Skip to content
Part 25 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Rilwan abokin Malam Abbo shi ya gaji da halin da ake ciki, ya samu Malam Abbo ya ce, “Haba Aliyu meyasa kake haka ne? Baka san haƙuri ba ne ko baka san ƙaddara ba? A haka kana tunanin kana burin mutuwa ka shiga aljanna, bayan iyayen da ake samun aljanna ta sanadinsu kai su kake cusawa baƙin ciki da damuwa, dan Allah Aliyu kayi haƙuri haka nan komai ya wuce.”

Malam Abbo da ya zabge a sati guda, kaman wan da yayi cuta, ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce, “Rilwan na jima da haƙura, amma kai ma ka sani abu ne mai wuya a ce wannan tabon ya gogu a zuciyata cikin sauƙi haka, na tabbata da wani ne ma da yanzu haka yana asibiti, baka san ciwon rashin masoyi ba, musamman a lokacin da ka gama sanya wa ranka za ka mallake sa na har abada, ba’a kyauta mini ba sam amma bakomai na bar wa Allah lamurana.”

Rilwan ya ce, “da haka kayi tun fari ai da ya fi, Allahn ne bai nufa za’a yi ba shi yasa, idan ka fawwala masa komai kana mai ƙas-ƙas da kai, sai ka ga ya baka wacce ta fi ta.”

“Uhmn”, kawai Malam Abbo ya ce tare da miƙe wa ya zauna.

Sosai Rilwan ya masa faɗa, ya nusar da shi gaskiya, har ya amince zai koma gida zuwa dare, ko dan saboda musabaƙan da za’a yi, yasan zai samu ya je ya kalli Faɗima a can, idan Allah ya nufa rabonsa ce to ko gaba zai mallaketa.

Haka ake son abota, duk abotar da babu faɗan gaskiya a cikinta to ba abota ba ce kuma bata da fa’ida, Allah bamu dama da ikon amfanuwa da juna, yacce za mu yi alfahari da hakan ranan gobe ƙiyama.

Malam Abbo dare na yi ya shirya staf da shi, duk damuwan da yake ciki bai hana sa yin gayu ba, wucewa gida yayi, yana isa kuma dai-dai zai shiga, sai ga Ya Hussain yana fitowa, ai da sauri ya ƙarisa gare sa ya rungume sa yana faɗin, “Aliyu haidar ina ka shiga haka? Za ka sa mu zauce a gari.”

Murmushin yaƙe kawai Malam Abbo yayi ya ce, “Ku yi haƙuri Ya Hussain ina lafiya.”

Kallonsa yayi da kyau, ya ce, “a yacce ka rame kaman mai fama da cutan ƙanjamau ɗin ne kana lafiya, ka kalli kan ka kuwa Ali? Ka ga yacce ka fita a hayyacinka a sati guda kawai.”

Malam Abbo bai ce komai ba, Ya Hussain ya sauƙe ajiyan zuciya ya ce, “To Allah ya kyauta, mu koma ciki, daman magani zan je sayo wa Abiy, hawan jininsa na son tashuwa, amma tun da gaka nasan kai ne maganin zai warke yanzu, mu je ko”, ya Hussain ya faɗa tare da juyawa ciki, Malam Abbo na bin sa a baya.

Ɗakin Abiy suka shiga da sallama, suna shiga Abiy ya miƙe yana faɗin, “Hussaini har ka sayo maganin..?” Tsayawa yayi da maganan yana kallon Malam Abbo.

“Ali kai ne ka koma haka? Akan mace Ali, ina ka ajiye imaninka na imani da ƙaddara kairi ko sharri?” Faɗin Abiy yana mai gyara zamansa.

Malam Abbo ƙarisawa yayi gaban Abiy ya durƙusa ya ce, “Ka yi haƙuri Abiy ka yafe mini.”

“Bakomai Ali ya wuce, Allah ya yafe mu duka, Allah ya maka albarka, daman ni ban riƙe fushi da kai a rai ba, duwana dai ka cire damuwan wannan abin a ran ka.”

“In Sha Allahu Abiy komai ya wuce.”

“To Masha Allah! Kai kuma Hussain kabar maganin kawai, ina ganin ɗan auta na ciwon ya gudu, daman na begen ganinsa ne.”

Duk murmushi suka yi har Malam Abbo, kuma wannan karon murmushin daga ƙasan zuciyarsa ne.

Ya Hussain ya ce, “ai nima ina ganinsa na ce ga maganin Abiy ya zo da ƙafafuwansa, ɗan autan Abiy da Ummi.”

“Yauwa Ali tashi ka je ka bai wa mahaifiyarka haƙuri, ita ma tana cikin damuwa na rashin ganin ka, zuwa gobe har gidan yayyunka mata duk ka leƙa ka gaida su, idan kuka dawo daga musabaƙan naku ma ina son za mu yi magana akan tafiyanka Madinan”, faɗin Abiy da idanuwansa ke kan Malam Abbo.

Malam Abbo gyaɗa kai kawai yayi, tare da miƙewa ya fice a ɗakin ya nufi cikin gida wajan Ummi.

Ya Hussain ya ce, “Abiy gaskiya nima ina goyon bayan a ƙyalesa ya tafi Madinan kawai, idan baya kusa zai fi jin abun ya fice a ran sa.”

“Hakan ma za’a yi In Sha Allah Husain.”

Malam Abbo samun Ummi yayi zaune tana linke kaya, ƙarisawa yayi gabanta ya durƙusa tare da cewa, “Ki yi haƙuri ki yafe ni Ummi.”

Ummi da tun ganin Malam Abbo tayi suman staye, abin ka da uwa har da ƙwallanta ta ce, “haka ka rame Ali? Ka yi haƙuri kai ma ka yafe ni, da alhaƙinka da na ɗauka Ali.”

Murmushi Malam Abbo ya ƙwaƙulo yayi ya ce, “bakomai Ummi ya wuce.”

“To Allah ya maka albarka, idan ita rabonka ce kuma alkairi a gare ka to Allah tabbatar da alkairi.”

“Uhmn!” Kawai Malam Abbo ya ce, ya miƙe ya wuce ɗakinsa.

Washe-gari gidan yayyunsa mata duka ya je, ya basu haƙuri, su ma suka ƙara rarrashinsa, suka tabbatar masa da yanzu kam duk sun amince, idan alkairi ne Allah ya tabbatar, daman ba su amso kayan ba, shi dai Malam Abbo duk idan sun yi wannan magana, sai dai ya ce, “uhmn!” yayi shiru.

Haka Malam Abbo ya shirya ya je tahfiz, aka shirya komai na tafiyan da shi, amma bai shiga ajin ɗalibai ba, Malaman duk sai jaje suke masa da fatan alkairi, shi dai Malam Abbo wani sabon miskilanci ya ƙaro, abin ka da masu suna Aliyu.

Tun ranan Sunday su Umaima suka tattara suka tafi jimeta, a can suka kwana aka shirya komai da komai dan da jirgi za su yi tafiyan, washe-gari Monday jirginsu ya ɗaga sai babban birnin tarayya Abuja, suna isa ba ɓata lokaci aka wuce da su masauƙi, duk abin da ya kamata an yi sai jiran isowan Banafsha su wuce filin taron.

*****

ACM ƙoƙarin zama yake a ƙasa amma Mami ta dakatar da shi, ta ce, “Ɗan Mami zauna a sama abin ka.”

Murmushinsa mai stada ya saki sannan ya zauna akan kujera, cikin girmamawa ya ce, “Antashi lafiya Mami? Ya gajiya-gajiyan biki?”

“Alhamdulillah ɗan Mami, sai yau ka samu zuwa kallon Mamin taka har na kusa yin fushi.”

Murmushi yayi tare da shafa kiston kan sa, haka kawai ya ji Mami ta masa ƙwar jini, wani kunya-kunyanta ma yake ji, a hankali ya ce, “Afuwan Mami, wallahi ayyukan ne ba sa barinmu sai a hankali, yau-yau ɗin nan dawowanmu daga Philippines na wuco nan, musamman na zo mu gaisa.”

Mami na murmushi ta ce, “To Masha Allah! Sannu da ƙoƙari, Allah taimaka ya kuma dafa muku, Allah ƙara starewa ya ƙaro nasarori, Allah muku albarka, sannunka da hidima da kuma ƙoƙari, Allah saka da alheri ya kawo mana surkarmu lafiya.”

Murmushi ya kuma yi, cikin jin daɗin Mami bata ce ta gari ba kaman yan da kowa ke cewa, ya amsa da sauri ya ce, “Ameen Maminmu.”

“Bari na ƙira maka ƙanwar ka ku gaisa ko.”

“Uhmn! Mami da kin bari ma sai na dawo yanzu zan ɗan fita ne”, faɗin ACM cikin inda-inda, saboda gaba-daya ya kasa sakewa, kunyan Mami ya cika sa.

Mami murmushi kawai tayi dan ta fahimci kunyanta yake ji, cewa tayi, “To ɗan Mami a dawo lafiya, ka saki jikinka fa nima kaman Mom taku haka nake a wajanku, Allah muku albarka.”

“Ameen Mami”, ya faɗa tare da miƙewa da sauri ya fice, har da wani ɗan gumi ya haɗa kaman wani mara gaskiya, shi da kan sa mamaki yake, irin yacce ya ji ya kasa sakewa a wajan Mami kaman wata surkuwar sa, ai ko surkuwar sa ce yanzu an daina irin ƙauyancin nan, normal ne ka yi hira da dariya da surkuwanka(an gaishe da ɗan gidan General da Mami), idan ta kama ma a tafa.

Gari ya shiga ya ƙamshin dahuwa, missing na ƙannensa yake yi, yau son kai su yawo yake amma basa nan, Majeeder kuma yasan tana fama da karatu, idan ya ce su fita da ita to bai kyauta ba, sai dai idan sun je Abujan sa iya zuwa yawon.

ACM Bunayd yana gama abin da ya fita yi, ya wuce gidansa a can ya huta, shi ne bai dawo gidan Papi ba sai wajan ƙarfe goma, yana dawowa kuma ya shige sashin General, samun General ɗin yayi yana nasa ayyukan, waje ya samu ya zauna tare da faɗin, “General kawo na taya ka.”

General ƴar dariya guntuwa yayi ya ce, “Me haɗin land army da kuma air force? Dan haka bar ni nayi aiki na, kai kaje ka huta, saboda ku tafi da wuri, ai flight za ku bi ba?”

“In sha Allah! Flight za mu bi, irin na 8 ɗin nan, before 10 mun isa, tun da 2 hours ne da mintuna, ke kai mutum Abuja daga Kano”, faɗin ACM yana ɗan kishingiɗa.

General ya ce, “A’a my Man, sai dai ko jirgin 6 ina ga zai fi, kai dai ka kwanta, dan ka tashi da wuri, ita kam nasan za ta kwana cikin shiri, a kan idonta ƙarfe shidan zai buga.”

Murmushi ACM yayi a ransa yana faɗin, lallai idan Majeeder ce za’a ga tashi 6, amma dai zai shirya dan su isa da wurin, a fili kuma gyara kwanciyansa yayi ya ce, “Allah nuna mana goben da rai da lafiya.”

“Ameen my Man”, General ya faɗa yana kan aikinsa.

ACM Bunayd kitchen ya je ya haɗo musu tea shi da babansa General, ya miƙa wa General nasa, shi ma ya ɗau nasa ya sha sannan ya ɗan kishingiɗa.

General da ya kurɓa tea ɗin sai ya murmusa, ya ce, “My Man yan da ka iya tea haka wa zai ce kai goyon gauro ne.”

Murmushi kawai ACM yayi, can kuma ya ce, “Ai daman ni goyon Momsee ce General.”

General ya ce, “Au haka ne fa ashe.”

Sai suka murmusa duka, General na kurɓan tea nasa yana aikinsa, shi kuma ACM a wajan ya kwanta yana lasta wayansa, har sai da dare ya ja sosai wajan sha biyu, sannan ya miƙe tare da yiwa General sai da safe ya wuce ɗakinsa, General aikinsa ya ci-gaba da yi a system nasa, bai sarara ba sai wajan biyun dare, sannan ya kulle ya wuce ya watsa ruwa, ya ɗaura alwala yayi nafila sannan ya kwanta.

Mama Hadiza tana fama da rigiman Majeeder da na Banafsha, ka ranste ita ce kakarsu dukansu, dan ma har yanzu Banafsha bata gama sake wa ba, tana nan da damuwanta cikin zuciyanta, kawai tana ɓoye wa ne saboda farincikin Maminta.

Suna zaune a palourn ƙasa suna kallo, Mami ta sauƙo daga sama, da sallama ta iso palourn suka amsa mata, waje ta samu ta zauna tare da cewa, “Barka da war haka Mama Hadiza, kina ta fama da surutun ƙawayenki.”

Mama Hadiza ta ce, “ai surutun shi aka fi so, shirun nan ba daɗi, shiyasa ma ni yanzu Hauwa’u ce mutumiyata, ita Faɗimatu baƙin hali ya mata yawa.”

Majeeder ta ce, “sannu da fitowa Mamina, kaka Dije ki faɗa gaskiya ba ruwan Banafsha ta.”

Mama Hadiza ta ce, “Za ku ji da shi dukanku.”

Banafsha dai tana shiru bata ce komai ba, sai murmushi da tayi, Mama Hadiza ta galla mata harara, Mami kuma ta girgiza kai tare da faɗin, “Sai ki je ki kama karatu da shiri, dan gobe da wuri za ku wuce, ke da yayanku.”

Majeeder ta ce, “Lah! Mami Yaya ACM ne zai kai ta, Allah sarki kaman na bi su.”

Mami murmushi tayi tana faɗin sai Majeedern ma ta shirya su je tare, amma Majeeder ta ce lala-lala su dawo lafiya, ba ta zuwa.

Banafsha miƙewa tayi ta shige ɗakin da yake nata, daman Mami ta jera mata duk wani abu nata da kan ta a ɗakin, dan haka wajan da ta ajiye mata Qur’ani taje ta ɗauka, karatunta ta fara dubawa, karatun take bata sarara ba har sai da lokaci ya ja, sannan ta miƙe ta wasta ruwa ta kuma yin alwala, a taƙaice dai baccin da tayi ba da yawa ba.

Da asuba Mami na zuwa tashinta ta samu har ta farka tana kan sallaya, jinjina kai tayi sannan ta ce, “Allah ya miki albarka gudalliyan Maminta, Allah taimaka, ki tabbatar zuwa ƙarfe shida kin gama komai kin fito, abin karyawanku ma ɗauka muku za ki yi, kwa karya a hanya”, tana gama magana ta juya ta fice.

Zuwa ƙarfe shida Banafsha ta gama shiri, Egyptian abaya ta saka, maroon color wanda ya amshe ta ba kaɗan ba, ba wani makeup ta saka hijabinta baƙi ɗan dai-dai, wan da stayinsa bai wuce iya guiwan hannunta ba, tana ƙoƙarin fitowa Mami na shigowa, ganin ta gama komai Mami ta murmusa kawai tare da juyawa suka fice tare, da ɗan ƙaramin trolleynta yana hannunta, suka fice a palourn, compound na gidan suka fito, nan ta hango Alhaji Mukhtar da General Sufyan da kuma wani matashin saurayi a gefensu wan da bata kallon fiskansa, gani tayi ya buɗe ƙofan mota na baya ya shige.

ACM Bunayd kamun a ƙira sallah ya zama ready, yana sallahn asuba kuma ya gama komai har karyawa yayi, anan sashin General ya haɗa tea nasa ya sha, sannan suka fito tare da General, fitowansu yayi dai-dai da fitowan Papi, ACM agogon da ke maƙale a hannunsa ya kalla tare da jan guntun staki ya ce, “Allah mastalan tafiya da yaran nan kenan Sir, ga shi abu dai nasu ne amma su ke ɓata wa mutane lokaci.”

Alhaji Mukhtar ya ce, “Sai haƙuri ACM, Allah dai ya kai ku lafiya, dan Allah ka kula da yarinyar nan sosai, amana na baka ka ji.”

ACM kallon Alhaji Mukhtar yayi ya ce, “Yanzu sai an bani amananta Papi? To wallahi nidai ban amshi amana ba, idan ta mini rashin ji a hanya kwaɗeta zan yi.”

Murmushi General yayi ya ce, “A’a ba za’a yi haka ba my Man, Ka yi haƙuri kasan lamarin mata gaba ɗaya sai a hankali, a ce maka an halicci mutum da ƙashin haƙarƙari ai kasan dole a karkace ya ke sai dai haƙuri, idan ka masta to sai dai ka karya shi, balle ma wannan ba su Suhaila ba ce tana ji.”

ACM bai ce komai ba ya buɗe ƙofan baya ya shige, yana shiga kuma dai-dai lokacin Mami da Banafsha suka iso.

Banafsha rusunawa tayi ta gaishe da General da Papi duka, suka amsa mata, faɗa suka mata sosai akan ta kula ta kuma tabbatar ta yi ƙoƙari, sannan Papi da kan sa ya buɗe mata ƙofan motan ya ce, “Faɗima shiga ko.”

ACM hankalinsa na kan wayansa yana ta aikin jan staki, Banafsha kuma ba tare da ta kalli na cikin motan ba ta shiga ta zauna, wani irin ƙamshi ta ji ya daki ƙofofin hancinta, wan da ya haddasa mata lumshe idanuwanta, tana karanto addu’oe a zuciyanta, dan bata san waye ne yayan nasu, da ake nufin za su tafi tare ba.

Kaman yan da yake a ɓangaren Banafsha, to haka ɓangaren ACM Bunayd ma, domin wani irin sansanyar ƙamshi ya ji ya dakar masa hanci, wan da ya san ya shi jan numfashi kaman shan yaji haka, rasa a ina yasan ƙamshin nan yayi, mamaki yake Majeeder kuma yaushe ta sauya turare oho, ƙira ne ya shigo wayansa dai-dai driver ya ja mota, sun fice a gidan.

Ganin layin Abeed ne guntun staki ya ja tare da ɗagawa ya ce, “Wai kai ma baka da mata ne kake ƙiran mutane a irin wannan lokaci?”

Abeed a ɗaya ɓangaren ya ce, “Ai kuwa ni ke da mata, ga ni ga ita, ni ba gauro irinka ba mai kwana da pillow, dan ma ka ci sa’a an ƙiraka, to faɗa maka zan yi nayi mafarkin ka.”

“Idan na alkairi ne ina sauraranka, idan ba na alkairi ba riƙe abin ka bana son ji, ka yi sadaka kawai.”

Dariya Abeed ya kwashe da shi ya ce, “Ɗan iska na alkairi ne musamman a wajanka, yan da kake gauron nan nasan kullum da burin haka kake kwana kake tashi, ina ga fa sai mun haɗa maka da Suratul Yusuf ACM, haba mutum a ce abu ya gagara.”

ACM fiska ya haɗe ya ce, “Kasan Allah zan kashe wayana Captain, bana son irin shirmen nan da safiyan Allah, dole ne ma sai ka faɗa mini mafarkin?”

“Dole ne na sanar da kai wallahi, mafarki nayi wai ka haɗu da Gimbiyarka har magana ta kankama, kar ka ga kyawunta, wayyo na taya ka murna Allah tabbatar, happy marriage life in advance ɗan jagaliya mijin ƴar jagaliya”, Abeed ya ƙarishe yana dariya.

Staki ACM ya ja tare da daste ƙiran, dai-dai sun iso airport, ya juya ga Banafsha da ke rakuɓe a dungun mota, rai a ɓace ya ce, “Majeeder har mun zama mate’s ko? Ni kike jira na gaishe ki?”

Banafsha da ta ke kallon hanya jin abin da ya faɗa, a hankali ta juyo tana faɗin, “Ka yi haƙuri yayaaaaa…….” Maganan da ke bakinta ne ya maƙale ganin wan da ke zaune a gefenta, kutumar dumadu ta faɗa a ran ta, wannan ɗan renin hankalin ne daman ake ta wani, cewa yayanta-yayanta, guntun staki ta ja tare da haɗe fiska ta galla masa harara.

ACM Bunayd kallon wacece a cikin motansa ba ƙaramin mamaki ya basa ba, bai dawo daga duniyan mamakin da ya tafi ba sai da ta galla masa harara, ɗan stiririn ƙaran tsakinta shi ya dawo da shi hayyacinsa, ai take ya haɗe fiska kaman ya ga maƙiyinsa a filin daga, a hankali kaman bai son magana ya ce, “You again?”

Hararansa Banafsha ta kuma yi ta murguɗa baki ta juyar da kan ta gefe.

ACM wani irin lumshe idanuwansa yayi, yana buɗe su kuwa tuni sun yi jajir na ɓacin rai, ita wacece da za ta ja masa staki, ta harare sa har da murguɗa baki? Ya bar abin da zai yi ya ɗauke ta a motansa zai kai ta wata uwa duniya, kuma tana masa stiwa da rashin kunya, ina fucking useless mijinta ya ke?

Wani wawan stawa ya dakawa driver ya ce, “Stooopppp this car right now.”

Bai gama rufe laɓɓan bakinsa ba, tuni har driver yayi parking, daman sun riga da sun iso airport ɗin, cikin ɓacin rai ya ɓalle murfin motan ya fice tare da ƙarisawa gefen da take zaune ya buɗe ƙofan da ƙarfin gaske, fiskan nan a haɗe ya ce, “Hey U idiot get out of my car before i loose control.”

Banafsha hararansa tayi tare da fitowa, ta kuma jan masa staki, cikin ɓacin rai ya dunƙule hannu zai kwasheta da mari, me kuma ya tuna ya fasa, tare da kai wa iska bugu, faɗi yake a ran sa ta ci albarkacin Papi da General.

ACM rai a ɓace ya fiddo wayansa a aljihu, layin General yayi dialing, bugu ɗaya ya ɗauka yana faɗin, “General ba zan samu zuwa Abujan ba.”

General a ɓangarensa ya ce, “meyasa my Man?”

Rai a ɓace Bunayd ya ce, “Sir nidai ba zan samu zuwa ba.”

General da yake yana ƙaunar yaronsa, ba tare da damuwan komai ba ya ce, “shikkenan babu mai masta maka tun da baka son zuwa, amma dai ka ƙira yaya ka sanar da shi tukunna, ko za’a san yan da za’a yi.”

Bunayd daste ƙiran yayi, yana mai ƙara tamke fiska ya shige motansa ya zauna, tare da ƙiran layin Alhaji Mukhtar, ita kuwa Banafsha tana staye ta cika tayi fam, ita a rayuwanta ta rasa ma me za ta yiwa wannan mara mutuncin ta huce, sam sam ta stanesa, ko tsanan da ta yi wa ya Danish to me sauƙi ne, akan yacce ta tsani wannan mara kirkin, dan ma yana cin albarkacin kuɗin jinyan Maminta da ya biya, kuma shi ma tana yin kuɗi za ta biya shi, ba’a son abin hannunsa kada ma ya rena su, hararan motan tayi tare da jan tsaki ta kuma yin ƙwafa(ni ko na ce Hajiya Faɗima hattara dai a bi duniya a sannu, mugun stana fa na iya komawa mugun soyayya🫡)

Alhaji Mukhtar na ɗauka ya ce, “wai har yanzu jirgin naku bai tashi ba ne?”

ACM haɗe fiska yayi kaman yana gaban Alhaji Mukhtar ya ce, “Sir ba zan iya zuwa Abujan ba.”

Ai a take Alhaji Mukhtar ya hayayyaƙo masa, “Bunayd ka shiga hankalinka, har ni zan ce ka kai ƙanwarka waje ka ce ba za ka iya ba, kar ka bari ka ɓata mini rai, kuma daga yau kada ka kuma faɗa mini wani Sir.”

ACM Bunayd cikin jin haushin Banafsha da stanarta ya ce, “Papi please..”

Papi Kaste masa maganan da zai yi yayi ya ce, “Bunayd bana son jin komai, ka kai Faɗima Abuja, kaman yan da ka ce baka da abin yi za ka jira har su gama, to ko nan da 1 month ne ban yarda ka baro Abuja ba tare da Faɗima ba, sannan ka kula da ita sosai, na baka amanarta.”

ACM kaman zai yi kuka ya ce, “Papi ba zan iya riƙe amana ba, zan dai yi sauran, sannan kuma jirgi ya riga ya tashi ya za mu yi.”

“Ko fiffike za ka nemo ka maƙala ka yi, ka nemo ka maƙala ka fire ka kai ta, ko goyonta za ka yi koma mene dai, ka tabbatar yau ɗin nan da yardan Allah ka kai ta Abuja akan lokaci, dan in baka da abin yi to ita tana da shi, kuma kar na ji kar na gani.”

“Normal Papi, amma maganan amana babu.”

“Ko ma yaya dai na faɗa maka, ka kula mini da yarinyata, maza ma bata waya.”

ACM hararan wajan motan yayi sannan kawai ya kashe wayan bai ce wa Papi komai ba, staki ya ja tare da duba lokaci, jirgi ya jima da tashi, yanzu ko su yi booking na wani ko su tafi a mota, kai idan ya kai ta a jirgi ma ai ta ji daɗi, tafiyan mota za su yi, yau za ta gane bata da wayo, da yake ya koma gaban motan, kallon drivern yayi tare da faɗin ya faɗa wa yarinyar da ke waje ta shige baya su tafi.

Drivern zagayowa yayi wajan Banafsha ya ce, “Maa get in let’s go.”

Banafsha wani ɗan iskan kallo ta masa, tare da gyara stayuwanta, driver ya gama turancinsa ya zagaya, ya shiga motan tare da faɗin, “Oga i tell her but she dey there standing.”

Wani irin killer smile ACM ya saki tare da buɗe ƙofan motan ya fito, kallon up and down ya mata sheƙeƙe ya ce, “magana ɗaya nake yi bana sake wa, za ki shiga ne ko kuwa nayi tafiya na, cuz mastalanki ne in kin fasa nayi tafiyata”, yana faɗan haka ya juya ya shige motan ya zauna.

Har kusan mintuna biyar Banafsha na tsaye, bata mosta ba balle batun shiga, Bunayd faɗa wa drivern yayi ya ja motan su koma gida, har driver ya kunna sun juya, Bunayd ganin har yanzu bata mosta ba sai yayi murmushi kuma, yana faɗin wato yarinyar bata ji, ita ma tana ji da ɗanyen kai da tashen balaganta, dole ya gyra mata zama, saka drivern yayi ya staya, ya fito tare da tunkaro ta, Banafsha na tsaye ƙiƙam rai a haɗe ko motsa wa bata yi ba.

Bunayd ba tare da ya damu da idanuwan jama’a ba, ko kuwa ya damu da auren da ke kan ta ba, haka ya naɗe hannun riga, bata ankare ba sai jin ta tayi a hannun mutum kaman jaririya, yayi sama da ita, bai dire ta ko ina ba sai cikin mota, ya ajiyeta ya kulle ƙofa ya wuce wajan zamansa yana faɗin, “da ke da fucking marriage da ke kan ki baku dame ni ba, tun da shi mijin naki useless human being ne to nothing concern me.”

Banafsha dai tun da Bunayd ya ɗaga ta tabar duniyar da mutane suka, domin da ƙamshinsa da wasu sinadarai da bata san na menene ba, su suka taru suka wuce da ita wata duniyar, shiyasa ta kasa komai, har ya ajiyeta ya koma wajan zamansa, yana gama surutun sa ta dawo hayyacinta, ƙanƙance idanuwanta tayi cike da masifa ta ce, “ka taɓa wuta, ban yafe ba, Allah ya isa, ɗan iska mugu, mai taɓa jikin mata.”

ACM Bunayd ko a jikinsa ya murmusa tare da faɗin, “Dan ma ke yarinya ce da kin ga abin da ya fi haka, idiot kawai za ki gwada wa waye kin fi sa ɗanyen kai.”

Banafsha dan taƙaici kaman ta yi kuka, wannan mara mutuncin ya shammace ta da yawa gaskiya, ya ɗaga ta a idon jama’a ba kunyan mutane, balle storon Allah, haka ta din ga mita ita kaɗai, Bunayd kuwa hankalinsa kwance ya fidda wayansa yana dannawa, driver ya saka musu kiɗa, sai lokacin saƙon Momsee ya faɗo wa Bunayd, ashe wannan Faɗimar ake nufi da ya bai wa waya, taɓe baki yayi ya ce ba da kuɗinsa ba kam, tayi kaɗan ya bata wannan wayan.

Banafsha din ga jan Allah ya isa ta din ga yi, sannan a fili ta ce, “Sai dai kai ne useless ba mijina ba kam.”

“Hakan na nufin tana da auren kenan?” Bunayd ya tambayi kan sa, taɓe baki yayi irin ko a jikinsa, duk abin da take yi bai kula ta ba, shi ya san maganinta, ya godewa Allah ma da bai goge application ɗin can ba.”

Banafsha yunwa ta fara ji, tuni ta nemo takeaway da Mami ta bata, ta buɗe za ta ci, sai kuma ta jiyo muryansa kaman daga sama.

ACM Bunayd ya ce, “Ba’a cin abinci a mota na.”

Banza da shi tayi tana ƙoƙarin kai wa bakinta ya buge, abin ya koma cikin roban, bata gama shan mamaki ba ya ɗaga roban, ba ruwansa da abin da ke ciki haka yayi jifa da shi, Banafsha ji tayi kaman da rayuwanta yayi jifa, musamman yacce take jin wani bala’en’en yunwa, ulcer ta mosta, wani irin kwallan haushi da taƙaici da tsanan Bunayd ta maste, hawayen da bata san san da suka zubo ba, balle ta mai da su.

ACM Bunayd kuwa duk abin da take yana kallonta ta mirrow, har da hawayen nata ya gani, dan haka cika yayi da farinciki, ga shi ya fara ramawa na saka shi zuwa Abuja da za ta yi dole, dole sai tayi kuka ita ma ta ji zafin ya ji.

Tafiya suka yi kusan na hour biyu, sannan sai ga ƙiran Papi ya shigo, Bunayd ɗauka yayi a dake ya ce, “Papi muna hanya.”

“Good ya fi maka, yanzu sai ka ba ta wayan, tun da ni na ƙiraka ba kai ka ƙira ni ba, shashasha yayan gwaza mai ƙaiƙayi a wuya kawai.”

ACM rai a ɓace ya saka wayan a speaker tare da miƙa wa Banafsha, ita kuwa jin muryan Papi tuni ta amsa, sai ga hawaye a idanuwanta rau-rau, muryan na rawa suka gaisa da Papi, ya tambayi ko lafiya ta ce lafiya ba komai.

Wayan ya bai wa Mami suka gaisa,tana jin muryan Banafsha ta ce, “sam-sam bakya ji Banafsha, Allah kika kuskura naji wai kin masa reni ko wannan halin naki ba sai na saɓa miki, ki kula sosai ki mai da hankali.”

Banafsha haushi ne ya ƙaru mata, wato ya mata abu amma Mami na goyon bayansa, ko a bata ce ba kawai ta miƙa masa waya, shi ko da yake yana jin duk abin da Mami ta faɗa murmushi yayi, ya ce, “Barka Mami.”

Mami ta ce, “Yauwa ɗan Mami, ka yi haƙuri da halin ƙanwar taka ka ji, Banafsha sam bata ji halinta sai a hankali, amma fa idan ta maka rashin kunya to ka zane ta.”

ACM murmushi yayi har da ɗan cija leɓensa, cikin girmamawa ya ce, “bakomai ma Maminmu, insha’Allah ma mun kusa isa a taya mu da addu’a.”

“To Allah kai ku lafiya, Allah ya muku albarka duka.”

“Ameen Mami”, yana faɗa Mami ta kashe wayan.

ACM ba abin da yake yi sai murmushi.

Ɓangaren su Mami kuwa tun da take magana Alhaji Mukhtar ke kallonta, sai da ta kashe wayan sannan ya ce, “Wai faɗa masa kike ya taɓa yarinyar nan? Ba ki san Bunayd da baƙin hali ba fa, haka yake cin zalin ƙannensa idan alluran ya mosta, to idan ya ji maganank ya taɓa Faɗima, har naji labari to zai dawo ya same ni sai na saɓa masa.”

Murmushi Mami ta saki ta ce, “Ka dai daina goyon bayan Banafsha, baka san halin yarinyar nan bane da rena yayyunta.”

Ƙwafa Alhaji yayi bai ce wa Mami komai ba, ita kuwa ganin haka sai ta shige jikinsa, tana stokano sa har sai da yayi dariya, sannan fa aka shiga wani sabon babin, Alhaji cikin raɗa ya ce, “Na gama haƙuri Amarya a bani haƙƙi na.”

Mami da daman cike take da mamakin ko me dalilin Alhaji na ɗaga mata ƙafa, kaman wata yarinya, abin da yanzu ma ko yaran ba’a ɗaga musu ƙafa, amma ita yau aure na neman sati biyu ba komai da ya shiga tsakaninsu, ita ta ɗauka ma ko daman wani dalili ne yake da shi na daban shiyasa ya ɗaga mata ƙafa, amma tun da ya buƙata dai-dai ne, daman ita ma tana mararin mijinta kawai dai haƙuri take yi, cikin raɗan ita ma ta ce, “Daman ai ba’a hana ka ba yallaɓoi.”

Murmushi Alhaji yayi, yana rage kayan jikinsa ya ce, “Ba’a hana ni ba amma dai nasan ana gajiye ne, kada na ce zan kwana raya sunna a ce mini an gaji, shiyasa na bari ki gama hutawa, haƙurin da nayi ina haɗiye yawu na shekaru goma sha duka a yau nake so na ɗan huce su.”

Mami murmushi tayi kawai bata ce komai ba.

Alhaji ya ce, “Ya kika yi shiru?”

Mami ta ce, “Kullum kuma a ko da yaushe ina maraba da Alhajina, angon Ramlatu, ka ga yin magana ma ɓata baki ne, mu haɗu a filin daga ka ga maganganun da idanuwanka.”

Alhaji ƴar dariya yayi ya ce, “Shiyasa nake ƙaunarki, Allah bar mu tare ya bamu ikon haƙuri da juna.”

“Ameen Alhajina, amma dai ka ga yanzu safiya ne, ka bari sai zuwa dare tun da ka ce kwana za ka yi.”

Alhaji wani kallon so ya yiwa Mami ya ce, “Wannan maganan ne kuma ba zan ma ji ba balle na gane, a hannu nake.”

Mami murmushi tayi tare da shigewa jikinsa, cikin ƙwarewa da soyayya suke sarrafa junansu, abu ne na manya kuma dai an jima ba’a haɗu ba, ko na ce an ɗau shekara da shekaru ana burin irin wannan shauƙin(kunsan Alhaji bai taɓa kusantan Mami ba duk tsawon shekarun da ta yi tana karuwanci).

Alhaji ya zauce ya susuce, kai ba za ka ce manya ke abin ba, soyayya da ƙauna duk sun gwadawa junansu Masha Allah, Alhaji ji yayi mai raba sa da Mami sai mutuwa, domin bai taɓa jin yanayi irin na yau ba tun da yake a rayuwarsa, ko budurwa ba za ta nunawa Mami wani abu ba, haɗewa, sura, garɗi da komai, domin kaman sabuwar budurwa haka ya same ta.

Duk da Mami babba ce amma fa ta ji maza, ta ji a jikinta, sai dai ta daure, sun yi soyayya har sun soye, Alhaji ya sha sumbatu abin sa, kyauta kuwa da albarka ba’a magana, ji yake kaman ya shige jikinta dukkansa ya huta, saboda soyayya da shauƙi.

Mami ma a nata ɓangaren Alhaji ya goge mata karatun kan ta duka, Mami ji tayi kaman duka sauran maza mata ne Alhajita ne kawai namiji, shekarunsa sam ba su hanasa gwangwajeta yan da ya kamata ba, soyayyansa da ƙaunarsa ne suka ninku a zuciyanta, ji take ba kuma namijin da za ta iya rayuwa da shi idan ba Alhaji ba.

Alhaji ya ɗau lokaci mai tsawo yana amarcewansa, dan sai da ya tabbatar da idan bai sarara ba zai ƙure Mami sannan ya ƙyale ta, amma duk da haka Mami har da ƙwallanta, Alhaji share mata hawayen yayi yana mai sakin wani irin haɗaɗɗen murmushi ya ce, “Allah ya miki albarka matata.”

Mami ƴar kukan shagwaɓa ta saka bata amsa sannun ba ma, nan Alhaji ya din ga riritata kaman ƙwai, kowa ya samu waje dole yayi shanya, hhh mata kuna sha’aninku, ɗan rigima na amarcin nan kam yana da kyau yin sa kada ki bari ya wuce ki zo kina cije yasta.

Tare Mami da Papi suka shige toilet, Papi ya tayata ta gasa kan ta sosai sannan suka yi wanka suka starkake jikinsu, fitowa suka yi tare da bin lafiyan gado, Alhaji sai zolayan amaryansa yake, wai ko ya ƙara, Mami ta ce ai bai ƙure ta ba a bari a tashi bacci tukun, a haka suna nishaɗinsu har bacci yayi gaba da su.

Banafsha tun tana kuka har bacci yayi gaba da ita, na wahala dan yunwa take ji sosai, Bunayd na jin mostinta shiru ya ɗan waiga sai ya ga bacci take yi, murmushin mugunta ya saki, tare da ɗaukan goran ruwan da ke gefensa ya buɗe ya stiyaya mata, ai a firgice Banafsha ta tashi tana ɓata fiska, shwagaɓe fiska tayi tana faɗin, “Auch Maminaa.”

ACM kuwa yan da ta yi da fiskanta ne ya ɗan shagala kallo ta mirrow, duk mostin da take yana kallo, yana gani ta aikawa seat da yake zaune harara, sannan ta duba jikinta ganin ruwa sai ta ɓata fiska.

Wani yunwan ne ya murƙusheta, nan ta kuma mastar wani ƙwallan, a fili ta ce, “Allah ya isa na da abinci na da aka zubar.”

ACM yana jin ta yayi banza da ita, shi yasan me yake ƙullawa, dole fa sai yayi maganin yarinyar nan, tun da ita juninta fistara, shi ba’a masa ya bari, ita kuma tun da ta ce ba ta da kunya, to su zuba su ga waye zai kwashe, ba za ta yi bacci ba kuma ba za ta ci masa abu a mota ba.

Kamun su isa Abuja tuni Banafsha ta fice a hayyacinta, idan ka kalleta kasan kaɗan take jira ta sume, dan ma a haka Allah ya taimake ta tafiyan da za su yi a a 6 hours da mintuna, sun yi shi a awannin da ba su cika biyar ba, sakamakon gudun da drivern ke yi.

Da yake Papi ya riga da ya yiwa ACM bayanin komai, direct wajan taron ya kai ta, yana isa kuma ya ƙira layin da Papi ya basa na Malaminsu, ƙiran na shiga Malamin ya ɗauka, a taƙaice Bunayd ya masa bayani, ai cikin hanzari Malamin ya ƙariso wajan motan su Bunayd tare da su Umaima da dai tawagan su, dan su ma basu jima da isowa wajan ba.

Sai da Bunayd ya tabbatar da sun iso ya kallesu sannan a daƙile ya ce, “fice mini a mota.”

Abin da ACM bai sani ba kuwa shi ne, tuni Banafsha ta jima da ficewa a hayyacinta, ran sa ne ya ɗan sosu na banza da shi da ta yi, buɗe ƙofan motan yayi ya fito, dai-dai lokacin Umaima ma sun iso wajan motan, mamakin kallon Bunayd Umaima tayi, domin bata manta fiskansa ba, ta tuna shi ne wannan wan da suka yi rigima da masoyiyarta a asibiti lokacin rashin lafiyan Mami.

Ɗaukin ganin Banafsha shi ya hana Umaima stayawa dogon tunani, kamun Bunayd ya buɗe ƙofan motan tuni ta buɗe ta hango Banafsha ai farinciki ya sanyata rungumeta, sai dai ji tayi jikinta da zafi sosai, da mamaki ta ɗago tana faɗin, “Lafiyanki kuwa masoyiya?”

Banafsha da ta gama ficewa a hayyacinta bata ce komai ba, ta ƙoƙarta ta ja jikinta ta fito a motan, tana stayuwa a kan ƙafafuwanta kuwa tuni jiri ya kwashe ta, ji kake luuuu tayi baya za ta faɗi, Umaima ta kasa tare ta, sai Malam Abbo da ke gefe, komai ke faruwa a kan idonsa ne yayi gaggawan nufo su, abin mamaki kamun ya iso har Bunayd ya tallafe ta, fiskan nan a haɗe ba mutunci, domin ya ga yunƙurin da Malam Abbo yayi, shi kuwa Malam Abbo ganin Banafsha a jikin Bunayd wani iri ya ji, kaman an soka masa kifiya a ƙirjinsa.

Umaima ai kuka kawai ta saka tana faɗin, “Na shiga uku masoyiya me ya same ki?”

ACM magana ya yiwa drivern sa ya miƙo masa ruwa ya shafa mata, ai a take ta buɗe idanuwanta tana jero ajiyan zuciya, ga wani yunwa da ke cin ta, tuni ta fara hawaye.

Malamin da suka yi waya da ACM yana kallon duk abin da ke faruwa, amma bai kawo komai a ran sa ba, tun da daman Alhaji Mukhtar ya sanar masa da cewan yayanta ne zai kawo ta, sai dai da ACM ya masa magana za su juya da ita tun da ba ta da lafiya, sai ya dage basa haƙuri akan za su kula da ita, lallai-lallai suna buƙatan shiga filin taron da ita yanzu.

ACM ba tare da ya kuma cewa komai ba ya juya ya shige motansa, dirver ya ja suka yi tafiyansu.

Umaima da sauran ɗalibai ne suka riƙe Banafsha, gefe suka yi da ita aka kawo musu first aid box nasu, Malamin ya sa aka ciro magani za’a bata, Banafsha a hankali ta girgiza kai tare da faɗa musu abinci take so, Umaima tayi mamaki jin wai abinci take so.

Malamin ne ya sa aka kawo mata abincin ta ci, aka bata magani ta sha, sannan suka lallaɓa suka shige wajan taro.

ACM tun da suka yi tafiyansu ya sauƙe ajiyan zuciya, tare da faɗin shi da waiwayo ta kuma, sai ranar komawa ko kuwa ya gudu Lagos ya ƙyaleta da driver, yarinya ta bi ta zamo masa jarfa, yanzu ba dan ya riƙe ta ba, da ya bari wancan gardin ya riƙe ta(Malam Abbo), ai shikkenan kuma ta ja masa a wajan Papi, staki ya ja mai rai kawai tare da faɗa wa drivern hotel ɗin da za su je.

The Envoy hotel suka je ya kama ɗaki guda, babban hotel ne na ƙusoshin ƙasa.

Su Banafsha haka aka yi taron ranan aka tashi, ita kawai tana wajan ne amma ita tasan me take ji, daman ulcernta mara mutunci ne, idan ya tashi ba ya mata ta daɗi.

Ana tashuwa taro kuma jikinta ya ƙi jin sannu, sosai zazzaɓi ya rufe ta ruf-ruf, Malamin gwada ƙiran layin ACM yayi, amma cikin rashin sa’a bai shiga ba, dan lokacin ACM ya kashe wayansa ya kwanta bacci abin sa.

Sai a sannu jikin yayi sauƙi, haka suka shafe sati guda suna musabaƙan, kuma duk stawon kwanakin nan ACM ko ta kan Banafsha bai ƙara bi ba, tun da ya ajiyeta yayi tafiyansa, ko ƙuransa bata kuma gani ba, dan ta fi stammanin ma yayi tafiyansa ba ya Abuja.

ACM kuwa yana nan a cikin Abuja, ba abin da yake yi sai yayi bacci, ya tashi ya cika cikinsa, ya kuma tafi yawonsa kaman wan da aka turo honeymoon, hankalinsa kwance har wani ƴar ƙiba yayi, ya ƙara haske Masha Allah!, Kuma ya kashe wayoyinsa duka, bai ƙira Papi ba balle ya saka sa zuwa wajan mara kunyan can a dole.

General a ranan da su Banafsha suka tafi, ya tattara ya koma Lagos, akan sai su Bunayd sun dawo zai zo su wuce Sokoto ɗin.

Alhaji Papi kuwa da amaryansa Mami, soyayya suke ba kama hannun yaro, amarcinsu suke sha hankali kwance, har Papi ma na lissafin za su honeymoon idan sun dawo daga Sokoto, Papi ya ƙira layin ACM ya fi a ƙirga amma ba ya shiga, sosai ransa ya ɓaci sai da ƙyar Mami ta lallashesa ya sauƙa, tun da yana waya da Malamin su Banafsha yana jin lafiyanta, dan ta ce kada a faɗawa su Papi bata da lafiya, kuma ga shii suna kallon su a TV, shiyasa ya sauƙa, ya ce shi Bunayd ɗin idan ya ga dama ya ɓata ma, shi ya jiyo shi da ubansa General.

ACM Bunayd a ranar da ya tabbatar da su Banafsha sun gama musabaƙan nasu, a ranar ya je ɗaukanta, wayan Malaminnasu ya ƙira, ya faɗa masa in da suke a masauƙinsu, yana zuwa Malamin ya zo suka gaisa, ACM ba ɓoyel-ɓoyel ya faɗa ma Malamin ya zo ɗaukan ƙanwarsa ne.

Malamin ya ce, “Muna jiran sakamako zuwa gobe, da an bar ta tukunna.”

ACM uzurinsa ya kawo na buƙatar tafiyansu, dan dole Malamin ya ƙira Banafsha ta fito suka tafi, ita kuwa tun da ta fito take haɗe rai, take harare-harare, ACM ko kallo bata ishe sa ba, bai bar ta sun yi sallama da su Umaima ba, ya sa driver ya ja mota sai airport, komai ya kammala jirginsu ya ɗaga sai Kano, driver kuma ya kama nasa hanyan komawa da mota.

A jirgi ACM ko nuna yasan wata Banafsha bai yi ba, kuma ita ma a nata ɓangaren haka ne, duk haushin juna suke ji, jirginsu na sauƙa driver ya zo ya ɗauke su, a bakin gate na gidan Alhaji ya sa drivern ya staya, ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce, “Fita mini a mota.”

Banafshan buɗe motan tayi ta fice tare da juyowa ta aika masa da harara, ta ce, “akwalan motanka na banza da wofi, mtswwwwwww!”, Ta ja dogon tsaki tare da yin gaba abin ta.”

ACM wani irin zuciya ne ya hauro masa har wuya, ai bai san lokacin da ya buɗe murfin motan ya fice ba, taku ɗaya biyu har ya iso in ta, amma kamun ya kai hannu da niyan damƙo ta, tuni ta ari na kare ta shige gidan ta bugo ƙofan da ƙarfi.

Ƙwafa yayi ya juya rai a ɓace, ya kulle ƙofan da ta bari a buɗe ya shige ya zauna, yana ta jan staki shi kaɗai, lallai dole ya takawa yarinyar nan birki da maganan ja masa staki, zai yi maganinta Allah kuma haɗa su.

Banafsha kuwa da mugun gudu ta shiga gidan kaman za ta ci da baki, sai da ta ji ba sawun ƙafansa sannan ta staya tana mai da numfashi, hararan hanyan tayi ta ce, “Kuma wallahi za ka san ka yi da Faɗima, Danish ma bai share ba balle kai suɗin bayan ludayi.”

ACM gidansa ya wuce ran sa a mugun ɓace, yana isa ƙiran General na shigowa, faɗa General ya masa na kulle wayansa da yayi kwana biyu, amma ya basa haƙuri ya faɗa masa sun dawo ɗazu ma, shi ma gobe zai wuce Lagos ɗin, General ya ce a’a yayi zamansa shi zai shigo anjima, dan gobe za su wuce Sokoto dukkansu, ACM kaman ya stala ihu dan taƙaici, haka ya amsa kawai suka yi sallama.

Banafsha kuwa tana shiga da Majeeder ta fara karo, ai da mugun stalle ta rungumeta tana faɗin, “Banafshata ta dawo, ta dawo, ta dawo, mutanen Abuja sannunku da hanya.”

Murmushi kawai Banafsha ta sakar mata ta amsa sannun, sai ga Mami da Mama Hadiza sun iso su ma suna masu sakar mata murmushi, Banafsha da sauri ta je ta rungume Maminta, sai kuma ta saka kuka.

Mama Hadiza ta ce, “Jarababbiya ja’ira ta dawo kuma, kukan me kike.”

Mami ta ce, “Bana son halinkinnan fa Banafsha na shagwaɓa da girmanki, ba ga shi kun je lafiya kun dawo lafiya ba, kuma muna kallon karatun naku ai a TV, sannunku da ƙoƙari Allah yayi muku albarka.”

Banafsha sai da Mami ta rarrasheta sannan tayi shiru, tana ta tura baki na surutun da Mama Hadiza ke mata.

Sai da Banafsha ta huta sannan Mami ta zo tana tambayanta, lafiya ta ga ta rame, Banafsha kuka ta sanya wai ai bata da lafiya ne, ciwo tayi.

Mami ta ce, “Ba kin ga mastalana da ke ba, yanzu daga tambaya sai kuka.”

Cunna baki Banafsha tayi ta ce, “Uhmn! Mami to ba ulcer na ne ya tashi ba, kuma Allah duk wannan mugun ne.”

Kamun ta rufe baki Mami ta kawo hannu za ta buge bakin nata, amma sai ta kauce tana ƙara tura bakin.

Ƙwafa Mami tayi ta ce, “Inƙara ji kin ce masa mugu ki ga abin da zan miki, da ya kai ki har ya jira kuka dawo tare, wato bai burge ki ba, ke baki san an miki kirki ba, to ki sake ki faɗa wa Alhaji wani abu, ki ga yan da za mu yi da ke a gidan nan.”

Banafsha kuka ta saka tana faɗin, “Ni dai wallahi Mami kin daina so na, shikkenan yanzu yaron wasu kike so ba kya son ƴar ki.”

Miƙewa Mami tayi ta ce, “idan kin gama rashin jin naki, sai ki zo ki amshi magani ki kuma kwanta ki huta, dan gobe In sha Allah za mu wuce Sokoto, daman ku muke jira ku dawo, kuma kun dawo lafiya alhamdulillah”, Mami na gama magana ta fice.

Banafsha kuwa gaba ɗaya jikinta sanyi yayi jin batun zuwa Sokoto gobe, kwanciya tayi kawai tana addu’an Allah ya sa su ji alkairi.

General ƙiran Papi yayi suka yi magana, akan yana hanya tun da su Faɗima sun dawo, sai a wuce Sokoto goben kaman yan da aka yanke, Alhaji ya amsa da Allah ya kawo sa lafiya.

Sai da General ya iso sannan suka dawo gida tare da Papi, tambayan Mami suka yi ina Faɗima, ta tura Majeeder ta dubo ta, Majeeder ta samu tana bacci, da ta dawo ta faɗa wa su Papi, sai suka ce to a ƙyaleta tayi baccinta, ta huce gajiya.

Washe-gari da wuri duk suka shirya, Alhaji ya faɗa wa General ya ƙira yaronsa ya zo da wuri, ko su wuce su ƙyalesa, General dai murmushi yayi yana faɗin, “Bansan me kuma yarona yayi ba yaya, amma ayi haƙuri, yanzun nan zai iso, daman a shirye ya kwana.”

Ƙwafa Papi yayi ya ce, “Ya fi muku, kuma idan Bunayd bai fita idona ba sai nayi mugun saɓa masa.”

General dai haƙuri ya bai wa Papi, suna nan ba jimawa sai ga ACM Bunayd ya sha shirinsa, kaman mai zuwa gasan nuna wanka, tun da ya gaishe da Papi ya amsa fiska a haɗe, sai ya kama bakinsa, General ma ya amsa gaisuwan yaron nasa da fara’a yana faɗin, “Sannunku da hanya mutanan Abuja.”

Amsawa ACM yayi sannan ya haura sama sashin Mami, sai da yayi sallama ta masa izinin shiga sannan ya shiga, tana murmushi suka gaisa ta ce, “Sannunka da ƙoƙari yaron Mami, Allah yayi albarka angode sosai.”

Kan da a ƙasa ya ce, “Bakomai Mami yi wa kai ne.”

Banafsha da fitowanta daga ɗakin Mami kenan, tana faɗin, “Mami na ɗauko mu tafi, su Papi na jiranmu”, ganin wan da ke palourn sai ta haɗe fiska tare da wucewa za ta fita.

Mami girgiza kai tayi, ganin abin da Banafshan tayi, fiska a haɗe ta ce, “Ba ki ga yayanku ba ne?”

Cunna baki tayi, tare da bubbuga ƙafa, ACM kuwa kan sa a ƙasa amma yana satan kallon abin da take yi, murmushin gefen leɓe yayi, domin shi Mami bata burgesa ba da ta stayar da fitsararriyan, da ta ƙyaleta yayi abin da yayi niya.

Mami ta ce, “Faɗima.”

Bunayd murmushin yaƙe yayi ya ce, “Lah! Mami bakomai fa, ina ga bata kalleni ba ne, Ƙanwata sannunki ya gajiyan hanya?”, Ya faɗa tare da fakan idon Mami ya aikawa Banafsha wani mugun kallo.

Banafsha ƙara haɗe fiska tayi, dan staf ta ga kallon da ya mata, kuma tasan maganan na munafurci ne kada Mami ta ce yana mata mugunta, bakin nan a ture ta ce, “Sannu, gajiya alhamdulillah”, ta faɗa tare da yin gaba za ta fita abin ta.

Sai da Banafsha ta zo dai-dai wajan Bunayd, sannan ta ja staki, shi kuwa yi yayi kaman bai ji ta ba, sai da ya kuma fakan idon Mami sannan ya sanya mata ƙafa, kamun ka ce me, ji kake tiffff!, Banafsha ta sha ƙasa, shi kuwa kan sa a ƙasa kaman bai san abin da ke faruwa ba.

Banafsha ƴar ƙara ta saki, take idanuwanta suka kawo ƙwalla, za ta buɗe baki tayi magana, sai Mami da ta sake baki kallon Banafshan ta ce, “Tashi ki fice kamun na ƙara miki.”

Miƙewa Banafsha tayi ta fice kaman za ta fire sama, ga duka ga stinka jaka, a zuciyanta ta dinga ja masa Allah ya isa.

Mami ƙwafa tayi ta ce, “Allah ya shirye ki Faɗima, yaron Mami kayi haƙuri da halin ƙanwar taka.”

Murmushi Bunayd yayi, kai a ƙasa ya ce, “Bakomai Mami, yaranta ce sai a hankali”, ya faɗa yana miƙe wa.

Mamin ma miƙewa tayi ta ce, “To sai na fito ko.”

Bunayd ya amsa ya fice, yana fitowa ya tamke fiska kaman ba shi ya gama murmushi ba, hannayensa a cikin aljihunsu ya iso palourn, Mama Hadiza ya gaisar cikin girmamawa, ta amsa ita ma tana masa sannu da gajiyan hanyan Abuja.

Mami sai da ta gama abin da za ta yi sannan ta fito, da yake ita kawai ake jira, tana fitowa suka ja ƙofa suka fice a sashin dukkansu, mota ɗaya Mami, Mama Hadiza, Majeeder da Banafsha, driver na jan su, sai ɗaya motan kuma Alhaji Mukhtar, General Sufyan da ɗan gidan General, su ma driver na jan su.

Airport suka nufa, ba jimawa jirginsu ya ɗaga, awanni biyu da rabi ya kai su garin Sokoto birnin Shehu, suna sauƙa General daman ya riga yayi magana da abokanan aikinsa da ke nan, Manyan sojojin da ke Sokoto an turo musu motoci guda uku, nan suka shige aka yi Masarautar Sokoto da su.

Tun da aka iso Sokoto yanayin Mami ya sauya, gaba ɗaya Mami ji take ma kaman ta koma, bata san yanzu kuma da wani ido Mai martaba zai kalleta ba, zai amshe ta a matsayin ƴar sa ko har yanzu yana fushi da ita, ya yafe mata ko kuwa idan ya ji labarin rayuwar da tayi, zai ƙara tsananta ya koreta ne, zuwan nan zai zama sanadin sanin asalin mahaifin Faɗima ka yaya? “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, allahumma ajjirni fi musibatin wa aklifni khairan min ha, la’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mini-zzalimin”, waɗannan kalmamo su kawai Mami ke maimaita wa, har motansa ya tsaya a babban ƙofan mashigan masarautan.

Sakamakon sauyin rayuwa da aka samu, da kuma ƙarin wayewancewa na zamani, to masarauta ta sauya ba kaɗan ba, ganin yan yanayin masarautan ta koma sai da Mami tayi ƙwalla, domin canjin da aka samu kaɗai ya isa ya sanar da ita ta jima rabonta da mahaifar ta, share hawayenta tayi, tana addu’an Allah kawo komai cikin sauƙi, Allah kyautata gamon ta da mahaifinta.

Masu staron sai da suka bincike su sannan aka bari suka shiga, masarautan Sokoto akwai girma, kasancewansa masarauta ta musulunci, to yana daga cikin masarautun da ake ji da su a faɗin Nigeria.

Motansa suka ja har wajan da ya kamata, suka perker su sannan suka fiffito, shi dai ACM mamaki ne cike a cikinsa, na me dalilinsu na zuwa Sokoto kuma dai masarautan Sokoto, haka ma Majeeder mamaki kawai take yi, Banafsha kuwa zuciyanta tuni ya karye, dan bata san yanzu kuma wani abun da zai ɗaga mata hankalin za ta ji ba, addu’a take Allah sa asalinta ya zama mai kyau ne, Allah sa masu jifanta da munanan magana su kunyata.

Ba-fade ne ya iso su, suka gaisa General ya masa bayani, sannan ya wuce fada ya sanar da zuwan su, aka umurce sa da ya shigo da su, ya koma ya musu iso.

ACM da ya gaji da stayuwa, duk haushin tafiyan ne ma ya ƙara cika shi, lokacin da aka musu iso, shi kuma daman ya koma cikin mota yayi zamansa, magana General ya mishi akan su isa, amma ya ce ya biyo bayansu, haka suka bi bayan ba-faden suka yi tafiyansu, Banafsha sai harara take aikawa motan kaman yana kallonta.

Da sallama suka shiga fadan, wani stoho cukuf ne a kishingiɗe, ya stufa sosai, fiskansa ya tattare har kaman idanuwansa a kulle, ga furfura har gashin idonsa har giransa, amma duk da stufansa hakan ba zai hana ka ganin kyawunsa ba, domin Mami ta gado Mai martaba da Ummanta duka a kyau.

Amsa musu sallaman aka yi, duk suka zauna, General da Papi duka cikin girmamawa suka gaishe da Mai martaba suka kuma gaishe da waɗanda suka samu tare da shi, bayan sun amsa, Mama Hadiza ma ta ɗaga musu gaisuwa, Mami bakinta na rawa ta mosta leɓenta, kamun ta fara magana tuni kuka ya ƙwace mata, cikin kukan ta ce, “Baa..baaaaa”, iya abin da ya fita daga bakinta kawai kenan kuka mai stanani ya ƙwace mata.

Mai martaba daga kishingiɗen ya gyara ya zauna tare da faɗin, “Ramlatu ke ce?”

Cikin kuka Mami ta shiga jijjiga kai alaman eh.

Mai martaba jinjina kai yayi ya ce, “Allahu Akbar, Allah mai girma, Allah maji roƙon bayinsa, Ramlatu ke ɗin ce dai ba wata ba?” Ai kawai sai ga hawaye a idanuwan mai martaba, daurewa yayi tare da yiwa ba-faden nan magana akan ya shigar da su ciki a yiwa matan gidan magana Gimbiya Ramlatu ce ta dawo.

Mutanen da ke zaune tare da Mai martaba duk sai kabbara suke na ikon Allah, bayan stawon shekaru ga yarinyar Sarki ta dawo.

*****

<< Yar Karuwa 24Yar Karuwa 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×