Su Umaima na dawowa, washegari suka kai wa Umma Sabeera ziyara, sun samu ta rame ta ƙwanjame, ta fice a hayyacinta, idan ka ga Umma ba za ka ce ita ba ce, Umaima kuka ta din ga yi kaman ranta zai fice, sai da ƙyar Ummu da Umma suka lallasheta, don su ma da akwai mai rarrashin nasu to tabbas kukan za su yi, don Umma tayi laushi sosai ta jima da yin nadama, ba dan ta shiga wannan hali tayi nadama ba sai dan storon haɗuwanta da Allah, ga shi gidan yari daman an ce da shi gidan. . .