Skip to content
Part 3 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Sanin halin ƴan anguwanmu iyayen sa ido sai muka roƙi mai nafen ya kai mu har ƙofan gida, hakan kuwa aka yi kaman yanda muka buƙata, muna sauƙa muka yi sallama, Umaima ta juya ta nufi gidansu, ni kuma na shige gidanmu. 

Ashe mu bamu san tun sauƙanmu a mashine ya Danish dake staye a ƙofan gidansu yana kallon mu ba, Umaima ta zo shigewa gida kenan, kaman daga sama cikin stawa aka ce mata, “Keeee! me ya haɗa hanyar ki da na yarinya mara tarbiyan can?” 

A razane ta juyo jin muryan ya Danish, ita duk stammaninta ya koma Camaroon ɗazu, ashe yana gida, tuni hanjayen cikin Umaima suka ɗuri ruwa ganin irin kallon da yake jifanta da shi. 

Ya Danish kenan, saurayi chocolate color kyakkyawan gaske, wanda kana ganinsa kaga Fulanin Camaroon dan hatta dogon gashin su shi ma ya bari, idan kaga kansa sai ka ce na wata mace mai tsayin gashi ce, mutum ne mai zafin hali ga kuma ji da kai baya son reni ko kaɗan, ba shi ne babba a gidan ba amma za ka ranste shi ne babban su saboda halinsa. 

Umaima kaman za tayi kuka ta ƙaraso gabansa ta stugunna tana cewa, “Kayi haƙuri yaya ba zan ƙara ba.” 

Wani mugun kallo ya aika mata kaman zai kifa mata mari, cikin ɗaga murya ya ce , “Idiotttt! ɓace mun a gani kamun na ɓalla ki, kina haɗa hanya da ita salon ace kema ba ki da tarbiya ko? kina son ki ɓata mana sunan gida.” 

Miƙewa Umaima tayi da mugun gudu, bata jira ya gama faɗan abinda zai faɗa ba ta shige gidannasu tana haki. 

Ummu-Khultum Aliyu Muhammad Yawonde!

Shi ne asalin sunan ƙawata Umaima wacce ta kasance ƴar Auta a ɗakin Umma Sabeera. 

Matan Abbansu Umaima, Alhaji Aliyu Muhammad yawonde biyu ne, Umma Sabeera da Ummu-khultum wacce ƙawata Umaima take takwararta, Ummu ta kasance mace mai fara’a da sanyin hali, ga sanin ya kamata ga kuma haƙuri ba ruwanta haka yaranta ma ba ruwan su, saɓanin Umma Sabeera da take masifaffiya ba haƙuri kuma bata ƙaunar kowa sai nata bata son reni amma yaranta basu iyo halinta ba. 

Umma Sabeera ita ce Uwar gida, yaran ta huɗu, Yaya kabeer wanda muke qira da Yaya babba, sai ya Danish, sai Ya mus’ab sai Autar su ƙawata Umaima, duka yaran Umma Sabeera sanyin hali ne gare su tamkar Ummu ce mahaifiyar su ba Umma ba, musamman dai Umaima takwara ga Ummu wacce kamun awa Ummu takwarar ma sai da aka sha daru da Umma Sabeera akan ta ya za’a sanya wa yarinyarta sunan kishiyar ta.  Ya Danish shi ne kusan ya ɗauko rabin halin Umma Sabeera amma dai ba duka halin nata ya ɗauko ba, dan shi yana da haƙuri kawai ya cika faɗa ne da kuma rashin son reni. 

Ummu kuma yaranta uku 3 ne, Yaya Farooq wanda yake babban yaronta sai kuma Yaya sadeeq sai kuma ƴar Autar ta Balkisu wacce ake qira da Nana.

Yaran Ummu ba ruwan su kaman Ummu haka suma suke da sanyin hali, idan ka shigo gidan za ka ɗauka duka yaran gidan yaranta ne, dan ba ruwan Ummu da banbanci ko wani abun, duk da Umaima ta girmi Nana, amma duk abinda za ta yiwa Nana sai ta yiwa ƙawata Umaima, wani lokacin ma sai ta saya ma Umaima abu ba tare da ta saya wa yarinyar ta ba. 

Tun da na taso a anguwan nan na ganmu kuma naga Ummu kan shigo gidanmu lokaci zuwa lokaci inda har ƙawance ya shiga tsakanina da Umaima tun muna yara har Allah yasa muka girma, amma Umma Sabeera da ya Danish kwata-kwata basu son ganin Umaima tare da ni, ita kuma Umaima ƙaunata take dan Allah soyayya ce da aminta stakaninmu ba kaɗan ba, tun daga primary school har secondary har zuwa yanzu da muke matakin gaba da secondary duka makaranta ɗaya muke yi kuma aji guda, haka a ɓangaren Arabic ma makaranta guda muke, ƙawata Umaima na da ƙwaƙwalwa nima hakan shiyasa ko a makaranta kullum mune a gaba. 

Duk gidan nasu kyawawa ne dan Abba suka ɗauko amma kyawun ya Danish ya fita daban dan shi kaman ya haɗa dangi da baƙaƙen larabawa amma bafulatanin Camaroon ne su gaba da baya, Abba da Umma Sabeera ƴan camaroon ne Ummu ce kawai ƴar Nigeria anan cikin Mubi amma ita ma bafulatana ce. 

Kowa na sona a gidan su ƙawata Umaima, banda Umma Sabeera da kuma ya Danish wanda su biyun nan har ƙirana da sunan da nafi stana a rayuwata suke yi, wato ƴar karuwa. 

Ya Danish ko kallo na yayi sai ya harare ni ko kaɗan baya ko son ganin ina shiga gidansu, shiyasa wani lokacin Mamina ke hanani amma Abbansu yakan stawatar masa shi da Ummansa akan su daina tsangwamata, amma Umma Sabeera in ta tashi sai ta kaada baki ta ce ai Abba so yake shima yabi karuwar Uwata, shiyasa yake haɗani da yarinyanta dan haka ba da ita ba sai tasa Ya Danish ya dinga dukan Umaima akan ta daina kula ni, amma Umaima ko me zai mata sai ta shigo gidanmu kuma sai dai in bata ganni ba sai ta mini magana, ran da aka ci sa’a Ummu na gida to ko me Umma Sabeera za ta ce bata bari ya Danish ya taɓa Umaima, dan tana sonta sosai wanda Umma Sabeera ke faɗin, wai soyayyan na munafurci ne. 

Ya Danish mutum ne da bai damu da yawan magana ba, kawai dai in har ya ƙi abu to ya ƙi sa ne ko hanya baya son haɗawa da shi, wanda kuma abinda bai sani ba shine nikam ba iya shi na tsana ba gaba-ɗaya maza na tsane su a rayuwata, da ya kwantar da hankalinsa da stangwamata da yafi masa dan nima na stane shi fiye da tunanin mai tunani tun ranar da ya fara cemun ƴar karuwa, tun ranan ya fice mini a rai. 

Ummu ganin Umaima ta shigo gida da ghdu kaman an biyo ta, sai leƙa bayan Umaima take yi dan taga wa ya biyo ta amma bata ga kowa ba, kallonta tayi ta ce, “Umaima lafiyanki kuwa? Ke da wa da gudu haka?” 

Umaima na haki ta ce, “Ummu wallahi ya Danish ne ya biyo ni.” 

Kaɗa kai kawai Ummu tayi ta ce, “Nasan za’a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, to Allah ya kyauta kawai, Danish ko kaɗan baya ji bansan me Banafsha ta ci masa ba, dan nasan ba zai wuce dan ita ya biyo ki ba, wuce kije ki huta ki ɗiba abinci a kitchen ki ci, shi kuma zai shigo ya same ni.” 

Amsawa Umaima tayi ta wuce cikin ɗakinsu ta sauya kaya ta watsa ruwa tayi sallah sannan ta ɗibo abinci ta dawo palourn tana ci tana kallo sai ga Nana ta shigo, kallonta tayi ta ce, “Ke kuma daga ina?” 

“Taya ni tambayan ta dai”, faɗin Ummu da ke zaune ita ma tana kallon. 

Nana tura baki tayi ta ce, “Daga gidan babban yaya nake”, tana faɗa ta wuce ɗakinsu.  

Ni kuwa ina shiga gidamu na tarar Mamina tana shanya kaya na da ta gama wanke wa, rungumeta nayi na ce, “Sannu da aiki Mamina, maimakon ki bari idan na dawo nayi ko da gobe ne tunda bamu da class.” 

“Parrot daga dawowa sai surutu wuce ciki ai na gama wankin” faɗin Mamina tana min murmushinta mai tsada. 

Nima murmushin nayi na shige ciki ina jin farin ciki haka kawai bansan dalili ba, Uniform nawa na cire sannan na fito palourn namu na tarar komai a gyare staff ko ina sai tashin ƙamshi yake kawai, “Uhmn! Mamina kenan ga tsafta ga son ƙamshi, ga kuma kyau Allah barmun ke Uwata ya kuma dai-daita rayuwarmu”, abinda na faɗa kenan na wuce kitchen namu, abinci na ɗibo shinkafa da miya da ya ji ice-fish ga coslow a gefe, ɗan kaɗan na ɗibo kaman an roƙo, wanda ko yaro aka bawa zai cinye tass bai ƙoshi ba, na dawo palour na zauna ina addu’an kar Mamina ta shigo ban fara ci ba ta gane ban ɗibo da yawa ba. 

Nasa cokali zan fara ci sai kawai Mami ta shigo, rau-rau nayi da idanuwa na kana gani kaga na mara gaskiya, kallo ɗaya Mami tamini da ni da plate ɗin dake gabana ta girgiza kai ta wuce ɗakin ta bata ce komai ba, ganin ta shiga ɗaki da mugun sauri nima nayi nawa dakin, naci abincin na sha ruwa sannan na tashi na ɗauro alwala nayi sallahn azahar. 

Kyautan da Alhaji ya kawo min na jida na kai wa Mamina, nan ta dinga jin daɗi tana masa addu’a, sai ta ce, “Yauwa Banafsha kinga ma kin tuno min, dama ya ce na tambaya makarantar ku ana musabaƙa ne ko kuwa ba kwa yi, in bakwa yi sai a sanja miki wai dan musabaƙa na ƙara sa yaro zama mai hazaƙa da ƙoƙari.” 

“Uhmn! Mami nifa ban cika son musabaƙan nan bane, dan ana ce masa wai karatun riya ko kuma gasar karatu wanda aka maida shi tamkar abin jan fitina, a makarantar mu ana yi nice kawai bana so dan kwanaki ma Umaima ta ce mu yi naƙi, duk da kuwa malaman na zaɓan mu, amma sai mu bada uzuri.” 

Murmushi Mami tayi ta ce, “Eh tom kinga dai cewa kika yi wasu ne suke faɗin hakan, ba wai duka mutanen duniya ke faɗa ba, amma yanzu ke a me kika ɗauki musabaƙa akan ra’ayinki?” 

“Ni Mami na ɗauke sa tamkar dai wata hanya da dama da ake bawa ɗalibi dan ganin yan inganta karatunsa, a zahiri za kayi karatu ne dan kar ka faɗi amma a ainafin niyar abun an saka shi ne dan ka ƙara mai da hankali akan karatu.” 

“Yauwa yarinyar kirki Nana Faɗima batoorler, kin fahimta da kyau haka nake so dama ako da yaushe tunanin ki yasha ban-ban da na sauran mutane, ta ko wacce siga ki kasance kin ɗauko halayyan mai sunanki, abinda nake so ki ƙara akan wannan tunanin naki shi ne ki ɗauko hadisi na farko a cikin arba’una Hadith ki ƙara a kai.” 

Kallon Mamina nayi na ce, “Mami hadisin na nufin dai komai ana yin sa ne da niya kuma komai kayi yana tafiya ne da niyan ka.” 

“Good girl! Kinga kuwa ashe in kika ƙuduri naki niyan daban ba dan riya ba ko gasa kinga ke daban saura daban, Allah subhanahu wata’ala yace “muna duba ne zuwa ga zuqatan ku ba jikkunanku ba” kinga kuwa abinda ka ƙudurta a zuciyanka shi ne abu na musamman da Allah zai tuhume ka akai.” 

Murmushi nayi cikin gamsuwa da zancen Mami na na ce, “Shikkenan Mami, na fahimta in Allah ya yarda zan gyara niya na.” 

“Yauwa ina so wani musabaƙan ya zama da ke aciki, sannan ki dage ta yanda al’umman Annabi SAW za suyi alfahari da haihuwanki, ki kulle idonki ki toshe kunnenki kawai ki fuskanci abinda kika sa a gaba inhar dai bai saɓawa mahaliccin ki ba, ki kula sosai a ko ina ki riƙe mutuncin kanki dan shi ne ƙimarki da darajarki a gidan mijinki, Allah ya miki albarka ya albarkaci dukkan rayuwanki FAƊIMAH.” 

Duk maganan da Mamina ke yi idanuwa na kan ta ina kallon ta ina mamaki a zuciyata da lamarin Mamina, anya lafiya? Mamina tana da ilimin boko da Arabic fiye da tunani na, Mami tasan hukuncin ko wanni laifi da ayar da aka sauƙe hukuncin barin ma dai Zina, amma me yasa Mami na ta zaɓi rayuwar karuwanci? Me yasa ta zaɓi take sanin ta? Me yasa ta kauda kai akan ayar Allah? Ta zaɓi zubar mana da mutunci akan adana mana shi, sannan sai tace na riqe mutunci na, koma dai menene addu’a ita ce maganin ko wacce iriyar cuta da musiban rayuwa, in Allah ya yarda ni kuma zan dage da kai kukana ga Allah na dage da addu’a… 

Maganan da Mamina ke yi shi ya dawar da ni daga duniyan zancen-zuci zuci da na faɗa, “Banafsha me kike tunani haka? Cewar Mamina idanuwanta a kai na. 

Buɗe baki na yi da niyan faɗa mata amma sai na kasa kawai na ce, “Mami ina tunanin assignment da aka bamu ne gashi hangout na yana wajan Umaima.” 

“To maza tashi kije ki karɓo daga nan ki gaida min Ummun ku.” 

Miƙewa nayi na tafi ɗakina dan saka hijab amma ina shiga ganin mayafin dogon rigan material dake jikina sai na fasa ɗaukan hijab, na ɗau mayafin tunda dai gidan su Umaima kawai zan je. 

Ina fitowa Mami ta kalle ni ganin mayafi na saka ba hijab ba sai tace “Banafsha ke kuma ina za ki da mayafi ba hijabi?” 

“Mami Allah ba inda zan je, iyakaci na gidan su Umaima kuma ina karɓa zan dawo.” 

Mamina ta ce, “Amma dai kinsan gidan su Umaima ba su kaɗai bane ko, kinsan akwai maza ba iya mata ba ne, kuma ba muharramanki ba, yanzu ko muharraminka ma ba ko wani irin shiga ake so ka yi ya gani ba balle wanda ba muharraminka ba, maza koma ki sako hijabinki bana son shirme, yarinya ta girma bata san ya girma ba.” 

Marairaicewa nayi na ce, “Allah yanzun nan zan dawo Mamina.” 

“To maza kiyi sauri ki dawo, kinsan ba son fitanki da mayafi nake ba tunda kema kinsan ƙirar da Allah ya miki yarinyar fuk-fuk kaman kazar gona.” 

Murmushi nayi kawai na fice tun da dai ta barni na tafi hakan, amma inajin kunya dan nasan nufin Mami, Allah ya wadata ni da arziqin mazaunai wanda kaga ƙuguna ka ranste nasan maza, ƙirji na kuwa Masha Allah dan suma Allah ya azurta ni da su, shiyasa Mamina idan ta tashi take cemun kazar gona (brolas) fuk-fuk, ga shi idan ina tafiya komai na jikina mostawa yake, kuma dai ba rigima nake ba haka Allah yayo ni. 

Da sallama na tura ƙofan gidan na shiga, kaina a qasa na tunkari hanyan shiga babban palourn gidan, ban ankare ba kawai na ji ni nayi karo da mutum, nayi baya zan faɗi haka wanda muka yi karon nan ko ya hanani faɗuwan ta hanyan tare ni, sai da na zauna da ɗuwawuna daɓass a ƙasa.

Ƴar ƙaramar ƙara na saki na ce, “Washh! Wayyo Allah!! Mamina mazaunaina sun yi targaɗe.” 

Stakin da aka ja shi ya sanya ni dawowa hayyacina, na ɗago fiska a hasale cikin tarin taƙaici da masifa, duk da ganin wanda muka yi karo da shi ɗin amma hakan bai sanya ni shanye haushin tsakin da yamun ba, da ƙyar na miƙe ina riƙe ƙugu na ce, “Mstww!! Mutun ba abinda ya iya sai son taɓawa mutane jiki wai ahakan shi kamemme ne kuma nagari, to kai ɗin ma dai ba wani na kirki ba ne”, ina gama faɗa na yayiɓo mayafina da yayi gefe na miƙe zan wuce amma sai ya yi saurin shan gaba na yana ƙaremun kallo sama da ƙasa. 

Tufar da yawu yayi sannan ya ce, “ƙaramar ƴar iska ba ki da abinda zan kalla ma balle na taɓa.” 

Hararansa nayi cikin ɓacin ran abinda ya mini, nima na tufar da yawu kaman yanda ya yi, amma yawuna direct sai akan takalmin sa, na murguɗa masa baki tare da harara na ce, “Alhamdulillahi tunda ni ƙaramar ƴar iska ce, kai kuma sannu babban ɗan iska mai digiri mai son taɓa mata to wallahi dan kaji Banafsha ƙwalelen ka ce, dan ni ba irin su bane nafi ƙarfinka, sai gani sai hange daga nesa, ƙwalelen biri da hantar kura.” 

A zuciye Ya Danish ya ɗaga hannu da niyan sauƙe mini mari, har na runste ido ina jiran sauƙan mari sai muryan Ummu ne ya sauƙa a kunnenmu, wanda yayi nasaran tsayar da shi Allah ya taimake ni, cikin ɓacin rai ya juya yabar wajan yana min kallon da nasan fassaransa bai wuce karki sake mu haɗu ba ne. 

Ummu ƙarasowa tayi ta ce, “Banafsha mai Danish ya miki? Naji ihunki.” 

Tura baki nayi na faɗawa Ummu yanda aka yi, nan ta ƙara bani haƙuri ta ja hannuna muka shige cikin gidan ina ji a raina kaman na koma na ƙarisa gaya masa maganan dake rai na tunda shi ya ce babban ɗan iska ne shi, ni ba ruwana ka gayamun A na ƙarisa maka har Z, bancika magana ba amma aka taɓoni antaɓo stuliyan dodo, ba wani kirki bane da ni, na iya tijara sosai. 

Umaima da ta shigo palourn hannun ta riƙe da wayar Ummu da ake ƙira, miƙa mata tayi Ummu ta amsa tayi ɗakinta ita kuma ta zauna gefe na tana cewa, “Masoyiya me ya faru?” 

Hararanta nayi na ce wannan mugun yayan naku mana shi yasa nayi targaɗe a mazaunaina, yanzu har ji nake sunamun ciwo, kuma Allah sai na rama.” 

Umaima da ta fahimci wanda nake nufi sai tayi murmushi ta ce, “ya Danish ba shi da kirki ko kaɗan nima ɗazu saura kaɗan ya sanya ni na rasa haƙora na wai akan ya ganmu tare, bansan me kika tsare masa ba wallahi ya cika takura.” 

Taɓe baki nayi nace “oho masa kuma haka zai ganni ya barni dan ni muruccin kam duste ne atou, kuma in bai da kirki ne nima ban da shi, ni ko mutunci ma ban da shi, idanuna ba ruwa sai na masa stirara tsaff idan yayi wasa, dan ba kunyan ganinsa ba wando zan yi ba, ai shi ya nema, wa ya ce ya ƙirani yar iska,ya ce ƴar karuwa hakan bai ishesa ba sai ya ƙara da ƴar iska, to wataƙila dai da shi na taɓa iskancin.” 

Umaima tana dariyan maganana ta ce, “Masoyiya ko dan ya ganki ba hijabi ne ya rikice har ya sanya kika targaɗa mazaunanki? Ya ga kaya” ta ƙarishe maganan tana wani dariyan. 

*****

<< Yar Karuwa 2Yar Karuwa 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×