Skip to content
Part 18 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Bayan wani lokaci Mami ta warke rass da ita, amma bata yi maganan Umma ba, lissafi kawai take yi da tunani akan rayuwa, musamman maganan Malam Abbo da Banafsha, dan Banafsha ta dage ba za ta yi aure ba sai dai Mami ta yarda ta yi ita ma, ko kuwa ta koma wajan danginta, wannan zaɓi biyu na Banafsha sun damu Mami, domin burin Mami bai wuce aurar da Banafsha ba, akan hakan kuma za ta iya yin komai, sai dai tuno abubuwa da dama na mata kastalanda akan amincewa da abin da yarinyarta take buƙata kamun a ce tayi aure.

Yau Abbaa ya shirya abinsa ya je wajan Mami, ba tare da ta nuna wani abu akan akasin da aka samu ba, haka ta tarbesa da fara’a, kuma ko Abbaa ya ji daɗin hakan, sai ya ji ta ƙara kwanta masa a rai sosai, ya ƙara son ta.

Cikin nistuwa Mami ta gaishe sa tare da tambayansa Ummu, amsawa yayi yana washe baki.

Abbaa cewa yayi, “Da farko dai ina mai baki haƙuri Hajiya Ramla, ina kuma baki haƙuri, dan Allah ki yi haƙuri da abin da ya faru, daman jiran warkewanki ake yi sai a fara shari’a ma, Insha Allah za’a ƙwatar miki ƴancin ki.”

Murmushi Mami tayi wanda ke ƙara mata kwarjini, sannan makari ga duk wani damuwanta, cewa tayi, “Lah! Ai ba komai Abbaansu, na haƙura wallahi na yafe mata، saboda duk wata mace mai kishin mijinta za ta iya aikata fiye da haka, kuma ƙauna da soyayyar miji ke kawo kishi, duk da dai kishi ba hauka bane, amma da gaskiyanta ni banji haushinta ba ko kaɗan, da ina hayyacina ma ba zan bari abin ya kai ga hukuma ba, ko nine a mastayinta idan ba wai na danne zuciyata ba, to zan aikata abinda ya fi wanda ta aikata, dan sai na haɗa da mijin duka na ƙone su, kawai dai haƙuri ake tun da Allah ya halatta muku, sai dai mu ce Allah bamu ikon fin ƙarfin zuƙatanmu, Allah kuma ya bamu haƙuri da dangana, tun da ko matan Annabi SAW ma sun yi wannan kishin, har sai da ta kai Allah ya sauƙe aya guda a kan su a cikin Suratul Tahrim, dan haka dai ita kishi halitta ce, Sunna ce, ba yan da za’a yi ka guje mata sai ikon Allah, faɗin Manzon Allah SAW ne ma cewan kaicon ma’auratan da basa kishin junansu, tun da dai sai da kishi sannan ake samu a kiyaye wasu dokokin Allah a zaman auren, to kada ka ga laifinta, Allah ya kyauta kawai.”

Abbaa shi dariya ma Mami ta basa, jin wai idan ita ce sai ta haɗa da mijin, jinjina kai yayi ya ce, “To yanzu dai idan na fahimta, Hajiya Ramla cikin ruwan sanyi take kafa mini sharaɗi, wato na kulle ƙofa daga kan ki, babu ta huɗu kuma ko na ce ta biyu dai.”

Wani kallon rashin fahimta Mami ta masa ta ce, “Abbaansu ba dai nufinka ka sallami Maman Kabeer ba?’

Abbaa jinjina kai kawai yayi ya ce, “Eh! Saboda bana son tashin hankali da rashin haƙuri, Ita Ummu-khultum ai tana da zuciya da nata kishin, amma ta haƙura duk da haka, tun da ƙarin aure Sunna ce, ga kuma yanayin zamani ya zo ƙarshe.”

Murmushin taƙaici Mami tayi tare da jinjina kai ta ce, “Ai daga wannan kuma ka riga ka faɗi zaɓe Abbaansu, ai yanzu na faɗa maka nima idan ba wai Allah ya taimaka ba zan yi fiye da haka, duk da ba sharaɗi bane amma ai hannunka mai sanda ce, gaskiya Abbaansu ka yi haƙuri kawai ka dawo da matarka, ku cigaba da zamanku lafiya, ni xan fi son hakan, domin yanzu gani zan yi kaman nima aje-aje gaba za ka iya mini haka akan wata, ka yi haƙuri amma zai fi ka dawo da matarka uwar yaranka, da stohon zuma ake magani, kuma da kake maganan Ummu ai kai ma cewa ka yi nata kishin daban, to da haka za ka fahimci kowacce mace da irin nata kishin, ba duka aka zama ɗaya ba, kar garin gudun gara ka faɗa wa zago kuma, a zo ni nafi Maman Kabeer kishi da rashin haƙuri, ka ga ai akwai mastala babba ma sosai.”

Abbaa murmusawa yayi ya ce, “Ba zan iya dawo da Sabeera ba, saboda idan akan kishi ne kaɗai ta yi hakan, to da sauƙi dan nima nasan kowa da irin halittan kishin da Allah ya masa, amma har da dalilin dan Danish ya ce yana son Faɗima a nema masa izinin nemanta.”

Da mamaki Mami ke kallon Abbaa, wato dai ranan gaskiya kunnenta suka jiyo mata, daman was-wasi take ko dan storita ne ya sa ta ji kaman Maman Kabeer ta ce, yaronta na son Banafsha, su mayu ne sun lashe mishi zuciya, murmushin yaƙe Mami ta yi ta ce, “Allah ya bawa Maman Kabeer haƙuri, Allah ya huci zuciyanta, in Allah ya yarda tun da bata so, to Banafsha ba za ta auri Danish ba, in ba dai Allah ya rubuta hakan a ƙaddaransu ba, to babu yanda muka iya kuma, sai dai addu’a da fatan alkairi, dan haka wannan ma ba dalili bane da zai sa ka rabu da iyalinka, ka yi haƙuri Abbaan yara, mu mata sai a hankali, haƙuri ake da mu, kaga Allah bai haɗa jininmu da ita ba shiyasa bata son ma ɗan ta ya auri Banafsha, to nan ma ina bayanta, saboda maganin bari kada a soma.”

Abbaa wani gauron numfashi ya sauƙe cikin ƙara jin haushin Umma akan abin da ta aikata, kallon Mami yayi a yanayi na tausayi ya ce, “Hajiya Ramla a taimaka mana ni da Yarona, gaba-ɗaya tun da aka yi abin nan hankalina ya ƙi kwanciya, sannan yaron nan kwata-kwata ma ya ƙi zuwa ma, balle kuma ya san halin da ake ciki, ya ce sai ya ji labari an yarda ya nemi Fatima sannan zai zo, dan Allah a taimaka mana.”

Mami ajiyan zuciya ta sauƙe cikin duba lamarin Maman Kabeer, dan ba za ta yarda Banafsha tayi aure a irin wannan gida ba, ita ma babba an yi ƙoƙarin kasheta balle kuma Banafsha yarinya, duk da dai yaron na ƙaunarta(kunsan Mami bata san abin da ke faruwa ba, duka wannan staman stakanin Banafsha da Danish bata da labari), amma ba za ta iya ba, dan haka duban Abbaa ta yi ta ce, “afuwan Abbaan yara, amma magana ta gaskiya Faɗima tana da manemi, wanda zuwa yanzu izini kawai yake jira ya turo manyansa a yi maganan auren su, bai kamata nima duk da ina mace ba, amma na zama mai magana biyu, kuma dai nema cikin nema ko a addinan ce babu kyau.”

Abbaa kallon Mami yake kaman ya ƙwala ihu, ya ce, “sosaima Hajiya Ramla, nema, cikin nema babu kyau, dan haka in Allah ya yarda zan yi ƙoƙari na basa haƙuri ya nemi wata, amma nima a duba tawa buƙatan, ina matuƙar ƙaunarki Hajiya Ramla, a taimake ni, idan ban same ki ba akwai mastala babba ma kuwa.”

Furucin Abbaa na idan bai sameta ba akwai mastala babba, dariya ya bata, dan haka ta maste dariyanta, ta murmusa kawai, a ranta mamaki take irin na halin maza, wato manya da yara duk daɗin baki ta cika su, namiji ya dage da idan bai sameki ba kaza-kaza, amma abu mai wuyan ki amince ne ayi auren, shikkenan kin zama permanent kuma sai haƙuri, idan ba ki yi sa’a ba baƙin cikin yau daban na gobe daban, to dai Allah kyauta ya kuma haɗa kowa da sa’ar sa yayi dacen samun na gari, amma sam-sam halin wasu mazan bai haɗu ba, duk da wasu matan su suke nemawa kan su irin wannan rayuwan, Allah kyauta kawai.

Mami murmushi tayi ta ce, “Alhaji ka yi haƙuri, amma dai ni abinda ya dame ni yanzu shi ne ka dawo da Maman Kabeer.”

Abbaa kallon Mami yayi cikin ido ya ce, “kin tabbata idan ta dawo za ki amince mini ki aure ni?”

Murmusawa Mami tayi ta ce, “ban yi alƙawari ba, sai dai shi Danish zai iya zuwa wajan ita Faɗima, idan sun dai-daita taga shi ya fi mata, to shikkenan Allah sanya alkairi, dan abin da yaro ke so shi za mu masa.”

Abbaa sosai wannan amsa dangane da Danish ya masa daɗi, dan haka ya sa a rai shi ma zai ci-gaba da zuwa yin magiya, har Allah ya sa ta amince dan abin zai fi ba da armashi.

Bayan sun gama hiransu, sallama suka yi, Abbaa ya tashi yayi tafiyansa, Mami dai duniyan tunani ta faɗa, juya abubuwa da dama take a ranta, ƙiran wayan da ya shigo mata ne ya kaste mata tunanin, ganin mai kira sai ta saki murmushi ta ɗauka, cikin zazzaƙar muryanta ta ce, “Alhaji bar ka da war haka.”

Alhaji Mukhtar a ɗaya ɓangaren shi ma yana murmushinsa ya ce, “Barka dai masoyiya ta, fatan kina lafiya، ya kuma yarinyata Banafsha take?”

“Duk muna nan lafiya yallaɓoi, ya ƙasar mutane?” Faɗin Mami.

Alhaji cewa yayi, “Lafiya Alhamdulillahi! Ga mu cikin ta, sai fama nake da kewanki, yanzu badan-badan ba ai da kuɗin jirgi zan miki ki biyo ni, ko kuma ma na sakoki a gaba mu taho tare, ga shi duk mutanen ƙasar masu irin kyawunki ne.”

Mami cikin ƴar shagwaɓanta ta ce, “To ai ni na ɗauka ma ka dawo, sai naga ba layin Nigeria ba ne, nima kewanka nake, kwana biyu babu customers, ina ga kore su ka yi da za ka tafi, ga shi dai ni a buƙace nake, badan-badan ba nima da na biyoka.”

Alhaji a nasa ɓangaren dariya yayi, dan yasan watarana Ramla na irin magannan ne da gan-gan dan ya ji haushi, amma abun da bata sani ba shi ne, wani irin soyayya yake mata wan da ko turmi da taɓarya ya kalleta da namiji, to ba zai cire masa son ta ba, shi baisan ko dan a cikin irin rayuwan ya san ta bane, amma shi a haka ma yake mugun ƙaunarta, yana kishinta ba kaɗan ba, amma a yanzu burinsa ya mallaketa sai yayi kishin yan da ya kamata, sai da ya gama dariya sannan ya ce, “Ko taurarin sun fara yin ƙasa ne mu godewa Allah, amma dai kar ki damu soon za ki ganni, suprise kawai, ki shirya ganina a ko wanni lokaci daga yanzu, tun da kina buƙatata ai zuwa ya zama dole, nima a buƙacen nake, wata biyu ba mata, ina dawowa na bai wa Hajiyata rabonta, zan wuco na zo ke ma na baki naki rabon masoyiya, duk ƙishin sai na kawar miki, ke dai ki adana mini kan ki kar na zo kuma kin riga da kin kashe ishinki ni ki kasa kashe mini nawa.”

Mami murmushi tayi suka ci-gaba da wayansu cikin soyayya, ka ɗauka mata da miji ne, tuni ma ta mance da wata maganan da suka yi da Abbaa, sai da suka yi sallama sannan ta ajiye wayan tare da yin murmushi, wato Alhaji Mukhtar mutum ne, tun ranan da ta yi kuka ya ce ba zai kuma mata maganan aure ba, to bai kuma ba, sai kawai Mami ta ji ya bata tausayi.

Ɓangaren Alhaji Mukhtar da ya kwashe fin wata biyu a Egypt, suna gama waya da masoyiyarsa ya murmusa tare da addu’an Allah shirya su ya dawo masa da ita hanya.

Abbaa ko da ya koma ya ƙira Danish akan zai iya zuwa wajan Banafsha, idan ta aminta da soyayyansa shikkenan sai ayi maganan aure, amma ya faɗa masa bayan shi akwai wani mai nemanta.

Danish duk da ya kwana da sanin Banafsha na da saurayi, amma ya ƙudurcewa ransa sai ya ka da saurayin nata, shi yanzu ko bin mazan da ya ce tana yi baya gani, wani mugun son ta da ƙaunarta ne yake damunsa, burinsa kawai ya mallaketa, dan haka tsaff ya shirya wannan satin ya taho Mubi.

Ɓangaren su Banafsha sun duƙufa akan karatunu musabaƙan da za su yi, gaba ɗaya yanzu ko Malam Abbo sai ya dage yake samun lokacinta, ga shi tsakaninta da Maminta indai ta mata maganan aure to ranan sai Mami ta saka ta kuka, ita ta dage sai Mami ta yi aure ita ma, ko kuwa ta koma wa danginta, sannan za ta yi aure, Mami kuma bata amince da ko ɗaya ba, ta dai dage sai Banafsha ɗin ta yi aure.

Mami bata faɗa wa Banafsha zuwan Abbaa ba, sannan bata mata maganan Danish ba, ta bar ta dai, idan ya mata ta ji tana son sa, to da kanta za ta yi maganan wanda take so tsakanin shi da Malam Aliyu.

Umma tana can zaune a prison har yanzu ba’a fara case nata ba, ko da Mami ta je station ɗin ma akan ta yafe mata a ƙyaleta, amma nunawa suka yi ai case ya riga da ya koma court, kuma ba daman janye ƙara, kuma yanzu a ƙarƙashin ma’aikatan prison take ba ma’aikatan station ba, dole haka Mami ta dawo ba dan ta so ba, yaya babba ko da yaji labari jinjinawa haƙuri irin na Mami yayi, Umaima ma sai ji tayi ta ƙara ƙaunar Mami, Ya Mus’ab ma har da godiya ya yiwa Mami dan sun san yanzu abin zai zo da sauƙi, tun da ta ce ta yafe, ko a court ne to abin da sauƙi.

Banafsha da ta ji wai Mami ta yafe wa Umma, sai ta samu Mami ta ce, “Mamina me yasa ba za ki bari a hukuntata ba? Yunƙurin kashe ki fa ta yi, kisa fa Mami, da yanzu na zama marainiya ban da kowa.”

Murmushi Mami ta yi ta ce, “Innallaha ma’assabirin! Allah na tare da mai haƙuri Banafsha, yafe mata da nayi, sai kiga nima Allah ya dubi wasu laifukana ya yafe mini, ya kuma shirya ni ya dai-daita lamurana, Banafsha ita komai a duniya ƴar haƙuri ce idan ɗan Adam ya gane.”

Kallon Mamina nayi na ce, “haƙuri Mami? Shikkenan ta yi a banza? Ni fa duk da Umman Umaimata ce amma ya kamata a hukuntata, dan wasu masu irin wannan yunƙurin su hankalta, tun da an ce gani ga wane ya isa wane storon Allah.”

Murmushi Mami ta kuma yi ta ce, “Ba na yafe mata saboda wasu su ji daɗin aikatawa bane, a’a na yafe mata ne saboda waɗanda aka wa laifi irin nawa ko fin nawa, su ji daɗin yin yafiya da nufin su ma Allah ya yafe musu wani yanki na zunubansu, Banafsha akwai wani kissa daga Manzon Allah SAW kan cewa, watarana a gaban Allah ranan tashin ƙiyama, akwai wani mutum da za’a tattara ladansa a biya bashuka, zalunci, munafurci, ha’inci da sauran su, duk za’a biya haƙƙonƙin jama’a da ya ci, da ladan ayyukansa na alkairi, sai ya zamana dai-dai da ƙwayan zarra ba shi da lada ko guda, to ana cikin haka kuma wani mutumin zai ƙara ɓullowa ya faɗawa Allah, ai shi ma yana bin wannan mutumin bashi dan haka asaka shi ya biya sa, idan Allah ya ce wa wannan mutumi mai laifukan ya ji abinda wannan ya faɗa, sai ya kama murmushi, ko da Allah ya tambayi dalilin murmushin nasa, sai ya ce ai gani yayi bai da lada ko ƙwayan zarra, duk ladan an biya jama’a da shi, yanzu ba shi da komai sai zunubi, Allah ya kuma duban mai kawo ƙara ya ce kai ma ka ji abinda ya faɗa ai ba shi da lada, sai mai kawo ƙara ya ce, in mutumi mai laifin bai da lada, to ai shi yana da zunubi, dan haka a ɗiba, zunubinsa gwargwadon haƙƙinsa da ke kan mutumi mai laifin, a ƙara masa akan nasa zunuban, Allah zai ƙara kallon mutumi mai laifin ya faɗa masa ya ji abinda mai ƙaransa ya faɗa, sai mutumin yayi murmushi ya ce ya ji ya amince, sai Allah ya sa a nuna wa mai laifin yan da jahannama ta ke, idan ya kalli jahannama sai hankalinsa ya tashi, daga dariya ya koma kuka, idan Allah ya tambayesa yana dariya kuma mai yasa ya koma kuka tun da ya yarda, mutumi mai laifin cikin tsananin kuka da tashin hankali zai faɗawa Allah yana son yayi magana da wannan mai ƙaran nasa, to Allah zai basu wata farfajiya su magantu, wannan mai laifin yana kuka zai haɗa mai ƙaransa Allah da Annabi ya taimaka ya yafe masa, idan ya ce a ƙara masa zunubinsa zai ƙara masa azaba ne, kuma idan yana da zunubai da yawa to shi ma ba zai hanasa shiga wutan ba, dan haka sai wannan mai ƙaran ya yafe masa, su koma gaban Allah mutumi mai ƙaran ya faɗawa Allah ya yafe ma mutumi mai laifin, idan Allah ya tambayi dalili sai ya faɗa masa ai shi ma yana da zunubi, dan ya ce a ƙarawa wani zunubinsa ba zai hanasa shiga wuta ba, kawai ya yafe, sai yayi haƙuri, to saboda wannan yafiyan da ya yiwa mutumi mai laifin ya kuma haƙura, sai Allah ya yafe musu duka ya saka su a aljanna, saboda Allah ya ce yana ƙaunar masu haƙuri, to sai Sahabbai suke mamakin yan da ake wannan al’amari duka a gaban Allah, Manzon Allah SAW ya faɗa musu abinda ake nufi da wannan al’amari shi ne haƙuri, Allah na tare da mai haƙuri, Allah na son mai haƙuri, Allah yana sakawa ga mai haƙuri, saboda Allah shi ne ahkamul hakeemin, shi ya fi kowa iya hukunci…”

Tun da Mamina ta fara wannan bayani na stura mata idanuwana ko kiftawa bana yi, har sai da ta kai aya, sannan na sauƙe ajiyan zuciya tare da lumshe ido na ce, “To Allah ba da lada Mamina, Allah kuma ya yafemu baki ɗaya, Mami amma dan Allah me yasa kika kasa haƙuri da danginki? In kuma ke ce kika musu laifi me ya sa ba za ki je, ki basu haƙuri ba tare da nusar da su fa’idan haƙuri da yafiya ya za su miki, Mami shi kuma mahaifina me ya miki? Ina yake? Mamina dan Allah dan darajan Annabi SAW ki taimaka ki amsa mini waɗannan tambayoyin.”

Mami murmushi tayi tare da ƙarisa wa da salati Manzon Allah SAW, ta ce, “Insha Allah Banafsha zan ba ki duk amsoshin tambayoyinki amma ba yanzu ba, kuma ba yau ba, ban faɗa rana na amma na kusa sanar da ke komai kin ji, ki yi haƙuri ki ƙara haƙuri.”

Kwantawa nayi a jikin Mamina ban kuma cewa komai ba, wannan mutumin da muka haɗu da shi a asibiti ne ya faɗo mini a rai, tura baki nayi lokaci guda kuma na murmusa, tuno abinda ya faru, Mamina kallona ta ce, “Lafiya da murmushi haka gudalliyan Maminta.”

Murmushi nayi ba ɓoyel-ɓoyel na ce, “Mami bansan me ya same ni ba lokacin da kika yi rashin lafiyan nan, amma gaba ɗaya na zama kaman parrot a surutu, wannan Soja da Abbaa ya faɗa miki shi ya biya kuɗin komai, Allah haka kawai na dinga masa masifa na rasa me ya sa, sai kuma yanzu abin nake tunawa, ni da ba halina ba, meyasa na masa haka oho، kuma fa bai biye mini ba, ce mini kawai yayi idiot” na ƙarishe maganan ina tura baki.

Shafa kai na Mami tayi tare da sakin murmushi ta ce, “Allah ya amsa albarka ya saka masa da alkairi, ga shi ko sunansa ba mu sani ba, wannan su ne masu yin abu dan Allah, fisabilillahi, ke kuma Allah shirya mini ke, ai daman Banafsha bakya ji, kin cika stiwa da manyance.”

Tura baki nayi, muka ci-gaba da hiranmu da Mamina tana shafa kai na, gaba-ɗaya hasaso wannan bawan Allah kyakkyawan soja nake ina murmushi, har ban sani ba bacci yayi gaba da ni.

Danish kuwa tun da ya zo ya ji labarin abin da ya faru, ba ƙaramin damuwa yayi ba, musamman da ya kasance shi ne sanadin komai, haƙuri ya bai wa yaya babba, bayan ya masa faɗa sosai, tare suka shirya suka tafi wajan Umma, amma da ƙyar aka bar su suka kalleta, nan ma sai da Danish ya bada kuɗi masu yawa na cin hanci.

Duk maganan da suke yi Umma ko ƙala bata ce musu ba, bayan amsa gaisuwansu da ta yi, tambayan Umaima tayi da kuma matar yaya babba ko ta haihu, bayan sun bata amsa shiru ta ƙara yi, gaba-ɗaya sai tausayin mahaifiyarsu ya rufe su, ta zama abin tausayi ta rame ta yi baƙi, shiru ta musu har lokacin su ya cika, suka tashi za su tafi, sannan Umma ta buɗe baki ta ce, “idan yayi ku kawo mini Autana Umaima na gan ta.”

Cikin tausayin Umma, yaya babba ya ce, “Insha Allah Umma za’a kawo miki ita.”

Ficewa suka yi suka tafi, daga nan kuma suka ci-gaba da tattaunawa akan yan da za su yi Ummansu ta fito.

Gaba-ɗaya mun zama busy a maganan makaranta, ko kaɗan duk ƙoƙarin Ya Danish na ganin ya samu daman stayuwa da ni ta ƙi samuwa, har ya cinye weekend nasa, yau Sunday zai koma, dan haka yau ya dage komin dare to kamun ya koma sai ya haɗu da ni.

Ni da Umaima mun je tahfiz na yamma, mun dawo, muka yi wa junanmu sallama, ta shige gidansu nima na wuce namu, kai na a ƙasa ina sakin murmushi ni kaɗai, saboda hiran Soja muka gana yanzu da Umaima, ba tare da na kula ba na ji nayi karo da mutum na yi baya zan faɗi, sai aka riƙo hannuna, idanuwana a lumshe nayi hamdala sannan na buɗe su na ɗago ina faɗin, “Na gode….”, maganan baki nane ya maƙale ganin wanda na yi karo da shi, kuma ya riƙe ni ban faɗi ba.

Haɗe fiska nayi na ce, “Allah ya isa na, hannuna da ka taɓa.”

Maimakon na ga ya ɓata rai, ya fara ci mini mutunci yan da ya saba, sai naga saɓanin haka, murmushi yake sakar mini tare da faɗin, “Afuwan gimbiyata.”

Ƙara kallonsa nayi dan na tabbatar da shi ya faɗi abin da kunnena ya jiye mini, murmushi ya sakar mini tare da ɗaga gira guda.

“Hmmn!” Na faɗa tare da jan dogon staki, fiskana a haɗe na ce, “let me have my way.”

Murmushi yayi ya ce, “faɗa da hausa gimbiya.”

Wani bansan harara na aika masa da shi, sannan na ce idan ya na yiwa Allah da Manzonsa ya bar mana ƙofan gidan mu.

Ya Danish ko a jikinsa, ya ce, “Nima ya zama gidanmu ai, please Beb ki saurare ni, da farko ku yi haƙuri da abin da Umma ta yi, duk nine na ja, amma dan Allah a yafe mata, ki taya ni bai wa Mami haƙuri, Insha Allah next week zan shiga na bata haƙurin da kai na, and beb please ki yafe mini abubuwan da suka faru, ba da intention nayi ba, sharrin shaiɗan ne da kuma soyayyanki.”

Maganansa dariya ya bani, amma duk da haka na maste, ko kallonsa na ƙi yi, har Ya Danish ya gama shirmen maganganun sa ya tafi ko ƙala ban ce masa ba, yana barin wajan na ja dogon staki na shige gida, ina faɗin, “Ni za’a renawa wayo ɗan iska mara kirki, in ma da wani salon ka zo to duk ina dai-dai da su.”

Ya Danish cikin farin cikin ya bulbular da abin da ke ran sa ya tafi bayan ya ce mata, “ILOVE YOU BEB”, ko cikin gida bai koma ba, ya ja motansa yayi gaba, shi ko haka ma Alhamdulillahi ya gode wa Allahn da ya jarabce da da soyayyanta.

Ni kuwa mita na dinga yi, har Mami ta gaji ta buge mini baki, tana tambayan menene ya faru, faɗa mata nayi, maimakon ta goyi bayana, sai naga tana murmushi kawai, ganin haka ƙara kuluwa na yi, a haka kuma da fushina nayi bacci, Allah ya so ma idan na tuno soja inajin kukan ya tsaya sai kuma dariya akan abin da ya faru ranan.

Tun daga ranan duk bayan kwana biyu sai na ga ya Danish a Mubi, kuma idan ya zo ya dinga takura mini kenan, wulaƙancin da ya mini, ba irin wan da ban rama ba, har ma da alakoro na masa, amma ko a jikinsa.

Mami ta dage da maganan aurena, yau Alhamis muna zaune, Mamina ta ci kwalliyanta, daman jiya ta yi kistonta har da ƙunshi, ba tare da ta kalleni ba ta ce, “Faɗima.”

Murmushi nayi na ce, “Naam Mamina.”

Mami ta ce, “faɗima ki stayar da mutum ɗaya cikin masu nemanki, idan Aliyu ne ki faɗa masa ya turo, idan kuma Danish ne, za mu yi magana da Abbaanku, daman ina tunanin ko shi zai ba da aurenki.”

Murmushin taƙaici wan da ya fi kuka ciwo na yi, na ce, “Mami ban da uba ne? Ko da gaske ba ta hanyar Sunna kika same ni ba, Mami wallahi idan ba auran mutum kika yi ba, ni ban yarda ya zama waliyina ba, kuma Allah sai ana auren na gudu, nima na shiga duniya kawai kowa ya huta, nima na ɗaura daga inda kika tsaya…”

Ban ida rufe baki ba na ji sauƙan mari a bakina, wan da take bakina ya fashe, Mami cikin surutu take cewa, “Banafsha wato dan ina miki shiru, shi ne kika dage ko? To kuwa zan nuna miki ni ce mahaifiyarki ba ke kika haife ni ba.”

Idanuwana a bushe ba ko alaman hawaye na ɗago su, cikin dakiya na ce, “Mami ko kasheni za ki yi, ba zan auri kowa ba sai kin yi aure, Mami ke fa ranan kika faɗa mini Allah na son mai haƙuri, to me yasa ke ba za ki kasance cikin waɗanda Allah ke so ba? Me yasa ba za ki kasance cikin masu ɗaukan ƙaddaransu ba? Mami me yayi zafi shi ba wuta ba, Mami duk fa tsanani na tare da sauƙi, Ya mahaifiyata ki yi haƙuri, amma a yanzu ki samu Abbaa da maganar nan, kema kin san ba ki yi adalci ba Mami, kin ƙi sa kuma ki ce yayi wa yarinyar ki walittaka, ki duba lamarin da kyau.”

Mami masifa ta fara mini, in da take shiga ba nan take fita ba, ni kuma yau na dage ba zan yi aure ba sai ta yi, saboda ɓacin ran da Mami ke ciki tuni ta fara jibgana yan da muka saba idan na mata irin magannan, duk dukan da Mami ke mini bakina bai mutu ba, kuma babu ko ɗigon hawaye, abu ɗaya kawai nake faɗi, “wallahi Mami ko kasheni za ki yi, ki kashe ni, na yafe miki kuma, amma ba zan yi aure ba sai kin yi…”

Ban fasa surutu ba, Mami bata fasa dukana ba, muna cikin haka sai ganin Alhaji Mukhtar muka yi, ba zato ba tsammani, Alhaji da sauri ya janye Mami ya riƙe hannayenta yana faɗin, “Ramla ba ki da hankali ne? Me ke damunki? Kashe ta za ki yi?”

Mami kawai fashewa tayi da kuka ta ce, “gwanda na kashe ta na huta, tun da baƙin ciki da damuwa ita ma take son cusa mini, in kai ta mahaifinta an faɗa mata tana da uba ne? Bayan sanadinta na rabu da kowa nawa, farin ciki na, mai so na, iyayena, dangina,mastayi na, da komai nawa, duk dan saboda ita na haƙura da su, na zaɓe ta akan kowa nawa, har sau nawa take so na dinga sadaukar mata da farin ciki na? Haka iya wan da na mata bai isheta ba?”

Jin furcin Mami tuni hawaye yayi shaɓe-shaɓe a fiskana, kuka na kama bilhaƙƙi kaman rai na zai fita, me Mami take nufi da bata san uba na ba? Mutum na fita a jikin bishiya ne? Ko mace na haihuwa ita kaɗai ba tare da namiji ba? Ɗagowa nayi ina kuka na ce, “Mami bayan jin wannan furucin naki, sai na kuma samun ƙwarin guiwan ƙin aure, Mami ba zan yi aure ba sai kin yi, kuma sai kin koma ga danginki..”

Kamun na rufe baki Mami ta iyo kai na, ta hau jibgana, da ƙyar kuma Alhaji ya riƙe ta bayan ya ce na tafi, haka na tashi ina haɗa hanya na nufi ɗakina, amma ina shigewa kamun na isa ga gadona, tuni wani mugun jiri ya ɗibeni, inajin jiri-jiri, baya na yi luuu na faɗi, lokaci guda numfashina ya ɗauke.

Ɓangaren Mami kuka ta dinga yi sai da Alhaji ya dage da lallashi, cikin soyayya yake lallashinta ya ce, “haba Ramla, da girmanki da tunaninki da komai naki, kike irin wannan furucin? Me yasa ne wai ke baki yarda da ƙaddara ba? Me yasa ba za ki mata abin da take so ba?”

Mami kuka ta dinga yi mai matuƙar ciwo da cin zuciya, ba abinda take nanata wa sai istigfari, bayan Alhaji ya gama lallashinta da mata nasiha, sai ya ga kawai ta miƙe stuttt! Kaman wacce aka stikare ta, share hawayenta ta ci-gaba da yi, tana faɗin, “faɗima zan yi abin da kike so in zai sa ki farin ciki ki kuma yar da ki yi aure..” tana magana ta wuce ɗakin Banafsha, sai dai tana shiga daga bakin ƙofa ta tarar da ita a yashe a ƙasa bata ko numfashi.

Mami ganin haka, ihu ta stala tare da faɗin, “innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Faɗimana kada ki mini haka.”

Alhaji jin ihunta ya shigo da sauri, ganin halin da Banafsha ke ciki, da sauri ya ɗauke ta yayi waje da ita, Mami haka ta bi sa ba mayafi, sai shi ne ya koma ya ɗauko mata, sannan ya ja mota suka yi asibiti, Mami sai ƙoƙari take wajan danne ƙwallan da ke fito mata, kada ta yi hawaye wa yarinyarta.

General hospital Alhaji ya kai su, suna isa kuwa cikin sa’a suka samu Dr Arshan na duty, yana ganin Mami ya ganeta, nan yasa aka yi da Banafsha emergency, sai da ya dubata sannan ya sanar da su Mami kada su ɗaga hankali, suma ne tayi saboda wani abu da ta gani ko ta ji ya sa bugun zuciyanta ƙaruwa, ya firgita ta, amma zuwa ba jimawa za ta iya farfaɗo wa, ko zuwa gobe.

Alhaji da Mami ne suke zaune a kan Banafsha, Alhaji sai tausan Mami yake yana bata baki, har dare sannan ta farfaɗo tana sumbatu, Mami cikin hanzari ta rungumeta tana faɗin ta nistu ga ta nan kusa da ita, Alhaji kuma ya ƙira likita, sai da ya mata allura sannan a hankali kuma ta koma bacci yayi gaba da ita, tana sakin ajiyan zuciya.

Washegari da ta farka jikin ya zama normal, sai da ta ci abinci ta yi sallolinta, sannan Mami ta fara magana cikin lallashi, cewa tayi, “Faɗima ki kwantar da hankalinki kin ji, Inshà Allahu Maminki za ta yi duk abin da kike so da kuma abin da zai saki farinciki, zan yi aure kaman yan da kike so, sannan zan ba ki labarin dangina, zuwa gaba kuma Insha Allah zan haɗa ki da su.”

Ina daga kwance amma a take na tashi na zauna, kallon Mamina nake cikin farin ciki da ƙaunarta, me nake nema a duniya ina da Mamina? Tuni ma na ji ciwon da ke damuna duk sun fece, karo na farko a rayuwa da naji tabbas mastalana sun ƙare, ko ba komai indai Mamina za ta yi aure to shikkenan, alhamdulillahi abin da nake so kenan, ko maganan danginta bai dameni irin maganan ta yi aure ba, ai rungume Mami nayi cikin farin ciki, ina sauƙe ajiyan zuciya, yayinda Mami kuma ke ƙoƙarin mayar da ƙwallan da ke son zubo mata.

Dr Arshan ya zo ya duba ni, da mamaki ya tambayi me ya faru haka, har komai da ke damuna ya setu, daga yanayin bugun zuciya na har jinina da ke neman hawa ya wuce misali, murmushi kawai na masa da yake mun ɗan saba kwanaki da Mami ta kwanta.

Sai yamma sannan aka sallamemu, Alhaji ya jido mu muka dawo gida, bayan ya siya duk wani magani nawa da ake buƙata, kuma ya bi mun saya fruits da sauran su.

Muna dawowa gida da yake juma’a ne yamma ma ta riga da ta yi, sai ga Umaima ta shigo, ɗakina muka wuce da ita bayan ta gaishe da su Mami, muna shiga ta tambayi me ya faru bata ganni ba tun jiya, kawai faɗa mata nayi ban da lafiya ne, mun je asibiti kuma Dr Arshan ma ya ce a gaisheta.

Amsawa tayi ta mini Allah ƙara sauƙi, sai da muka taɓa hira sannan na shiga na wasta ruwa, na zo na kwanta, ita kuma Umaima ta yi wa su Mami sallama ta fice.

Mami ta biyo ni har ɗaki ta bani magani da abinci, sannan ta mini sai da safe bayan ta ƙara kwantar mini da hankali, kwanciya nayi ba jimawa bacci yayi gaba da ni.

A ɓangarena da yake yanzu na samu nistuwa, ba jimawa bacci yayi gaba da ni hankali kwance.

Mami kuwa gaba-ɗaya kan ta chaji ya ɗauka, dan haka ba su wani yi dogon hira da Alhaji ba, ta tashi ta shige ɗakinta, wanka ta yi ta shirya staff sannan ta fito, sai da safe ta yiwa Alhaji, kallonta yayi yana murmushi ya ce, “Ramla sai da safe kuma, ba za ki ce nazo mu kwanta ba? Ko kin manta ke kika ce na dawo kina buƙatata?”

Mami murmushin yaƙe tayi ta ce, “Ai nasan ko na ce ba zuwa za ka yi ba, dan haka Allah tashe mu lafiya”, ta faɗa tare da shigewa ɗakinta.

Alhaji murmushin shi ma yayi kawai tare da girgiza kai, ya ce, “Allah shirya mini ke cikin gaggawa ya nusar da ke gaskiya, ina matuƙar ƙaunarki da kuma buƙatanki Ramla, amma zan ci gaba da kiyaye wa har zuwa lokacin da zan mallake ki, sannan ke ma ina addu’an Allah baki ikon jure naki buƙatan, Allah stayar da duk wani mummunan ƙaddaran rayuwanki haka nan.”

Mami ko da ta shiga ɗaki, neman baccin tayi sama ƙasa ta rasa shi, kwanciya kawai ta yi tare da zubawa saman ɗakin nata ido, lissafi take akan yanzu wa za ta aura? Alhaji tana son sa ba kaɗan ba, amma tana tunanin kar nan gaba zargi ya zo cikin aurensu ko wani abu daban, tun da ita zuciya sai a hankali balle ma da a wannan harkan ya sameta, sannan Abbaa kuma tana gudun a ƙara samun akasi da Umma, ko kuwa Ummu ma ta kasa haƙuri nan gaba da kawo gori da tashin hankali stakaninsu, kishi masifa ce, duk iya daurewanka watarana sai an samu akasi, sannan bata buƙatan auren da za ta yi saki ya biyo baya, Abbaa tun da ya saki Umma uwar ƴaƴansa tana ganin ita ma zai iya sakinta watarana idan ta aure sa, Alhaji kuma idan ya zarge ta zai iya sakinta shi ma, kuma bata fata da addu’an tayi aure ta fita, cikin mugun damuwa Mami ta busar da zazzafan iska a bakinta, a hankali ta buɗe baki ta ce, “Allah ka mini zaɓin alkairi, Allah Astagfirullah! Na tuba maka Ubangiji na.”

Haka Mami ta kasance cikin zullumi, wan da har kan ta ya fara ciwo saboda tunani da nazari, so take ta yi auren saboda Allah kuma saboda Banafsha ma ta yi, ita ba ta da farin cikin da ya wuce mata tilon ƴar ta, kuma bata da burin da ya wuce ta aurar da ita cikin aminci da mutunci, dan haka za ta iya yin komai dan Banafsha, har da bayar da ran ta ma.

Daga ƙarshe Mami yanke hukuncin yin istihara ta yi(neman zaɓin Allah), tashuwa ta yi ta ɗaura alwala ta zo ta tayar da nafilanta raka’a biyu, sai da ta idar sannan ta karanto addu’anta ta gabatar da buƙatanta ga mahaliccinta, sai da ta idar ta shafa sannan ta samu nustuwa ta bi lafiyan gado ta kwanta.

Shi addu’an istihara ba wa iya aure ake yi wa ba, domin an karɓo daga jabir ibn Abdallah, cewa mun kasance tare da Manzon Allah SAW yana nusar da mu duk abin da za mu yi, mu nemi zaɓin Allah a kai(istihara), sannan yana koya mana addu’an, kaman yan da yake koya mana Surah daga cikin Alƙur’ani mai girma, kuma ita sallar istihara ba dole sai da dare ake yin ta ba, ana iya yin ta da safiya, da marece, da dare, da rana, hatta bayan la’asar da ba’a mata nafila, to mutum zai iya yin wannan sallah ta istihara, raka’a biyu sallama ɗaya, idan mutum ya idar, zai karanto addu’an kaman haka :-

ALLAHUMMAH INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA, WA ASTAƘDIRUKA BI ƘUDRATIKA, WA AS’ALUKA MIN FAD’LIKAL AZIM, FA’INNAKA TAƘDIRU WALA AƘDIRU, WA TA’ALAMU WALA A’ALAMU, WA ANTA ALLAMUL GAIBU, ALLAHUMMAH IN KUNTA TA’ALAMU ANNA HAZAL AMRA ( sai ka faɗi abin da kayi sallahn saboda shi anan ) KAIRUN LEE WA FI DINI, WA MA’ASHI, WA AƘIBATI AMRI, FAKDURHU LEE WA YASSIRHU LEE, SUMMA BARIK LEE FIHI, WA IN KUNTA TA’ALAMU ANNA HAZAL AMRA SHARRUN LEE WA FI DINI WA MA’ASHI, WA AƘIBATI AMRI FASRIFHU ANNI, WASRIFNI ANHU, WAƘDUR LIYAL KAIRA HAISU KANA SUMMA RADDINI BIHI.

Wannan ita ce addu’an, Ubangiji Allah ya tabbatar mana da alakiran rayuwanmu, Allah ya sa mu dace.

Washe-gari da safe sai da na lallaɓa na yi wa Mamina ayyukanta, sannan na shirya na fito muka wuce tahfiz tare da Umaima, ga mamaki na Ya Danish na tsaye a ƙofa yana bi na da kallo har muka wuce, amma ni ko nunawa nasan da halittansa a wajan ban yi ba.

Mun je mun yi karatu sannan an yanke tafiyanmu musabaƙa a cikin jimeta nan da sati biyu, akan mu sanar wa iyayenmu, kamun malamai za su zo har gida a sanar wa iyayen duk wan da za’a je da shi.

Ana tashinmu muka kamo hanyan gida, tafiya muke muna hira, faɗa wa Umaima nake Dr Arshan fa kaman son ta yake, dariya tayi ta ce, “ai ke dai sam bakya gani da kyau, kina ji mutum ya ce yana da mata kuma ba zai ƙara aure ba, balle a masa maganan adalci, shi ne kike wannan batun.”

Dariya nayi sabo da na tuna, masifan da nayi ranan akan ya duba ɗan uwan soja, bai Duba Mamina ba, shi ne na ce masa baya da adalci, ba zai iya riƙe mata biyu ba, haka muna hiranmu muka tinkaro gida, tun daga nesa na hangi mutum staye a ƙofan gidanmu, kuma sarai na gane Ya Danish ne, haɗe fiska nayi tare da jan staki na ce, “Mutum ba zuciya sam-sam haka Allah ya yi sa, ka gama ci mini mutunci ka zo kana ƙoƙarin lashe aman da ka yi.”

Umaima murmushi tayi dan ta san da wa nake yi, kallon ƙofan gidan mu tayi ta ce, “Masoyiya a taimaki yayana, Allah jiya ma in faɗa miki shi ya sanya ni zuwa na dubo ki ko lafiya, da na ce masa ba ki da lafiya kada ki ga yan da hankalinsa ya tashi, har ya bani tausayi, na ce Allah mai iko, kaman ba shi ya gama miko rashin kirki ba, ga shi Allah ya jarabce sa da son ki, dan Allah Masoyiya ki yi haƙuri ki yafe masa ki kula sa.”

Taɓe baki nayi na ce, “ke baki san waye yayanki ba ne shi yasa, baki san me ya mini ba, ni da ya Danish ko shi kaɗai ya rage namiji a duniya to ba zan aure sa ba, Malam Abbo na zan aura, Insha Allah.”

Sallama muka yi da Umaima ta shige gidansu, nima na wuce namu, ina isowa ƙofanmu kaman yan da ya saba ya fara mini magiya, tambayan ya jikina yake yi amma na yi banza da shi na shige gida.

Bayan na karya na huta sai Alhaji yayi ƙira na, zuwa nayi cikin ladabi na gaishesa, amsawa yayi tare da tambayan ya karatun namu da kuma jikinsa.

Murmushi nayi na ce, “Alhamdulillah!”

Jinjina kai Alhaji yayi tare da miƙo mini, leda mai ɗan girma ya ce, “Ga kyautan ki da na yi alƙawari, sannan an faɗa mini result naki, yayi kyau sosai a ƙara mai da hankali, yanzu kuma sai ki faɗi abin da kike so ko ƴar gidan Mami, idan bai fi ƙarfi na ba, Inshà Allah zan miki koma menene.”

Tun da Alhaji ya fara magana, nayi ƙasa da kai na ina wasa da yastuna, na jima da tanadar amsan da zan bawa Alhaji idan ya bani wannan daman, amma kunya nake ji na rasa ta ina zan fara, ajiyan zuciya na sauƙe tare da lumshe ido na cikin ƙarfin hali na ce, “ka yi haƙuri da abin da zan faɗa idan zai ɓata maka rai, amma shi ne iya abinda nake buƙata.”

Alhaji murmushi yayi cikin yabawa da hankali irin na Banafsha ya ce, “ina sauraranki Banafsha.”

A hankali na ce, “Alhaji dan Allah dan darajan Annabi da ƙur’ani, ka taimaka ka auri Mamina, dan Allah ku bar irin wannan rayuwan da girmanku, mu yaranku ba ma jin daɗi musamman ma ni, kuma nasan idan su Majeeder ma za su ji haka ba daɗi zai musu ba, dan Allah Alhaji ku mini wannan alfarman, wallahi shi kaɗai ne abin da nake buƙata daga gare ka, har ma da Mamina”, ina gama magana kuka ya ƙwace mini, amma na danne sautin kukan dan kada Mamina da ke kitchen ta jiyo muryana.

Alhaji aniyan zuciya ya sauƙe tare da kallona, yana murmushi ya ce, “In Allah ya yarda Banafsha zan auri Maminki, ke dai ki taya ni da addu’a da kuma shawo kan ta, Maminki ce sai a hankali amma in Allah ya yarda wannan karon zan dage kin ji, na miki alƙawarin yin abinda bai fi ƙarfina ba, dan haka auren Ramla bai fi ƙarfina in Allah ya hukunta hakan, kema kuma ina son ki daina saka damuwa a ranki, ki kuma cigaba da yiwa mahaifiyarki biyayya.”

Jinjina kai nayi cikin gamsuwa da maganansa, na gode sosai sannan na shige ɗakina, wanke fiskana nayi, sannan na buɗe ledan da Alhaji ya bani, kwali ne a ciki, na kuma buɗe wa, ganin wani ranstasten kyakkyawan system tuni na stala ihu ba shiri, ihun nawa har ya jawo hankalin Mamina ta shigo da sauri a firgice tana faɗin, “lafiya Banafsha? Menene ya saka ki ihu?”

Cikin farin ciki na nuna mata system da ke hannuna, ita ma da mamaki take bi na da kallo ta ce, “Banafshaaa ina kika samo computer?”

Ina murmushi na ce, “Alhaji ne ya bani yanzu, wai shi ne kyauta na”, ina faɗa na rungume Mami cikin farin ciki, ina faɗin ta tayani gode masa.

Abubuwan cikin ledan na ƙarisa cirowa, nan kuma wani sarƙa ya faɗo da ɗan kunnensa da zobensa, da abun hannu, masu shegen kyau da ɗaukan ido, Mami da ke staye, waro idanuwa tayi ta ce, “Gold dai?”

Ai ban staya ba, na fice palourn, amma na samu Alhaji baya palourn yana cikin ɗakinsa, komawa nayi ɗaki cikin farin ciki, ina kallon kyautan da Alhaji ya mini, sarƙan gold, system, ga kuma wani haɗaɗɗen dogon riga wan da kana gani kasan ya ci uban kuɗi shi ma, kayan ma dai ka san ba na Nigeria ba ne, farinciki kaman nayi yaya.

Mami komawa tayi ta ƙarishe aikinta, ta shirya sannan ta shiga ɗakin Alhaji, samunsa tayi yana waya da yaronsa, murmushi tayi tare da zama a ɗan nesa da shi, har sai da ya gama, ya dubeta yana murmushi ya nuna mata gefensa, amma Mami sai ta gyaɗa kai kawai, cewa ta yi, “Alhaji sannu da hidima mun gode Allah saka da alheri.”

Murmushi Alhaji yayi ya ce, “Kada ki gode mini Ramla, dan kin cancanci fiye da haka a wajena, kuma duk wani wan da ya shafe ki zan masa fiye da haka, Ramla soyayya nake miki na tsakani da Allah, ranan na iso ana cikin yanayi mara daɗi ne shiyasa, amma ke ma ga naki staraban na Egypt ɗin”, Alhaji ya faɗa tare da miƙa wa Mami wani jibgegen leda.

Amsa Mami tayi, tana jin kaman ta rungume Alhaji, amma tasan ba zai so haka ba dan yan da yake gudun abinda zai saɓawa Allah, ita kuma ba za ta masa abin da bai so ba, dan haka cewa tayi, “To ka zo mu karya rankashidaɗe.”

Alhaji miƙewa yayi da murmushi ya bi bayan Mami, ni ma Mami ƙirana ta yi, duk muka karya, na godewa Alhaji sosai, amma ya nuna ba komai nima ƴar sa ce.

Mami kuwa kayan a Alhaji ya kawo mata, dogayen riguna ne na Egypt masu shegen kyau kusan kala biyar, sannan da wani haɗaɗɗen waya ta yayi Redmi, ga turaruka, ita ma har da sarƙanta na diamond, da takalma, sai kuma wasiƙan soyayya da ya jefa a ciki, Mami duk da ba wannan bane karo na farko da Alhaji ke mata kyauta, amma farinciki kaman ta yi kuka, musamman kalaman da yayi amfani da su a wasiƙan nasa.

Washe-gari Lahadi, muna zaune da Alhaji da Mami sai aka mana sallama, Alhaji ne ya fita ganin mai sallaman, gaisawa suka yi, da ya faɗa masa ya zo gaishe da Mami ne sai ya masa iso, tun da ya shigo nake kallonsa da mamaki, Ya Danish a cikin gidanmu, yau wace rana, amma sai na dake na miƙe na shige ɗakina ban ce masa ko sannu ba.

Mami cikin fara’a suka gaisa da Ya Danish, ya tambayi jikin Banafsha ta amsa masa da sauƙi, suka gaisa da Alhaji kuma, sannan ya ajiye ledan da ya kawo da kaya niƙi-niƙi na dubiya, sallama ya yiwa Mami ya tashi zai tafi, sai Mami ta ce, “Banafshan tana zuwa ko.”

Ya Danish a waje ya staya jirana, ni kuma ina ɗakina kwance ina danne-danne a system na(su Banafsha duniya sabuwa, ƴan gayu ƴan uwan masu nuƙud), Mami shigowa tayi da sallama, tun da na kalleta na tura baki dan nasan ba zai wuce ta ce naje ba, ai kam hakan ne kuwa, fiska a haɗe ta ce, “kin ga mutum kin tashi kin gudo ɗaki, ko gaisuwa babu kuma kin san wajanki ya zo ko, to maza kamun na ɓata miki rai ki tashi ki je waje yana jiranki, kuma idan kika amsa rashin kunya sai na saɓa miki, yarinya hankali sam-sam babu, wa ya faɗa miki ana wulaƙanta ɗan adam, maza tashi ki wuce”, Mami na gama magana ta fice tana ƙwafa.

Ni kuwa tura baki nayi, sannan na miƙe, mayafi kawai na yafa na fice, fuuu! Haka na wuce su Mami a palour na yi waje, a cikin haraban gidan mu na tarar da shi, ƙara haɗe fiska nayi sannan na ƙarisa wajan da ya ke tsaye, ko kallonsa ban yi ba balle ya sa ran zan masa magana.

Ya Danish cikin damuwa ya ce, “dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mini, haka nan ki kulani Banafsha, wallahi da gaske nake son ki, kibar tunanin wani abu, idan kuskuren da na aikata rana ne ma wallahi ba da niya na yi ba, kuma ko da ace Abbaa ba su iso sun same mu haka ba wallahi ba zan iya ƙeta wa wata mutunci ba balle kuma ke, ki yi haƙuri.”

Tsaki na ja na ce, “Dole ka ce ba da niya ba tun da dole aka saka ka, ka yage mini hijabi, ka haɗa jikinka da nawa, har da bakinmu ka haɗe, sannan a haka ka ce ba niya? Ka dai ji baiwa ne a jikin sai ka ga gwanda ka yaudareni ka aure ni ko, to bari kaji ko maza sun ƙare ba abinda zan yi da kai, ballema ina da wanda nake so, kuma kwanannan za ka ji an yi aurenmu.”

Danish ji yayi kaman ta wasta masa ruwan zafi ne a zuciyarsa da wannan kalaman, kaman zai yi kuka ya ce, “Wallahi sharrin zuciya ne, saboda irin kalaman da kike faɗa mini..”

Saurin dakatar da shi nayi na ce, “nake faɗa maka ko kake jifana da su? Ko ka mance ka ce mini ƴar iska mai bin maza? Ko ka mance cewan da ka yi bana da abin da za ka taɓa? A haka ka yi kokarin ƙeta mini mutunci ka kuma zo yanzu da niyan aurena wai a faɗanka, duk ka mance abin da ka faɗa ne? Ta ina naga abinda za ka taɓa? Sannan ka ƙirani da mara tarbiya, shashasha ƴar iska, ka sanya hannunka a jikina kuma da sunan duka, ban da duk waɗannan ma abu mafi muni da na stana a duniya, sunan da bana son sa bana ƙaunarsa, sunan da yake ƙaddara ga rayuwata, ka ƙira ni da shi Danish, ƳAR KARUWA MARA TARBIYA, ka faɗa mini, sannan a haka kake tunanin na so ka har na aureka? To tabbas ka yi wa kanka ƙarya, dan na tsaneka! Na tsaneka! Na tsaneka! Bana ƙaunarka bana son ka, bana son kallonka, ko mai irin sunanka bana ƙauna, kai ka sa na stani maza na stani aure, amma Alhamdulillahi yanzu da nayi gwanina mai ilimi da sanin ya kamata to naji ina son aure kuma zan aure sa.”

Ya Danish runste ido yayi kaman wan da aka kikkifawa mari, guiwansa ya saka a ƙasa ya ce, “Duk abinda kika faɗa ba sharri na faɗe su kuma na yi su, baki ƙara komai ba sai ma ragewa da kika yi, kuma nasan na yi ba dai-dai ba, ban kyauta ba, bayan haka uwata ta yiwa mahaifiyarki illa, dan Allah da Manzonsa ki yafe mini, dan darajan Annabi ki yafe mini, duk abin da na miki kuma idan ba ki manta ba, babu wanda baki rama ba a take ma kuwa, sannan ga shi Allah ya ɗaura mini soyayyanki, ki yi haƙuri Banafsha, ina sonki ina ƙaunanki dan Allah, ko da baki aure ni yanzu ba, zan zauna dakon jiranki har idan Allah ya sa ke rabona ce, to mijin zai bar mini ke ko kuwa zai mutu na aureki.”

Jikinane yayi sanyi saboda yan da ya haɗa ni da Allah da Annabi, wan da ya halicce ni da kuma wan da aka halicci dubiya baki ɗaya saboda shi, Allah ya wuce komai ya wuce abin wasa, sannan kana ɗan Adam bai kamata a ce ka yi abu dan Allah ko Annabi ka ƙi yi ba, sannan na tuna maganan Mamina na ranan akan haƙuri, dan haka ajiyan zuciya na sauƙe tare da faɗin, “Na yafe maka duniya da lahira, komai kuma ya wuce, amma dai ka sani ina da wan da nake so, kuma in Allah ya yarda idan ya aure ni mutuwanma tare da shi zan yi”, ina gama faɗan haka na juya na shige gida.

Ya Danish ajiyan zuciya ya sauƙe jin na yafe masa, sai ya ji wani abu mai nauyi ya sauƙa masa a zuciya, domin kuwa tun ranan da yayi ƙoƙarin ƙeta mata mutunci shikkenan abin yake damunsa, tun da yasan nan gaba shi ma uba zai zama.

Ni kuwa ina shiga gida na wuce ɗakina, ko ta kan ledan da Mami ta nuna mini ban bi ba.

Alhaji dai ya kasa haƙuri sai da ya yiwa Mami magana Danish, faɗa masa komai ta yi bata ɓoye masa ba, har da akasin da suka samu da mahaifiyar sa, da kuma son ta da Abbaa ke yi, Alhaji ya ji kishi jin wani na son Mami har ga yaronsa ba son Banafsha, sai ya ji ina ma shi da yaronsa ne za su mallaki Mami da ƴar ta, amma dai Alhaji sai ya ɓoye bai nuna ba, addu’a yayi kawai da fatan alkairi.

Ya Danish a ranan da yamma-yamma ya koma wajan aikinsa, cike da ɗimbin soyayyan Banafsha, musamman ma da ta ce ta yafe masa.

Bayan sallahn isha’i kuma sai ga Malam Abbo, Alhaji da yake ya sheda sa shi kam, gaisawa suka yi, suka gaisa da Mami sannan suka bamu waje, sai da na ɗan shafa kwalli da man baki sannan na fito, cikin fara’a muka gaisa da Malam Abbo, nan ya fara baza hajar soyayyansa yanda ya saba, kalamai masu shiga jini da jijiya, su tsaga ƙashi da ɓargo su kai maka har ƙwaƙwalwanka, gaskiya wan da ya ce ustazai ba su iya soyayya ba sai wa’azi to gaskiya yayi kuskuren fahimta, gaba-ɗaya Malam Abbo idan yana kalamansa tafiya yake da tunanina.

Malam Abbo ya jima sannan ya mini sallama ya tafi, ni kuwa na shige ɗakina cikin dimbin tunanin Malam Abbo da soyayyar sa da nake ji yana kama ni.

Washe-gari Litinin, Alhaji sai da ya ajiye ni a makaranta sannan ya wuce zai koma gidansa, wannan karon bai jima ba saboda yana da shungulla, ina makaranta Malam Abbo ya zo suka gaisa da Mami ya faɗa mata batun tafiyanmu Yola musabaƙa, Mami ta yarje ba komai bayan ta musu addu’an nasara, da kuma roƙon a kula musu da yara, kada a ci amanan iyayen yara a ɓata musu tarbiyya.

Bayan na dawo makaranta, Mami ta faɗa mini, sai lokacin ma na tuna nikam, na faɗa mata ai muma an faɗa mana na sha’afa ne, murmushi kawai Mami ta yi ta ce, “je ki wasta ruwa ki ci abinci, idan kun dawo makaranta zuwa anjima za mu yi magana ko.”

Amsawa nayi na miƙe n shige ɗakina, ruwa na watsa sannan na ci abinci na yi sallah, shirin tahfiz kuma na yi, sallama na yiwa Mami na fice muka tafi tare da Umaimata.

Bayan mun je mun dawo, zuwa dare muna zaune da Mamina ta dubeni ta ce, “Banafsha!”

Da murmushi a fiskana na ce, “na’am Mamina.”

Ajiyan zuciya Mami ta sauƙe ta ce, “Banafsha na sadaukar miki da abubuwa da dama a rayuwata, tun kina ciki har zuwan ki duniya, ban taɓa gajiya ba kuma bana fatan gajiya watarana indai zan sa ki farin ciki, kaza bata taka ɗan ta saboda bata son sa, a’a saboda tarbiyya take haka, nasani kina da tarbiyyan da na baki dai-dai gwargwado, kina jin maganata kuma kina kiyaye ɓacin rai ba, Banafsha ina da dalilin ƙin aure, amma kuma dalilin nawa bai kai naki ba na yan da kike so nayi aure, Allah ya ce ko iyayene idan suna ba dai-dai ba ka faɗa musu gaskiya, dan haka zan yi abin da kike so, nasan ke ma ba ƙin abinda nake so kike yi ba, zan yi aure da yardan Allah, zan kuma baki labarin dangina kaman yan da na faɗa, zuwa gaba kuma zan kai ki gare su, aure dai yanzu zan yi, labari kuma zan baki shi ne a matsayin kyautan bikinki, dan haka idan kin amince kin turo miji to kin shirya jin labarin Maminki.”

Ajiyan zuciya na sauƙe cikin sanyin jiki na ce, “Mami Allah nima ina son ki kuma zan iya sadaukar da komai saboda ke da farincikinki, ki yi haƙuri ki yafe ni idan na ɓata miki.”

Murmushi Mami tayi ta ce, “Ya isa haka Banafsha, yanzu dai ke ce ƙawar Maminki, ke ce mahaifiyar Maminki, kuma mahaifin Maminki, ƙanwata, yayata, yarinyata kuma komai na, dan haka sai ki bawa Mami shawara wa ya kamata ta aura tsakanin Abbaanku da Alhaji”, Mami ta ƙarishe maganan tana murmushi.

Wani farinciki ne ya lulluɓeni, tun ba’a je ko ina ba, na fara ganin sakamakon haƙuri da kuma jarrabawan rayuwa da na shiga, Mamina ke mini wannan magana, lallai uwa-uwace, bai ma kamata mutum ya haɗa soyayyan mahaifiya da na kowa ba a duniya, cikin ƙaunan Mamina na ce, “Mami tsakani da Allah da farko Abbaa nake so ki aura, amma yanzu na fi son ki aure Alhaji.”

“Saboda me kika so na auri Abbaa kuma kika fasa, Sannan saboda me kika ƙi Alhaji yanzu kuma shi kike so Maminki ta aura.”

Murmushi nayi na ce, “Mami da farko na ga ƙoƙarin Abbaa ne na stawon shekaru yasan irin rayuwan da kike yi amma yake dakon soyayyanki har zuwa yanzu da ya faɗa miki shiyasa na so ki aure sa dan gani ga Umaima ta, amma kuma da wannan abu faru sai hankalina bai kwanta da hakan ba, Abbaa ya saki Umma kuma saboda ke yana son aurenki, to bana son kema ya miki haka nan gaba, sannan kar Umma ta kashe mini Mamina.”

Murmushi Mami tayi ta ce, “Sayyada Faɗima, ina jinki shi kuma Alhaji fa.”

“Uhmñ! Mami haushinsa nake ji saboda yan da yake zuwa gidannan yayi kwanaki, kuma da aurensa da yaransa, yana ta ɗawainiya da mu wataƙila baya yi wa matansa da yaransa, shi ne bana so dan kada ya aureki ya miki haka, amma yanzu na fahimci ba haka bane, da gaske Alhaji yake son ki, dan Allah Mamina ki amince ki aure sa, wallahi ko ba za ki kai ni wajan dangin babana ba to na yarda ya bayar da aurena.”

Mami jinjina kai ta yi ta ce, “Madalla da yarinya ta mai halin manya, tunanin nesa da kuma nazartan rayuwa, Allah miki albarka Banafsha, naji shawaranki kuma na ɗauka indai hakan zai saka ki farin ciki, amma kuma zan cigaba da neman zaɓin Allah, kema ina son ki dage da addu’a da istihara duka, tsakanin Aliyu da Danish Allah zaɓa miki mafi alkairi, idan dukan su ma ba alkairi bane, to Allah baki nagari wan da ya fi su, saboda duk halin da kuke ciki da Danish na sani, ina kallonki ne kawai da ido, to ki dena ki bari bana so, ba kyau wulaƙanta mutum dan ya ce yana son ka, aya ce guda a ƙur’ani mai girma cikin Suratul baƙara da ya ce, “ASA AN TUKRAHU SHAI’AN WA HUWA KHAIRUN LAKUM, WA ASA AN TUHIBBU SHAI’AM WA HUWA SHARRUN LAKUM” dan haka ina son ki cire stanan kowa a ranki ki yi addu’an alkairi kawai, Allah miki albarka ya tabbatar mana da alkairi.”

Da, “Ameen” na amsa cikin gamsuwa da maganan Mamina.

Haka rayuwa ta din ga tafiya Umma har yanzu tana kulle kuma tukunna ba’a fara shari’anta ba, amma dai an kai Court ɗin, kuma ana ƙoƙarin farawa.

Ɓangare na kaman yanda Mami ta mini faɗa to naji, addu’a nake na neman zaɓin Allah, idan Ya Danish ya zo ba hantara ba komai zan kulasa amma dai ba dan ina jin son sa a rai na ba, Malam Abbo ma duka ina kula shi.

Ɓangaren Mamina ma ta cigaba da addu’a, kuma zuwa yanzu Alhajin ne take jin ya kwanta mata a rai, dan haka ba ɓata lokaci ta fara shiri tana gyaran jikinta, ni ma tana bani wasu abubuwan.

Bayan sati biyu komai sai hamdala, Case ɗin Umma, su ya Mus’ab sun dage yanzu dai nan da sati guda za’a fara sauraran Shari’an.

Ni da Umaima kuma mun shirya staf dan washe-gari ne za mu tafi Yola ɗin, Abbaa kuma tun da ya je Mami ta basa haƙuri shikkenan ya haƙura ba dan ya so ba, sai dan ganin Mami da gaske take ba za ta auresa ba.

Washe-gari ranan tafiyanmu, a ranan matar yaya babba ta haihu, Umaima an kai ta wajan Umma, ta sha kuka ba kaɗan ba sai da Umma ta rarrasheta ta bi ta da addu’an alkairi a musabaƙan.

Mun shirya tare da sauran ɗalibai da malamai, mota ce babban ta jide mu muka nufi Yola, sai da muka kwashe awanni uku zuwa huɗu sannan muka isa cikin ikon Allah lafiya-lafiya, a wani babban makaranta aka mana masauƙi, akwai masu kula da mu da komai, ɓangaren mata daban na maza daban, haka ma na malamai, sannan har da jami’an staro akwai ana kula da shige da fice na kowa.

Satinmu guda curr a a Yola aka gama musabaƙa, muka juyo cikin farin ciki sai addu’an sauraran sakamako, daga dawowanmu kuma aka fara shirye-shiryen yaye mu, dan ba zai wuce wata biyu ba nan gaba, wan da ake saka ran kamun a yaye mu idan Allah ya sa mun yi nasara a wannan musabaƙa da muka yi, to sai mu je kuma na ƙasa da ƙasa a garin Abuja.

Mamina ta ƙira Alhaji ta sanar da shi ta amince da batun aure, Alhaji saboda farin ciki ya rasa ma me zai ce, ko me zai yi, abu na farko dai da yayi ya bata goron kyautan kujeran Makka na albishir ɗin da ta masa ta amince, sauran abubuwan kuma ya ce sai ya zo, sannan ya tura mata kuɗaɗe masu yawan gaske akan ta fara shirya masa kan ta tun yanzu, irin maganganun da Alhaji ya fara faɗawa Mami yana sakin layi tuni ta ji a karo na farko ta fara jin kunyarsa, dan kaman wan da aka ce masa an basa budurwa kyauta.

Mami shiri ta fara ba kama hannun yaro, mu kuma lokacin muka fara test a college, idan ka kalli Mamina za ka ɗauka wata balarabiya ce, sosai take gyara kan ta.

*****

ACM Bunayd gidan Papi ya wuce, yana danna horn aka buɗe masa ƙofa ya shige, da sallama ɗauke a bakinsa ya shige cikin gidan, samun Hajiya Sa’adatu yayi a hakimce a kan kujera tana kallo.

Amsawa tayi tare da sakin murmushi ta ce, “Bunayd iso ka zauna.”

ACM Bunayd murmushin da yake iya leɓensa yayi, a fili ya ce, “Ai gidan babana ne Mom, ba sai kin ce na zauna ba”, ya faɗa tare da zama, ya gaisheta.

Hajiya Sa’adatu amsawa tayi dan abinda ya faɗa bai dameta ba, tambayansa tayi jikin abokin nasa, ya amsa mata da sauƙi a taƙaice, wayansa ya fidda yana dannawa, sai can ya ce, “Wai ina yaran nan ne na ji gidan shiru?”

Hajiya Sa’adatu hankalinta na kwana TV ta ce, “suna sama ne ina ji, kasan Majeeder ba ji take yi ba, ni duka sun fitineni ma, kai ba da haihuwa da yawa ba, kai bakinka yayi stayi, yaushe za su koma gidansu ne?”

Murmushi Bunayd yayi ya ce, “Insha Allah gobe za mu koma gidanmu Maa!”

Hajiya Sa’adatu juyowa tayi ta kallesa ta ce, “kaga wannan sunan naka na rena mutane ba son sa nake ba, ni ce maa ɗin? To ranka zai ɓaci, ai ita Huraira baka faɗa mata haka Momsee kake ce mata tun da ita ta haifeka ba ni ba, kuma kai ai nan gidanku ne ba can bane gidanku.”

Bunayd shafa kiston kansa yayi ya ce, “To ai mastala da aka samu kika ki riƙe ni, ita ta riƙe ni shiyasa amma dai ki yi haƙuri Mom, da ni da su Ramla duk abu guda ne, idan can gidansu ne to nima can ne gidanmu, idan kuma nan ba gidansu bane to nima ba gidanmu bane, dan ni nafi son su a kan Majeeder ma.”

Hajiya Sa’adatu ƙwafa tayi ta ce, “Zan kuwa shiga ƙafan wando guda da kai.”

Ɗan murmusawa yayi ya ce, “wannan kam sai da Papi, ni ina wando guda xa ta ishemu da ke Mom.”

Hajiya Sa’adatu murmusawa tayi jin amsan da ya bata, ta ce, “Allah ya shiryaka.”

“Ameen”, ya faɗa tare da miƙewa ya haura sama, samun su Majeeder yayi suna ta hira suna dariyan shirme akan wai wani ya ce yana son Ramla a wajan bikin Ya Abeed, ganin Bunayd sai duk suka yi shiru, suka yi zuru-zuru da idanuwa, waje ya samu ya zauna ya ce, “Idan duniya da gaskiya ku yi hiran na ji nima na samu na yi dariya?”

Duk dariya suka kwashe da shi, sai kuma Bunayd ya gimste fiska, ganin haka duk sai suka sha jinin jikinsu, a daƙile ya ce, “maza ku tashi ku shirya na kai ku yawon da kuka ce, sannan muna dawowa ku shirya gobe za mu wuce”, yana gama magana ya fice.

Su kuma cikin farin ciki suka miƙe, har da stalle, sharp-sharp har sun shirya, sauƙowa ƙasa suka yi suka same sa, nan ya ja su suka fice, yawo ya kai su ba na wasa ba, zagaye Kano suka yi, aje nan aje can, suka je babban Shopping-mall ya musu siyayya, sai dare suka dawo gida, yana ajiyesu ya ce, “Ku tabbatar kun shirya da wuri.”

Majeeder ta ce, “yaya har da ni?”

Haɗe fiska yayi ya ce, “Bayan kin je kuma wani zuwan kikeson yi, wa zai miki karatun?”

Tura bakinta tayi, amma Bunayd ko kallonta bai yi ba ya ja motansa tare da yin ƙwafa yayi tafiyansa.

Ɓangaren Abeed kwana yayi ƙafansa yana ciwo, ga shi kuma abun daman a cinya ne, daurewa yake ya kasa, a haka ya kwana a daddafe, Nusaiba hankalinta a tashe kaman za ta yi kuka, duk da ciwon da Abeed ya ji mata amma shi take tausayi, ko ta kanta bata yi.

Washe-gari da sassafe Abeed ya ƙira Bunayd wanda ya gama shirin tafiyansa staff, Abeed faɗa masa an samu akasi yayi, Bunayd kuwa cewa yayi tun da shi ya kasa haƙuri shi ya nemawa kansa dan haka ba zai hanasa tafiya ba yana da abin yi a gida, dan haka sai da ya biya ya ɗau su Ramla sannan ya bi gidan Abeed, ya jide su suka yi asibiti.

ACM Bunayd sai da ya gama seta komai tare da likitan da zai duba Abeed sannan ya masa sallama ya ja ƙannensa suka tafi, Abeed sai ƙwafa yake, ya gode Allah ma an ce mastalan ba sosai bane, kwana ɗaya kawai zai ji sauƙi, idan yana son kada ƙafan ya dinga damunsa to ya bari sai nan da sati biyu zuwa uku kamun ya cigaba da amarci.

Jirginsu Bunayd ya sauƙa a Lagos da wuri, tuni dakaransa suka zo suka jide su a airport da shegun motocinsu masu ɗan banzan gudu, har sun nufi banana island amma sai ya ce musu Victoria Island za su kai su, nan suka yi gidan Affa General.

Suna isa ya shige ciki, su Suhaila kuma suka tattara kayakinsu su ma suka yi ciki, lokacin General baya gida sai Momsee kawai, dan haka da kanta ta yi wa yaranta abinci ta kai ma Bunayd har sashinsa, amsa yayi ya na godiya, Momsee kunnensa ta ja ta ce addu’a ake yiwa iyaye, godiya kam wannan dama ɗawainiya ne da ke kan su kula da yaransu, Bunayd sosai yake son Momsee, sai da suka taɓa hira ma sannan ta fice ta bar sa, ya ɗan cika cikinsa ya wasta ruwa, lafiyan gado ya bi ya kwanta, amma ya ciro waya ya ƙira Abeed tukunna, yana ɗauka Abeed ba ko sallama ya ce, “mugun ACM kawai, to ta Allah ba taka ba har na dawo gida kuma zuwa gobe zan warke.”

Murmushi Bunayd yayi ya ce, “Daman ai komai ta Allah ce, kuma dama haka nake so ka koma gida da wuri ka ɗaura a inda ka staya, ba dai ka ce babu haƙuri ba, to ka ji ai, tana tare da kai ka bari ka warke just week kawai ko cinye ta ka yi, amma just 1 night ka kasa, to stayuwan me zan yi nima ga shi na dawo lafiya.”

Abeed ƙwafa yayi ya ce, “ɗan banzan likita da yake bai da mata may be shi ne wai na jira 2 week’s kamun na ƙara, ai ba hauka nake ba, halan bai san daɗin abin ba ne, ko kuwa matarsa Salam ce.”

Bunayd na dariya ya ce, “sunan wata wai Salamatu ba, hhh, to kada ka haƙura, ai ka dinga ciwo kenan ba ruwanmu.”

Abeed ya ce, “Zan dai bar ta sati guda ta warke ita ma, amma kuma daga nan ba ɗaga ƙafa, sai dai ciwon ta dinga tashi kullum ina asibiti, ni da matata ma zan koma Adamawan haka kawai,wannan duniyar hidiman ba za ta wuce ni ba, kai amma gaskiya ACM an sha ka wasa, wai yanzu dai kana nufin baka san daɗin tukunyar zuma ba? Hhh honeypot duniya ne, Allah ƙarawa mata lafiya da ni’ima, ni nayi gaba sai ka zo.”

Waya suka ci-gaba da yi cikin barkwanci, har suka yi sallama Bunayd ya kwanta baccinsa.

Ko da Bunayd ya farka mamakin mafarkin da yayi yake, shi har ya mance da wannan yarinyar, ƙwafa yayi kawai tuna kallon da ta masa bai mata komai ba har ya taho, dan idiot da ya ce mata is not enough.

Ɓangaren su Abeed haka ya daure yayi 2 week’s a daddafe yana kewan tukunyar zuma, amma a ranan cewa yayi baisan zancen ba, tun da garin Allah ya waye, ya fara bin Nusaiba da wani narkakken malalacin kallo wan da sai da ta ji a jikinta yau akwai yaƙin sojoji kuma, dan haka cikin dabara ta ƙara shirya kan ta da duk abin da ya kamata, ta kurɓa, su dangin fruit, a daddafe Abeed ya sa ta shirya suka je gidansu, ko bari bai yi ba sun wuni ya ce su dawo, tun a hanya ya fara rikita mata lissafi, Nusaiba langwaɓe kai ta yi ta ce, “my captain ka bari kada mu yi hastari.”

Abeed wani kallon so ya sakar mata, tare da faɗin, “your wish is my command babyloff”, tuƙi yayi da mugun gudu, suna isa gida kuma ya ɗagata caɗak yayi ciki da ita, tun daga palourn ya fara bata passionate kisses, Nusaiba cewa tayi a bari sai dare, Abeed ya ce baya fahimtan Yaren da take yi, ɗaga ta yayi suka wuce ɗaki, bai direta ko ina ba sai stakiyan gado, ya bi ta ya haye jikinta.

Wani irin soyayya suke gwadawa juna mai matuƙar stayuwa a rai da zuciya, Abeed kaman maye haka yake lashe ta ko ta ina, ba abinda yake marari kaman ya ji mandhood nasa a honeypot, haka sai da ya tabbatar ya gama lalata lissafin nusaiba sannan ya fara neman hanyarsa, dan zuwa lokacin Nusaiba ma ta gama goge masa sauran haddan kansa, bata staya wani duhun kai ba ta solle mijinta soso da sabulu, tun da ya isa inda yake son zuwa, kuwa ba abinda kake ji sai sumbatunsa, Nusaiba dai yau zafin da sauƙin, dan haka ita ma taya da kukan daɗi take yi, wan da ke ƙara zautar da shi, stawon lokaci suka ɗauka suna hidima har suka samu nistuwa a lokaci guda, wanka suka yi tare ya gasa ta, sannan suka zo suka bi lafiyan gado suka kwanta.

Abeed na tashuwa bacci jin ƙafansa lafiya lau, sai kuma ya fara neman ƙari, nan Nusaiba ta ba da kai bori ya hau, amarci kawai suke ci ba ƙaƙƙautawa.

Bayan wani lokaci Bunayd yanzu ya zama so busy, yau yana ƙasar nan gobe yana wancan, yanzu haka ma yana Turkish ne, gidan da Suhail yake a can ya ke zaune, haɗaɗɗen gida ne na gani na faɗa, zaune yake a palourn tare da Suhail suna game wanda ake yin sa a abu kaman tv, ƙira ne ya shigo wayan ACM Bunayd, ganin layin Papi sai ya murmusa tare da ɗauka, cikin zolayan mahaifin nasa ya ce, “good day Sir.”

Alhaji murmushi yayi ya ce, “Ina farinciki ba zan biye maka ba, albishir.”

ACM Bunayd ya ce, “goro Papinmu, yau dai nishaɗi ake ji za’a wa ɗan fari albishir.”

Papi ya ce, “Sai ka cika alƙawarinka, ka mana kaya na gani na faɗa.”

ACM baisan san da dariya ya ƙwace masa ba ya ce, “Yanzu Uwata za’a yi wa kishiya shi ne ni zan yi kaya?”

Papi ya ce, “har da sadaki kai za ka biya, wa ya ce ka yi alƙawari.”

Bunayd yana murmushi ya ce, “Allah tabbatar da alkairi, in Allah ya yarda komai normal Papi baka da mastala, ni na zama ɗan Amarya ma atou, dan haka zan gwangwaje Uwata Amarya, Allah nuna mana, yanzu dai Papi har za ka ƙara second wife ban yi aure ba, Gaskiya to ba zan bari General ma ya ƙara ban yi ba duk da ba zamu bari ya yiwa Momsee kishiya ba, ita kam tana ƙoƙari, Mamata Amarya ma watarana dole mu nuna mata hali muna taya uwarmu kishi.”

Dariya Papi yayi ya ce, “Allah shirya ka ya baka tagari, kuma idan ka yiwa matata hali zan saɓa maka ne.”

Ɓata fiska Bunayd yayi ya yiwa Papi sallama kawai, dan ya ce Allah basa tagari shi ne ran sa ya ɓaci, Suhail da yake yana jin su dariya yayi ya ce, “easy!easy!easy dai ACM.”

Murmushi Bunayd yayi kawai, a take ya ƙira General ya faɗa masa, sannan ya haɗa su da Momsee ya faɗa mata zai saka mata kuɗi za’a haɗawa Papi lefe, dariya Momsee ta dinga yi, wato shi Bunayd ba ya kishin uwarsa, shi kuwa da an ce baya kishin Mom sai ya ce, ai ita ta ja, wa ya ce ta kasa renon sa, shi ko ajikinsa ya koma ɗan amarya, sai da suka gama magana da komai sannan suka yi sallama.

Ya ƙira Abeed ma ya faɗa masa, shi ma Abeed ɗin dariya ya dinga yi ya ce, “Kai fa ɗan iskan yaro ne wallahi, General ya lalata ka da yawa, wato ma ka zama ɗan Amarya?”

Bunayd taɓe baki yayi ya ce, “iyye, yanzu ma Momsee za ta haɗa ma mamana Amarya lefe, kuma sadaki ma mai stadan gaske zan biya, Allah dai ya sa kada ta bani kunya, Allah sa ta kula da Papi sosai, kuma Allah sata haihu da yawa ta ci gado tun da Mom bata son gado.”

Abeed me zai yi idan ba dariya ba, ya ce, “To saura watarana halinka ya mosta ka mata halin ɗan kishiya, ba ruwan Papi da kai ka biya amsa sadaki, tuni ya ci ƙaniyarka.”

“A’a rabani da mata halin ɗan kishiya, ai ana tare ni da Amaryan Papi ta koma Uwata, na bar wa Majeeder Mom, idan naga tasan duniya ma tuni na ce ta nema mini mata ko a danginsu ne.”

Haka suka ci-gaba da hiransu suka dara, sai da suka yi sallama, sannan kuma suka ci-gaba da hira da Suhail suna dariya kaman abokai, kuma ba kaɗan ba Bunayd ya girmi Suhail.

*****

<< Yar Karuwa 17Yar Karuwa 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×