Suhail yana dariya ya ce, "Yaya ACM wato ainahin Allah sa Mom ta ji ka, mu dai ba ruwan mu, Mom muka sani kuma muna bayanta, Aunty Amarya kuma mun bar mata kai."
Bunayd murmushi kawai yayi ya miƙe, tare da fadin, "je ka shirya mu fita."
Suhail ɗakinsa ya wuce ya wasta ruwa ya shirya cikin ƙananan kaya, Suhail ma fa ba ƙaramin kyakkyawan saurayi ba ne, saboda yan da kuɗi da jin daɗi suka zauna musu, idan ka gansa ba za ka ce twin's brothern Suhaila bane, musamman da yake namiji, shekarunsu 17 amma. . .