Skip to content
Part 27 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

General yana mai kallon Mama Suwaiba ba ko gifatawa ya ce, “Mama dan Allah ki amsa mini, nine baban Faɗima? Kina nufin ki ce Faɗima yarinya ta ce?”

Mama Suwaiba ta buɗe baki da niyan yin magana, sai harshen ta ya naɗe ba daman cewa komai, ta girgiza kai shi ma ya ƙame ba daman mostawa, jikinta kam daman ya jima da tashuwa aiki, sai kawai da ido take kallon kowa tana hawaye, ga ta da rai amma ta sanƙare ba daman yin ko da mosti ne.

Adda Habiba ce ta fashe da kuka sosai, ta ce, “Kai ne mahaifin Faɗima, halak malak, amma ku yafe mu da muka zama sanadin samuwanta ba ta aure ba.”

Banafsha da ta zama mutum-mutumi, kai ba za ka ce ga in da take kallo ba, ko ga abin da take tunani, tun da Mama Suwaiba ta gama labari, shikkenan Banafsha ta fara sumbatu, tun tana faɗa a hankali iya wuyanta, har ya fito fili, sautinsa ya karaɗe palourn, faɗi take ta maimaita, “Ta tabbata ba da aure aka haife ni ba, ta tabbata ban da uba, ƴar karuwa ƴar shege, ni ƴar kamun fatiha ce…”, Abin da Banafsha ke ta maimaitawa kenan, hawaye na bin fiskanta.

Duk wanda ya ji zancen Banafsha a palourn, ba wan da bai tausaya mata ba, domin mayar da maganan tayi kaman bitan karatu, Mami kuka kawai take yi, ta rasa ma me za ta fara faɗa, tabbas duk da ba da son su bane, amma sun ɗauki alhaƙin Banafsha, ga ba’a sameta ta hanyan da ya dace ba, kuma ga rayuwan da taje tayi wan da ya zamo wa ƴar ta tabo, har ake ƙiranta da sunan ƳAR KARUWA, a hankali cikin muryan kuka ta ce, “Ki yafe mana Banafsha.”

General ya rasa wani yanayi ɗaya yake ciki, farin ciki ne zai yi ko baƙin ciki, amma dai abu guda ya sani shi ne yana mai godiya ga Allah, a fili ya furta, “Alhamdulillah ala kulli haleen, Allah ya miki albarka Faɗima, Allah ya shiryaki kuma.”

Alhaji Mukhtar da ke gefensa, ya ce “Ameen ya Hayyu ya Qayyum”, ya faɗa, sai dai shi sam-sam babu damuwan komai a zuciyarsa, indai akan ƙaddaran Mami da General ne, abin da bai masa daɗi ba shi ne jin abubuwan da suka faru, amma kuma wannan ma sai dai addu’an Allah yafe mu duka, waɗanda suka riga mu gidan gaskiya kuma daman lokacinsu ne yayi, Allah ya musu Rahama.

A ɓangaren ACM kuwa abubuwan da suka faru ne basu masa daɗi ba, amma idan ba haka ba shi bai ga wani abun kuka ko damuwa dan haifeka ba da aure ba, ai ba laifinka bane, Allah ne ya so hakan, da mutum ke zaɓa wa kan sa ƙaddara, ai da kowa mai kuɗi mai mulki da jin daɗi zai fito, shi a wajansa hakan normal ne, ko Mami da General bai ga lafinsu ba, ko da ace suna hayyacinsu ne ai soyayya ce, sai aka samu tangarɗa ciki ya shiga, amma kuma basa hayyacinsu ba su da wani laifi kwata-kwata, sai dai a ce Allah kare na gaba.

Mama Hadiza ita ta jawo Mami jikinta, ta din ga bata baki, tana rarrashinta.

Ita kuma Banafsha General ne ya sa ƴar sa a jikinsa, yana shafa bayanta alaman rarrashi, yana faɗin tayi haƙuri tayi shiru.

Bunayd ganin abin da Banafsha ke yi, sai taɓe baki yayi, irin kayan amai zuciya yaƙi tashin nan, dan shi bai ga wani abin da za’a wa kuka a nan ba, iyayi ke damunta da samun waje, shi haushinshi ɗaya ma, da aka ce General ne babanta, ina laifin a ce shi Papi shi ne babanta, amma wai General, yanzu kenan za ta koma Lagos da zama, lallai ya daina zuwa gidan General tun da abin haka zai zama.

Mai martaba tun da yayi shiru yana sauraran labari bai kuma cewa komai ba, har komai ya ɗan lafa na koke-koken nasu, sannan yayi gyaran murya ya ce, “Alhamdulillah ala kulli halin, duk da abu bai yi daɗi ba, ba yan da aka so ya zo ba, to ya zama dole mu godewa Allahn da ya ƙaddaro hakan, Sarki gwani gagara misali, a daɗi da rashin daɗi godiya a gare sa wajibi ne, domin komai ya same mu a wajansa hakan ne alkairi, kuma ko muma idan za mu cire son zuciyanmu mu duba to mun san alkairin ne, duk rashin daɗinsa za mu ga zai yi silar faruwan wani abu mai daɗi, da zai zama sanadin mantar da mu wannan rashin daɗin, Ramlatu da Sufyan da kuma ƴar ku Faɗima ina mai matuƙar baku haƙuri, ƙaddara ce ta rayuwa tana da sababai da yawa, ba ta in da Allah ba ya jarabtar bawansa, kuma wannan abu izinane ga masu ƙetare iyakar dokar Allah, mutanen da idan abu ya dame su ba za su kai wa Allah kukansu ba, sai su wuce wajan wani halittan Allah wai shi zai biya musu buƙata, bayan shi ɗin ma Allah ke biya masa, wataƙila ma idan aka bincika sun fi shi imani, kuma addu’ansu ya fi nasa saurin karɓuwa a wajan Allah, to zamani ne ya zo sai sai a ce Ƙalu innalillahi wa inna ilaihirraji’un!, Domin wannan abu a yau ba iya mata ba har mazan ma, akan abu ƙalilan sai ka ga mutane na shirka wa Allah, wan da kuma duk mun sani shirka na daga cikin manyan kaba’ir, mafi girman laifin da ake yiwa Allah yaƙi yafiya idan ba’a tuba akan lokaci ba to shi ne shirka, akan sana’a, akan karatu, akan neman aure, akan biyan mutum haƙkinsa, akan abota, kai hatta akan adashe wannan wasu na saɓa wa Allah, wai a kame musu bakin mutum, to mu dai ba abin da za mu ce sai Allah ya kyauta ya kuma shirya mu ya shirya mana zuri’a.”

“Abu na gaba kuma da nake so ku sani, wan da zan yi maganan da ita Faɗima ne da kuma ire-irenta, masu tunanin su ƴaƴan da ba da aure aka haife su ba ne, sai ka ga yara wasu saboda wannan dalilin su ma sun faɗa harkan banza, daga nan kuma sai ɓarna ya yawaita su ma su samar da wasu, to ina so duk wata irin Faɗima ko iyayen Faɗima su sani, a zamanin yau, babban abin da ta addabe mu kuma ta dami rayuwarmu, wacce take daga cikin alamomin ƙarshen duniya, ita ce zina da kuma yawaitan ƴaƴan da ba da aure aka haife su ba, a nan kuma mutane sukan fassara hakan ne da ana nufi da iya zawarawa ko ƴammata da basu da aure, su ke zina ko su ke haifan yara ba da aure ba, to ina so mu sani dan mu kiyaye, abu uku da ba’a wasa da su inji Manzon Allah SAW su ne :- aure, sakin aure, mayar da aure(kome), wannan ba’a wasa da su, to shi sakin aure a cikin kalamanmu ma namiji na sakin matarsa ba tare da saninsa ba, jahilai marassa ilimi ba su gane hakan, masu ilimin kuma sun sani suna takewa, namiji ne zai yi wani furci da ya zama saki ga matarsa, sai ya zo ya tara da ita har a samu ciki ta haihu, musamman idan a ce wajan da shika ɗaya ya rage aure ya ɓaci, kun ga kuwa ai wannan ɗa yana fake ne da aure, amma a asalin zahiri shi ba ɗan halak ba ne, to wannan zamani da muke ciki wannan mastaloli sun yawaita, kuma shi ne yawaitan shegu da ake faɗa, dan Allah jama’a al’umman Annabi SAW mu kiyaye, haifan ƴaƴan shegu a gidan aure a yau shi ya fi komai yawa da kuma sauƙi, sannan kuma a hakan ma akwai matan da suke bin wasu mazaje a waje da aurensu, mace ta yi cikin wani ta haifa da sunan ƴar mijin da take aure, wannan annabo ma ta yawaita, domin a wasu wuraren idan ka je sai ka samu matan aurena sun fi yin zina da kuma haifan yara ba ta hanyan da ya kamata ba, fiye da budurwaye ko zawarawa, dan Allah da Manzonsa al’umman Annabi a kiyaye, mastalolin suna da yawa ire-iren haka, har da wan da ban ambata ba, mu dai al’umma mu ji storon Allah mu gyara, domin manufar wannan labari kacokan kenan dan irin wannan masifa da annabo da ake ciki, na zina da kuma haihuwa ba ta hanyar da ya kamata ba.”

“Sai kuma ga irin yaran da ake haifa ta wannan hanya, abu guda da za su duba shi ne, ko wani bawa fa yana tafiya ne akan hanya da ƙaddaran da Allah ya rubuto masa, kada ki ce anhaife ki kaza, ana ƙyamar ki, ke kaza ke kaza, a’a rungume ƙaddaranki ki ji storon Allah, domin idan ɗan shege ya ji storon Allah ya riƙe kansa, to wallahi wasun su sun fi waɗanda aka haifa da aure komawa ga Allah, dama tun can tun fil’azal Allah ya rubuta ba da aure za’a haifeki/ka ba, dan haka sai ka yi haƙuri kai kuma kayi ƙoƙari ka ga ka ji storon Allahnka, domin kai/ke sam-sam ba ku da laifi a kan hakan, ba ku kuka yi kuka kawo kanku duniya ba, yi aka yi aka kawo ku ta haka, duk wani alhaƙi na kan iyayenku, dan Allah ku ma ina mai jan hankalinku da nusar da ku hakan, kada maganan wani ƙyarar wani ko kyamar wani ya sa ku saɓa wa Allah ku ma, a ko wanni hali ka samu kan ka sai ka godewa Allah, sai ka sha mamakin sakamakon da za ka samu na godiyan da ka yi da amsan ƙaddaranka hannu bibbiyu.”

“Al’umman Annabi, in da abun ta ke kuma in da gizo ke saƙar, mutane su ke jefa kan su da ƴan uwansu cikin halaka, dan an haifi wani ba da aure ba ina ruwanka/ki? Kai ma baka wuce haka ba, kaman yan da wannan bai wuce jarabawan Ubangiji ba to kai ma baka fi ƙarfin hakan ba, baka wuce hakan ta same ka ba ko ta faru da kai, idan kun hantare su kun ƙyamace su ribar me kuke samu? Ƙarshe tare da naku zuri’an suke lalacewa, sannan fa akwai abu guda tun asali, muddin kana jifan mutum da magana, ko da kuwa ya aikata ko kuma bai aikata ba, to ka sani kai ma ba za ka gushe ba har sai Allah ya ɗaura maka wannan abun da kake jifan wani da shi, hadisi ne guda mai inganci ya kawo haka daga bakin da baya ƙarya, idan ka ga mutum ba za ka iya faɗan alkairi ba to ka yi shiru, domin musamman akan zina ita bashi ce, idan mutum ya aikata to wallahi ƙaranci a faɗan malamai shi ne a samu mutum goma a zuri’arsa da Allah zai kama su da bashin da wanin su ya ci, kuma fa a hakan ko da ya tuba ne, to a ce mutum ɗaya haka, wannan mutane goman ma kuma a ce ko wanne mutum ɗaya ko ya tuba sai mutane goma sun biya wannan bashin, me kuke tunani na irin masifar da za ta auku ga zuri’a? Mu kiyaye bayin Allah.”

“Sufyan da kuma Ramlatu, ba ku da alhaƙi tun da ba’a hayyacinku kuka aikata ba, amma fa ku sani sai kun tuba wa Allah, sannan idan son samu ne ku kai kan ku a muku hukuncin hakan, domin ku ƙara starkake kan ku daga kamungar Allah, sannan Faɗima ina mai alfahari da ke, musamman yan da kika zama a rayuwa, wannan ma babbar izina ce ga maƙullata sharrinku, Alhamdulillah, ina mai fatan za ki amshi ƙaddaranki kuma kada ki damu da wasu mutane can a gefe, domin da yawa mutane sai sun take laifinsu suke hango na wani, tun da daman shi laifi tudu ne tsani ne, dan an fasa aurenki akan wannan dalili kada ki tashi hankalinki, Allah ne bai ƙaddara aurenku ba tun asali, sannan ina da tabbacin za ki samu wan da ya fi shi, misali ma ga ni ɗan saurayi da ni, mastashi mai ji da samartaka, ga ilimi ga kuɗi da mulki ga kyau, ko ban miki ba?” Mai martaba ya ƙarishe zancen yana kallon Banafsha.

Banafsha da ke jikin General, tuni dariya ya ƙwace mata bata sani ba, Mama Hadiza ma darawa tayi, Alhaji da General da ɗan gidan General duk murmusawa suka yi, hatta Mami da ke kan kuka sai da ta murmusa, haka ma su Adda Habiba, Mama Hadiza ta ce, “Amman kam tana da kai Sarki guda me za ta yi da wani can jinjiri da shi.”

Murmushi Banafsha tayi, a hankali ta ce, “Sai dai idan ni ce zan zama sarkin.”

Mai martaba murmushi yayi cikin samun nistuwa, na damuwan jikarsa da ya tafi ya ce, “Ai daman sarautan naki ne, ba ki ga duk iya rikici babu kowa ba sai ke sai mahaifiyarki, ga shi nima na ƙi mutuwa saboda kada a bai wa wasu har sai da kika iso, takawanki lafiya Sarauniya sarkiya.”

Ƴar dariya Banafsha tayi har sai da fararen haƙoranta suka bayyana rass da su, Masha Allah, mai kyau ko kuka take kyau take yi, balle kuma ta gama kukanta.

Mai martaba ajiyan zuciya ya sauƙe tare da mayar da dubansa kan su Mama Suwaiba, ya girgiza kai tare da faɗin, “Yanzu wa gari ta waya? Ai ko ba’a ce muku komai ba to kukan kurciya jawabi ne, duk da dai sai mai hankali ke kula, ni ba abin da zan ce muku, cutarwa ne kun cuceni, kun cuci zuri’a ta, amma ba komai Allah ya yafe mu duka, tun da dai Allah ya taimake ni ban haɗa zuri’a da ku ba balle ku bar mini baƙin tabo a zuri’a to alhamdulillah, Allah ya kyauta, na yafe muku, sai ku nemi yafiyar asalin waɗanda kuka yi wa laifi.”

Kamun su Umma Talatu su yi magana, tuni Mami ta tari numfashinsu, share hawayenta tayi, muryanta na rawa ta ce, “Nima na yafe ku duniya da lahira Umma, Mama da Adda, Allah ya yafe mu duka, komai ya wuce, insha’Allah Ummata da ƙannena duk ba komai, domin Annabi ya ce ka kasance mai yafiya, idan ka yafe wa wani kai ma sai Allah ya dube ka akan wani laifin naka ya maka rangwami ya yafe maka, kuma ba wan da yafi ƙarfin yin laifi a wajan Allah, dan dai kawai shi gafurur-rahim ne.”

Mami na rufe baki General shi ma ya amsa, ya ce, “Nima na yafe muku, Allah ya yafe mu duka.”

Banafsha murmushi tayi ta ce, “Nima na yafe muku kakanai na kishiyoyi na, ba ruwana da amaryan Mai martaba dan storo ta ji ta mutu tun da wuri ta gudu ta bar mini fili, kun ga ni ce amaryanku yanzu ta huɗunku”, Banafsha ta faɗa tana juya ido.

Duk abin da take akan idon Bunayd, murmushin gefen baki kawai yayi ya ce a ransa, “Wannan fitsararriyan ma A ce, na ɗauka za ta cigaba da shirmenta ne, ashe tana da ɗan hankali da tunani, sai dai duk da haka akwai notirin da ya kunce a kan ta, dole ma ni zan ɗaure mata shi da kyau.”

Alhaji Mukhtar ma murmushi yayi ya ce, “Masha Allah! Alhamdulillah Allah ya yafe mu duka.”

Duk palourn aka amsa da Ameen.

Mai martaba yayi nasiha sosai-sosai, har aka ɗan taɓa hira, amma ban da Mama Suwaiba da ke sanƙare waje guda.

General ne yayi gyaran murya ya ce, “Rankashidaɗe ina da magana idan ba damuwa.”

Mai martaba yana murmushi ya ce, “Muna sauraranka baban Faɗima.”

Murmushin jin daɗi General yayi, domin sunan ya masa daɗi, kuma hakan na nuni da ƴar sa ba shegiya ba ce, tana da uban ta, domin yaran da ba’a san taƙamamman ubansu ba su ke amsa wannan sunan, cikin nistuwa General ya fara koro bayani, “Am da farko dai ina mai baku haƙuri da shawara da kuma hukuncin da na yanke ba tare da shawari da kowa ba, kuma ina addu’a da fatan hakan yayi muku domin zan yi farin ciki sosai, kuma ina neman afuwan yaran nawa da hukuncin da na yanke ina mai tunanin ina da cikakken iko da su, kuma ba zan yanke musu abin da zai cutar da su a rayuwarsu ba, tun farkon fari da na ɗaura idanuwana akan Faɗima na ji ina ƙaunarta fiye da yan da nake ƙaunar su Suhail, bansan manufan hakan ba dan da farko na ɗauka, saboda nistuwanta da hankalinta da kuma tarbiyyanta ne, musamman da ta kasance ƴa ga wacce na so a baya, kuma ƴa ga yayana, ashe da ikon Allah nine mahaifinta, abin ya mini daɗi sosai Alhamdulillah, tun farko na kwaɗaitu da nemawa yarona Bunayd aurenta, amma kuma sai nayi shiru, duba da halin da ake ciki musamman ita, na fasa aurenta da aka yi, da kuma sarƙaƙiya da ake ciki, amma tun da yanzu alhamdulillah komai ya fito ya warware, to ina mai nemawa yarona Bunayd aurenta, sannan kuma dai na bai wa yarona Bunayd auren yarinyata Faɗima, na basa ita halak malak, kuma a yau nake so a ɗaura auren, wannan shi ne burina na ƙarshe a yanzu, kuma burina da ya fi ko wanne, wan da zai samar mini da nistuwa ko da na faɗi na mutu a yanzu ne.”

Idan ka cire Faɗima da Bunayd to babu wan da bai washe baki ba a palourn, wan da hakan ke nuni da lamarin duk ya ƙayatar da su, sai ma ka rasa dai waye ya fi wani farinciki, musamman stakanin Mami, Alhaji Mukhtar, Mai martaba, Mama Hadiza da kuma shi uban gayyan General.

Mai martaba yana washe baki ya ce,”Kai Masha Allah! Alhamdulillah abu yayi kyau ba kaɗan ba, abu yayi daɗi sosai, wannan haɗi ba wan da ba zai yi alfahari da shi ba Insha Allah, ashe dai daman an taho ne tare da abokin takara na, zuwa yayi har gabana ya ɗauke mini amarya, naga samu naga rashi, to sai ya biya kuɗin ƙiyayyanta.”

Alhaji Mukhtar ma murmushi yayi, domin ji yake kaman ya saka ƙanin nasa a baya su din ga zagaye Sokoto, wannan abu shi ne abu mafi daɗi da ƙaninsa ya masa a rayuwa, ko riƙe Bunayd da komai bai kai masa wannan daɗi ba, ya jima yana burin aurawa Bunayd wannan yarinya Faɗima, tun bata yi wayo ba har ta girma, sai kuma gashi cikin ikon Allah jininsu ce ita, kuma maganan aure har ya dai-daitu.

ACM Bunayd dai ba za ka ce ga yanayin da yake ciki ba, domin shiru yayi kaman wan da ruwa ya cinye shi, ya rasa ma mai zai tuna ko mai zai ce, bai isa ya musawa General ba, Papi zai iya saka sa yin abu ya kawo uzuri ko ya ce baya so, amma ba zai taɓa iya yiwa General wannan butulcin ba musamman da ta kasance ƴar General ɗin ce, da ma ace lokacin da ba’a san hakan bane to zai iya musawa, shi sai yanzu ma ya ji kunyan ƙiran General da yayi ya ce ya fasa kai ta Abuja, ai ko bai mata abu dan halinta ba zai mata dan General, ba abin da ba zai yi saboda farincikin General ba muddin bai saɓa wa Addini ba, yan da ya ɗau General kuma yake jin sa a rai ko Papi baya jin sa haka.

Banafsha kuwa a nata ɓangaren ji take kaman ta kwasa a guje kada a samo ta, tana farinciki za’a lalata mata farincikin, a rasa wa za’a ce ta aura sai wannan mara mutunci da kirkin, mutumin da Sam bai da Imani, bai san Imani ba bai san in da ya bi ba, ita ba za ta musa wa mahaifinta ba, amma idan ya kuskura ya aure ta zai san ya aurowa kan sa ƙaddaransa da damuwansa, sannan kuma ba ɓoyel-ɓoyel za ta faɗa wa Mami gaskiya, kada a cuci bawan Allah bata son sa bata ƙaunarsa, ita da ta aure sa ai ta gwammace ta auri Ya Danish, indai aurar da ita ake son yi kawai a aura mata Danish.

General kallon Bunayd yayi, dan ya fahimci abin da ke zuciyarsa, tun da an ce labarin zuciya a tambayi fiska, amma sai ya ga Bunayd ya sakar masa stadadden murmushinsa, hamdala yayi dan daman damuwansa kenan, yasan Faɗima ba ta da mastala, kuma ko da ya juya gare ta, ita ma fiskanta normal ya kallesa, da suka haɗa ido ma ƙasa tayi da kan ta, alaman ta ji kunya, sai kawai ya saki murmushi, sannan ya ce, “Rankashidaɗe sai ka wakilci amaryanka, ni kuma na wakilci yarona, a sa lokacin yau dai kamun mu koma.”

Mai martaba ya ce, “Ina ga a bari daga nan zuwa juma’a zai fi, idan muna da tsawon rai da lafiya, yau talata ne, kaga kwana biyu ne kawai stakani.”

General ba dan ya so ba ya amsa cikin biyayya, ya ce, “To Allah kai mu da rai da lafiya.”

Nan taro ya waste, su Mami suka koma ciki.

Wuni suka yi a masarautar, daga ranan kuma aka fara shirye-shiryen ɗaurin aure, amma General da Papi washe-gari suka koma sai ranan ɗaurin auren za su dawo, ACM Bunayd kuma Mai martaba ya hanasa tafiya dole yana nan, sai Alhamis zai wuce Lagos ranan juma’an su dawo tare da su General.

Adda Habiba da Umma Talatu duk sun ƙara yafan juna da Mami, yanzu dole su amshi abin da yake dole, dan haka gyara yarinyar su suke yi, da kuma jikar su(kunsan aikin hannun sakkwatawa ba wasa, idan suka yi wani abun sai namiji ya mance sunan sa, uwar batoorl na yin ku sakkwatawa.)

Banafsha ganin Mami bata mata magana ba, sai ma wasu abubuwa da ake tultula mata ake kuma turarata da su, kaman na lokacin auren Malam Abbo har ma sun fi su, dan haka da kan ta taje wajan Mami ta same ta da maganan, Banafsha ta ce, “Mami magana nake so muyi ayya.”

“Ina sauraranki Banafsha ya aka yi?”, Faɗin Mami da ta tattara hankalinta gaba ɗaya ta mayar kan gudalliyanta.

Banafsha cunna baki tayi, tare da yin rau-rau da idanuwanta ta ce, “Mami ni fa Allah bana son sa bai da mutunci, ki ce a fasa auren, ni gwanda na auri Ya Danish ma akan na aure shi.”

Wani irin kallo Mami ta aika mata da shi tare da faɗin, “Ke ɗin mutuncin ne da ke? Ko an faɗa miki bansan rashin kunyan da kike masa ba ne? To ba wani auren da za’a fasa, ni nafi kowa farinciki ma da wannan magana, domin nasan Insha Allah watan shiryuwanki ne ya kama, ɗan albarka zai gyara mini ke ki daina wannan rashin jin, da kike cewa kuma gwanda ki auri Danish akan ki aure sa, to za ki iya zuwa ki samu baban naku ke da shi, ki fada masa ke bakya son yayanki kuma yaronsa, ina mai baki shawara ma, kada ki kuskura wannan shashancin maganan naki ya kai kunnen babanki, idan ya ce ban miki tarbiya ba to ban yafe miki ba, dan shi dai ya yiwa yaronsa tarbiya dan ba wan da zai kalli fiskan Bunayd, ya ce bai amshi auren nan hannu bibbiyu ba, dan haka gwanda tun wuri ki saka wa zuciyanki soyayyansa, ki kuma dage ki san yan da ake kula da miji, a mallake zuciyarsa ki zama tauraruwa a wajansa, ta yacce ko baki da abokiyar zama matan waje ba za su burgesa ba, idan ma kina da abokiyar zama to ki zama sarauniya a wajansa, ki mayar da hankalink ki nistu Banafsha, abin ki ya fara isa na, yarinya shekaru ishirin kike neman cika wa, amma har yanzu ba ki da wayo sam-sam sai girman jiki, to kiyi hankali tun wuri, idan ba haka ba kika tsaya shirme, tuni aka ƙwace miki miji sai dai ki zama ƴar kallo, yaro ga hankali ga kyau ga komai Masha Allah, Allah ya basa, ki godewa Allah, domin ke ce aka taimaka da aka haɗa ki da shi mummuna da ke, tashi ki ɓace mini a gani, sannan kibar ganin babanki kaman ba ruwansa, to mutum mara saurin fushi bai iya ɓacin rai ba, kika yi ba dai-dai ba, tuni na saka shi a tura ki guard room tun da dai kinsan soja ne shi.”

Banafsha tura baki tayi ta tashi ta bar ɗakin gaba ɗaya, har da ƙwallanta wai Mami ta daina son ta, ɗan mijinta take so yanzu(jama’a ku ji mini fistaran Banafsha, ashe gaskiya ACM fistararriyan ce), haka ta koma ɗakin da suke da Mama Hadiza da Majeeder.

Mama Hadiza tana ganin yacce Banafsha ta shigo, murmushi tayi ta ce, “magananniya ke da waye kuma?”

Banafsha zama tayi tana kan tura baki ta ce, “Ni fa bana son auren nan, bai da kirki.”

Majeeder da ke kwance a gefe ta ce, “Tun da bakya so a bari mana Banafshaty, ba’a dole fa yanzu.”

Mama Hadiza dan-ƙwalon su tayi, dukkansu biyu ta ce, “Ke Hauwa’u da yake baki da hankali dole ki ce haka, ɗan uwan naki kike wa baƙin ciki, ke kuma Faɗima na ga ranan shiryuwanki, yanzu baki san ita Hauwa’u ta zama dangin mijinki ba ne, dangin miji ko ɗan goye ne ba’a shaƙiyanci a gabansa, yanzu sai su fara gwada miki halinsu, kuma idan ba neman magana irin naki ba, ai wannan yaro bai da maƙusa ko kaɗan, dan ni gani nake ma ya fi ki hankali nesa ba kusa ba, dan haka babu ruwan Hadiza a wannan magana.”

Majeeder miƙewa tayi zaune ta ce, “kaka Dije yayana Bunayd shi ne mijin?”

Mama Hadiza ta ce, “Idan baki da labari ma to kin samu labarin yanzu, da ɗumi-ɗuminta ranan juma’a za’a ɗaura, tun wuri ina faɗa miki ki fara nuna mata halin dangin miji ko za ta yi hankali.”

Kamun Mama Hadiza ta rufe baki, tuni Majeeder ta buga ihu tayi sufa ta haye jikin Banafsha, “Wayyoo Allah daɗi kashe ni, daman sai da na faɗa wa Ya ACM ya aure ki idan kin zo, amma ranan ya kora ni, ashe ya ji shawarana, wayyo ɗan uwa rabin jiki, Allah tabbatar da alkairi, zuwan farko ki santalo mini yara kyawawa kaman ku guda huɗu” faɗin Majeeder da ta rungume Banafsha.

Banafsha tura baki tayi, sai da Majeeder ta sake ta sannan ta yi murmushin yaƙe kawai, ta fice a ɗakin ta tafi wajan Adda Habiba wacce daman ita ke stuma Banafsha.

Shiri ake babu kama hannun yaro, Banafsha kuwa ita a jikinta yanzu tana jin akwai error, domin idan ta zauna sai ta bar danshi a in da ta tashi, ga ƙamshi ga ni’ima(Palace fa ya haɗe saura haɗuwansa da Oga ACM).

Ko da General ya koma gida, faɗa wa Momsee yayi komai a taƙaice, Momsee tayi kuka na tausayin rayuwan da Mami ta fiskanta, amma ta taya ta murna da komai ya wuce, kuma tayi haƙuri ta cinye ƙaddaranta, sannan tayi murna sosai fiye da tunani da aka ce Banafsha ƴar General ce, ji take ina ma ace General ya taho mata da ita, amma ba komai tun da ga abin da ya fi komai daɗi, Bunayd zai auro ta ai shikkenan, kamun ka ce me tuni Momsee ta fara shirye-shiryen kayan gyara amarya, so take ta gyarawa ɗan ta matar sa sosai, ko ba Faɗima zai aura ba wannan dole ne a kan ta, balle kuma Faɗima ce.

ACM kuwa yana komawa ya wuce gidansa, text ya tura wa Abeed akan bikin ranar Friday, Benue da komai, sannan ya kashe wayansa baya don damuwa, shi bai san shirin me ma zai yi ba, ai da Jan auren da aka yi zuwa Friday da an ɗaura kawai a ranan komai ya wuce, 2 day’s kuma me mutum zai yi.

Ko wani ɓangare fa shirye-shiryen biki ake yi ba kama hannun yaro, kuma har yau ba labarin Mom, Papi ya ƙira layukanta shiru, dan haka shirinsu kawai suke, abin ka da kuɗi suna magana to komai da komai da ya kamata an yi sa a kwanaki biyu stakani, lefe ne kawai yayi cikas saboda 2 day’s ba zai isa Momsee ta zaɓo komai ba, ga kuma shirye-shirye na gida, su Suhaila su Ramlah duk murna suke yayansu zai auri Banafsha, ɗinkuna kuwa su ma sun sha shi, General ya gwangwaje su, hatta da kayan da ake ƙira da hana gori ya yiwa Banafsha, kaya ya musu iri ɗaya da Bunayd kowa akwati guda-guda.

Ranar juma’a kuwa da wuri duk suka nufo Sokoto, hatta da Abeed da sauran abokanansu duk sun hallaro, har Dr Arshan, amma dai babu ango tukunna.

ACM Bunayd ya haɗu ya gaji da haɗuwa fan’s, kana ganinsa kasan auren ba na wasa bane, Banafsha ta shirya ko bata so shi yana yi, da alama ba zai ci amanan sadaki ba shi ma(faɗin Jay a littafin JAHILCI KO AL’ADA).

ACM ko da ya iso mamaki ya dinga yi na abokanansu da ya kalla, kuma yasan aikin Abeed ne, dan haka ma ya fitar da shi, normal ne, ana idar da sallah aka fara ɗaura aurarraki, har aka zo na su Oga ACM.

An ɗaura auren BUNAYD MUKHTAR SULE KWALLI & FAƊIMA SUFYAN SULE KWALLI, akan sadaki Naira dubu ɗari biyu, auren da ya samu halartan dubban jama’a, sosai ACM yayi mamakin mutanen da yake gani, domin bai yi zaton Abeed zai yi gayya har haka ba, gaskiya ba shi da bakin godewa Abeed duk da daman sun riga da sun zama ɗaya.

*****

Su Umaima ana gama komai a Abuja, aka haɗa result da komai, har aka faɗa sakamako, sannan suka juyo cikin ɗimbin farinciki, domin Adamawa su suka zo na ɗaya, kuma Banafsha ce ta laso musu, Malam Abbo sai da yayi kukan da bai yi ba da farko, na rashin wannan babbar kyautar Allahn da ya yi.

Dr Arshan kuwa yana sane ya ɗaga wa Umaima ƙafa, domin ya riga da ya haɗu da yayanta ya Farooq tun da daman a asibiti guda suke, ya masa bayanin musabaƙan da za su yi, kuma yana kallo a TV har suka kammala aka faɗa result, sosai ya taya su murna kuma ya shirya zuwa wajan ta daga zaran sun dawo, sai dai abin da Umaima bata sani ba, tuni Dr Arshan ya tura magabatansa wajan Abbaa, an basa izinin nemanta, jiran dawowanta kawai ake yi a fara shirye-shirye kuma.

*****

<< Yar Karuwa 26Yar Karuwa 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×