Skip to content
Part 21 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Littafi Na Biyu

An tayar da sallah, an idar akan lokaci, ba jimawa kuma aka fara ɗaura aurarraki, dan auren ba ɗaya ba kuma ba biyu ba.

Tun da aka fara gabatar da ɗaurin aure, su Alhaji suke baza ido ta in da za su ga ɓullowan dangin mijin Banafsha, amma shiru babu su ba labarinsu, ko Malam Abbo da ke cikin masallacin ma ba su kula da shi a wajan ba, saboda hankalinsa shi ma yana wani wajan daban, tunani yake na abin da ya hana su Abiynsa zuwa.

Abbaa ne ya dubi Alhaji ya ce, “Anya mutanen nan lafiya kuwa shiru ba su ba labarinsu?”

Alhaji cikin damuwa ya duba haɗaɗɗen agogon da ke maƙale a hannunsa, sannan ya kuma baza idanuwansa a cikin masallacin, dubansa ya mayar kan Abbaa ya ce, “kuma ga shi ba layin wayansu ko?”

General Sufyan da ke gefe tare da su Alhaji Idris, cewa yayi, “Lafiya kuwa yaya?”

“Lafiya General, kawai waliyan mai auren yarinyar ne ba mu gansu ba.”

Suna cikin magana sai ƙira ya shigo layin Abbaa da sabon number, ɗauka yayi tare da yin sallama.

Amsawa aka yi a ɗaya ɓangaren tare da cewa, “Baffan Aliyu ne wan da zai auri Faɗima, ina wajan masallaci dan Allah ka fito za mu yi magana idan ba damuwa.”

Abbaa sanar da Alhaji yayi, suka fice tare, daga gefe suka hango mutumin, nan suka ƙarisa, suka gaisa cikin mutuntawa, Abbaa ya ce, “bawan Allah ya muka ji ku shiru haka? Ga shi ana ta gudanar da ɗaurin aurarrakin har an kusa namu.”

Mutumin ajiyan zuciya ya sauƙe tare da faɗin, “ku yi haƙuri na rashin sanar da ku a kan lokaci, domin ko shi yaron ma bai sani ba, ku yi haƙuri amma yaronmu ya fasa auren ƴar ku, saboda wasu dalilai da kunsan da su, kuma kuka ɓoye mana.”

Alhaji ya kasa ma yin magana, da kallo kawai yake bin mutumi mai maganan, amma kana ganinsa kasan ransa a ɓace yake.

Abbaa cikin ɓacin rai ya ce, “Wani irin dalili ne haka muka ɓoye muku da za ku mana wannan tozarcin, meyasa ba ku sanar da mu tun ba yau ba, jiya da yau da safe duk saboda me? Sai yanzu da ake ƙoƙarin ɗaurawa, to ku sani duk wanda ya tozarta wani bawan Allah, to shi ma sai Allah ya tozarta sa.”

Baffan Malam Abbo ya buɗe baki zai yi magana sai Alhaji ya dakatar da shi ya ce, “menene dalilan naku? Shi kawai muke so ka sanar mana.”

Ajiyan zuciya Baffan Malam Abbo ya sauƙe, sannan ya ce, “Ku yi haƙuri, abin da kawai aka turo ni na faɗa kenan, amma dai babban dalilin shi ne an ce yarinyar ba’a san ubanta ba, kuma ba ta hanyar Sunna aka haifeta ba, sannan mahaifiyarta karu..”, Alhaji bai bar sa ya ƙarisa ba ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu, rai a ɓace ya ce, “Ya isa mun gode.”

Abbaa ransa yayi mugun ɓaci, Alhaji duk rashin fushinsa yau idan ka kallesa kasan ran sa a ɓace yake, haka suka juya suka bar mutumin a wajan suka koma cikin masallacin, shi kuma mutumin ya juya cikin sanyin jiki yayi tafiyansa, yasan yarinyar ba ta da nasaba da asali mai kyau, amma abun sam bai yi daɗi ba, haka kawai a fada aure kwastam ba sanarwa akan lokaci.

Alhaji ba abin da yake yi sai aikin stuka, Abbaa ne ya ja dogon numfashi ya ce, “Yanzu Alhaji ya za’a yi? Za’a sanar da ita Hajiya Ramlatu ne ko kuma za’a yi wata dabarar daban?”

Alhaji lumshe idanuwansa yayi yana seta kan sa, ji yake ina ma yana da cikakken iko da Banafsha, to da ba shakka sai ya aurawa Bunayd ita, yanzu kuma idan ya ce zai yi hakan shi ba mahaifinta ba, to bai yi adalci ba balle gaskiya, ga ɗan gidan Abbaa yana son ta, bai ɗaura da shi ba, ya ɗaura da ɗansa da ko saninsa Banafsha bata yi ba, wannan shiga haƙƙin yarinya ne, dole kawai ayi haƙuri abar maganan ɗaura aurenta, Allah bata nagari wan da ya fi shi, Allah kuma ya sanya hakan ya zama alkairi a gare su dukansu biyun.

Cikin damuwa Alhaji ya ce, “Abar sanar da Ramla yanzu kada hankalinta ya tashi, ina ga kawai a haƙura da ɗaurin auren, Allah bata nagari wan da ya fi shi, Allah bai nufa yanzu za ta yi aure ba ne shiyasa haka ta faru.”

Jinjina kai Abbaa yayi, yana mai na’am da furucin Alhaji, duk da ya so ace Danish ya halarci ɗaurin auren, da idan aka sanar da Hajiya Ramla, to sai a ɗaura da Danish ɗin, amma bakomai wannan ma wata damar ce, idan da rabon ya aureta zai aureta, Allah sa dai hakan shi ne alkairi ga Faɗima.

General Sufyan duk yana kula da yanayin Papi da kuma na ma Abbaa, amma ya bari sai an gama idan sun fita, sai ya tambaye su ko lafiya, yanzu dai sun mai da hankali wajan liman da ke ɗaura aure, dan yanzu za’a gabatar da na su Mami da Alhaji, dan Abbaa ya lallaɓa ya sanar da liman an fasa ɗaura auren Aliyu da faɗima, dan kada a ƙira sunansu kuma tozarcin yayi yawa.

Bunayd da Abeed suna tare da Dr Arshan, har aka idar da sallah, su basu san ma wainar da ake tonawa ba, Abeed magana suke ƙasa-ƙasa da Dr Arshan suna dariya, dan da alama labarta masa badaƙalar Bunayd da Banafsha yake yi, shi kuma Bunayd haɗe fiskan nan yayi tam, hankalinsa na wajan liman da ke ta ɗaura aurarraki, mamaki kawai yake na irin auren da ake yi, amma a haka mata da mazan ba sa ƙarewa (ina za su ƙare kai ma gauro ne ja’iri ɗan gidan General).

Auren Papi da za’a fara ɗaurawa shi ya stayar da su Abeed daga hiransu, suka mayar da hankali kan liman.

ACM leƙawa yayi wajan su Papi, miƙewa yayi ya ƙarisa wajansu, sai lokacin ya kalli Abbaa kuma ya tuno sa, shi ma Abbaa ya gane Bunayd, murmushi ACM Bunayd ya sakar ma Abbaa ya gaishesa, sannan ya miƙa wa Papi keyn mota ya ce, “Sir a ƙara a kan sadakin.”

Alhaji washe baki yayi tare da sanya wa Bunayd albarka, dan yayi surprising nasa, General kuma shi ya biya kuɗi.

Abbaa ne waliyin Mami, General kuma waliyin Papi, an ɗaura auren MUKHTAR SULE KWALLI & RAMLA HASHIM ABUBAKAR akan sadaki Naira dubu ɗari uku da keyn Mota ƙirar Jeep.

Alƙawarin Allah ya cika, Allah ya nufa Alhaji Mukhtar ya zama miji ga Mami, kar ku so ganin yacce Alhaji ke washe haƙoransa, kaman wan da aka yi wa bishara da an yafe masa zunubansa.

Ana gama ɗaurawa kuwa, sojoji suka buga bindigunsu, Bunayd sai murmushi yake kaman wani shi aka yi wa auren, dan haka kawai yake jin kan sa cikin farin ciki, shi har mamaki yake na yadda sam ko kaɗan baya jin haushin, za’a yi wa Mom tasa kishiya.

Abbaa dai mamaki yake na me haɗin Alhaji, da sojan da ya biya wa Maman Banafsha kuɗin asibiti, amma ya bari sai sun fice ya yi wa Alhaji maganar.

Sai da aka gama komai sannan suka fito, da motocin Sojojin duka suka nufi gidan Mami, Dr Arshan ma har da shi, dan abota ne ya ƙullu stakaninsa da su Abeed, har exchanging numbers sun yi da Abeed da Bunayd duka.

A ƙofan gidan Mami motocin suka ya da zango, suna isowa Sojojin suka sassauƙa, daman ga su cikin uniform, nan suka fara ɓarin bindigu, tuni mutane kowa ya kama kan sa, mastorata irin Uwar batoorl kuma tuni cikin mu ya ɗuri ruwa, sai zuru-zuru muke da idanuwa kaman an tare kule a buta, har na hango masoyiya bealky da nata gwala-gwalan idanuwan, ga kuma su Hafsat Umar ƙawayen Mami, da su Mom muhmd mutan garin masu bindiga an saba da ƙaran ko a jikinsu, ƙanwa eclema Amarya ana can tare da su Banafsha ita da kakarta besty seeyath mutanen Mubi, su Ummu Adeel mai jego kuwa ana ƙunshe a ɗaki da ɗan jinjirinta.

Ɓangaren Malam Abbo, tun da aka idar da sallah ya fara dube-duben su Abiynsa, ko kula da su Abbaa bai yi ba, gaba-ɗaya hankalinsa ya tashi, wani irin stinkewa zuciyarsa ke yi, ko su Ya Hussain bai ga alamansu ba, balle baffanunsu, kar kuma a kai ga Abiy.

Abokanansa na masa magana amma ko jin su baya yi, ya fiddo waya da niyan ƙiran Abiy, sai ga ƙiran Ya Hussain ya shigo, ɗauka yayi da sauri ya ce, “Ya Hussain lafiya kuwa ban gan ku ba? Ko baku gane masallacin ba ne?” Ya ƙarishe maganan cikin zaƙuwa.

Ya Hussain a nasa ɓangaren ajiyan zuciya ya sauƙe, sannan ya ce, “kwantar da hankalinka Ali, lafiya lau ba komai, amma Abiy ya ce na faɗa maka yana buƙatar ganinka yanzu.”

Malam Abbo cikin rashin fahimtan in da maganan Ya Hussain ya dosa, ya ce, “Abiy kuma yana buƙatar ganina sannan ka ce lafiya, shi ɗaurin auren kuma fa ya za’a yi da shi? Ga iyayenta suna jira, ga ni da abokanayena duka.”

Ya Hussain ya ce, “saƙo aka sa na ƙira na sanar maka, kuma na faɗa maka Abiy na neman ka, shikkenan sai ka zo”, yana faɗan haka ya kashe wayansa kitt.

Malam Abbo hankalinsa idan ya kai dubu ma to ya tashi, wani irin Abiy na nemansa, maganan ɗaurin auren ya za’a yi da shi? su iyayen nata kuma fa? wai me ke faruwa ne?, cikin rashin makama da taƙamammen mai amsa masa tambayoyinsa, ya sharce gumin da ke ƙeto masa, rasa ma wajen abokansa zai koma ko kuwa gida zai yi oho.

Juyawa Malam Abbo yayi cikin ɗimbin damuwa ya wuce kawai, ɗaya daga cikin abokanan nasa ne da ya ga fitansa sai ya tambayi sauran ko me ya sa Aliyu ya fita, su ma basu sani ba, dan haka ƙiransa yayi yana ɗauka ya ce, “Ango ina za ka je kuma bayan kasan ba jimawa za’a daura.”

“Rilwan gida zan je”, faɗin Malam Abbo cikin damuwa.

Rilwan ya ce, “gida kuma a wannan lokaci, me ya faru? Waye ba lafiya? Ɗaurin auren fa ya za’a yi da shi?”

Guntun tsaki Malam Abbo ya ja, ya ce, “ko ɗaya nima ban da amsar da zan baka, neman mai amsa mini nake yi ni ɗin ma.”

“To yanzu kai ka tafi mu kuma yaya kenan bayan kasan dan kai muka zo.”

“Rilwan plss bari na isa gidan, ko me ake ciki zan ƙira ka, ku yi haƙuri”, Malam Abbo na faɗan haka ya kashe wayansa, kaman zai yi kuka haka yake ji, mashine na ɗaya daga cikin abokanansa ya ja ya nufi gidan nasu.

Tuƙi yake cike da ganganci saboda damuwan da yake ciki, ikon Allah ne kawai ya kai sa gida lafiya, yana zuwa ba sallama balle jiran ko Abiy na tare da baƙi, haka ya shige palourn Abiy.

Abiy da ya ga shigowan yaron nasa da yanayin da yake ciki, sai ya ji tausayinsa ya kamasa, lallai basu kyauta masa ba, yanzu ita kuma yarinyar ya za ta ji kenan, shi namiji ma dubi yanayin da ya shiga tun bai san abin da ke tafiya ba.

Malam Abbo zama yayi dirsham a gaban Abiy kaman mai neman gafara ya ce، “Abiy gani.”

Abiy sai da ya ja dogon numfashi sannan ya ce, “Ali magana nake son na maka ta fahimta, cikin sigan haƙuri da kuma rarràshi, sannan da umurni muddin na isa da kai.”

Malam Abbo sam-sam ba ya ma gane me Abiy yake faɗa, shi kawai damuwansa ya ji me ya faru, kuma me ake nufi da batun ɗaurin aurensa.

Abiy ya ce, “Ali maganan aurenka da yarinyar nan an fasa, shiyasa ma baka ganmu a masallacin ba, sannan na tura an sanar da waliyyanta.”

Tun da kalman an fasa auren su ya dira a kunnen Malam Abbo, shikkenan jin sa ya ɗauke na wasu daƙiƙu, gaba-ɗaya idan ka kalli fiskan Malam Abbo ka ce jira ya ke a ce fitt ya falla a guje, saboda yan da ya zaro idanuwansa, kwata-kwata ma ƙwaƙwalwansa ba ya gane abin da Abiy ke faɗa, tun da ya ji kalman an fasa shikkenan yake ta maimaitawa a kan sa, kaman wan da aka basa bitan karatu.

Abiy da ya gama dogon maganansa, jin malam Abbo bai ce komai ba, wan da ke nuni da hankalinsa ma baya tare da shi, zuba masa idanuwa yayi cikin tausayinsa ya ƙira sunansa, “Ali fatan ka ji duk abin da na faɗa.”

“Abiy ban ji ba”, haka kawai Malam Abbo ya faɗa yana ajiyan zuciya, wan da take idanuwansa suka kaɗa jajir, kaman mai jiran ƙiris ya saka kuka.

Jinjina kai Abiy yayi tare da gyara zamansa, ya ce, “Ali.”

“Na’am Abiy”, faɗin Malam Abbo da idanuwansu ke kan Abiy.

“Ali ka yi haƙuri akan abin da muka yanke, kuma ina mai fatan za ka mana biyayya akan hakan.”

Jinjina kai kawai malam Abbo yayi, yana mai sauraran Abiy.

Abiy ya ce, “Ali maganan aurenka da Faɗima babu shi, ka yi hakuri kawai, Allah baka tagari wacce ta fi ta zama alkairi a gare ka, nasan kana da iliminka, sannan kana aiki da shi dai-dai gwargwado, to ka ɗauka kawai Allah bai nufa ta zamo matarka ba ce, in kuma Allah ya nufa, to na tabbata ko nan da yaushe ne za ka mallaketa, ko da kuwa bayan ran mu ne, don bawa bai isa ya hana abin da Allah ya ƙaddara ba.”

Malam Abbo kaman mai shirin yin kuka, ya ce, “Saboda me aka fasa Abiy?”

“Ali na faɗa maka, ka ɗauka kawai akan Allah ne bai nufa ba, dan da Allah ya nufa to ba wan da ya isa ya hana ko da mutuwa ce.”

Malam Abbo idanuwa ya zubawa Abiy, rasa abin faɗa ko abin yi yayi, gaba-ɗaya ji yake kaman mafarki yake, ji yake kaman a wata duniyar yake ta daban, cikin damuwa ya lumshe ido tare da haɗiye wani mugun abun da ya tokare masa maƙoshi, ba tare da ya ce uffan ba ya mike, yana jin jiri na ɗibansa haka ya fice a palourn, bai ma tsaya sauraran ƙiran da Abiy ke masa ba.

Cikin gidan ya nufa, yana zuwa ya shige ɗakin Ummi, samunta yayi zaune tare da yayyunsa mata, bai ko ce musu ƙala ba ya ƙarisa wajan Ummi ya durƙusa a gabanta ya ce, “Dan Allah dan Annabi Ummi ki yi haƙuri ki bari na auri Faɗima, dan ƙaunarki ga ahlul-bait.”

Haɗe fiska Ummi ta yi, ta ce, “Ali bana son rashin hankali, idan aka bar ka sai ka auri yarinya mara tarbiya tun da baka da hankali kuma baka da mafaɗi ko? “

“Ummi wallahi Faɗima na da tarbiya fiye da tunaninki, na tabbata ko kece mahaifiyarta to iya tarbiyan da za ki mata kenan” faɗin Malam Abbo.

Ummi ta ce, “To ba za ka aureta ba, yarinyar da bata da uba, ba’a san ubanta ba, a yawon ta zubar aka yi cikinta, kuma uwarta na karuwanci ai komin kamun kan ta bata isa ta ce ita tagari ba ce, wannan ya shiga yau, wannan ya shiga gobe, ta lalace da ganin mazaje da yawa ina za ta iya nistuwa ta yi zaman aure, wa ma zai auri irin wannan ƴar.”

“Ni ina son ta a haka, zan aureta a duk yan da take, Ummi ko ya Faɗima take zan aureta, ni zan zauna da ita ba kowa ba, dan Allah ku bari a ɗaura auren nan Ummi.”

“Ni kuma na ce ba za ka aureta ba Ali, ba za mu haɗa jini da gurɓatattun mutane ba, haka kawai ka yayuɓo mana fitina a zuria’a.”

“Ummi ki yi haƙuri dan Allah dan…”, Malam Abbo bai gama faɗan abinda zai faɗa ba Ummi ta dakatar da shi ta hanyar masa mugun tsawa, tana masa nuni da ƙofa, dan ya fice mata a ɗaki.

Cewa tayi, “Ali tashi ka fice kamun ran ka ya ɓaci, maza ɓacewa ganina kamun na saɓa maka, shashasha kawai, kuma karatunka bai maka amfanin komai ba, tun da ka kasa banbance tsakanin abu mai kyau da mara kyau.”

Malam Abbo ƙasa yayi da kan sa ya ce, “ki yi haƙuri Ummi, amma ina tunanin a karatun da na yi, addini ya karantar da mu hatta matan ahlul-kitab an lamunce mu aura, sannan ita fa Faɗima musulma ce, wallahi na yarda da tarbiyyan Faɗima ɗari bisa ɗari, nasan yara na za su samu tarbiyya mai kyau..”

Tassss! Kake ji Aunty Mardiyya ta kwashe Malam Abbo da mari tun bai ida maganansa ba, ƙofa ta nuna masa ta ce, “tashi ka bamu waje Ali, tun da har ka zama mara kunyan da zai ce iyayensa karatunsu bai kai ba, soyayyan banza soyayyan wofi, tashi ka bamu waje.”

Dafe kumatu Malam Abbo yayi, murmushin taƙaici yayi dan shi sam ma bai ji haushi ko zafin marin ba, yana kallon Aunty Mardiyya ya ce, “Kada ki manta Aunty ke ma auren soyayyan kika yi, meyasa ni za ku hana ni farin ciki na?”

Aunty Sajeeda ne ta kallesa, cikin tausayi ta ce, “ka yi haƙuri Ali, tashi ka je abinka, Allah baka wacce ta fi ta alkairi, ka yi haƙuri ka ji maganan manyan ka.”

Ummi da ran ta ya gama ɓaci, cewa tayi, “To ko bayan rai na ban yarda ba ka auri yarinyar nan, tun da akan ta kake mana rashin kunya, tashi ka bamu waje.”

Sumui-sumui Malam Abbo ya miƙe yana jin jiri na ɗibansa, ficewa yayi a ɗakin, yana haɗa hanya har ya kai kan sa ɗakinsa cikin ikon Allah, faɗawa yayi kan katifansa cikin mastanancin ciwon kai da damuwa, ga ƙiran abokanansa da ke shigowa tun ɗaxu ko ta kan wayan ma bai bi ba, rasawa yayi kuka zai yi ko me? Me yasa iyayenmu suke ɗaukan wani abu daban da bai kamata ba su ɗaura a kan su, me laifin Faɗima? Ita ma mahaifiyarta me laifinta? Ko akwai wan da ya fi ƙarfin ƙaddara da jarabawan Ubangiji ne.

Malam Abbo bai ankare ba sai hawaye masu ɗumi ya ji suna bin kuncinsa, yanzu kenan an raba sa da ruhinsa, ya zama mayaudari a wajanta, duk burinsu na zama aure an rusa shi, damuwa ne sosai ya rufe Malam Abbo( Allah ba ka wacce ta fi Banafsha alkairi Malam Aliyu, Uwar batoorl ma ta ji tausayinka).

Su rilwan kuwa a masallaci da suka gaji da jiran Malam Abbo, sun ƙirasa ya fi sau ɗari baya ɗauka, hankali tashe suka laluɓo layin yayansa Hussain, yana ɗauka Rilwan ya ce, “Ya Hussain dan Allah waye ba lafiya? Muna masallaci an ƙira Aliyu ya tafi gida, shiru kuma har yanzu bai dawo ba mun ƙira sa bai ɗauka ba, kuma su Abiy ba su zo ba, ga shi har an gama ɗaura aurarrakin.”

Ya Hussain a nasa ɓangaren cewa yayi, “Rilwan ku yi haƙuri, anfasa ɗaura auren ne, ba’a sanar da shi yana masallacin ba ne dan kun san halin zuciyan Ali ɗin.”

“To Ya Hussain, Allah rufa asiri ya sa hakan ne alkairi.”

“Ameeñ Rilwan, ku yi haƙuri fa.”

“Ba komai ya Hussain sai anjima”, Rilwan na gama faɗa ya kashe wayan cikin jinjina lamarin da kuma tausayawa abokin nasu, domin duk sun san yan da Aliyu ke ƙaunar Faɗima, har zolayansa suke kaman wata ita kaɗai ce mace a duniya, amma sai ya ce idan ba ita ba zai yi aure ba.

Cikin damuwa ya sanar da sauran abokanan nasu, duk jajanta lamarin suka yi, da bin su da addu’an alkairi (abin ka da maza ba gulma kaman mata, da yanzu an fara bin ba’a si).

*****

Mami tun da ta ji an sauƙo juma’a ba abin da take sai washe baki dan farin ciki da murna, ji take kaman ta sauƙe dusten dala a kan ta, ta aurar da yarinyarta lafiya-lafiya cikin ikon Allah sai godiya, daman da alwalanta, dan haka nafilanta ta yi raka’a biyu tare da jero addu’oe, tana mai fatan alkairi da zaman lafiya a gare su duka, tana idarwa kuma ta kare fesa turare ta zauna abin ta, jiran ƙiran Alhaji take yi, dan a yanzu ba ta da abin da take so kaman ta yi tozali da alhajinta, yau ga ta a matsayin matarsa, mallakinsa halal nasa, lallai mahaƙurci mawadaci, duk daran daɗewa za ka dafa duste har ka sha romonsa, a hankali Mami ta ce, “Alhaji ka yi haƙuri kuma ka cimma nasaran haƙurinka.”

Ɓangarena kuwa duk murmushin da nake da ƙawayena, to na yaƙe ne, dan kuwa wani irin stinkewan zuciya nake ji na musamman, jira nake kawai na ga ƙiran Malam Abbo, dan nasan muddin aka ɗaura to fa zai ƙirani, na mastu na ga ƙiransa dan nasan ɗaukin Malam Abbo da irin alwashin da ya ci wa wannan rana, ta musamman a garemu.

Umaima kallon Banafsha tayi ta ce, “Su masoyiya Amaren zamani nasan yanzu haka lissafi da tunanin uhmn kike.”

Hararan Umaima nayi na ce, “mtsww! Tun da an ce miki ai kowa iskanci ne a gabansa ko kowa irinki ne ai, ni ba ruwan Malamina da wannan abin.”

Dariya Umaima ta yi, da yake ƙasa-ƙasa muke maganan ba wan da ya ji, lokaci na duba kawai, ganin time ya ja sai na miƙe na shige ciki, sallah na nayi na kuma yi nafila na ɗaura da addu’oe, duk da Malam Abbo bai ƙirani ba, amma nasan Insha Allah yanzu kam anɗaura, kuma na masa uzuri wataƙila jama’a ne suka masa yawa.

Na dawo wajan su Umaima na zauna sai muka jiyo ƙaran motoci har da jiniya, can kuma ba jimawa sai ga ƙaran bindigu, ai tuni kowa ya nustu, masu saurin storita kuwa har cikinsu ya ɗuri ruwa, abinka da ba’a raba ta yankin mu da ƴan ta’adda.

Umaima ta ce, “Masoyiya da alama dai angwaye ne a ƙofan nan, bari na zo daman akwai abokin da muka yi magana da shi, idan sun dawo ɗaurin aure za mu yi wani shawara akan ɗaukan aure.”

“A dawo lafiya, ki kula”, kawai na faɗa tare da miƙewa na bar cikinsu, na koma gefe na kwanta dan sosai stinkewan zuciyata ya ƙaru.

Umaima cikin nistuwa take tafiya har ta fice a gidan, su Abbaa ta fara kallo a gefe tare da Alhaji da wani mutum(General), ƙara dubawa ta yi amma bata ga alaman abokanan Malam Abbo ba, cike da mamaki take ta dube-dube, har idanuwanta suka sauƙa a kan Dr Arshan da tun fitowanta ya kalleta, dan tabbas ya gane ta, tare suke da Faɗima mutumiyar ACM Bunayd, murmushi ya sakar mata tare da tinkaro ta.

Ita dai Umaima kallonsa take kawai, ta rasa ma a ina ta san fiskan shi, ga kuma tana gani ya tunkareta yana murmushi, tana ƙoƙarin juyawa ashe bata ankare ba har ya ƙariso in da take, yana murmushi ya ce, “Assalamu’alaikum barka Hajiya.”

Umaima amsa sallaman tayi kawai tare da kawar da kan ta.

Dr Arshan murmushi ya saki ya ce, “Da alama dai hajiyar bata gane ni ba, nine Dr Arshan wan da kuka yi jinyan mamanku a wajansa, ke da ƴar uwanki Faɗima”, ya faɗa cikin maganansa mai kama da rigima.

Umaima zaro ido tayi, sai kuma ta saki murmushi tana faɗin, “Afuwan, wallahi ganin kaman na gane ka nake maka, amma na kasa tunawa a ina ne, sai yanzu na tuno.”

Murmushi yayi ya ce, “bakomai Hajiya, ya ƴar uwanki? Ya kuma mai jiki? Wa kike nema na ga tun fitowanki kike ta kalle-kalle.”

Umaima ɗan ɓata fiska tayi kaman mai shirin yin kuka ta ce, “Wani ne amma dai ban ga alamansa a nan ba.”

Dr Arshan ma ɓata fiska yayi ya ce, “A’a ba wani bane, Arshan kike nema daman kuma ga ni.”

Murmushi kawai Umaima tayi ta ce, “Uhmn! Rufa mini asiri, ni ina zan kalli mijin wata.”

Murmushin gefen baki yayi wan da ya ƙara masa kyau( fan’s Dr Arshan ma fa ƙarshe ne a kyau, ga aji sannan ga kuɗi), hannayensa ya sa a aljihu tare da cewa, “Ina ƴar uwanki?”

“Tana ciki, yau ma auren ta, yanzu ma abokin mijinta na zo dubawa sai naga basu iso ba.”

Ƙara ɓata fiska Dr Arshan yayi ya ce, “Ni fa ƴar uwanki na tambaya ba wani ba.”

“Sorry”, faɗin Umaima da ke ƙoƙarin juyawa.

Dr Arshan ya ce, “Ban fa sallameki ba Hajiya.”

Cikin mamakin ƙarfin hali irin na Dr Arshan, Umaima ta juyo tare da kallonsa cikin ido, amma suna haɗa ido ta ji wani iri, ya mata ƙwarjini sosai, tura baki tayi kawai ta kawar da kai gefe tana magana a zuciyanta ita kaɗai.

Ƙayataccen murmushi Dr Arshan ya saki tare da cewa, “Hajiya saki ran ki, nima fa na iya shagwaɓan.”

Umaima dai mamaki take na ƙarfin hali irin na Dr Arshan, kaman wani wan da ya san ta da jimawa, ba tare da ta kallesa ba ta ce, “Zan shiga ciki Amarya na jirana.”

“To Amarya kuma ƙawar amarya, kinsan an ce ƙawar amarya ma amarya ce, ki gaishe mini da ita Allah sanya alkairi, amma ki taimaka mini da numbernki kamun ki tafi”, Dr Arshan ya faɗa yana miƙa mata haɗaɗɗen ƙaton wayansa mai stadan gaske.”

Umaima cikin gajiya da stayuwan tun da bata saba ba, ta ce, “Ni ban da waya, kuma Abbaana yana kallona kar ka ja mini faɗa.”

Murmushi ya kuma yi ya ce, “Ba matsala kada mu yi wa Abbaa laifi, tun da naga gidanku shikkenan, sai kin ganni, ki shirya tarban baƙo.”

Cunna baki Umaima tayi ta juya abinta ta shige gidan Mami, Dr Arshan kuma da kallo ya bita yana sakin murmushi mai ƙayatarwa, sai da ya ga shigewanta gida sannan ya shafa gashin kan sa ya juya ya nufi wajan su Abeed yana murmushi shi kaɗai, dan sosai yarinyar ta tafi da imaninsa, tun ranan da ya gan ta a asibiti ta burgesa, amma da yake mara lafiya suka kai shiyasa bai mata magana ba, sai daga baya kuma tunaninta ya addabesa, cikin ikon Allah kuma yau juma’a mai sa’a sai ga shi ya gan ta, ya ga gidansu, godiyansa ga Allah ma da ta ce Abbaanta zai mata faɗa, hakan na nufin bata stayuwa da samari kenan, dole ya gaggauta yin abin da ya kamata, tun kamun ta masa nisa.

Tun da Dr Arshan ya bar wajan su Abeed ya nufi Umaima, sai dariya Abeed yake yi yana faɗin, “Da alama fa wannan likitan ma mayen mata ne irin ka ACM.”

ACM Bunayd, Hararan Abeed yayi tare da jan guntun staki bai ce komai ba, daman suna zaune a cikin motansu ne, dan haka danna wayansa yake yi hankali kwance, shi ko kallon wacce Dr Arshan ya je wajanta bai yi ba.

Dr Arshan na isowa Abeed ya tare sa da dariya ya ce, “likita bokan turai, ku ke ganin mata dole ku maƙale musu, ku ne son mata, jiki duk ehen-ehen, mu dai a bar mu da bindiga kawai”, ya ƙarishe yana dariya.

Dr Arshan zagayawa yayi ɗaya gefen ya zauna a in da ya tashi, ya ce, “Captain ba ka da dama wallahi, ina yarinyar da na baka labarinta mutumiyar ACM, to ranan tare na gan su a aisibiti da wannan, to yanzun ma na tambayeta mutumiyar ACM ne, shi ne take faɗa mini ai yau ma auren ita yarinyar.”

Abeed tsayawa yayi da dariyan kaman wan da aka bawa saƙon mutuwa ya ce, “kashh! Sam-sam abu bai yi daɗi ba gaskiya, ta ya wani zai aure mana future wife namu, ni fa har na bawa ACM yarinyar, dan da alama ita ce dai-dai shi, amma ba komai Allah ba mu wacce ta fi ta, ko kuwa ya sako mana ita mu aura da ba ruwanmu da virginitynta.”

Dr Arshan murmushi yayi ya ce, “Gaskiya na taya Angonta murna, ACM kuma ina masa jaje dan yayi rashi, yarinyar ƙarshe ce, duk da bata kai wannan kyau ba, kuma dai gaskiyan ACM dan virginity ba wani big deal bane idan da soyayya, daman abin da ya sa aka fi son auren virgin ɗin dan dai kada ta saba da size na wani, ka aureta kuma ka fi wan da ta fara sani big size ka zo ka fi ƙarfinta, bata jurewa buƙatunka, ko kuma wancan ya fi ka big size ta zo sam-sam ba ka isar mata da abin in da take so hole ɗin ya fi size naka, shi ne kawai mastalan auren wacce ba kai ka fara amfani da ita ba, kasan normally mata yawancinsu wan da ya fara amfani da su, suka saba da shi to yan da yake haka za su kasance.”

Dariya Abeed ya saka ya ce, “ai dama son kai shi ne asalin so, kana ƙaunarta dole ka ce ta fi kowa kyau, kaman yacce nima nake ganin babyloff ta fi kowa haɗuwa, wato ku likitoci fa kun san kan Palace da Dragon yan da ya kamata, .”

Dr Arshan girgiza kai kawai yayi yana dariyan maganan Abeed, ya ce, “fatan za ku zo auren ma?”

“Daga ganin Sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi, har ka lissafo aure kenan, kai ma a hannu kake kaman oh’o”, ya faɗa yana kallon ACM Bunayd.

Dr Arshan dariya yayi, suka ci-gaba da hiransu da Abeed, Bunayd dai a zahiri hankalinsa na kan waya ko ƙala bai ce musu ba, amma fa a zuciyansa haushi ya ji na wai wancan idiot ɗin ta yi aure, bai rama kallonsa da ta yi ba, ta ci banza kenan, ƙwafa yayi a zuciyansa ya ci-gaba da lasta wayansa yana sauraran hiran su Abeed.

Nabeel da Suhail duk abin da ake suna nan suna gefe abin su, kowa na danna wayansa, su damuwansu su kalli matar Papi amma sun san ba dama, yan da ake da jama’a sosai ɗin nan.

Umaima kuwa tana komawa ciki ta wuce wajan Banafsha, tana zuwa na miƙe daga kwancen na ce, “Umaimaty kin ga su Malamina ɗin?”

Hararana Umaima tayi ta ce, “masoyiya ni ba wan da na gani, angwayen nan wulaƙanci suke ji, amma za mu rama ne, Allah kai mu anjima.”

Ajiyan zuciya na sauƙe tare da komar da kai na, na kwanta na ce, “Malamina kwata-kwata har yanzu bai ƙira ni ba, Allah sa lafiya, zuciyata sai stinkewa take.”

Umaima minstinina tayi ta ce, “mayyar miji tun ba’a fara abun ba, iyye Malam Abbo ya ga ta kansa, mutanen tahfiz kuma sai haƙuri dan ya auri mayya.”

Guntun tsaki na ja na ce, “Gaskiya Umaima kina da mastala d fassara mutum, ni da mijina ba zan damu da halin da yake ciki ba sai dan wani abu.”

Umaima taɓe baki tayi ta ce, “oho dai, idan ma kika yi haƙuri daga nan zuwa yamma za mu kai ki, kuma ko zuwa dare zai iya miki abin.”

Cikin taƙaicin maganan Umaima na miƙe tare da mata dundu na ce, “Wallahi za ki ji da shi Umaima, ke kin fiye son maganan banza, ni ki ƙyaleni, dama haushinki nake ji kin minstina wa Malamina jikin matarsa.”

Dariya Umaima ta saka ta ce, “Masoyiya su miji man zakara, inyee su an yi miji manya.”

“Eh ɗin, kuma saura na gan ki a gidana, idan kin ji haushi ke ma ki turo mayenki da kike wulaƙantawa a yi auren ki yi miji”, na faɗa ina hararanta.

Umaima na dariya ta ce, “Yauwa kin tuno mini, likitan da ya duba Mami lokacin ya ce na gaisheki, Allah ba da zaman lafiya da ciki da goyo sai kin je awo.”

Dundu na ƙara kai mata ta kauce, na ce, “ina amsawa, ke kuwa ina kika gan sa?”

“Wallahi yanzu a ƙofan gida da na je duba su Rilwan, ko ni nayi mamaki….”, ta labartawa Banafsha yan da suka yi da Dr Arshan duka.

Tun da aka ɗaura auren sai yanzu na ji dariya, murmushi nayi na ce, “inyee kina ji ya ce miki shi mijin mace ɗaya ne, matarsa ta ishe sa sannan ki dage za ki lalatawa baiwar Allah miji za ki mata snatching, wayyo Allah shiga tsakaninmu da ƴanmata irinku.”

Dariya Umaima tayo ta ce, “su Masoyiya tun ba’a san daɗin mijin ba har an fara neman stari da kishiya, to Allah ya taro ki, fatan alkairi ake yi atou, kuma dai idan ya ce yana ciki tuni na ba da kai bori ya hau, ɗan kyakkyawan likita da shi ɗan gayu, ah ni ya mini ma Allah kawo sa lafiya, tuni za ki ji labarin aurenmu, idan kika yi wasa ma sai na rigaki santalo baby, ba ruwana da matarsa.”

Hararan Umaima nayi kawai na ce, “za ki ji da shi ai, ni mijinane damuwata yan zu.”

Hira muka din ga yi da Umaima cikin raha, har ta sa na mance damuwa da stinkewan zuciyan da ke damuna.

Abbaa da su Alhaji kuwa tun lokacin fitowan Umaima, Abbaa ya musu iso zuwa palournsa, duk zama suka yi Abbaa ya shiga cikin gidan ya sa aka kawo abin mosta baki, duk saka zauna suna taɓawa suna hira, duk da gefen Alhaji a ƙage ya ke ya ga Ramlatunsa, abin da ya hana sa ƙiranta kuma maganan Banafsha ne, dan ya rasa ta ina ma zai ɓullo mata.

General Sufyan ne ya ce, “Yaya kai da Alhaji Aliyu kam menene ya faru, tun ɗazu kaman akwai mastala, amma ba ku sanar mana ba dan asan ko akwai abin da za’a yi.”

Alhaji Mukhtar cikin damuwa ya ce, “General wallahi wani ɗan aka si aka samu ne, ba daman na faɗa muku auren guda biyu za’a ɗaura ba, namu da kuma na yarinyar mu, to kuma mutanen sun ce wai sun fasa, sannan ina da tabbacin ita Hajiyar tawa bata da labari, to bamu san ta ina za mu ɓullo mata ba akan al’amarin.”

General Sufyan da mamaki ya ce, “ai nima da na so nayi magana, amma sai na yi shiru, nasan dai auren biyu ne, amma naga naka kawai aka yi, to wai menene ya sa mutanen suka fasa, kuma su rasa lokacin da za su sanar da fasawan nasu, sai lokacin da ake ƙoƙarin ɗaura aure, dan neman tozarta jama’a.”

Abbaa da yake cike da haushin maganan cewa yayi, “General Sufyan ka bari kawai, ji nake kaman na ga mutanen nan na musu abin da bai kamata ba, dan kawai sun ɗauke mu yara ƙanana, kuma ba su zo da kan su ba, sai wani suk turo wai an fasa, saboda yarinya bata da uba an ɓoye musu, wa ya mutu wa ya dawo, kame-kame kawai, kuma tun farko sai da muka sanar musu ni da Alhaji, cewa mahaifinta ya rasu amma mu ne waliyyanta, kuma yanzu ai tun da Alhaji y auri mahaifiyarta ai mastayin mahaifi yake a gare ta, kai ko bai auri mahaifiyarta ba ya ci wannan matsayin, sannan nima ai idan da kara na isa haka, amma mutanen saboda sun rasa makama wai suna faɗa mana bata da uba ba ta Sunna aka haifeta ba.”

General Sufyan ai take idonsa ya rine ran sa ya ɓaci kaman wan da aka yi wa ƴar cikinsa ce haka, abin ka da Soja, cewa yayi, “amma da kun sanar da ni halin da ake ciki da wuri, ai da sojojinnan sun gyarawa shi ɗan aiken nasu zama, may be daga nan za su gane tana da uba, wasu mutanen dai suna wasa da lamarin aure, amma gaskiya ba su kyauta ba.”

Abbaa ya ce, “Allah shirya kawai ya kyauta, amma sun tozarta mu.”

Alhaji Idris ya ce, “basu kyauta ba sam-sam, amma sai haƙuri kawai, Allah bai nufa ba shiyasa, Allah kuma ya bata wan da ya fi shi, Allah sa hakan ne alkairi a gare su duka.”

Duk suka amsa da Ameen, sai Alhaji Tasi’u baban Abeed ya ce, “Yanzu dai Alhaji Mukhtar tun da mahaifiyarta iyalinka ce, sai ka san yan da ka faɗa mata cikin nistuwa ka kuma bata baki, kada ka nuna mata ɓacin ran ka, za ta damu sosai, ka nuna mata kawai ayi haƙuri Allah ne bai ƙaddara shi mijinta ba ne, Allah kuma ya bata nagari mafi alkairi.”

General Sufyan ya ce, “haka za’a yi yaya, sai ka sanar da ita akan lokaci, yanzu tun da an samu wannan akasin ba zai yiwu ma mu gaisa da ita ba, idan ka sanar mata sai mu wuce kawai, sai an zo ɗaukanta kuma.”

Alhaji Mukhtar ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce shikkenan, ya miƙe ya fice a palourn, wayansa ya ciro tare da dannawa layin Mami ƙira, tana ɗauka ya saita kan da tare faɗin, “rankishidaɗe Amarya a mini izinin shigowa na zo ns ga kwalliyan Amaryata.”

Mami a nata ɓangaren murmushi ta saki, tare da gyara zamanta, cikin soyayya ta ce, “an maka izini Angon Ramla, ina zaman jiran ka a ɗakinka dan daman nawa na bar wa baƙi.”

Alhaji amsawa yayi, suka ɗan soye abin su, sannan ya kashe wayansa ya mai da ajiihu, yayi waje, cikin nistuwa ya shiga gidan Mami, gaisawa yayi da jama’an ciki yana fara’a, har ya samu ya shige ɗakinsa in da Mami take.

Mami daman suna gama magana ta ƙara gyarawa sannan ta kawo abin sha da abinci duka ta ajiye zaman jiran isowan mijin nata.

Da sallama Alhaji ya tura ƙofan ɗakin ya shiga, Mami ta amsa masa tana sakin wani irin stadadden murmushi mai zautar da nistuwan Alhaji Mukhtar.

Ganin murmushin Mami kaɗai ya ƙara masa ƙwarin guiwa, ƙarisowa yayi tare da cire babban rigansa (gare), ya ajiye a gefe, ya ƙarisa waja Mami da tun shigowansa ta yi ƙasa da kai cikin jin kunyan Alhajin nata.

Alhaji zama yayi a gefenta tare da cewa, “Amarya ta.”

Mami na murmushi ta ce, “Naam Angona.”

Alhaji jawo Mami yayi jikinsa ya rungumeta, kusan a tare suka sauƙe ajiyan zuciya, a hankali Alhaji ya ce, “Alhamdulillahi ala kulli halin, haƙuri gishirin rayuwa, kuma ginshiƙin zaman lafiya, sannan daɗin zaman duniya, Ramla na godewa Allah da ya amshi addu’a ta ya mallaka mini ke, dole a ce ko shekaru nawa ka ɗauka kana addu’a, dan abin da kake nema bai samu ba kada ka ce za ka yi fushi, ko kuma ka ce Allah baya son ka bai amshi roƙon ka ba, dan muddin ka roƙi Allah to zai amsa maka kuma zai baka, idan ka ga ya jinkirta to lokacin faruwan abun ne ko samunsa bai yi ba.”

Murmushi Mami tayi tare da kwantar da kan ta a jikin Alhaji, tana jin wani irin nistuwan da bata taɓa jin sa ba duk kusancinta da namiji, a hankali ita mata ce, “sosaima mijin Ramla, haƙuri shi ne komai ma rayuwan duniya wan da zai taimaka maka ka dace a lahira, domin haƙuri na daga cikin halayyan fiyayyen halitta Annabinmu stira da amincin Allah su tabbata a gare shi.”

Dogon numfashi Alhaji ya ja, dan an zo dai-dai in da yake so a zo, a hankali ya ƙira sunan Mami ta amsa, ya ce, “Ramla nasan kinsan haƙuri da fa’idansa, sannan kinsan komai sai Allah ya nufa yake faruwa.”

Jinjina kai Mami tayi ta ce, “sosaima Alhaji.”

Alhaji Mukhtar cikin sigan da ya kamata ya bi ya fahimtar da Mami komai, sannan ya faɗa mata komi yan da aka yi da yan da ya faru.

Mami ba ƙaramin damuwa tayi ba da jin wannan maganan, musamman idan ta tuna yan da Banafsha ta saka abun a ran ta, amma kuma kaman ta Alhaji ne ba mai ja da ƙaddara ko kuwa abin da Allah bai nufa ba, dan haka addu’a kawai suka yi na Allah ya sa hakan shi ne alkairi.

Alhaji ganin Mami dai abin ya dameta, sai ya ƙara rarrashinta, sannan ya faɗa mata ta lallaɓa Banafsha sosai, ta kuma yi haƙuri ta toshe kunne da abin da jama’a za su ce, komai ya zo ƙarshe Insha Allahu, kuma tafiyansu Kano an dawo da shi baya tun da ga abin da ya faru, ranan Lahadi kowa mai kai Amarya ya shirya, masu ɗauka za su zo, kuma Flight xa’a bi, dan tafiyan ba kaɗan ba idan aka ce da mota.

Mami ta dage Alhaji ya bari sai Monday, amma ya ƙi, ƙarshe ma sallama ya mata za su koma da mutanensa, saboda halin da ake ciki ba za su samu gaisawa da ita ba, kawai sai an kawo ta tun da za’a yi wasu hidiman a can.

Alhaji fitowa yayi bayan ya sallami Mami, ya koma gidan Abbaa, sai da suka yi sallah suka ci abinci sannan suka fito dan tafiya, Abbaa ya ce, “wai nikam wannan Yaro mai kama da General ɗin nan yaron ku ne Alhaji?”

Alhaji Idris ne ya riga Alhaji Mukhtar magana, yana dariya ya ce, “Ai ɗan gidan General ne Alhaji Aliyu.”

Murmushi Abbaa yayi ya ce, “Shiyasa suke kama sosai ashe, lokacin da Ramla ba ta da lafiya mun haɗu da shi a asibiti har ma ya biya mana bill na komai.”

General Sufyan murmushi yayi ya ce, “Yarona kenan ɗan albarka mai taimako da tausayi, kaman yasan Amaryan yaya ce.”

Alhaji Mukhtar ma murmusawa yayi ya ce, “Alhaji Aliyu ka ce ɗan gidan General ne yayi wannan aikin ladan, to Allah masa albarka angode, ai Bunayd watarana hankali kaman ka yi sadaka da shii.”

Duk dariya suka saka, suna hiransu har wajan mota Abbaa ya raka su, suka shige duka, sai da ma ya ga tashuwan motansu sannan ya juya cikin gidansa.

Su Abeed ma sun yi sallah, sun ci abinci amma dai ACM Bunayd bai ci komai ba, suna zaune abin su, suna hira jefi-jefi yanzu har da Bunayd ɗin, har su Abbaa suka fito, sai sannan suka yi sallama da Dr Arshan ya kama nasa hanyan, su ma suka shige nasu motan su ma suka yi gaba.

Sojoji sai da suka kuma harba bindiga sannan suka ja motansa a sittin.

Mami tun da Alhaji ya fita ta rasa ta ina za ta fara, dan haka dole ta tashi ta fito dan ta ƙira Banafsha su yi magana.

<< Yar Karuwa 20Yar Karuwa 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×