اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله
A Haka Ummu ta shigo ta same mu muna ta aikin kuka, Umaima nayi nima ina yi kuma har yanzu ina fama da tarin da kuma zafin jikin, Ummu ganin haka rai ɓace ta rufe Umaima da faɗa sannan ta ɗaga ni ta bani magani, da ƙyar na haɗiye maganin kaman zan amayo da ‘yan hanji na, Ummu koran Umaima a ɗakin tayi ta dinga shafa min kai na ba jimawa bacci yayi gaba da ni ina ta faman ajiyan zuciya, sai da nayi bacci sannan Ummu ta miƙe ta fice tana bina da addu’a.
Umaima taya Ummu aiki ta yi har dai lokaci ya ja, na sha bacci na sosai duk da ba na daɗi ba ne, sai can yamma na farka, kuma a dai-dai lokacin Umaima ta shigo fes da ita dan har ta yi wanka, a kan ta na sauƙe idanuwa na da suka mini mugun nauyi, murmushi ta sakar mini tana tambayan ya jikin nawa, da kai na bata amsa na kuma mayar da idanuwana na lumshe su in ambaton Allah a zuciyana dan har yanzu ba wai naji abinda ke damuna ya tafi duka ba ne.
Muna ɗaki Mamina ta shigo cikin gidan, a palour ta samu Ummu zaune tana waya, Ummu kaste ƙiran tayi ta tari Mami da murmushi suka gaisa, Ummu ko kaɗan bata cewa Mami komai akan abinda ya faru ba dan kuwa in da sabo to an saba da hakan tsakanina da Mamina.
Mami ce ta numfasa tare da cewa, “Ummu ina yarinyar taki ta shiga?”
Ummu na murmushi ta ce, “suna ɗaki da mutumiyar ta, da bacci take yi amma ina ji yanzu ta tashi dan na jiyo mostinsu.”
Da yake Mami ta kan shigo gidan sa’i da lokaci idan irin haka ta faru, kuma ta san ɗakin da nake zama idan na shigo, sai ta wuce ɗakin da muke, da sallama ta shigo, Umaima ce ta amsa da ƙarfi, amma ni ciki-ciki na amsa kuma ba tare da na buɗe idanuwana ba, Mami ganina a kwance bata kawo komai a ranta ba ta murmusa tare da ƙarasowa bakin gadon, sai da ta amsa gaisuwan da Umaima ke mata sannan ta ce, “boɗɗin Maminta taso mu tafi ko.”
A hankali na buɗe idanuwana da suka kumbura ga kuma hawaye kwance a cikinsu na zubawa Mamina su, ban ce komai ba kuma ban mosta ba dan bana jin zan iya tashuwa balle tafiya, Mamina tana kallon yanayi na ta shiga damuwa dan bata san banda lafiya ba ne, a rikice ta zauna bakin gadon ta taɓa jikina, da yake zuwa lokacin zazzaɓin ya sauƙa, to zafin jikin ba sosai ba, amma duk da haka da ɗumi, Mamina duk ta bi ta rikice, kaman za tayi kuka ta ce, “boɗɗi me ke damunki?”
Nan ma shiru nayi ban ce komai ba, Mamina cikin damuwa ta ce,”Banafsha ki daina saka abu a ranki, ki saki ranki mamana, ki dinga taya ni da addu’a kawai dan wani abin nima ba da son raina nake yi ba, tashi muje gida kiyi wanka.”
Yanzunma dai ban ce komai ba sai ƙoƙarin miƙewa da nayi ina runste idanuwana dan har yanzu kai na yana mugun sara mini, amma tunda Mami ta ce mu tafi ba zan iya mata musu ba dan Allah ma ya gani ina ƙaunar mahaifiyata ina son mahaifiyata fiye da yacce nake son kai na, duk wani mafarki na da buri na ita ce ba wanda na sani sai ita ba wanda ido na ya taɓa gani da za’a nuna ace ɗan uwanane ko wani nawa sai ita, ita kaɗai gare ni shiyasa bana haɗa soyayyan da nake mata da na kowa.
Miƙewa nayi amma ganin jiri na neman yasar da ni sai Mamina ta hau da ni bayanta kasancewar ba wani nauyi ne da ni ba duk da dai in ka ganni za ka ɗauka nafi shekaruna, ko na kai irin ishirin da ɗori hakannan.
Fitowa muka yi a ɗakin ina bayan Mami na lafe abuna, Ummu ganin mu sai ta girgiza kai tare da yin murmushi ta ce “Yau kuma taɓaran Banafsha ya tashi, har goyo ya kai a mata, ah lallai ƴar gidan Mami jin daɗi ya zauna miki.”
Umaima tana murmushi ta ce “Nima Mami biyo ki zan yi a goya ni nima dan masoyiya ta fini nauyi ma.”
Mamina murmushi tayi wanda ako da yaushe yake zama makari sannan sirri na kyau da Allah ya mata, dan in ka kalli Mamina za ka ranste balarabiya ce ko bafulatana amma kuma duk ba abinda ya haɗa mu da yare biyun, bayan su Ummu sun gama zolayansu Mami ta fice da ni a bayanta tana murmushi muka yi gidanmu, kasancewan ba nisa tsakanin gidanmu da na su ƙawata Umaima.
Jahar Adamawa a ƙaramar hukumar Mubi anguwan Kwaccam, nan ne anguwan mu, anguwa ne na masu saka ido da kuma damuwa da rayuwar da bata shafe su ba, mutane masu kiwon mutum ba dabba ba, komai aka yi idanuwansu na kai, ɗan madai-daicin gidanmu flat ne mai ɗauke da center palour sai kuma ɗakuna guda uku wanda ko wanne akwai banɗaki a ciki sannan daga gefe akwai kitchen, ba abinda Mamina bata saka mana ba na more rayuwa a gidan, dai-dai buƙatan talaka mai rufin asiri, wanda in ka samu irin sa dole ka ce Alhamdulillahi! dan kuwa wani ko kwatan-kwatansa nema yake bai samu ba, a filin gidan namu akwai kitchen a waje sannan da banɗaki, gidan bashi da wani faɗi sosai kuma ciki duka interlock ne.
Har ɗakin da yake nawa Mami na ta kai ni ta kwantar da ni a kan madai-daicin gadona, juyawa tayi ta fice a ɗakin sai can ta dawo da abinci a plate da ruwa a cup da kuma magani.
Ɗaga ni tayi ta zaunar da ni tana jero mini sannu ta ce, “FAƊIMAH tashi ki ci abinci ki samu kisha magani, kinji ko ƴar albarka ta Maminta.”
Miƙewa nayi na zauna tare da zuba wa Mami idanuwana, kallon mahaifiyata nake yi ina mai jin ƙaunanta na ƙaruwa a raina yana tsigar mini a ko wani sassa na zuciyata, ina jin ina ma muyi rayuwanmu mu biyunmu a haka ba tare da wasu sun shigo ciki ba, ina jin ina ma shikkenan Mamina ta daina wannan rayuwan, mu zauna haka abunmu ta kula da ni nima na kula da ita, amma sai dai kashh! nasan hakan ba mai yiwuwa bane, tana ƙaunata tana tausayina amma wannan rayuwa ya zamo ƙaddara a garemu ni da ita, kuma amsa sunan ‘YAR KARUWA ƙaddara na ne, sai dai na yi haƙuri na karɓe sa da hannu bibbiyu.
A baki take bani abincin ina ci kaman zan yi kuka, saboda a rayuwata ni bana ƙaunar cin abinci wanda ta wannan dalili ne har ulcer yayi nasaran mini mugun kamu, amma a haka Mami ta cigaba da bani har na kawar da kai na ƙoshi, sannan ta ɗau magani ta ɓare ta miƙo mini, nan fa gizo ke saƙar dan kuwa wannan ga’bar ita ce daru, nan na fara hawaye ina kuka ina girgiza kai banason sha.
Kallona Mami tayi cikin lallashi da ta saba min a duk lokacin da zata ban magani ta ce, “Haba Sayyada Faɗimah shugabar mata, Nana Faɗimah, Fatima Bintu, batooler, Faɗimatu zahra’u, Sadiƙa, yarinyar kirki jaruma, da girmanki ai sai dai magani ya ji storonki, takwara ga ɗiyar ma’aiki SAW, yi haquri kibar kukan ki karɓa kinji zan baki abu mai daɗi.”
Ina kukan ina yarfe hannu na karɓa na sha, ajiyan zuciya na dinga jerowa kamun na koma na kwanta amma Mami ta tashe ni wai na wasta ruwa, langwaɓe kai nayi cikin shagwaɓa na ce, “Mami nikam ba zan iya ba sai anjima.”
Kallona ta yi ta murmusa sannan ta ɗaga ni ta fara cire min kayan jiki na, tana gamawa ta ɗaura min towel tana cewa, “Yanzu Banafsha da girmanki kike so ki ce sai na miki wanka, kin fa zama budurwa yanzu, shekaru ishirin 20 ba wasa ba, ko in na aurar da ke haka zaki sa surki na sai ya dinga miki wanka kullum kaman bai da aikin yi?”
Tura baki nayi idanuna har ya kawo ƙwalla dan maganan da tayi na ce, “Mami ni ki bari bana so, ba ruwana da maganan nan, kuma ba ruwa na da namiji balle aure.”
Mami ajiyan zuciya ta sauƙe kamun ta zauna tana kallona cikin yanayi na muhimmin magana za ta yi, sai ta ce, “Banafsha, na hane ki wannan magana, banda abinda ya ragemun a rayuwata a yanzu sai ganin na aurar da ke, domin kuwa aure shine mutunci ko wacce ɗiya mace kuma buri ga iyayenta suga sun miƙata gidan miji lafiya cikin mutunci, in Allah ya yarda mijin da zai auri Banafshan Mami sai ya kasance mai matuƙar sa’a, wanda ba shi da stara, in Allah ya yarda za ki rayu a gidan mijinki rayuwa ta matar Sarki.”
Wannan magana da Mamina tayi ba ƙaramin fama min ciwon dake zuciyata yayi ba, kuka ne ya ƙwace mun ba tare da nayi niyan kukan ba, cikin kukan na ce, “Mami ashe mutuncin ko wacce ɗiya mace aure ne? Mamina kinsan da hakan amma me yasa kika take sanin? Mami kema fa kina da iyayen amma me yasa ke ba zaki cika musu nasu burin ba ki riƙe mutuncinki, sannan kuma ki zauna a gidan miji, meyasa Mamina? Meyasa kika zaɓar mana wannan rayuwa? Why Mami?” Na ƙarishe maganan cikin matsanancin kuka mai cin rai.”
Miƙewa Mamina tayi ranta a matuƙar ɓace, wanda na tabbatar rashin lafiyan dake damu na shine kawai ya cece ni daga samun sadakan mari ko kuwa duka daga Mami, a fusace ta nuna ni da yasta cikin fushi da ɗaga murya ta ce, “Banafsha, kar ki yarda ki tunzura ni har ɓacin rai yasa na miki baki.”
Kallon Mamina nayi ina kan kuka na ce, “Mami wallahi ko kin stine mini ba zai taɓa kama ni ba har abada in dai akan wannan maganan ne, domin Allah ya faɗa ba ya kama bawansa da laifin da bai aikata ba, Allah ba azzalumi bane, sannan Allah ya sani gaskiya ce kuma Allah da kansa ya ce ko iyayenmu ke yin ba dai-dai ba mu faɗa musu gaskiya komin ɗacinta, dan Allah Mamina kiyi haƙuri gaskiya ce na faɗa, amma in har na ɓata miki rai to ki yafe ni, kada kiyi fushi da ni, Allah huci zuciyanki Mamina.”
“Tashi kije ki wasta ruwa kuma kina fitowa ki tabbatar kin yi sallah kamun ki kwanta” Mami na gama faɗan haka ta fice a ɗakin.
Taso wa nayi na shiga banɗaki ina cike da tunani dan zuwa wannan lokaci idanuwana sun kafe ba hawaye, kukan yau kuma ya tsaya sai kuma na gobe, dan wannan wani abu ne gare ni da kullum shine sana’a ta kuma ƙalubale na, ba ranar da gari zai waye har rana ya faɗi ban yi kuka akan halin Mamina ba ko wani abun idan ta mini.
Ina gama wanka na ɗaura alwala sannan na fito, ko mai ban shafa ba balle wani abun, humran da Mami ke sayamun kawai na shafa a inda ya kamata na sassan jikina, sannan na buɗe drawern kayana na ciro simple material riga da wando da mayafin sa wanda ɗinkin ke kama da Pakistan-dress, ina saka wa na ɗau hijab na tada sallahn magrib, ina idarwa na ɗauki Qur’ani na fara karatu, nice ban tashi akan darduman ba har sai da nayi sallahn isha’i na tabbatar hadda na ya zauna, sannan na naɗe na ajiye sa, da hijab ɗin jikina na fito palourn namu, amma mutumin da na gani zaune a palourn namu shi ya sanya ni juyawa da sauri wanda kamun ace na ƙarisa shigewa ɗaki Mami na da fitowan ta kenan ta ganni ta qwalamun ƙira, kuma ƙiran nata ne ya tsayar da ni, ban shige ɗaki ba kuma ban juyo ba ina dai tsaye a wajan cikin taƙaici da haushin mutumin da ya zo wajan Mamina.
Mami na kyakkyawa ce ta gasken-gaske, farar mace ce mai ƙaramin ruwa dan in ka ganta ba zaka ce ta haife ni ba, tana da dogon hanci da tsayin gashi wanda hakan ke sanya wasu mutanen mata kallon bafulatana, sannan tana da kyakkyawan ƙira, wanda har zuwa wannan lokacin da nima na zama budurwa amma ƙirjinta basu kwanta ba ko dan ni kaɗai ta shayar ne oho, kuma Mamina tana gyaran jikinta sosai, sannan tana da ƙugu wanda ke ɗaukan hankalin mutane dan nima a wajan ta na gado ƙugun da mazaunai, wasu in suka ganni ma har cewa suke nima na biyewa Uwata na fara bin maza dan kusan kallon da mutane ke mini kenan akan nima nasan maza na buɗe.
Jin muryan Mamina ta ƙara ƙiran sunana a karo na biyu, kuma nasan palourn take so na dawo, tura baki nayi dan kuwa na tsani wannan mutumin da ke zaune a palourn namu, saboda duk cikin masu zuwa wajan ta a manyan mutane shi yake ban haushi ganin babban mutum kaman sa ga kuɗi ga kyau amma yake biyewa bin mata dan na tabbata yana da yaron da zai kusa sa’an Mami na dan daga ganinsa ya bai wa shekaru hamsin 50 baya, saboda babban mutum ne sosai kyakkyawa har da furfuransa.
Wannan karon ina jin muryan Mami na Juyo, cikin nistuwa nake tafiya kaman bana so, a haka na ƙariso cikin palourn fiskana a haɗe, sam-sam babu annuri ko kaɗan, kallon da Mamina ta jefo mini shi ya sanya ni tura baki ciki-ciki na ce, “Anwuni lafiya Alhaji?”
Alhaji Mukhtar washe baki yayi dan sosai yake ƙaunar mahaifiyata, wanda wannan soyayyan da yake mata shi ya sanya nima yake ƙaunata tamkar ƴar cikin sa, kayayyaki ne menene duk idan ya tashi zuwa sai ya kawo min, kwanaki har ya sayamun waya babba mai kuɗi, amma kuma Mamina ta maida masa ta ce ba zan riƙe waya tun yanzu ba.
Amsa gaisuwan yayi yana ta saka mini albarka, amma ni fiska na ko Annuri babu balle batun amsa albarkan da yake sanya min, na tashi zan koma ciki sai ya tsayar da ni ta hanyar cewa “yarinyata Banafsha ga tsaraban ki taho ki amsa.”
Cikin takaici na juyo, ji nake kaman na shaƙesa ya mutu na huta, durƙusawa nayi na miƙa hannayena bibbiyu na karɓa abinda yake miƙa mini, na ce masa, “Nagode Alhaji, Allah ya ƙara arziƙi da ɗaukaka.”
Yana murmushi da jin daɗin addu’a ta gare sa kullum, dan muddin zai min kyauta to ni kuma sai na suburbuɗo masa addu’a ko ban yi niya ba, cewa yayi, “Ameen ya Rabbi! yarinyar kirki Allah ya miki albarka ya albarkaci karatun ki ya baki miji na gari.”
Amsa wannan addu’a sai Mami na ne tayi shi cikin fara’a dan tana ƙaunar mai ƙaunar gudan jininta, yarinyar ta gudan ɗaya tal kaman stoka a cikin miya, ni kuwa tuni na jima da shigewa ɗakina inda nayi jifa da ɗan ƙaramin jakan, dan abun hannunsa ba ya burgeni.
“Subhanallahi!” shi ne abinda baki na ya furta ganin wani haɗaɗɗen Qur’ani ɗan dai-dai ya faɗo ga carbin irge(counter), ga kuma sallaya ɗan ƙarami, ga kuma ruwan zam-zam duka suka faɗo daga cikin jakan.
Da sauri na sunkuya ina tattara su, wanda bansan lokacin da murmushi ya kuɓuce mini ba, dan a rayuwata sosai nake ƙaunar ganin anmin kyautan Qur’ani ko sallaya, nan na dinga tsalle da murna, inata jero masa addu’an Allah ya shirya shi yasa yabar bin mata, Mamina ma Allah shiryamun ita, tuni na mance da haushinsa da nake ji, na kama murna ina jiran Allah ya kai mu gobe na nunawa Umaima.
Ni da na shigo ɗaki da niyan bacci, amma ganin wannan kyauta bansan lokacin da na miƙe na ɗauro alwala na tada nafila ba, ina mai kai kuka na ga Allah na roƙawa waɗan nan bayin nasa shiriya.
Ɓangaren su Mamina, ina barin palourn ta dubi Alhaji Mukhtar da murmushi ta ce, “Mun gode sosai Alhaji, Allah ya saka da alheri, ya kuma ƙara arziƙi yawa zuri’a albarka.”
Alhaji Mukhtar murmushi yayi ya ce, “Ameen summa ameen, Hajiya ta Amarya ta.”
Hararansa Mami ta yi ta ce, “Za ka fara ko? To Alhaji bana son wannan magana kabar kawo mini shi.”
Cikin mamakin lamarin Mami ya kalleta ya c,e “Ramlatu wai me yasa kullum in nace miki ba lafiya a lamarin ki akwai wani abun sai ki musa min ki ce ba haka ba? Mutumin da yake lafiya ƙalau zai zaɓi irin rayuwar nan? In aka miki maganan aure kaman an kashe miki wani naki wai meyasa? Ramlatu ki sani ina sonki sonda ban taɓa yiwa wata ɗiya mace ba, amma dai ba komai zan barwa Allah duk wani lamari na ya iya min, ki sani kuma in anyi duniya dan Manzon Allah SAW, sai na aure ki dan na gaji da wannan rayuwa da muke yi mara fa’ida, da girmanmu da komai ga yara amma mu dinga saɓawa Allah bama tunanin abinda muke yi bashi ne, kuma za’a yi da yaranmu, wallahil Azeem Ramlatu dan ke naje Makka wannan karon dan duka addu’ata akan ki nayo sa, ina mai sa rai da fatan Allah ya amsa mini ya saita lamuranki, Insha Allahu wata shekara kema za kije dan ki ƙaro addu’an wa kanki, ni dai buri na na aureki muyi komai a inuwar sunna da lada, wannan ƙazamiyar rayuwan ta isheni.”
Mami da zuwa yanzu ta cika tayi fam kaman za ta fashe cikin ɗaga murya ta ce, “Alhaji Mukhtar ina ganin girmanka da darajanka, ko ba komai dan soyayyan da kake nunawa yarinyata wacce ta fi mini komai a rayuwa to shi yasa nake shiru nake cigaba da sauraranka, amma karka yarda ka fara tunanin wuce gona da iri, ko an gaya maka bansan duk abinda kake aikata min ba ne? Bansan mai kake shiryamun ba akan jama’a na? To ka riƙe girmanka, idan ba haka ba na kusa daina sauraranka, maganan aure ka aje sa a gefe, nayi aure na gama yi haka nake son rayuwata in ba za ka iya ba ka fita a rayuwata ka ƙyale ni, ai akwai mata da yawa a duniya, to kaje wani wajan ka nemi ta aure, ni ba aure ne a gabana ba.”
Alhaji dai kallon Mami yake kuma ba alaman ɓacin rai a fiskansa sai ma wani sihirtaccen murmushi da yake sakar mata, ga kuma fara’a wanda ako da yaushe in suka samu saɓani irin haka akan ya mata maganan aure tana bam-bami, to iya abinda yake yi kenan murmushi.
Ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce, “Allah ya huci zuciyanki Hajiyata kuma amaryata, in Allah ya so ya yarda.”
Cikin jin haushi Mami ta miƙe ta shige ɗakinta tare da banko ƙofa har da saka key, shi kuwa ganin haka sai yayi hamdala dan hakan yake so dama.
Taso wa yayi ya shiga ɗaya ɗakin ya wasta ruwa ya ɗauro alwala yayi nafilfilu yana mai ƙara miƙa kukansa ga Allah akan wannan baiwar Allah da yake matuƙar ƙauna, yana idar wa ya kashe wutan ɗakin ya kwanta.
Washegari da ya kama juma’a da sassafe na fito nayi shara da wanke-wanke da girki sharp-sharp, ina kammalawa na ɗiba nawa naci na koma ɗaki na shirya dan zuwa makaranta.
A bakin ƙofan ɗakin Mami na tsaya ina sallama, daga ciki Mami ta amsa mun ta ce na shigo, tura ƙofan nayi na shiga, na tarar da ita zaune a bakin gadonta, Alhaji kuma yana zaune akan kujeran zaman mutum biyu dake cikin ɗakin.
Durƙusawa nayi na gaishe da Alhaji, ina ƙara masa godiya sannan na gaishe da Mamina, ta amsa tana tambayan har na shirya kenan na ce mata, “Eh Mami na shirya class na 7:30 muke da.”
Mamina ta ce, “To Banafsha Allah ba da sa’a, a dawo lafiya, ba dai akwai kuɗin mashine a hannunki ba?”
Ɗaga kai kawai nayi na juya zan fice a dakin sai naji muryan Alhaji na cewa, “Daughter tsaya na ajiye ki a makarantar ko.”
Kaman an bani saƙon mutuwa haka naji amma ba yanda na iya haka na fice na tsaya jiransa a qofan gidan mu.
Sallama Alhaji yawa Mami akan zai tafi kuma zai fi sati bai zo ba ta kula sosai sannan baison yawan kule-kulen mutane.
Kallon sa Mami tayi tana murmushi ta ce, “Alhaji kana son jan magana, kai ba mijina ba, ba komai ba kana bani doka to gaskiya sai dai kayi haƙuri dan yanda ka ganni ka biyo haka kowa ma, shiyasa na faɗa maka tun farko, ni dadiro ba shi ne abinda ya dame ni ba, kowa ya samu rabonsa yayi gaba.”
Alhaji kaman zai yi kuka ya ce, “Ramla kibar faɗamun irin maganan nan kin dai sani tsakanina da ke daban da tsakaninki da sauran ko? Kuma idan maganan ban aure ki kike ba mai kike ci na baka na zuba? Ai in Allah ya yarda Mukhtar sai ya mallaki Ramla ba da jimawa ba, Allah raba mu da zaman dadironcin ma.”
Hararansa Mami tayi ta fice a ɗakin, shima bin ta yayi dan yasan suka tsaya sai su ɓatawa Banafsha lokaci akan maganansu, har bakin motan ta raka sa ya shiga ta saka masa hulansa tana masa murmushinta mai zautar da shi ta ce, “Allah stare hanya ya kai ka lafiya, Allah karemun kai, a gaida Hajiya da yaranmu.”
Alhaji ji yake tamkar ya ɗauke ta yanzu ya kai ta gidan sa, a matsayin matar sa amma ba hali, murmushi kawai yayi ya ce, “Ameen Mamin yara sai kuma kin ganni.”
Mami ta buɗe masa madaidaicin gate namu ya fito, sanda taga shiga na da tashin motan sannan ta kulle ta koma cikin gidan.
Tafiya muke sautin qira’an Alqur’ani mai girma na tashi a cikin motan, wanda da alama karatun musabaƙa ne dan daga yanayin karatun na gane.
Alhaji juyowa yayi ya kalle ni ganin ina bin karatun ya ce, “Karatun ya miki daɗi kema ko daughter?”
Ɗaga kai nayi kawai alaman eh dan duk da kuwa sonda yake nuna mini, da kulawa tamkar yarinyar cikin sa hakan baya hanani jin haushin sa, tunda shi ma biyewa mahaifiyata yake yi suna zubar da girmansu.
Yana murmushi ya ce, “Yarinyata ce wacce ba zata wuce sa’anki ba suka yi musabaƙan, sannan ta zo ta biyu, yanzu haka tana ƙoƙarin haɗa haddan ta, sunanta Hauwa’u amma muna kiranta da Majeederh.”
“Allah ya ƙara basira ya albarkaci karatu” iya abinda na furta kenan dai-dai muna shiga babban gate na makarantar mu College of health Mubi, inda nake a shekara ta biyu, ina karantan CHEW, muna a semestern ƙarshe.
Faɗa yamin na ƙara mai da hankali, sannan ya miƙa min kuɗi nayi na mashine amma naƙi karɓa, juyin duniya yayi da ni amma sam naƙi, ganin haka sai ya mayar da abinsa aljihu, ni kuma na sauƙa tare da masa addu’an a isa lafiya, shi kuma yaja motansa ya tafi.
Ajinmu na ƙarisa inda na tarar har malami ya shiga wanda ke ɗaukan mu environmental care, nan na samu waje na zauna ina sauraran karatu, sai da muka share hour guda har da ɗori kamun malamin ya juya ya fice, ina ƙoƙarin miƙewa naji mutum ya zauna gefe na, juyawa nayi ganin Umaima ce sai na haɗa fiska na wuce na fice a ajin, ina tafiya ta sha gabana ta kama kunne tana cewa, “Haba masoyiya ta Banafshaty, kiyi haƙuri mana.”
Ko kallon ta naƙi yi, na juya zan ci gaba da tafiya kawai sai ta rungume ni ta ce, “Wallahi masoyiya ba laifi na bane, Ya DANISH ne ya hanani zuwa gidanku ya ce shi zai kai ni makaranta, kuma kema kinsan halinsa in naƙi zai bulale ni ne, ni bansan jaraban da ya saka shi dawowa jiya Alhamis dare-dare ba, mutumin da juma’a ma sai yamma yake dawowa.”
Cikin gamsuwa da magananta na ce, “Shikkenan Umaima ya wuce, shi kuma mai niyan raba mutunci da soyayya Allah ya shirya sa, nima yau Alhajin da nake gaya miki inajin haushinsa sosai shi ya kawo ni.”
Nan muka wuce ƙasan wani bishiya muka zauna, har na bata labarin kyautan da ya kawo mini da kuma labarin yarinyar sa da ya bani.
Murmushi Umaima tayi ta ce, “Allah kuwa Banafsha wannan bawan Allahn kaman dan Allah yake son Mami.”
“Hmmn! Umaima kenan, in da gaske yake sonta ai sai ya aure ta, amma yake biyo ta har ya dinga kwana a gidanmu, na faɗa miki duk cikin masu zuwa wajanta shi kawai ke yin kwana har fin 1 wataran fa sai ya kai kwana huɗu har da ɗaki ɗayan can nasa ne, ni ban ma san shi kuma me yake cewa matan sa ba da har yake kwanaki a gidanmu, Allah na tsani mutumin sosai.”
Ganin raina na ƙoƙarin ɓaci sai Umaima ta kawar da maganan muka kama wani, har muka koma class aka ci-gaba da lecture, mu ne bamu tashi ba sai ƙarfe ɗaya ciff na rana, inda ana tashi ni da Umaima muka fito muka nemi mashine muka yi gida ba ɓata lokaci.
*****