Skip to content
Part 20 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Hajiya Sa’adatu a hasale cikin ɓacin rai ta ce, “munafuki, algungumi, mara amana, butulu kawai, to me za ka ce mini bayan abinda idanuwana suka gane mini, da wan da kunnuwana suka jiye mini, Alhaji Mukhtar ni za ka wulaƙanta? Ni za ka tozarta? Kishiya dai, aure fa, to wallahi baka isa ba, ba’a haifi uwar mai haifa mini kishiya ba, ni Sa’adatu na fi ƙarfin kishiya, tun wuri ka nistar da hankalinka waje guda ka dena wannan ɓaɓatun shirmen dan wallahi ban yarda ba, ba zan taɓa yarda ba, shekaru har talatin da ɗori da aurenmu, sannan sai yanzu rana staka ka stira ƙara aure, wai zaka mini kishiya, to ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa.”

Alhaji murmushi yayi, dan ko ɗaya bai ji zafin kalamanta ba, sannan ya stammani fiye da haka ma daga gareta, tun da ya san masifanta akan kishiya, amma bai zaci abin zai dameta haka ba, tun da dai ya ga ba wani damuwa ta yi da shi sosai ba.

Hajiya Sa’adatu hargagi ta fara da masifa da bala’i, tun bai ma yi magana ba, ta inda take shiga ba ta ban take fita ba, faɗi take bai isa ba, kuma za ta dawo masa da kuɗinsa dan bai yi arziƙin da zai mata kishiya ba, Alhaji dai ko ci kanka bai ce mata ba, murmushi kawai yake yi, yana shiru kaman wanda uwar sa ke masa faɗa, har ta gama masifan ta kuma koma kuka tana faɗin, “Amanata za ka ci Alhaji? Tozarta ni za ka yi? Me na kasa maka? Ta ina na gaza? Mene bana maka? Alhaji duk ƙawaye na kowa shi kaɗai a gidansa, amma ni me na maka za ka mini haka? To wallahi ka ji na rantse baka isa ba Alhaji”, tana surutunta tana kukanta har ta gaji ta fice a ɗakin, tana komawa nata ta fara ƙiran ƙawarta Hajiya Turai, suka haɗa conference call da Hajiya bushira, nan ta labarta musu abin da ta gani da wan da ta ji, duk abin da ke faruwa a taƙaice ta juye musu.

Nan fa suka fara famfa ta, akan tabar kuka, indai aure ke to Alhaji bai isa yayi shi ba, za su ɗau mataki, a take Hajiya Sa’adatu ta share hawayenta, sai da suka gama kiste-kistensu, sannan suka yi sallama, ta bi lafiyan gado hankali kwance ta yi baccinta.

Alhaji kuwa tana fita ya sauƙe ajiyan zuciya tare da murmusawa, ya ce, “mata ikon Allah, ɗan Adam kenan”, wayansa ya fidda ya ƙira Mami suka ci-gaba da wayansu har dai suka yi sallama.

Hajiya Sa’adatu tun daga washe-gari ta fara binciken ta, a in da Alhaji ke neman aure, amma sam-sam babu alama dan bata kawo Adamawa a ranta ba, ana tafiya har aka ƙara cinye sati guda, aure saura sati, amma ba ta in da bata bincika ba, ba labari, ga shi Alhaji ko fita ma baya yi balle ta ga ko wajan matar zai je, watarana idan ya fita kuma daga ƙarshe wajan abokansa ko kuma business nasa, ganin abu na ƙara mastowa dan haka yau ma samun Alhaji tayi cikin masifa ta ce, “ƴar gidan uban waye za ka aura Alhaji, da na bincika duk Kano babu ita ba labarinta, ai nasan ba zai wuce munafurci ne ya hanaka neman aure a Kano ba saboda kada na sani.”

Alhaji murmushi yayi ya ce, “Da kin kwantar da hankalink Sa’adatu, ai kina tambayana zan faɗa miki ba sai kin bincika ba, da farko dai ina mai baki haƙuri, kin sani shi aure nufi ne na Ubangiji….”

Kamun Alhaji ya ida maganansa, tuni ta tari numfashinsa, ta ce, “Kuma da son ran ka ba.”

Murmushi ya kuma sakar mata ya ce, “sosaima Hajiya Sa’adatu, da son rai na zan yi auren nan in Allah ya yarda, kuma ina addu’a da fatan Allah ya sa na dace na samu wacce za ta kula da ni.”

Hajiya a ƙufule ta ce, “Wato ni bana kula da kai? Ai maza daman ku baku da godiyan Allah, musamman a abin da ya shafi mata, yanzu idan ba butulci ba me na gaza? Me na kasa? A me na tauyeka ko kuma na rage ka Alhaji.”

Zama Alhaji ya gyara tare da numfasawa ya ce, “An zo wajan, ranan kin mini tambayan nan amma baki bani daman amsawa ba, yanzu kuma ina ƙoƙarin baki amsa sai ga shi kin maimaita, hakan yayi Masha Allah, da farko Hajiya Sa’adatu ina so ki sani, ba wai faɗa miki a iya me kika gaza zan yi ba, domin a komai kin rage ni, a komai kin kasa faranta mini balle ki kula da ni, abu mafi muhimmanci shumfiɗana, tsakaninki da Allah Hajiya yaushe rabon da ki zo gare ni? Idan na nemeki me kike faɗa mini, ba kin gaji ba? Ban taɓa hanaki kasuwancinki ba duk da yana taimakawa wajan rashin kula da ni, amma ke kin taɓa lura da hakan balle ki gyara? Ba ruwanki da yaushe zan dawo, ina zan je, kwana nawa zan yi, mai nake buƙata, idan na dawo ya ina buƙatar ganinki ko da ba za ki bani komai ba, duk babu ruwanki da wannan Sa’adatu, ko ƙarya na miki?”

Hajiya Sa’adatu cikin ɓacin rai, da rashin son gaskiya ta ce, “Ni ban ce ƙarya ba ne, amma har da ƙari a kai Alhaji, yanzu tsakani da Allah da girmanka da girmana, sai mun tsaya wani shimfiɗa-shimfiɗa kaman yara, kuma naga daga ni har kai kowa business yake yi, hakan bai ishe mu ba Alhaji.”

Murmushi Alhaji yayi ya jinjina kai, ya ce, “Tabbas nikam hakan bai ishe ni ba, domin na fi buƙatan nistuwa fiye da kuɗi, tun da Allah ya hore mana ya sa muna da wan da za mu rufawa kan mu asiri ko daga gida muke, har mu taimaki wasu ma, to kin gaza a ko ina musamman a nan ɓangaren, saboda ke kin sanni yan da nake ko wani saurayin albarka, bana jin zan girma wa samun nistuwa a shimfiɗa, ki kuma godewa Allah da rashin kulawanki bai yi tasiri ba, Allah ya taimake ni ya ceceni daga faɗawa hallaka, duk da na kusa stunduma cikin harkan neman mata, amma albarkacin wannan baiwar Allah da zan aura sai abun ya tsaya, to ki gode wa Allah ki gode mata.”

Hajiya Sa’adatu wani irin malalacin kallo ta ke jifan Alhaji da shi, idanu jajazir ta ce, “Karuwa za ka aura? Kuma daman da girmanka sai ka bi mata?”

Girgiza kai Alhaji yayi ya ce, “Ba karuwa ba ce, da mutuncinta da ƙimanta da komai, kuma idan Allah ya yarda aurena zai ƙara suturtata, domin ta fi wasu matan auren da suke kasa kula da mazajensu har su sanya su fita su nemi matan banza, sannan akan abin da ya zama ƙaddarana ban da wani girma, sannan akan abin da ya shafi buƙatuna nan ma ni ba kowa bane, na dai godewa Allah da mummunar ƙaddara bata same ni ba.”

Hajiya a hasale ta ce, “Wallahi bata fi ni ba, kuma idan dan wannan ne zan gyara ka bar maganan auren nan.”

Alhaji murmushi yayi ya ce, “Na riga da na faɗa miki ko ta ina kin tauyeni, da iya wannan ne da sauƙi nima zan iya haƙuri, Sa’adatu kin cire mahaifanki tun da kika haifi Majeeder, ko ƙarya ne?”

Hajiya Sa’adatu idanuwa ta zaro, mamaki take akan ya aka yi Alhaji ya sani, lallai allura ta tono garma.

Murmushi Alhaji ya kuma yi, nan ya faɗa mata yan da aka yi ya sani, dan yasan ba zai wuce mamaki take yi ba, cewa yayi, “kuma ni ina son haihuwa, Allah ya bani arziƙi alhamdulillahi, da a ce rashin haihuwanki na Allah da Annabi ne to ban da mastala shi ma, zan haƙura na gode wa Allah da biyun da ya bani, amma ba na Allah da Annabi bane, ke kika kista abinki, a yanzu ma na gode wa Allah, kuma ina addu’an Allah ya ma biyun albarka, amma idan da ƙari ina addu’an Allah sa matata ta haifo mini dozen, Sa’adatu wajaje da yawa kin kasa kaman yan da na faɗa tun farko, Sa’adatu fita kike ki hau jirgi ki yi tafiyanki babu izinina, idan kin dawo ma ba za ki bani haƙuri ba, kwata-kwata ma bakya tunani da jirgin da motan, duka ƙarfen nasara ne ba su da tabbatas, za su iya kai ki ga hallaka ba tare da kin nemi yafiyana ba, Sa’adatu kin kasa bawa yarana tarbiya balle ki kula da su, guda biyun ma, Sa’adatu ba abinda kika sani kuma ya dame ki sai business naki, ya isheni haka ba zan iya ci-gaba da haƙuri da halinki ba, aure zan ƙara, kuma matar Yar Adamawa ce, ba a nan Kano take ba, idan kina so ma har da address nata zan baki, domin ko me za ki yi ba za ta fasa aurena ba, tana so na kaman yanda nake ƙaunarta, Sa’adatu kawai kina zama da nine kina mini kallon bansan me nake yi ba, saboda shirun da nake yi sai kike tunanin juyani kike yi, to ki sani bana son tashin hankali ne, domin idan na bari rai na ya ɓaci da ke, to zan ɗau mummunan mataki, dan haka ki kiyaye kawo duk wani mastala a wannan biki, idan kin so ki zauna lafiya ki kuma gyara halinki, idan kuma kin so sai ki yi kishiyan hakan, amma ina mai tabbatar miki matakin da zan ɗauka ba zai mana kyau ba ni da ke”, Alhaji na gama magana rai a ɓace ya miƙe ya fice a gidan gaba-ɗaya.

Hajiya Sa’adatu a maimakon ta yi nadama, ta ɗau niyan gyara halayenta, ta kuma rungumi zuwan Amarya hannu bibbiyu, sai dai inaa, sam ƙara rikicewa tayi, ko kaɗan bata yi nadaman abubuwan da ta yi wa Alhaji Mukhtar ba, ba abin da take sai kumfan baki kan cewa ba za ta bari ayi auren nan ba, idan ma ta bari, to ba za ta bar matar ta zauna ba dole ta koma in da ta fito, Alhaji nata ne ita kaɗai.

Alhaji tun da ya fice rai a ɓace, gidan wani abokinsa ya je, amma sai da ya seta kan sa, dan ba zai sanar da sirrin gidansa ba, cikin fara’a suka din ga hira, abokin nasa sai zolaya yake masa, wai yanzu ne zai san daɗin aure, mata biyu duniya ne, idan kana zaune da mata ɗaya ba abin da ka sani tukunna(kun ji munafukan abokai masu ɓallo mana ruwa).

Alhaji Mukhtar yana tare da abokinsa, ƙiran Bunayd ya shigo wayansa, ɗauka yayi yana murmushi ya ce, “Air Chief Marshal.”

ACM Bunayd a nasa ɓangaren murmusawa yayi ya ce, “Papi Ango ka sha ƙamshi, ya shirye-shirye? Ina Mom fa, ina hanya zuwa mata danne ƙirji.”

Dariya Alhaji yayi ya ce, “Ubanka General, ba mu gayyaceka ba, tun da ka yi naka gudumawan ya isa ba sai ka zo ba, idan kuma so kake ka zo a stine maka shikkenan, ni ba ruwana.”

ACM kiston kansa ya shafa ya ce, “wai da zan kawo lefe ne, da kuma na danne ƙirji, kasan Momsee har da Mom ta haɗowa wai na faɗan kishiya.”

Alhaji dariya yayi ya ce, “Allah shiryeku kai da iyayen naka, yanzu dai maganan lefen nan a bar sa sai an kawo Amarya washe-gari, amma idan su Maman naku Huraira za su taho bikin za su iya zuwa da na Hajiya, kai kam ban ce ka zo ba, sai ɗaurin aure mu haɗu a Adamawan.”

Waya Alhaji yayi da yaron nasa, kaman ko yaushe cikin soyayya da annashuwa, sai da suka gama suka yi sallama, ya kashe wayansa ya dubi abokin nasa ya ce, “kana ji na da fitinannen yaron General ko.”

Dariya Alhaji Idris yayi ya ce, “Ai ni a rayuwata wannan ɗan gidan General ɗin burgeni yake, ga shi dai idan aka kallesa kaman an ga burtai a filin yaƙi rai a haɗe, amma mu’amalansa da jama’a, da halayyansa sai ina jin ina ma yaronane.”

Murmushi Alhaji yayi ya ce, “ai Bunayd sai addu’an shiriya kawai, sam fa baya ji, wannan da yaronka ne ma ba za ka iya masa ba, wannan halinsa sai irin ubansa General ɗin.”

Alhaji Idris ya ce, “Amma dai magana kake Alhaji Mukhtar, ai kuma Bunayd da jin magana da biyayya duk ba wanda aka bar sa a baya, a irin zamanin nan ka samu ɗan uwa irin General Sufyan ya riƙe maka yaro da amana haka ya masa tarbiya, ai sai ɗaɗɗaya.”

Alhaji murmushi yayi tare da sanyawa ƙanin nasa da yaron nasa albarka, sannan ya ce, “Allah dai ya shirya mana zuria’a ya kuma musu albarka.”

“Ameen”, faɗin Alhaji Idris yana dariya, ya ce, “Wato shi Bunayd har da wata hidima yayi, ah lallai mahaifiyarsa ta sani zai gane kurensa.”

Alhaji tuni ya mance da wani damuwan da Hajiya Sa’adatu ta cusa masa, hira suka din ga yi da Alhaji Idris abokinsa, suna dariya, rabi da kwatan hiran akan Bunayd ne da kuma batun auren Alhaji, har Alhaji Idris ke faɗin da yana da yarinya mace babba to da ya bai wa, Bunayd aurenta.

Safiya ta yi ta wuce, dare ya zo ya mamayeta, sannan gari ya waye, a haka ake tafiya yau da gobe har dai aka shiga satin biki, in da yau Alhamis, mutanen Lagos suka tattaro gaba-ɗaya har General da yaronsa, Suhail da Nabeel ma duk sun zo, an kamo hanyan Kano da su, kayan lefe ma duka an taho da shi, na Amarya da na Mom.

Jirginsu ya sauƙa da wuri, in da motoci suka zo jidansu, komai na gama zama ready, motoci suka ɗau hanyan Railway estate, suna isa kuma a ƙofan sashin General da yake a gyare a kimste suka ya da zango, ma’aikatan ne suka jidi akwatunan suka shiga da su ciki.

Sai da suka sha ruwa suka huta, sannan Momsee ta sa ma’aikatan suka ɗau iya na Mom suka yi part nata da shi, ita kuma Momsee ta bi su a baya.

Da sallama suka shiga sashin Alhaji, Mom na hakimce a kujera da ƙawayenta, ba wanda ma yayi gigin amsa sallaman, ma’aikatan dai suna ajiyewa suka juya abin su, Momsee ce ta ƙarisa ta samu waje ta zauna, ganin duk babu wanda ya bi ta da kallon rashin kirki balle na arziƙi, a hankali ta ɗaga musu gaisuwa, nan ma shiru ba wan da ya ce komai.

Momsee miƙewa tayi tare da cewa, “To Hajiya ga kayan faɗan kishiya, muna fata da addu’an Allah baku zaman lafiya da zaman haƙuri”, tana gama faɗa ta fice abinta, bata staya sauran ko A daga bakinsu ba.

Hajiya bushira ce ta ja wani dogon tsaki ta ce, “shegen iyayi, shishshigi shiga abin da bai shafe ka ba da Ghana-most-go.”

Mom ta ce, “Munafuka ba, wai ita ga ta tagari, tun da ita ƴar uwarsu ce, auren dangi ne, shi ne za ta dinga yi wa mutane shishshigi.”

Hajiya Turai murmusawa tayi tare da mikewa ta buɗe akwatuna, zaro ido tayi ta kama baki ganin irin arnun kayan da ke ciki, dan ko lokacin auren Hajiya Sa’adatu ai ba’a saka mata irin haka a lefe ba, nan baƙin ciki ya rufeta, amma sai ta yabi kayan, Hajiya bushira ma jefa bakinta tayi suka dinga kallon kaya suna koɗawa.

Mom kuwa haushin su take ji kaman ta shaƙe su, ko abu ɗaya bai burgeta ba, haushin komai take ji, ƙarshe cewa tayi su tattara kayan a gabanta ko ta cunna masa wuta, a haka suka sa masu aiki suka kai ɗakin Mom, tana faɗin bata so, duk wacce ta ga abin da ya mata a ciki ta ɗauka, ita bata son kayan.

Hajiya Turai ta ce, “To wannan shegun kayan wa ke na faɗan kishiya, wa kuma ya san ita munafukar Amaryan taki wani irin ƴan banza kaya aka mata, cigaba suka yi da hura Hajiya Sa’adatu, ita kuma sai karɓan iska take, ta cika ta baste ta yi fam kaman wacce ta ji yist, tana jiran fashewa.

Momsee dai ko a jikinta ta tattara ta koma sashinta, Bunayd kuwa tuni ya fice daman a gidan, General ma sun fita da Papi, Suhail yayi nasa wajan, Nabeel kuma yana can ɓangarensu.

Majeeder kuwa tun da Momsee ta bata nata kayan ankon da aka mata, ai farinciki kaman ta fire, daɗi kawai take ji Papi zai kawo mata Aunty, kuma za’a taho mata da ƙawa, dan Papi bai faɗa ma Majeeder akan cewa ƙawarta za ta yi aure ba, shungulloli sun sha kan sa, dan haka Majeeder ta sa rai, ba abinda take sai labartawa su Ramla maganan ƙawarta kuma har ta saya mata gift.

Washegari juma’a, da ya kama ranan ɗaurin aure, da wuri tawagar Alhaji Mukhtar suka shirya, suka hau jirgi sai Adamawa, sun isa da wuri, dan haka babu ɓata lokaci aka shirya motoci har da na sojoji suka kama hanyan Mubi, Alhaji Mukhtar, General Sufyan, Alhaji Idris, Alhaji Tasi’u(baban Abeed), Suhail, Nabeel, Bunayd, Abeed, da wasu sojoji abokanan aikin Abeed da na Air Force abokanan aikin Bunayd, motoci sun kai Goma suka kama hanyan Mubi, wani irin mugun gudu suke, duk da gargadan hanyan amma cikin awa uku suka isa garin Mubi dan ba maganan stayawa a checking point, masu checking point ɗin da kan su ke yin tafiyan, suna isa kuma masallacin da za’a ɗaura auren suka nufa, dan lokacin juma’a ya riga da ya yi, Alhaji Mukhtar dai ba abin da yake sai washe baki, shi kuwa Bunayd da ya jima da mancewa da wata idiot, sai da suka shigo garin Mubi ya tuno ta, addu’a yayi Allah ya sa ya ganta, za ta yi stallen kwaɗo yau ɗin nan.

*****

Ɓangaren mu da Mamina shiri muke ba kama hannun yaro, tun da biki ya rage sati guda kuma, Mami da kan ta tayi magana a tahfiz aka bani hutun wata guda, sai a satin da za mu tafi Abuja sannan zan dawo da zuwa, amma zan cigaba da karatuna da komai a gidana har lokacin yayi, duk da College ma zai kama hutunmu zai ƙare ne, nan da sati biyu, kenan bayan biki da sati guda, amma shi ma sai an yi wata guda zan koma haka Mamina ta yanka mini.

Wani irin ciccikowa jikina yayi ko ta ina, kyau nayi sa na musamman, ƙamshi kuma kaman a jikina aka halicci turare, fatan jikina kaman na jarirai, ga sulɓi ga yalƙi, ni da kai na nasan na sauya, Mami ta kashe kuɗi, kuma mata mai gyaran jiki tayi aikinta yan da ya kamata.

Kaman yan da na sauya na haɗe, haka Mamina tayi mugun kyau, sharr da ita kaman bata haifi kamata ba, musamman ma da take da ƙaramin ruwa, da kuma jiki mai kyau.

Shirin da ake yi a gidan Abbaa, za ka ɗauka ƴar cikinsa yake aurarwa, domin ya ma hana Mami a ɗaura komai a gidanmu, sai dai abin da ya kama dole.

Abu na farko da ya bani mamaki, shi ne ganin mutanen unguwa da ke gulman Mamina, duk sun zo taron da aka fara, duk da yake dai nasan Mamina ba ruwanta, lafiya lau take zaune da kowa, domin tun da nake da wayona, to bansan wanda zan nuna na ce, ga abokin faɗan Mamina ba, to ganin mutanen anguwa sai nayi hamdala, dan nasan wannan ma wata ni’ima ce ta Ubangiji, masu zaginka kuma su dawo suna cin albarkacinka.

Duk da Malam Abbo Ustaz ne kuma ɗan shi’a, amma bai hanani yin event ko ɗaya ba, dan ni ce na yanke ba wani abin da zan yi sai walima, Umaima kuma ta ce ban isa ba, dan ga classmates namu na college duk sun yi anko, ta dage sai mun yi ko bridal shower ne, idan ya so sai ayi walima da kuma Arab day, da farko Mami bata ce mana komai ba, har sai da ta ga na dage ba za’a yi ba, sannan ta saka baki akan mu yi tun da shi mijin bai hana ba, dan haka Umaima ta fitar da komai ta tsara shi, da ƴan College da suka zama ƙawaye su ma, har anko da komai an yi, ana shiga satin biki muka fara hidindimu.

Ranan Litinin muka sha ƙunshinmu ni da ƙawayena, muka dinga ɗaukan photuna, Mamina ce ta biya mana komai, dan kuɗaɗen da Malam Abbo ya bani na hidima suna wajanta, sannan wan da Alhaji ya bayar nawa da nata duk suna wajanta, washe-gari talata muka yi Arab day namu, na saka dogon rigan da Alhaji ya kawo mini daga Egypt, aka mini rolling na kuma sanya Safan hannu da ƙafa, fiskana ma ba abin da ake kallo sai idanuwana, ƙawaye ma suka sha nasu dogayen rigunan, kyau muka yi sosai, a haraban gidan Mami muka yi abinmu.

Washe-gari Laraba muka yi bridal shower, wannan a palourn Mami muka yi decoration, muka yi iya ni da ƙawayena, ranan Mamina ma tayi ƙunshinta, washegari Alhamis aka yi walima a tahfiz namu, a ranan kuma aka yi chin-chin da komai a gidan Abbaa.

Abu na farko da ya fara jawo ƙananun magana, shi ne dangin Ango ba su zo da yawa ba wajan waliman, to dai ni ban ce komai ba, komai aka yi da ido nake bi da kuma addu’a, Mamina ma ta musu uzuri, ta dai kwaɓi masu ƙananun maganganun akan ayi shiru.

Dare nayi kuma sai ga su, sun kawo kayan aure niƙi-niƙi, cikin mutunci da fara’a aka tarbe su, sai dai saɓanin haka aka gani a tattare da su, dan gaba-ɗaya ba fara’a ba komai kaman dole aka musu, ga shi Mamina bata wajan, nan ƙananun magana ya fara kacaɓewa, sai da Ummu da sauran manyan matan suka dakatar, abun tarban kayan ma da ake yi, sunƙi ɗauka, sai Ummu ce ta bi su da shi har waje ta basu haƙuri, aka samu wata dattijuwa dama-dama a cikin su, ta amsa suka yi sallama, suka tafi.

Maganganu kam yanzu sun samu wajan zama, dan shafi aka buɗe musamman a kansu ana yi, kaya yayi kyau sun yi ƙoƙari, akwatuna waɗanda ake yayi guda huɗu da kit, ga kuma na iyaye da na dangi, ga kayan rufi duka, jama’a na kallon kaya suna surutunsu.

Mami abun bai mata daɗi ba, kuma ya dameta, magana tayi abar zancen haka, sannan fa jama’an suka stagaita, wasu ma da suka gama kallon kayan suka tafi, wai sun yi zuciya Mami ta yi magana, mutane ikon Allah kenan, lokacin da ake jefanmu da baƙaƙen maganganu har da su, yanzu kuma da Allah yayi Allahnsa ya kawo mana sanadin rufin asirinmu, shi ne za su kawo wasu magana daga abu kaɗan wan da daman an san dole ne samun saɓani, musamman a hidiman biki, dole sai ana haƙuri kuma an haɗa da uzuri.

A haka aka gama kallon kayaki aka rufe, kowa ya nemi wajan kwanciyansa ya kwanta, sai dai ɓangaren Mami ranan bata yi bacci ba sam, damuwa ya taru ya mata yawa, gani take kaman daren nan ba zai wuce ba, balle kuma gari ya waye, tun da Mami take bata taɓa ganin dare mai matuƙar stayi ba irin wannan daren, wan da take ganinsa kaman almara, wai a washe-gari juma’a ne ɗaurin aurenta ita da ƴar ta, farin cikinta, gudan jininta, yarinyar da ta sadaukarwa komai nata, ta zaɓi rayuwa da ita akan tare da iyayenta.

Hawaye kawai Mami ta ji yana bin kuncinta, karo na farko tun da ta baro iyayenta, ta ji tana matuƙar kewansu, tana jin ina za ta gan su, su nuna mata gata a wannan rana ita da ƴar ta, Mami kuka ta yi ishashshe, har sai da ta ƙoshi da kukan, sannan ta tashi ta ɗaura alwala ta zo ta tada nafila, kwata-kwata bata kwanta ba balle ta yi bacci, har asuba ta kawo kai addu’oen alkairi take yi wa kan ta da yarinyarta, sai da aka yi sallahn asuba, ta yi nata sallahn sannan ta kwanta, da niyan anjuma za ta bawa Banafsha labarin komai, kaman yan da ta mata alƙawari.

A ɓangarena baccin nima dai rabi da rabi na yi sa, ƙarshe da na gaji da juye-juye, miƙewa nayi na ɗauro alwala na zo nayi nafila da addu’oe, addu’a na yi ga mahaifina idan yana raye ko yana mace, sannan nayi ga mahaifiyata ina mai mata addu’an, Allah sa mutuwa ce za ta fitar da ita a wannan gidan aure da za ta shiga, na yi wa al’umman Annabi, sannan nima na yi wa kai na, ina idarwa na bi lafiyan gado na kwanta, ina mai jin nistuwa na stirgani, cikin ƙanƙanin lokaci kuma bacci yayi awun gaba da ni.

Abu da duk su Mami basu sani ba, kuma ba su da labari, shi ne wani gagarumin ƙaramin yaƙi ake a ɓangaren su Malam Abbo.

Kaman yan da muka sani tun farkon labari, Malam Abbo ɗan shi’a ne, iyayensa shi’a suke gaba da baya, ƙarshenta ma babansa shi ne limamin babban masallacin su na juma’a, na ƴan shi’a.

Imam Adamu, wan da suke ƙira da Abiy, yaransu 7 shi da matarsa, Malama Hauwa’u, akwai babba wacce mace ce, Aunty Mardiyya, sai namiji Ya Hussain, sai Ya Hassan, sai Aunty Sajeeda, sai Aunty Zakiyya, ɗan Autan shi ne Ali(Malam Abbo).

Daga ƴan uwansa har iyayensa duka suna matuƙar ƙaunarsa, su a al’adansu ma ba ruwansu da musabaƙa, amma saboda soyayyan da Abiy yake yi wa Malam Abbo, ya bar sa ya shiga tahfiz yayi musabaƙa, wan da ya kai sa har matakin nasaran, da ya ciwo kujeran Makka, da kuma aka ɗauki nauyin karatunsa a Madina.

Yayyunsa maza da mata duk sun yi aure, kuma duka ƴan uwansu shi’an suka aura, to da Malam Abbo ya kawo maganan auren Banafsha, duk sun amsa sun yi na’am saboda tunaninsu ita ma ɗaya daga cikinsu ne, da suka ji tana tahfiz ɗin ma ba su ce komai ba, tun da sun san ta kusa gamawa, kuma Malam Abbo na makarantar, duk abin da Malam Abbo ke yi ko ya saɓawa starinsu, to sau tari Abiy yana masa uzuri, kuma yana tausan Ummi dan sosai Abiy yake ƙaunar Ali.

Ƴan uwan Abiy su suka fara yin bincike, nan suka ji labarin Maman Banafsha karuwa ce, yanzu ne ita ma za ta yi auren, ko da suka samu Abiy da maganan, ƙiran Malam Abbo yayi ya tambayesa akan ko ya san da labarin, Malam Abbo amsawa yayi da ya sani, kuma a haka yake son aurenta, jihadi zai yi, ai ba’a haramta auren karuwa ba balle kuma ƴar ta, wacce bata ji ba bata gani ba, babu ruwanta.

Abiy nusar da ƴan uwansa yayi akan kada su damu, sannan kada ma su yi aji maganan a bakinsu, ai ba komai a ciki tun da akwai a cikin magabata wan da yayi irin auren, shi karuwan ma ya aura da kan sa, kuma ƴar karuwa ai ba ana nufin karuwa ba ce, sannan idan aka ce ana ƙyamatan su ko a ce ba za’a aureta ba, so ake ta lalace kenan, dan haka da Abiy yayi nasiha sai suka ji, suka ci-gaba da shirin aure, amma yayyunsa mata duk basu sani ba.

To abu na farko da ya fara kunno kai shi ne, abokin Malam Abbo ne da kansa Zubair, ya tafi gidan babban addansu Aunty Mardiyya, kaman abin kirki ta tarbesa har tana zolayansa su angwaye ne, bayan sun gaisa sai Zubair ya karkace hulansa, rass ya zayyanowa Aunty Mardiyya ƙarya da gaskiya, ya kawo aya da hadisi yayi backing na maganansa da shi, ai zina bashi ce, abin da yake gudu kada a zo nan gaba a zuria’a abu yayi ba kyau.

Aunty Mardiyya kuwa ta ɗau zance ta zauna a kai daɓas, abin ka da mata sai s hankali, har da godewa Zubair tayi, yana tafiya ta ƙira sauran ƴan uwanta a waya, suka gama magana washe-gari suka haɗu a gida duka, Ummi suka fara samu suka zazzage mata komai, duk da tasan da zancen amma da yake, ƙarya da gaskiya ne Zubair ya faɗa, sai ya ƙara cika Ummi fam ta ce nan duniya Ali ba zai auri Faɗiman ba, tun da kalan tarbiyyanta kenan.

Abiy na dawowa shi ma Ummi ta hau bam-bami, wai ya sakalta Ali da yawa, ya sake masa sosai, ya rasa ƴar da zai aura sai mara tarbiyya to bata amince ba, Ummi na yi su Aunty Mardiyya na yi su ma, Abiy sai da ya gama sauraransu ya jira suka gama, sannan ya fara musu nasiha ya faɗa musu gaskiyan abin, amma Aunty Mardiyya ta ce ai abokinsa ne ya faɗa kuma shi ma malami ne a makarantar, ba zai yi ƙarya ba, Abiy tun yana nasiha har ya koma faɗa, sai da ya fatattake su ya korasu gidajensu, sannan ya samu salama, amma Ummi ta ƙi haƙura, har dai ran Abiy ya ɓaci, shi ma ya ce sai anyi, ita kuma ta ce ba za’a yi ba.

Su Aunty Mardiyya kuwa sai da suka ƙara zuwa ga baffanunsu, suka faɗa musu komai sannan suka koma gidajensu, baffanunsu suka samu Abiy da maganan, rai a ɓace ya ce ya gama magana, indai Ali bai auri Faɗima ba to Allah ne bai nufa ba.

Rikici ya ɓullo ta nan, wannan ma ya ɓullo ta nan, masu kawo gulma kuwa daban-daban, kowa kuma da karyan da yake shararawa har biki ya zo, duk rikicin Ummi da yaranta Abiy yayi jan ido sosai, dan dole suke komai ba dan sun so ba.

Har labari ya kuma isa ga Ummi da su Aunty Mardiyya, na cewa Banafsha ta yi bridal shower sun ta yin rawa da ƙawayenta, magulmata suka kuma ɗaura ƙarin gishiri, maganan Arabiyan day ma duka an ce sun yi rawan banza, nan fa Ummi ta ƙara kumbura, su Aunty Mardiyya suka ce ba mai zuwa wajan walima, Ummi ta hana kowa leƙawa, sai matan su Ya Hassan ne aka samu suka je, su ma mazajensu ne suka stawatar musu da Abiy yayi magana.

Wajan kai kayan aure kuma Aunty Zakiyya da Aunty Sajeeda, tare da su aka kai, amma a hakan ma sai da Abiy ya nuna ɓacin ransa sosai, kuma ya ajiye musu sharaɗin, idan suka yi faɗa ko wani abun tashin hankali to bai yafe ba, dan Abiy sosai yake ganin mutuncin iyayen Banafsha, tun da tare da shi aka je tambayan auren.

Zubair abokin Malam Abbo ya gama nasa, amma ashe bayan nasa da sauran masu kawo gulma, dan Garba ɗan gidan halliru yana gefe shi ma yana nasa shirin, tun da ya ce yana son Banafsha ta ƙi kulasa ta mayar da shi mahaukaci, ya yi ƙoƙarin samu ya illatata amma ta tsallake, to alwashi ya ci na ba zai bari tayi aure ba a garin muddin da ran sa, dan haka duk abin da ake yana bibiya, ganin ko ta ina Abiy yana dannewa yayi haƙuri ya ce za’a yi auren a haka, to sai kuma ya ɗau wani shirin na daban, jira yake kawai gari ya waye juma’a tayi ya ƙaddamar da ƙudurinsa.

Ya Danish babu shi babu labarinsa, ko da Abbaa ya ƙira sa akan yayi haƙuri, ya wastar da komai ya zo ɗaurin auren, tun da ita ma kaman ƙanwarsa ce, amma ya Danish ya fara kwane-kwane, da Abbaa ya nuna ran sa ya ɓaci sai ya amsa zai zo, amma daga suka gama magana sai ya kashe wayansa gaba ɗaya diff.

Malam Abbo Ango ya sha mai, duk wani badaƙala da ake da rikici, shi ko a jikinsa harkansa yake da shirye-shiryensa, musamman ma da ya ga Abiy ya staya masa, sannan duk wani abu da zai haɗa sa da Ummi kauce masa yake yi, dan abin da Abiy ya faɗa masa kenan, su bari sai anyi auren, sai su zauna su fahimtar da ita kuma ya bata haƙuri, sannan ya masa faɗa akan labarin da ya ji, na faɗima sun yi bidi’a wai bridal shower, haƙuri ya basa akan ba za’a kuma ba, za’a kiyaye, sannan yayi tafiyansa, dan haka Malam Abbo ko gidan ba ya shigowa saboda batun Ummi, yana hidimansa, yana kuma maƙale da wayansa, dan suna waya da Banafsha da layin Ummu.

Washe-gari juma’a, tun da gari ya waye ko wanne ɓangare ake shirye-shirye, amma dai shirin ya sha bam-bam, domin ɓangaren su Ummi gaba-ɗaya yau rikicewa tayi, akan ba maganan wannan auren kuma bata yarda da shi ba, su Aunty Mardiyya ma sun yi nasu tashin hankalin, baffanunsu ma sun zo da nasu maganan na bidi’a-bidi’an da Banafsha tayi da ƙawayenta, ba su yarda da shi ba, ga kuma ƙishin-ƙishin ɗin su Banafsha wai izala ne, da yake shi’a da izala sam-sam basa shiri.

Abiy idan ran sa yayi million to ya ɓaci, kan sa kuma ya ɗau chaji sosai, wato ka guji kaidin mata idan suka ƙi abu, da farko sun ce ƴar karuwa ce, an zo an ce tana bin maza, an ce bata da tarbiyya, an ce ta yi bidi’a har da rawan da bai dace ba, an ce..an ce..an ce ɗin da yawa ba kaɗan ba, duk kuma yana haƙuri saboda yaro yana son yarinya, sannan yanzu ga wani batu na wai su izala ne, sannan wannan kam yasan ƴan uwansa ba za su bari ba ko da ya stawatar, dan haka a ranan juma’an da kan sa ya bincika duk abin da ya kamata, abin da ya jawo kuskure babba kuwa shi ne mahaifin Garba, wato malam halliru yana cikin waɗanda Abiy yayi magana da su.

Lokacin sallah na yi, Malam Abbo ya shirya da abokanansa suka tafi masallaci, ba ma masallacin su da suka saba sallah suka je ba, direct babban masallacin da za’a ɗaura auren a can suka nufa shi da tawagarsa ta abokanansa.

Ɓangaren mu kuwa yan da shirin yake, komai dai-dai sai abin da ba za’a rasa ba na halin rayuwa, gaba-ɗaya hidima ya sa ko da Mamina ta tashi, a makare ta tashi lokaci ya tafi dan kusan ƙarfe ɗaya ta tashi, lokacin kuma an fara shirin tafiya masallaci, saboda biyu da rabi za’a ɗaura auren, ni da yake bansan da Mami yau za ta bani labarin da ta faɗa ba, to sai ban damu ba, da aka ce tana bacci na bar ta, ba wanda ya tashe ta, an bar ta wai ta huta.

Mami ta tashi lokaci ya ƙure, gaba-ɗaya bata ji daɗin hakan ba, dan ba ta tunanin akwai lokacin da za ta samu a nitse su yi maganan, dan ana sauƙowa ɗaurin aure ba jimawa, za’a ce an zo ɗaukan Amarya, tun da su a Mubi da yamma ake ɗaukan aure, ta rasa ya za ta yi, ga shi dai ana kai Amarya kuma shikkenan, sannan wannan magana ba wan da za’a yi sa a waya ba ne, dan haka a lokacin ta saka a shirya Banafsha tun da har ɗaya ta yi, idan an sauƙo ɗaurin aure kamun a ce anzo ɗaukanta, ko sama-sama za su yi maganan, dan yin maganan a yau ya zama dole, idan ba yau ba, ba zasu samu lokaci ba, ita tana gidanta a nan Mubi, ita kuma Kano za su wuce da Alhaji.

Shirya Banafsha aka yi cikin wani irin ranstaststen shinning les, fari da flower-flowern golden a jikinsa(leshin Amare), ɗinkin dogon riga ne wan da yayi mugun bin jikinta ya zauna mata ɗasss!, Banafsha bata son makeup dan haka simple aka mata kawai, aka aje mata wata shegiyar ɗauri, ta sanya sarƙan da Alhaji ya kawo mata na gold da komansa, idan ka ga irin kyawun da Banafsha tayi ba hmmn, ba’a magana kawai fan’s, amma Banafsha ta haɗu iya haɗuwa, ta kashe su ta bada kala ta raya wanka, ta suturta kyau yan da ya kamata, tun da aka gama kuwa sai pictures suke yi, har Mami ita ma ta fito da nata shirin cikin wani haɗaɗɗen yadi mai laushi da ƙamshi, ita ma nata ɗinkin dogon riga ne, fan’s uwa da ƴan duk sun yi kyau sai sambarka da fatan Allah ba da zaman lafiya.

Umaima ma fa ba’a bar ta a baya ba, dan ƙawar Amarya ma Amarya ce, Umaima ta haɗe ta cakare ta sha kyawunta kaman ita ce Amaryan, sai photuna kawai suke yi da sauran freind’s, Mami magana ta yi wa Banafsha akan zuwa anjima za su yi magana kamun a kai ta, Banafsha tun da Mami ta faɗi haka shikkenan yanayinta ya fara sauyawa, ta fara tuna za ta rabu da Maminta, za su yi nisa, duk shagalin da ake kawai dauriya take yi.

*****

Su Alhaji suna isowa suka haɗu da su Abbaa, nan aka dinga musabaha aka shige masallaci, General dai tun da ya zo garin ya ji ya burgesa.

ACM Bunayd, da su Abeed da abokansu suna nasu gefen, bai kula da Abbaa ba, shi ma bai kula da shi ba, haka su ya Sadeeq, kamun dai a shiga sallah cikin ikon Allah sai ga Dr Arshan, sosai yayi mamakin ganin Bunayd, dan ya gane sa, nan suka gaisa cikin fara’a (kunsan Bunayd bai cika baƙin hali ba).

Dr Arshan yana ganin Abeed ya gane shi ne patient nasa tun ba’a faɗa masa ba, ya jiki ya tambaya suka gaisa kaman abokanan da suka jima da sanin juna, Dr Arshan dai bai tambayesu me kuma suka zo yi Mubi ba duk da ya san daga Kano dai suke, bari yayi akan ko an ƙara dawo da aikinsu nan ne, ko da ya tuno Banafsha mutumiyar Soja, nan ya dinga dariya ya na faɗin Bunayd bai tambayi mutumiyar sa ba.

ACM ɓata fiska yayi, wai ya daina haɗa sa da idiot ɗin can, dan shi ko sunanta bai sani ba, Abeed kasa kunne yake ya ji me ake ciki, yana jin maganan mace ne tuni ya amsa yana dariya, yana faɗin Dr Arshan ya taimaka ya basa labari, Dr Arshan amsawa yayi akan zai basa amma sai sun fito sallah.

Nan suka shige masallacin su ma, suka bi sahu aka ta da sallah, Masha Allah, Allah ya ƙarawa musulunci ɗaukaka, alfarman Rasulullahi SAW, wato idan ka ga taron jama’a yan da ake sallahn juma’a kaɗai abin burgewane, ba ma sai an kai ga sallahn idi ba, alhamdulillahi bini’imatul Islam.

ME KUKE TUNANI DAI DA WANGA AURE NA MALAM ABBO DA MALAMA BANAFSHA?

FINALLY DAI ZA MU JI LABARIN MAMI, WACECE MAMI DA HAR TA RIƘE KARUWANCI A MATSAYIN SANA’A, MENENE SANADI? ME SILA? ME YA JA? DUK SABODA ME? TANA DA DALILI KUWA KO SON ZUCIYA NE? KUMA WAYE MAHAIFIN BANAFSHA?

<< Yar Karuwa 19Yar Karuwa 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×