Skip to content
Part 24 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

General cikin ƙoƙarin danne abin da yake ji ya ce, “Gimbiya Ramlat ki yi haƙuri, ba laifinki sam-sam a cikin abubuwan da suka faru a rayuwarki, gudumawan jama’a ne kawai, amma ki yi haƙuri yan da kika amshi ƙaddaranki tun farko to ki daure kada yanzu a ƙarshe ki kasa.”

Mama Hadiza ma share hawayenta tayi ta ce, “Ramlatu ke ce za’a bai wa haƙuri, domin ke ce kika taka wuta da ƙananun shekarunki, tabbas kin haɗiyi garwashi mai zafi da ƙuna, duk da dai a wani wajan ba ki kyauta ba, amma kuma duba da kina da ƙananun shekaru a lokacin, sannan kuma akwai furucin mahaifinki da ke bin ki, domin ko a wasa ba’a so mutum ya faɗa wa yaransa abin da bai kamata ba, shi bakin iyaye kaman guba yake mai saurin tasiri a rayuwan yaransu, ki yi haƙuri sam-sam ba ki mini laifi ba, kuma ban ji haushinki dan kin ɓoye mini gaskiya ba, ki yi haƙuri ki daina kuka, ke ma Faɗima ki yi haƙuri, komai ya samu bawa muƙaddari ne na rayuwarsa da Allah ya jima da rubutasa a rubuce a littafin ƙaddaransa, ki yi haƙuri Faɗima, domin ko a wajan Allah ba ki da laifi.”

Alhaji Mukhtar numfasawa yayi sannan ya ce, “kukan ya isa haka Faɗima, Ramlatu ki rarrasheta, kina yi tana yi bai kamata ba, yanzu duk ku yi haƙuri, a duniya duk yacce aka kai ga ɓoye abu, ko da rami aka tona aka yi magana, to in Allah ya yarda watarana sai ya fito, balle kuma ace wai ƙulle-ƙulle aka ƙulla aka yi wani al’amari, komai zai warware in Allah ya yarda, a bayan komai da ya faru akwai abin da Allah ke nufi da hakan, inma na wa’azi ga bayinsa ko kuwa dai wani nufin daban, dole akwai abin da Allah yake nufi da wannan al’amari, gare mu a yanzu da muke stakiyanta, da kuma ga ƴan bayanmu da kuma masu kallonmu ko karantar labarin mu, dan su ma ya zama izini gare su, dan kowa ya kiyaye.”

Momsee miƙewa tayi jiki ba ƙwari ta ƙarisa wajan Mami tana bata baki, Mama Hadiza ma ta dawo wajansu tana lallashin Banafsha, da ƙyar kukan Mami ya staya, sai jero ajiyan zuciya take yi, Banafsha kuwa kan kukan take tana sheshsheƙa.

Alhaji Mukhtar ya ce, “Mama Hadiza muna mai ƙara baki haƙuri, sannan kuma kaman yan da na ɗaukar muku alƙawari ke da marigayi Babanmu, to insha’Allah na cika sa dai-dai yan da Allah ya so, domin duk wani mostin Ramlatu ko da bana Mubi, to a kan ido na take yi, na kan ɗaga ƙafa ne kawai wani lokacin saboda kar na takura ta gane, dan na ga ta kusa harbo jirgin, ni nake kore mata mutane kuma ni nake hana su mua’amala da ita da ikon Allah, saboda musamman nake zuwa ƙasa mai starki dan ita, na mata addu’a ita kawai, kuma har ga Allah, jama’a ba za su yarda bane kawai, amma Ramlatu bata yi wani mua’amala da mutane, ta yan da har za’a ƙira sa da karuwanci ba, sai dai kawai abin da ba za’a rasa ba, kuma wannan ba bawan da ya fi ƙarfin ƙaddaran Allah daman, Allah kawai ya yafe mu duka ya kuma amshi tubanmu, Allah datar da mu duniya da lahira, yanzu abin da nake so, duk kowa yayi haƙuri, a huta a sallami ƴan biki, idan Allah ya kai mu wani sati sai mu tattara duka mu je Sokoto ɗin, dan neman gafaransu, da kuma sanin gaskiyan al’amari game da mahaifin Faɗima, dan na tabbata akwai wata a ƙasa, dole akwai masu masaniya akan faruwan hakan.”

Mama Hadiza ta ce, “in Allah ya yarda hakan za’a yi, Allah kuma ya kai mu da rai da lafiya.”

Duk palourn amsawa suka yi da Ameen, sannan General ya ce, “Gimbiya Ramlat ina mai ƙara baki haƙuri, domin nasan da na zo gare ki a lokacin da duk haka bata faru ba, amma alhamdulillah tun da Allah ya dube mu ya tura miki yaya, Allah ya haɗa ku kuma hakan yayi, domin hikimar Ubangiji daman yalwatacce ne, a lokacin ni da Ahmad duka an tura mu wani aiki ne wata ƙasa ta daban, dan sai da muka ɗibe fin shekara a ƙasar, kuma cikin ikon Allah Ahmad ya rasa rayuwansa a wannan yaƙin bayan nasaran da muka yi, kuma ko da na koma ce mini aka yi kawai kin yi cikin da ba’a san ubansa ba, kin kuma tafi, abin dai da aka faɗa mini daban ma da labarin da kika bamu, daga nan kuma da farko na ɗau fushi da ke dan gani nake kin ci amanata kin yaudareni, sai dai hakan bai hanani miki addu’a da fatan alkairi ba, kuma ina mai kyautata zaton ba za ki aikata hakan ba, ganin babu Ahmad kuma ke ma babu ke, shikkenan na ɗauke ƙafa a Sokoto tun da na auro Huraira, ga ta ita ce matata yanzu yaranmu biyar, ta farin kuma mai suna Ramlat ke muka yi wa takwara, domin Huraira tasan labarinki, yaya ma abin da ya sa bai sani ba, kawai ban son na basa labarin ne wani abun ya kunno kuma, shi yasa nayi shiru, domin shi ma lokacin da nake tare da ke ba ya ƙasar bai san alaƙanmu ba, ina mai fatan Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a masu albarka, in Allah ya yarda, kaman yan da yaya ya faɗa, ana sallaman baƙi za mu je Sokoto gaba ɗayanmu, dan daman mu ma mun jima da ɗauke ƙafa a can, tun da Allah ya yiwa mijin gwaggonmu rasuwa, wato mahaifin Huraira, ki yi haƙuri Gimbiya Ramlat, ke ma Faɗima ki yi haƙuri, insha Allah komai ya zo ƙarshe.”

Mami ba abin da take sai jero ajiyan zuciya kaman wacce ta sha gudu, gaba-ɗaya ta rasa me ke mata daɗi, wani irin sabon ciwon abubuwan da suka faru a baya ne ya tasar mata, ba wan da take tunawa a yanzu kaman Ummanta, da tana nan da duk haka bata faru ba, ko da ace duniya za su taru a kan ka, ciki har da mahaifinka da ƴan uwanka, to da tabbas dole mahaifiyar ka ta zama maka abu guda wan da yake tare da kai, majingina kuma madafa gare ka, sosai Mami ke nadamar rayuwan da tayi duk da ta san bawa ba ya wuce ƙaddaransa, ga kuma lamarin Banafsha, waye ya mata wannan cikin? Ta yaya? Ya aka yi duk wannan al’amuran suka faru kaman wani a labari, ba’a zahirin rayuwanta ba, wani irin hawaye mai azaban ɗumi ne ya gangarowa Mami, muryanta na rawa a fili ta furta kalmar, “Astagfirullah.”

Alhaji Mukhtar ne ya ce, “Allah ya yafe mu duka Ramlatu.”

Duk jama’an palourn suka amsa da Ameen, ban da Banafsha da take ta kan kukanta, ji take da ma bata ji wannan labarin ba, lallai dole a ƙira gaibu da rahama, ba iya sanin gaibun ranar mutuwar ka bane masifa, hatta wani al’amari idan ya ɓuya gare ka, to ɓuyan shi ne maslaha kuma kwanciyan hankali a gare ka, sanin wani al’amarin babbar mastalan ce, domin a yanzu ji take gwanda ya cigaba da amsa sunan ƴar karuwa, akan wannan rikicaccen al’amari na wai ba’a san waye ubanta ba.

Momsee ce ta miƙe tare da riƙo Banafsha, ita kuma bin Momsee tayi tiryan-tiryan tana kukanta, har suka fice a palourn Papi, Momsee bata kai ta sashin Mami ba, kawai ta ja hannunta suka fice a part ɗin, suka shige part na su General, har ɗakinta ta kai Banafsha sannan ta ajiyeta a bakin gado ta shige banɗaki, ruwan wanka ta haɗa mata mai ɗumi sannan ta fito ta umurce ta, da ta shiga tayi wanka tayi alwala.

Banafsha miƙewa tayi babu musu, tana kan kukanta ta shige banɗakin, wanka tayi ta yi alwala ta fito, samun Momsee tayi zaune tana jiran fitowanta, tana fitowan kuma ta miƙa mata dogon riga mara nauyi wan da za ka iya bacci da shi, Banafsha ta saka ta kuma amshi hijabin da Momsee ke bata, kan sallayan da ta shimfiɗa mata ta hau, sannan Momsee ta ce, “Faɗimatu kiyi nafila ko raka’a biyu ne, insha’Allah za ki ji nistuwa da sanyi a ran ki, muddin kika fawwala wa Allah al’amuranki, idan kika idar ki kwanta ki yi bacci, ki yi haƙuri, Allah na tare da mai haƙuri, kuma Allah na son mai haƙuri, sannan yana sakawa sakamako mai gwaɓi ga mai haƙuri “, Momsee na gama faɗan haka ya mata sai da safe ta fice, cikin tsananin tausayin Banafsha.

Momsee na fita, Banafsha ta yi ƙoƙarin rage sautin kukanta, ta fara sallah, sai da tayi raka’a kusan goma, sannan ta kai goshinta ƙasa, tana kuka tana addu’a, ta ɗau lokaci mai ɗan stawo, sannan ta ɗago ta shafa addu’an, ko cire hijabin bata yi ba ta kwanta a nan baccin wahala yayi gaba da ita, sai sheshsheƙa take yi.

Duka palourn ba wan da ya ce wa Momsee komai har suka fice da Banafsha, sannan General ya miƙe tare da cewa, “Gimbiya Ramlat ki yi haƙuri”, General iya abin da ya faɗa kenan ya fice, ji yake shi ɗin ma kaman ya rushe da kuka ko zai ji sanyi a zuciyarsa, macen da ya fara so a rayuwarsa, sai ga shi ƙaddara ta raba su, kuma ta haɗa ta da yayansa, wan da yanzu haka take a mastayin matar sa, ba’a mastawa da lamarin Ubangiji, watakila ma duk abin nan da ya faru saboda babu rabon aure tsakaninsa da Gimbiya Ramlat ne, shi daman rabo babu abin da baya yi, ya kashe mutum, ya kashe aure, ko kuwa ya haddasa wata fitinan, to Allah rufa asiri ya ba su zaman lafiya da yaya, Allah kuma ya basu zuri’a ɗayyaba, dole ya yakice Gimbiya Ramlat duka a zuciyarsa, domin ya jima da haƙura da ita ma.

Mama Hadiza numfasawa tayi sannan ta ce, “Ramlatu ina mai ƙara baki haƙuri, ki godewa Allah da ya nufe ki da nadama kamun mutuwanki, sannan ki yi addu’an Allah warware duk wani lamari da ya ƙulle kai, ita al’amarin duniya daman duk a stakanin jarabawa da ƙaddara ake, ke wannan ce taki, Allah kuma ya baki ikon ƙarisa cinye wa yan da kika fara, saboda daman sai aski ya zo gaban goshi yake zafi sosai, to Allah ya rufa asiri, haƙuri shi ne komai na rayuwa, kai ma Mukhtar Allahu ya maka albarka, Allah raya maka zuri’a, Allah sa ka gama da duniya lafiya irin wannan guddumawa da ka bada a rayuwan Ramlatu, duk ku yi haƙuri mu kwana lafiya”, tana gama faɗa ita ma ta miƙe ta fice a palourn, ta koma sashin Mami, tarar wa tayi su Umaima su aunty A’isha duk sun yi bacci, har Ummu ma, dan haka ita ma alwalanta tayi da nafila raka’a biyu, ta yi addu’oenta sannan ta kwanta cike da tausayin Ramlatu da Faɗima, da kuma jimamin hali irin na wasu iyayen da zafin zuciya, da a ce ita ce asalin mahaifiyar Ramlatu to da tabbas, sai ta tabbatar da ta nunawa Sarki kuskurensa, amma duk da ba ita ɗin ba ce, hakan ma ba zai hana ta faɗa masa gaskiya ba, domin shi haihuwa ka zama uba ai ba hauka bane, haka Mama Hadiza ta ƙarishe ƙwafanta, da zancen zuci har bacci yayi gaba da ita.

General yana komawa sashinsu, ya wuce direct ɗakinsa, samun Momsee yayi ta fito toilet kenan, murmushi ta sakar masa, amma gyaɗa kai kawai yayi.

Momsee ta masto ta taya sa rage kayan jikinsa, suka shiga bayin tare ta taya shi wasta ruwa, yayi alwala ya fito, sannan suka yi sallahn tare, addu’oe sosai-sosai General yayi, kamun nan suka kwanta.

General sai juyi yake ya kasa bacci, Momsee ma da yake idanuwanta biyu bata yi baccin ba, a hankali ta ce, “Dear Ka yi haƙuri.”

Ajiyan zuciya General ya sauƙe, sannan a hankali ya ce, “bakomai Dear, kawai maganan mahaifin yarinyar nan ne ya dame ni ya ɗaure mini kai, wannan wani irin ciki ne kaman na aljanu, abu kaman ba ƙalau ba, a kan wannan mastalan ne fa aka fasa auren yarinyar, kar kiji abin haushi, to Yanzu kuma ga magana ya fito haka ne, gaskiya ina tausayin yarinyar nan, ƙarama da ita ta tana fama da wannan damuwa, daga kukan da take yi ka kinsan abun na cin zuciyanta sosai, wa kuma yasan rayuwan da ta yi a baya kamun yanzu, gaskiya tana cikin jarabawa, a ce mata ƴar karuwa sannan a fasa aurenta, ga kuma batun ba ta da uba, Allah bata haƙuri ya warware mata wannan mastaloli, Allah ya bata miji nagari, Allah kuma ya bayyana mahaifinta.”

Momsee ma cikin jimami ta ce, “Ameen ya Hayyu ya Qayyum Dear, ni ina ga ma idan yayi mu tafi da ita Lagos kawai, tayi karatun ta a can, idan Allah ya bata miji nagari ita ma tayi aurenta, daman Allah yayi wancan ba rabon ta ba ne.”

“Yanzu dai sai mun je Sokoto kuma mun dawo, Allah dai ya sa mu ji alkairi.”

“Ameen”, faɗin momsee da ta shige jikin mijinta, ba jiwa bacci yayi gaba da ita, General kam sai da aka ɗau ɗan lokaci kamun baccin yayi nasaran ɗaukansa.

Mama Hadiza na fita, Mami ta buɗe sabon babin kukanta, yi take kaman za ta shiɗe, Alhaji cikin damuwa ya tashi ya ƙarasa kujeran da take zauna, zama yayi sannan ya jawota jikinsa, ya shigar da ita kirjinsa yana bubbuga bayanta alaman rarrashi, ita kuwa Mami cikin kuka take faɗin, “nayi nadama, nayi nadama, na yi nadaman rayuwan da nayi, nasan na so kai na kuma nayi son zuciya, nayi nadama Alhaji.”

Cikin stigan rarrashi Alhaji Mukhtar ya ce, “Ya isa haka Ramlatu, ki daina kukan kada kuma ya koma miki ciwo, komai ai da ya faru ya riga da ya faru, kuma ya riga da ya wuce sai dai mu ce Allah ya kiyaye na gaba.”

“Alhaji duk rayuwan da nake yi ban taɓa hango ranar nadama na zuwa mini a haka ba, yanzu me zan ce wa Banafsha? Na cuceta na kawo ta duniya ba ta hanyar da ta dace ba, kuma nima da kai na bansan waye mahaifinta ba, Faɗima tana ganin jarabawa a rayuwanta, daga wannan sai wannan, da ace ita ma mai budurwan zuciya ce irin nawa, wa ya san irin rayuwan da za ta yi? Gaskiya na cuci kai na, kuma ban kyauta wa yarinyata ba.”

Murmushin su na manya Alhaji Mukhtar yayi ya ce, “Alhamdulillah! Abin da ke ƙara mini soyayyanki a ko wani irin hali na same ki kenan, ko da kina yin ba dai-dai ba, to wani ɓangaren babu ya ke, kuma daman ko wanni ɗan adam haka yake, wani wajan perfect wani wajan kuma not perfect, to alhamdulillah, tun da har kika yi nadama da wuri haka a kan lokaci to Allah ya amsa tuban da kuma nadaman, daman abin da Allah baya so kawai bawa yayi laifi ya tuba, sannan ya kuma yi ya tuba, a haka har mutuwa ta riske sa, watakila ma ya mutu akan aikata laifin, amma muddin za ka yi nadama ka tuba, tare da starkake tubanka, to Allah na tare da kai, dan a wajan Allah ka fi wan da kwata-kwata bai yi laifin ba balle ya ɗaga hannu ya tuba, Allah mai afuwa ne, yana son mai roƙon afuwansa, Allah ya mana afuwa duka, ka zauna baka taɓa neman afuwan Allah ba dan baka laifi, to Allah baya son haka don kaman ka rena buwayar sa ne, Allah yana son masu roƙon sa, shiyasa hadisi guda na Annabi SAW, ya ce Allah na fushi da duk wani wan da yayi Sallah ya tashi ba tare da ya roƙesa komai ba, lamarin mahaifin Banafsha kuma ni ina ji a jikina, Insha Allahu muna zuwa Sokoto to magana ta ƙare.”

Mami na sheshsheƙa ta ce, “Allah ya sa Alhaji, nagode sosai Allah ya saka maka da alkairi, madalla da miji nagari irinka.”

Murmushi kawai Alhaji yayi ya cigaba da rarrashin Ramlatunsa, cikin sigan soyayya da ƙauna, tuni ya sa Mami ta ji dama-dama a zuciyarta, har suka yi alwala suka yi nafila tare da koro addu’oe, suna idarwa Alhaji ya fice da kan sa ya kawo musu abin sawa a hanjinsu, suka taɓa, Mami haka kawai sai kunyan Alhaji take ji yau, tana noƙewa yana bata har suka ƙoshi duka, ya tattare wajan ya dawo, yana bin Mami da wani irin kallon soyayya ya ce, “amarya a zo a taya ango wasta ruwa.”

Ɗan sansanyar murmushi Mami ta saki, wan da ya ƙara mata kyau, bata ce komai ba, duk yin Alhaji sai da ya haƙura ya shiga wankansa, yana ƙunshe dariyansa shi kaɗai, mamakin yan da Ramlatunsa ta sauya lokaci guda yake, abin da a da ita ke bin sa za ta masa sunan wanka, ko wani abun amma ya waske, sai yanzu da suka yi aure wai tana kunya, murmushi kawai yayi dan yasan na ɗan lokaci ne komai na setuwa, Ramlatunsa za ta kula da shi sosai ba sai ya tambaya ba.

Alhaji wankansa yayi ya fito, yana fitowa Mami ta shige ita ma ta wasta ruwan, rigan wanka na Alhaji ta saka kuma ya mata kyau sosai, da shi ta kwanta, bayan ta ɗan yi feshe-feshenta, Alhaji ma sai da ya gama shiryawa sannan ya haye gadon ya same ta, jawo ta jikinsa kawai yayi, tare da sakar mata kiss a goshi ya ce, “a huta gajiyan kuka ko Ramlatun Mukhtar.”

Murmushi Mami tayi cikin samun nistuwa da kwanciyan hankali, na ba abinda Alhaji ya nema, haka suka yi baccinsu hankali kwance, duk da kowa dai a gefen zuciyarsa da abin da yake saƙa wa, sai dai fatan alkairi kawai.

ACM Bunayd yana isa Lagos bai staya a gidansa ba ma ya wuce base nasu na air force, yana zuwa angama shirya komai daman, kawai sharp-sharp yayi nasa shirin, su da bata liyansu suka haye jirgi suka wuce aikin da za su je yi a ƙasar Philippines.

Washe-gari da ya ke ba abin da za’a yi, an riga an gama hidindimun bikin, Alhaji zuwa yayi sashin Mami suka gaisa da su Ummu, da aunty A’isha, sannan ya musu godiya sosai, sai kuma maganan komawansu, idan sun shirya sai su yi magana, dan a samu ayi booking na jirgi, amma Mama Hadiza za ta zauna da su tukunna.

Su Ummu sun amsa da ba mastala, daga nan zuwa azahar za su gama shiri, dan haka Alhaji ya sanar da General akan ya ƙira ACM ya faɗa masa, a shiryawa masu komawan abin da ya kamata, ashe ACM baya nan sai lokacin su Alhaji suke sanin baya nan, fatan alkairi da dawowa lafiya suka masa, General yayi duk abin da ya kamata.

Su Majeeder sai tashuwa suka yi da safe suka ga Banafsha a sashin Momsee, ai farinciki kaman su mai da ta ciki, amma Banafsha sam-sam bata yanayi, yanzu ma za ta karya ne dan girman General da take gani, da kuma Momsee da ba za ta iya mata musu ba.

Suna gama karyawa Momsee ta bata magani ta sha, ta kuma yin wanka, ta kawo mata kaya mai kyau sabo cikin wanda ta ɗinka wa su Majeeder, lace ne ɗinkin riga da skirt, sosai ya zauna ɗamas a jikinta kaman daman dan ita aka ɗinka, sosai ta yi kyau, duk da zuru-zuru da idanuwanta suka yi na kukan da ta sha jiya, za ta kwanta sai Momsee ta hana ta, wai idan ta zauna ita ɗaya damuwa zai dameta ta fito su yi hira da su Majeeder, sannan Momsee ta ce, “Ina wayanki Banafsha?”

Cikin sanyin murya Banafsha ta ce, “Ban da waya aunty.”

“Momsee za ki ƙira ni ba aunty ba kinji?”

Gyaɗa kai Banafsha tayi, sannan Momsee ta ce, “yauwa ƴar albarka, wayan naki ɓacuwa yayi ne?”

Banafsha ta kuma girgiza kai alaman a’a, bata da wayan ne duka-duka, Momsee ta jinjina kai sannan ta miƙa mata nata, ta ce, “To ga nawa ko za ki yi game ko, yanzu sai ki je cikin ƴan uwanki.”

“To Momsee na gode.”

Hannunta Momsee ta riƙo suka fito, a palourn ta zaunar da ita wajan su Majeeder ta ce musu, “Ga Banafshan taku ku yi hira, amma kada ku sa mata ciwon kai kuma”, ta faɗa tare da juyawa ta fice ta nufi part Papi, har ɓangaren Mami ta je, ta gaishe da su Mama Hadiza duka da su Ummu, sannan da Umaima ta gaisheta ta ce, “Umaima ƙawarki na can wajanmu, ki je kuyi hira duka da su Majeeder ko.”

Umaima da daman kaman jiran ƙiris take yi, tuni ta miƙe ta fice, da yake ta gane part na Momsee, can ta nufa, tana shiga palourn kuwa ta hangi Banafsha da su Majeeder suna ta mata hira, amma ita kuma yanayinta kaman na mara lafiya, ƙarisawa tayi ciki, duk suka amsa sallamanta, Ramlat ta ce, “yauwa gwanda da kika zo sis Umaima, ga Banafsha nan gaba ɗaya kaman ba ta da lafiya, mun tambaya ta ce ba komai, taya mu tambayanta ko ke za ta faɗa miki.”

Murmushi kawai Umaima tayi tare da samun waje ta zauna, tana tambayan Banafsha ko lafiya, amma ita ɗin ma ce mata tayi ba komai, haka dai suka din ga hiran a daddafe, Banafsha da nata damuwan a ran ta, Umaima ma da nata damuwan na rabuwa da Banafsha, wan da Banafsha ma bata san da komawansu yau ba.

Zuwa azahar duk sun gama shiryawa, Ummu, aunty A’isha da ƴar ta, Nana bealkysou, Umaima da ta samu ta jawo Banafsha suka shigo sashin Mami, sai lokacin Banafsha ta gan su duk kowa ya shirya, Ummu ta ce, “yauwa Umaima daman kiranki zan aika ayi, ki zo ki shirya ke muke jira mu wuce, jirgi ba mota bane lokaci nayi ba ruwansa da jira.”

Banafsha da idanuwanta har sun gama cika da ƙwalla, a hankali ta ce, “Ummu ni da Umaima za mu zauna faaa.”

Mami ma cikin tausayin yaran nata biyu da suka taso tare ta ce, “Ummu a bar mana Umaima ba yanzu ba.”

Murmushi kawai Ummu tayi ta ce, “Mamin yara kenan, ke ma biye wa shirmen nasu za ki yi kenan? Ai muddin ana raye to duk kusanci sai an rabu, ga aure ga sanadin barin gari, sannan ga babban rabuwa ma ta dole mutuwa, su yi haƙuri kawai.”

Mama Hadiza ta ce, “Faɗima da Ummul-khultum ku yi haƙuri ko, ke khultum je ki shirya kada ki ɓata muku lokaci.”

Umaima na hawaye ta shige ɗaki, a haka tayi wanka tana kuka, shiryawa tayi sama-sama ta fito, sannan duk suka fito a sashin Mami suka yi waje, a compound na gidan suka staya driver na saka kayakinsu a boot na mota.

Banafsha kan ka ce me fiskanta ya jiƙe sharkaf da hawaye, Umaima na yi ita ma tana yi, sun rungume junansu ƙam-ƙam, Mami saboda tausayinsu har da hawaye ta yi, kowa da ke wajan sai da suka basa tausayi, musamman idan ka ji irin shaƙuwan da suka yi da junansu.

Alhaji Mukhtar da General Sufyan, shigowansu kenan suka tarar da abin da ke faruwa, da yake Alhaji ma yasan ƙawancen nasu, cikin tausayinsu ya ƙarisa wajan su ya fara rarrashinsu yana faɗin, “Ku yi haƙuri ba raba ku aka yi ba, Faɗima za ta dawo gidanku ku ƙarisa College ɗin ko, sannan idan kuka gama ke kuma za ki biyota ku dawo nan mu zauna, zan faɗa wa Abbaanku, ku yi haƙuri kun ji.”

Banafsha na kuka ta ce, “Ni dai zan bi su.”

Alhaji Mukhtar yayi-yayi amma suna manne da juna, sai da General ya masto cikin dabara ya lallashe su ya raba hannayen nasu ya ce, “Kada ku damu yan da yaya ya faɗa haka za’a yi, kuma har miji ma guda za mu aura muku, ku yi haƙuri ko.”

Sai da Mami ta riƙe Banafsha, Ummu kuma ta ɓata rai ta tusa ƙeyan Umaima cikin mota sannan fa aka samu salama.

Ummu sallama suka yi da kowa duka, tare da godiya ga Alhaji Mukhtar da ishirin na arziƙi da ya cika su da shi, sannan suka shige mota, Ummu ta juya kuma me za ta gani? Ga Nana ma na yin nata kukan kaman an mata mutuwa, ai sai abin ya bata dariya, ita ma sai da aka mata jan ido ta shiga mota, Suhail da ke staye a gefe sai dariya yake yi wa Nana yana nunata, shi yarinyar haka kawai take basa dariya, tun zuwansu ɗaurin auren Papi ya kalleta, sai kuma ya ga an zo Kanon da ita, daman tun zuwansu yake rigima da ita, kukan nata na yanzu ma shi ya ƙara wa wutan fetur domin hankalinsa kwance yake mata dariya da gwalo, kuma yana mata video, ga ta yarinya amma sai stiwa.

Driver ya ja su Ummu sai airport, ba jimawa jirginsu ya ɗaga sai Adamawa, har suka isa Umaima na sheshsheƙan kuka, ta yi barci a jirgin amma bata bar sheshsheƙan kukan ba, suna isa jimeta nan ma suka samu motoci biyu sun zo ɗaukansu, aunty A’isha da yarinyarta suka shiga ɗaya ya wuce da su gidan mijinta da ke Dougirei, ɗaya kuma Ummu da yaranta suka shige aka yi Mubi da su, Umaima har ciwon kai ya kamata amma bata bar kukan ba.

Dr Arshan daman da sassafe ya shirya ya koma Mubi, tun da yasan ranan za’a waste, to za su haɗu da mutumiyar tasa a can insha Allah, dole ma ya hanzarta kai kan sa da ƙoƙon baransa, kaman yan da fan’s ƴar karuwa suka ba sa shawara, kada wani ya masa shigar sauri.

Mami jan Banafsha tayi suka wuce sashinta da Mama Hadiza, tare suka je suka din ga bata baki, lallashi da ƙyar ta yi shiru, saboda kukan da tayi jiya da yau, ga damuwan da ta saka a ran ta har da ɗan zabgewa tayi.

Suhail kuwa duk abin da aka yi sai da yayi video recording a wayansa, idan ya ga na Nana ya ta dariya, na su Banafsha kuma mamaki yake basa yan da suke kuka haka, kaman wasu tare aka haifo su, ai ko ƴan biyu ana raba su, kowa yayi aurensa, balle su kowa da iyayensa, taɓe baki kawai yayi ya ce, “ina ma ace ACM na nan da ya haɗa musu da bulala, da sun shiga hankalinsu.”

Nabeel da ke gefe ya ce, “Bro kai da waye kuma kake ta mita?”

Suhail ya ce, “Da masu draman kukan nan mana, rashin duka ke damun su.”

Nabeel yayi dariya ya ce, “Da kai ma ka je soja ai da abin ya fi haka kuma.”

Suhail ya ce, “ka tuna mini ma, tun da an gama shagalin biki mu tattara mu koma in da muka fi wayo, ACM ma ɗan amarya ya wuce aikinsa balle mu, back to school kawai.”

Abeed sai da suka kwana biyu sannan ya kawo nusaiba ta gaishe da Mami, sosai Mami ta ji daɗi ta kuma bai wa nusaiba kyautan turarukan gyaran jiki da sauransu, suka mata sallama suka koma, a ranan Abeed ya musu komai suka juyo Adamawa.

Suhail da Nabeel sun tattara sun koma abin su, kowa ya kama gabansa ya wuce ƙasar da yake karatu, su Suhaila ma ana school dan haka momsee ta saka su a gaba, suka koma Lagos ɗin, aka bar Majeeder da Banafsha kawai, sai su General.

Mama Hadiza suna tare da Banafsha da Majeeder a sashin ƙasa, Mami kuwa tana sashinta, amma duk da haka har yanzu ba abin da ya shiga stakaninta da Alhaji na mu’amalan aure, suna dai zaune.

ACM Bunayd ba su cika sati ba a Philippines suka yi nasaran aikin da suka je yi, daman sun je kai musu ɗauki ne akan wani mastalan da ke stakaninsu da wata ƙasar, sun ɗauka ma za su kai irin wata guda hakan nan, amma cikin ikon Allah ko sati basu cika ba, dan haka suka juyo cikin ɗimbin nasara, yana sauƙa a gidansa ya shirya ya wuce gidan General, Momsee kawai ya samu da ƙannensa, sun baro General a can Kano, dan haka ya shirya zai je Kanon, Momsee ta ce masa za ta saka masa kuɗi a account nasa, ya sayi waya babba mai kyau ya kai wa Faɗima, duk da bai gane wacece Faɗiman ba amma ya ce ta bari zai saya ya kai, dan kwata-kwata bai kawo cewa Banafsha ba ce, da yake shi ba wani sanin sunanta yayi ba.

Shiryawa yayi ya taho Kano, amma sai da ya bi ya saya waya haɗaɗɗe babba mai kuɗin gaske, sannan ya wuce gidan Papi, yana zuwa ya sauƙa a sashin General tun da ya san yana nan, kuma ba kowa a sashin sai shi kaɗai tun da su Momsee sun koma, wanka yayi ya kwanta baccin huta gajiya, sai da ya tashi sannan ya ƙira Abeed suka yi magana, ya faɗa masa ya koma ai tun kwana uku da suka wuce, ya kira layinsa bai shiga ba, nan ACM ya faɗa masa abin da ya faru da ƙiran gaggawa da aka masa tun ranan family and friends, suna gama magana ya miƙe ya fito, a palourn ya samu General zaune tare da Papi, da mamaki suke kallonsa yaushe a gari, shafa kiston kan sa yayi kawai ya zauna ya gaida su, General ya ce, “Masha Allah! Zuwanka ya fi zuwan governor My Man, daman yan zu lissafi muke na da kana nan da ka kai ƙanwarka Abuja, za su yi musabaƙan jiha da jiha, kuma bai kamata ace ta tafi ita kaɗai ba, ko driver ma bai yi ba duniyan nan ba abin yarda ba ce, amma tun da ga ka cikin ikon Allah to alhamdulillah sai ka kai ta.”

ACM da duk zatonsa Majeeder ake nufi, ba tare da ya musa ba ya ce, “Yaushe ne tafiyan?”

Alhaji Mukhtar ya ce, “gobe litinin da yardan Allah, idan ka kai ta ma za ka iya barinta cikin ƴan uwanta ɗalibai ka dawo idan kana wani abun, idan kuma ba ka komai sai ka staya har su kammala ku dawo, dan ina ga abin zai iya ɗaukan sati ko fin sati ma kamun a gama, ga shi idan kun dawo muna son tafiya Sokoto.”

ACM murmushi yayi ya ce, “To ba mastala, Allah kai mu goben, sai a faɗa mata ta shirya akan lokaci, ina tunanin wannan satin ba wani abun da zan yi, dan haka zan jira ta har su kammala mu dawo tare da ita.”

“Yauwa my Man Allah ya maka albarka “, faɗin General shi ma yana murmushi, cikin ƙaunar yaron nasa.

Nan suka ɗan taɓa hira da iyayensa, ya basu labarin yan da suka yi a aikin da ya je, duk sai addu’an kariya da ƙarin nasarori suke masa.

ACM Bunayd ya ce, “Nikam ya labarin Mom ne Papi?”

Alhaji Mukhtar ai a take ran sa ya ɓaci, shi Allah ya gani, ba wai dan yayi wani aure ba ne, amma gaskiya ya gaji da halayyan Sa’adatu, idan zaman auren ya ishe ta ai gwanda ta sanar da shi, ya sauwaƙe mata kowa ma ya huta, mutum yau a ce sati guda curr ba ya gida, ba ƙira ba komai, kuma wai da aure a kan sa.

General ne ya sauƙe ajiyan zuciya ya ce, “ACM Mom taku kam babu labarinta har yanzu haka da muke magana, yaya ka yi haƙuri dan Allah, ka ta addu’a Allah shiryata ya ganar da ita gaskiya.”

Alhaji Mukhtar ƙwafa kawai yayi bai ce komai ba, ACM ma cikin ganin ƙoƙarin Papi ya ce, “ka yi haƙuri sir, ba dan tafiya abujan nan ba da zan binciko ta, amma Allah ya sa ta dawo ma kamun mu dawo.”

General ya ce, “Ameen.”

Alhaji Mukhtar ya ce, “ai ko babu zuwa Abuja ban amince ka nemo ta ba da girmanta da hankalinta, ka ƙyaleta idan ta gama za ta dawo, yanzu dai ka je ka huta, idan Allah ya kai mu goben ku tafi da wuri, dan yanzu zuwanku Abuja shi ne abu mai muhimmanci a wajenmu duka.”

ACM gyaɗa kai kawai yayi ya miƙe ya fice a palourn, part na Papi ya shiga ya wuce sashin Mami dan ya gaisar da ita, bai samu kowa a palourn ƙasa ba, haka ma na sama, sallama yayi a ƙofan sashin Mami, daga ciki ta amsa masa ta masa iso, ya tura ƙofan ya shiga da sallama, ya samu waje ya zauna.

Mami na kallonsa ta saki murmushi, fiskanta ya yalwata da fara’a, dan tana kallonsa ta gane sa, musamman kaman da yake yi da General kaman shi ne ɗan cikin General ɗin ba sauran ba..

⭐⭐

Mutanen Mubi suna komawa Umaima ta fara ciwo, sai da Abbaa ya tsawatar mata sannan ta sararawa kan ta, a gida aka mata treatment har ta ji sauƙi, sai da suka kwana biyu sannan ta koma tahfiz, cikin kewan Banafsha take tafiya ta dawo, yanzu dai tare da Nana suke zuwa su dawo.

Umaima abin da ke bata mamaki ko alaman Malam abbo babu a tahfiz, addu’an Allah ya kyauta kawai tayi, suka ci-gaba da shirye-shiryen tafiya Abuja yin musabaƙa ranan litinin.

Ya Danish har yau bai zo Mubi ba, ya kunna wayansa amma ba ya ɗaukan ƙiran kowa, dan haka har yanzu bai san an fasa auren Banafsha ba, balle yasan ta koma Kano da zama.

Ɓangaren Malam Abbo sai da ya kwashe sati guda curr, bai leƙo gida ba kuma bai bari an san in da yake ba, tun abin ba ya damun Ummi har ya fara damunta, Abiy yasan dole Aliyu ɓoye kan sa yayi, dan haka addu’an alkairi kawai yake bin sa da shi, amma fa shi ma rashin ganin yaron nasa na damunsa.

Yayyun Malam Abbo maza da matan su ma abun ya dame su, musamman yayyunsu mata da suka taimaka wajan faruwan al’amarin tuni suka fara nadama, ji suke dama sun bari anyi auren a haka kawai, su kuwa mazan daman nasu ido ne, ko da aka janye batun auren, sun ba da haƙuri amma Ummi ta nuna ba ruwansu su cire bakinsu, yaronta ne, dan haka kallo kawai suke, suna addu’an Allah ya sa duk in da ƙaninsu yana lafiya.

***

Ina mai baku haƙuri sosai na rashin ji na jiya kwata-kwata, sakamakon wasu shungullolin da suka riƙe ni, waɗanda suka ƙira ban ɗauka ba a yi haƙuri, ga wannan ba yawa ku yi manage.

<< Yar Karuwa 23Yar Karuwa 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×