminsa aka same shi, tun sadaki bata huce ba ta salafce” Bunayd ya ƙarisa zancen yana dariya kaman ba lafiya ba, kana gani kasan dariyan mugunta ce.

Abeed saboda haushi ji yayi ma ya warke, hararan Bunayd yayi ya ce, “ɗan jagaliyan musulmi, bakinka ya sari ɗanyen kashi, in Allah ya yarda zuwa Sunday na warke, wato tun da baka ƙaunata dole ka mini fatan na kai 1 month a kwance, kuma Allah ya kai mu lokacin naka auren, za mu ga ko za ka gujewa abin da Allah ya hukunta” ya ƙarishe maganan tare da yin ƙwafa, dan ko shi a ransa ba haka ya so ba, irin soyayyan da suke da Nusaibarsa, irin burin da suka ci wa wannan rana ai ba haka ba, amma ba yanda mutum ya iya da ƙaddaran Ubangiji.

ACM Bunayd dariyansa ya ci gaba da yi, har da wata English music yake na babu hidimar Palace, sai da ya stagaita dariyan ya ce, “Amma ai da sauƙi tun da raunin ba’a Dragon ba ce, kawai dai tun da a cinya ne ba buga harka yan da ya kamata, sai dai a lallaɓa, ka ga fa’idan auren gantalalliya da nake faɗa maka ko, yanzu da ace ba kamila saliha ka aura ba, ai ba ka da mastalan komai tun da Dragon na lafiya, da kana kwance za ta gabatar da hidima ta yi su doro bucci, su gwara-gwara, a gwargwarawa Dragon chergy.”

Abeed mai da kansa yayi ya kwanta yana cewa, “Sai kuma ka yi ai, ni dai idan ba za ka ƙira mini ita ba, miƙo mini wayana.”

Bunayd yana murmushi ya miƙa wa Abeed wayansa, bayan ya masa dialing na layin Nusaiba Amarya.

Ƙira na shiga, kaman daman Amarya jira take, ɗauka tayi cikin farin ciki da ƙaunar mijinta ta ce, “Alhamdulillahi ala kulli halin na zama mallakin My Captain, sai addu’an Allah ba wa mijina lafiya.”

Lumshe ido Abeed yayi yana jin wani irin abu, a hankali ya ce, “babyloff am so sorry.”

Guntun murmushi Nusaiba ta yi ta ce, “sorry for what Captain? Ƙaddara ce, kuma da yardan Allah mun ma cinye ta, Allah baka lafiya, nikam lada kwasha-kwasha, tun yanzu zan fara cika bankin lada na, ana wastewa zan zo nayi jinyan Captain na.”

Murmushi Abeed yayi ya ce, “Masha Allah! Alhamdulillahi! Na gode wa Allah da ya mallaka mini ke, tun yanzu ma indai aljannarki a ƙasan ƙafata take, to na ɗage miki, lada kam kina kan samu tun da aka ɗaura albarka nake saka miki, saura albarkan bed kawai.”

Cikin jin kunya Nusaiba ta dinga amsawa Abeed, suka yi wayansu cikin farin ciki, suna gamawa Abeed ko kallon Bunayd da ke masa dariya, ya ƙi yi, gyara kwanciyansa yayi yana tunanin Nusaibarsa, ba dan ciwo ba ai da zuwa yanzu ko ɗan taɓe-tabe haka da ya yi.

Bunayd miƙewa yayi ya ce, “Captain kar ka saka ƴar mutane a corner, ka bari ciwonka ya warke, yau da gobe duk ɗaya ne”, yana gama magana ya fice.

Ƙwafa Abeed yayi ya ce, “ɗan renin hankali, ana sallamana a ranan ba ɗaga ƙafa wallahi, kuma kai ma lokacinka na zuwa zan rama ne ai.

ACM Bunayd komawa gidansa yayi ya shirya, daman freind’s na su suna gidan sa, suna jira a kai Amarya kamun su wuce, dan dinnern da za’a yi an mayar da shi sai idan Abeed ya warke, sai yayi fixing time ayi, shi yayi arranging na komai, aka ɗau Amarya aka kai ta gidanta, duk wani abun buƙata da za’a yi Bunayd ake tambaya, ya tsaya ciff akan komai, har aka yi aka waste ranan Lahadi.

Abeed ya ce Nusaiba ta kwana a gida tukunna ta huta, sai washegari litinin ta zo, amma sam firr ta ƙi yarda, dan haka shiryawa tayi Bunayd ya je ya ɗauko ta ya kawo ta asibitin, kamun isowansu kuma tuni Abeed yayi wanka ya yi sharr abin sa, kaman ba mai jinya ba, da yake ƙafan da sauƙi ma.

Bayan sun shigo ɗakin, tuni Abeed ya buɗe hannu wa Amaryansa, Nusaiba sunne kai tayi wai tana kunyan Bunayd, shi kuwa taɓe baki yayi ya ce, “kin yi a iska Amarya, kunyan mara kunya asara ne, yi abunki lokacinki ne, mu idan namu ta zo har da cherger Palace idan ta kama zan yi a gabanku ba ruwana” ya faɗa yana ɗage kafaɗansa, irin ko a jikinsa.

Nusaiba Amarya murmushi kawai ta yi, ta koma wajan mijinta ta zauna, amma bata yi hugging nasa ba, Abeed hararan Bunayd yayi ya ce, “Sai a bamu waje ai, kasan yanzu iyali gare ni, ni ba gauro ba.”

Murmushi Bunayd yayi ya ce, “Ni ba zan ce komai ba, amma dai ka bi a dai-dai, dai-dai kaman mai slow motion, dan wani ciwon baya yake komawa idan aka charger Palace bai warke ba”, yana gama magana ya fice kaman ba shi yayi maganan ba.

Abeed murmushi kawai yayi, tare da jawo Nusaiba jikinsa, wani irin ajiyan zuciya suka sauƙe a take, nan suka fara kallon juna cikin soyayya, har Nusaiba ta gaji ta kawar da kan ta, kalaman soyayya suka fara ɓari, daga ƙarshe Abeed haɗe bakinsu yayi, yana mata wani irin kiss mai isar da saƙon zuciya zuwa ga masoyi.

Sai da suka yi sati guda a asibiti sannan aka sallamesu, kuma kullum Nusaiba tana can, wanka kawai da girki ke kai ta gida, duk da ma Bunayd na yawan musu takeaway, ga kuma wanda ake kawowa daga gidan iyayen Abeed, da nata iyayen, Abeed kullum sai yayi kiss amma bai taɓa wuce kiss ba, yana daurewa ko yayi yunƙurin wuce kiss sai ya fasa, ya ce sai an sallamesi.

Ko da aka sallamesu Bunayd hidima bai ƙare ba, shi ya kai su gidan su, ko da Nusaiba ta shige ciki, tsayar da Abeed yayi ya ce, “Abeed ka bi a slow motion fa, serious ciwo bai cika son ana charging ba, ba ta warkewa da wuri.”

Abeed hararan Bunayd yayi ya ce, “Idan kai ka biyan mini sadaki to sai ka hana”, yana faɗa yayi gaba.

Bunayd ɗage kafaɗa yayi, ya wuce abinsa yana faɗin, shi ya gama nasa yayi duk abin da ya kamata, idan ya jawo wani abun ma su suka jiyo, amma gefe guda na zuciyarsa na cewa, “faɗa gaskiya ACM ko kai ne ba za ka ƙyale ba, sabuwar Amarya no be play”, murmushi kawai yayi ya ci-gaba da driving abin sa, gidan Papi ya nufa ba gidansa ba.

Abeed yana shiga gida ya saki hamdala, ganin Nusaiba na gyare-gyare, ƙarisa wa yayi tare da rungumeta ta baya, a hankali ya kai hannayensa kan na shanunta, wani irin gigitaccen ajiyan zuciya ya sauƙe, a hankali ya ce, “My life saver’s, babyloff bar aikin nan, ladansa kaɗan ne, muje ki yi mai lada da yawa.”

Nusaiba ajiyan zuciya ita ma ta sauƙe, ta ce, “My Captain ba ka warke ba fa.”

Abeed shi kaɗansa a zuciyansa ya ce, “Ashe gaskiyan ACM Bunayd, wato dai har faɗa mini take ban warke ba, ta rena Dragon, shikkenan ai za ta same sa yanzu kuwa”, yana gama zancensa a zuciya, ya mata dabara, yana tattaɓeta har ya ja ta suka yi ɗaki, gaba-ɗaya Abeed notin kam sa ya warware.

Nusaiba ma abu ya fara kai mata karo, tuni suka fara ƙoƙarin raba kan su da kayan jikinsu, cikin ƙarfin hali Abeed ya haƙura ya ƙyaleta, wanka yayi ya shirya, ita ma ta yi, suka wuni soyayyan su, dare na yi ya ce kuma bai san zancen ba, alwala ya sa ta tayi, suka gabatar da duk wani abu na al’ada, kayan cin su da Bunayd ya turo musu da shi, suka yi haniƙan, sannan fa aka fara zuba soyayya.

Abeed sarrafa Nusaiba ya ke yi kaman abinda aka turo sa yi a duniya kenan, tun da Abeed ya fara haukata mata boob’s nata, yana gyara musu lissafi, tuni ta fice a nata lissafin, hidima sosai Abeed suke yi, ko ciwon ƙafan ba ya tunawa, sai da ya tabbatar ya gama da ita, sannan a niste ya fara neman hanyarsa bayan addu’an da yayi, wanda Sunna ya tanada domin ma’aurata, ita wannan addu’a kuwa tana stare masu gabatar da Sunna daga sheɗan, sannan idan a wannan lokacin ma an samu ƙaruwa, to Insha Allah wannan yaro zai zama nistastte ba sheɗani ba, mata w ƙoƙarta ko miji baya yi ke ki dage ki dinga yi, duk iya fitanki hayyacinki, idan ma ba’a iya ba ko bismillah ayi ta wadatar, addu’ar na da matuƙar amfani da muhimmanci, addu’an ita ce BISMILLAHI ALLAHUMMAH JANNIBNASH SHAITAN, WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAƘ’NA.

Nusaiba ta ji azaba dai-dai gwargwado amma dai ta daure, Abeed gaba-ɗaya ma ya mance duniyar da yake, hidima yayi ba ta kaɗan ba, sai da ya samu nistuwa sannan ya janye jikinsa tare da rungumeta yana lallashinta, bayan sun starkake jiki, ta gasa kan ta, sun gyara wajan kwanciya, sun kwanta, nan ƙafan Abeed ya fara damunsa, wasa gaske zuwa safiya kaman ya yanke ƙafan ya huta dan azaba.

Jikin Mami yayo sauƙi sosai, satinsu guda da kwana biyu a asibiti, aka sallamesu, zuwa lokacin kuma DR ARSHAN sun yi sabo da Umaima da Banafsha, Malam Abbo ya zo har asibtin ya duba Mami.

Gefen Umma kuwa tana prison a ajieye, tukunna ba’a bi ta kan case nata ba ma, gaba ɗaya a sati guda kawai ta lalace ta fice a hayyacinta, da yake ƙaramar ƴar tasha ce har ta yi nadaman abin da ta aikata, dan ta galabaita.

Ya Danish tun da Abbaa ya faɗa masa ba su yi magana da Mami ba tukunna, sai ya fasa zuwa weekend ɗin, yaya babba kuma gani yake kaman Danish da gangan ne bai zo ba, sai bai tuntuɓe sa ba, kuma ko ya ƙira ba ya ɗauka, shi kuma ya Mus’ab daman ba gwanin zuwa gida ba ne, yana can abin sa.

Abbaa ganin halin da Mami ke ciki, sai ya ɗaga ƙafa ba yanzu zai sameta da maganan ba, har Mami ta kuma yin sati da dawowa asibiti bai mata maganan ba, zuwa lokacin ta ji sauƙi sosai, su Banafsha sun ci gaba da zuwa makarantansu boko da tahfiz, in da yanzu suke shirin tafiya musabaƙan su, wanda za su gabatar a cikin jimeta tare da sauran makarantun local ɗin Adamawan.

<< Yar Karuwa 16Yar Karuwa 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×