Skip to content
Part 4 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Hararanta nayi na ce “Munafuka mai ƙarawa wuta fetur, to ni me ma ya fito a jikina da za’a gani? Uhmñ! Inma dai hakan ne to ya sani ƙwalelensa ya gani, wannan jikin yafi ƙarfin wanda bai iya sarrafa kalaman bakinsa ba, banda lokacin maza balle irinsa mata-maza, mstwwww! Za ki sa ma raina ya ɓaci wallahi” na faɗa ina kai mata bugun wasa a cinya. 

Umaima na dariya ta ce, “Auchh! mai targaɗe a mazaunai nima targaɗa mini cinya za kiyi ne, ki cuci mijina da yarana? Ayi haquri a mana afuwa ni da yayana kar ran masoyiya ya ɓaci, yanzu dai ya Maminmu take?” 

“Mami na can gidanta, ita ma kinsanta da zuciya yanzuma sai da nace assignment aka bamu, hangout nawa na hannunki kamun ta barni na shigo, kuma kaman tasan mugun nan yana gari, fa shi na mata ƙarya kuma Allah ya kama ni, Allah na tuba.

Umaima ta murmusa ta ce, “Ya Danish ai sai shiriyan Allah, yanzu dai tashi muje na gaisar da Mami kamun sai mu wuce wajan gadan kwaccam yin aikan Ummu, dan tsakanin yau da dare ko gobe da safe Umma da Abba za su dawo kuma kinsan da safe muna zuwa Tahfiz.” 

Taɓe baki nayi ban ce komai ba na miƙe ina faɗin “mu tafi to.” 

Umaima ɗauko mayafi tayi ta yafa ta nufi hanyan fita tana cewa, “Masoyiya mu tafi kuma kin tsaya?. 

Konawa nayi na zauna ban ce komai ba, sai Umaima ta ce, “Banafshaty zaman me kuma? Ko dai har yanzu mazaunan ne?” 

Hararanta nayi na ce, “Yanzu ke dai kinsan ba da mayafi za mu fita ba to me na saka mayafi? Ki koma ki sako hijabi nima muna zuwa gidan Mami zan sanja dan tun daga gida ya Danish yamin rashin mutunci, idan na fita kam nasan sai an kusa jefeni a tsaye.” 

Umaima babu musu ta juya ta koma ta sako hijabi har ƙasa kamun nan na miƙe muka fice a palourn, duk sauri-sauri muke dan kar ya Danish ya ganmu domin staff zai hana mu fita tare, Allah ya taimake mu har muka fice a gidan bamu gansa ba, daa sallama muka shiga gidan Mami amma ba kowa a palourn dan haka ɗakin Mami muka nufa, kamun mu ƙarisa ɗakin sai Mami ta fito tana murmushi ganinmu tare. 

“Yar Mami an sakoki gaba sai kinyi rakiya ko?” Mami ta faɗa tana kallon Umaima. 

Murmushi Umaima tayi ta ce, “A’a Mami nice na ce zan zo gaishe da Maminmu.” 

Mami ta ce, “To Allah ya miki albarka ƴar Mami.” 

Tura baki nayi na ce, “Mami albarkan ita kaɗai banda ni?” 

Umaima dariya ta sanya tana kallona ta ce, “Masoyiya ashe mun koma kishiyoyi?” 

Hararan ta nayi na marairaice ina kallon Mami, amma Mami ko kallona bata yi ba ta ƙaraso palourn, nan muka zauna Mami na ƙara tambayan mu game da karatu.

Can ganin lokaci na tafiya sai na dubi Umaima na mata magana aikanmu da Ummu ta yi. 

Mami kallon ikon Allah take ta ce, “Yaran nan dama Ummun ku ta aike ku kuka tsaya aikin surutu baku tafi ba? To Allah yasa ta zane ku maza-maza ku tashi kuje kar Magrib ya same ku a waje.” 

Miƙewa muka yi na ɗauko hijabi na muka fice a gidan muka nufi shagunan kan gadan kwaccam, muna tafiya muna hira, ina murmushi na ce, “Umaima, Mami dai ta ce musabaƙan wannan shekara ayi da mu.” 

Duk da akan hanya muke amma farin cikin Umaima bai ɓoye ba kaman ta ɗaga ni sama haka ta dinga murmushi, har da ɗan tsallenta ta ce, “Kai amma Allah dai ya bar mana Maminmu, Alhamdulillahi tayi convincing naki yanzu kam kin cire wannan banzan ra’ayin naki, in Allah ya yarda kuwa bana da mu za’a je Makka dan sai mun lashe.” 

Hararanta nayi na ce “Yanzu kin ga irinta ko, ba zaki ce bana sai mun haɗa ba wai da mu za’a je Makka, yanzu damuwanki kyautan da zaki samu ba karatun ki ba ko?” 

Umaima ta ce, “Uhmn! Masoyiya ba zaki gane ba, tabbas inaso karatu na ya kammalu zuwa yanzu ya kamata ace mun haɗa, amma ina buƙatar zuwa Makka sosai dan akwai kukokin da nake so na kai wa Ubangiji na a ƙasa mai starki duk da anan ɗin ma ina yi kuma bana cire ran yana amsuwa amma can ɗin daban ne, sannan na kai ziyara ga ma’aiki SAW a madinatu.’ 

Idanuwa nane suka kawo ƙwalla jin abinda Umaima ta faɗa, domin kuwa ni ce na fi kowa buƙatan zuwa ƙasa mai tsarki, ni ce nake da kukokin da zan kai, share hawayen da ya zubo min nayi dai-dai mun iso shagon.

Umaima ce ta miƙa kuɗi aka bamu abinda muka zo saya muka juya cikin nistuwa muke tafiyanmu, muna tafiya dai-dai majalisan ƴan sa idon anguwanmu sai wani matashi ya taso ya tare mu yana kallona yana magana, ya ce, “Yarinya mai kyau da ƙira, gàskiya ni kin mini kuma ba ruwa na da mahaifiyarki karuwa ce ko me ni inasonki a haka.” 

Wani gululun baƙin ciki ne da kuma taƙaici suka taru a zuciyata suka min yawa wanda cikin ƙunan zuciya na nuna shi da yasta amma kamun nayi magana Umaima ta riga ni, ta ce, “Kai wani irin ɗan akuya ne? Ko shaye-shaye kake yi da har ka samu confidence na tsayuwa a gabanmu kana gaya mana baƙin magana kai waye?” 

Cikin ɓacin rai ya juya kan Umaima ya ɗaga hannu da niyan zai mare ta yana cewa “Ke ubanwa ya kasa da ke? Ki bari wacce na yi da ita ta bani amsa.” 

Hannun nasa da ya ɗaga zai mare ta na buge nayi jifa da shi cikin tsananin fushi na nuna sa da yatsa na ce, “Ubanka halliru mai bin gidan matan mutane kwartanci ne ya kasa da ita, kai akwai cikakken karuwa ma irin ubanka? Bai bar yara ba haka manya sannan matan aure, ɗan akuya ƙaramin mara mutunci baƙon bariki, waye aka gaya maka baisan ubanka na kwartanci ba kuma kuɗin da yake da shi kuka gagara ci kuna fatan mutuwansa waye baisan kuɗin tsafi bane? Ko an gaya maka ba’a san an kamasa da stohuwar da tayi jika da shi bane? Ka kama kanka ni ba sa’an yinka bane nafi ƙarfin ubanka balle kai, ka ƙara furta kalmar banza akan mahaifiya ta wallahil Azeem za kasha mamiki, tunda kai baka san darajan iyayenka ba to na fi ka rashin mutunci, jahili mara tarbiya, msttwwww!” 

Kama hannun Umaima nayi muka yi gaba yana tsaye cikin tulin kunya da ɓacin rai, ganin har mun kusa ɓacewa ganinsa cike da isgili ya ɗaga murya ya ce “ƳAR KARUWA ki sani ko kin ƙi ko kin so sai na je garin daɗinki dan ki sani asirinki zan rufa miki tunda ba wanda baisan cikin shege aka yi aka haife ki ba, kuma kema ƙafan uwar taki kika bi na karuwanci.” 

Maganansa ba ƙaramin sosamun zuciya yayi ba, musamman da ya sheganta ni, ai babu shiri a fusace na juyo da niyan komawa na ƙwada masa mari ina hawaye amma sai Umaima ta riƙe ni, ta ƙi barina na koma, ina ja tana jaa na, cikin taƙaici kawai na fashe da kuka na ƙwace hannuna nayi hanyan gidanmu ina kuka mai cin zuciya, saboda mahaifiyata ita ce lago na, ina da saurin kuka musamman akan irin waɗannan maganan, amma idan ba haka ba nima dai-dai nake da kowa ka mini na maka. 

Umaima fasa kai aikan tayi ta biyo bayana tana ƙiran sunana, tana ban haƙuri tunda tasan shiga da kukan ba maganin komai zai mini ba, sai dai ma ya ƙara min wani damuwan tunda yau ba’a ji ni da Mamina ba, amma naƙi sauraran Umaima balle na tsaya. 

Ina saka ƙafana a cikin palourn mu na kuma yin karo da mummunan abinda ya fi mini maganan da aka gayamun ciwo, Mamina tare da wani ƙaramin yaro suna shafa juna, cikin hanzari na juya ina ƙara sautin kukana wanda kana ji kasan abu ne mai ciwo ke cin zuciya na. 

Umaima za ta shiga amma sai na riqo ta dan banson ta ga abinda na gani, ita kuma ganina sai bata damu da ta shiga cikin ba, ta biyoni kawai muka yi gidan su ina kan kuka na mai stuma zuciya. 

Wannan matashin juyawa yayi majalisar su yana ta kan kumfan baki, sauran da basu san abinda babansa ya aikata ba sai da nayi magana, cewa suke “Garba wai dama abinda stoho yake yi kenan?” 

Cikin ɓacin rai ya miƙe yabar majalisar ba tare da ya tanka musu ba, amma ya ƙuduri aniyan sai ya ƙuntatawa ƴar karuwa tunda ta ci mutuncin ubansa ta tona masa asiri, su kuma ganin haka suka ta dariya suna cewa, “A lallai dole mu hankalta tunda Halliru na danne mata da yaran mutane” in suka faɗa sai su kwashe da dariya. 

inda sauransu kuma ke ta kan maganana wasu su ce sunji daɗin abinda Garba ya mini wasu kuma su ce basu ji daɗi ba.

Daman ita duniya haka take, wannan na sonka babu dalili, wannan na ƙin ka babu dalili. 

Da kuka na shiga gidan su Umaima inda kai tsaye na wuce ɗakin su, Ummu tun shigowanmu ta kalleni kawai ta girgiza kai dan in ta ce bata tausayin Banafsha to tabbas tayi ƙarya, yarinya ƙarama baƙin ciki na neman kasheta kullum abu ɗaya kuka-kuka. 

Umaima tana ajiye wa Ummu aiken ta juya za ta tafi ɗakinsu wajen Banafsha, sai Ummu ta tsayar da ita tana tambayanta me ya faru? Umaima kaman za ta yi kuka ta buɗe baki ta bawa Ummu Labarin duk abinda ya faru ta ɗaura da cewa, “amma Ummu bansan me Banafsha ta gani ta fasa shiga gidan Mami ba.” 

Ummu jinjina kai kawai tayi cike da ɗimbin tausayin Banafsha ta dubi Umaima ta ce, “Je ki rarrashe ta ina zuwa ko.” 

Umaima shigowa ɗakin da nake ciki tayi ta zauna gefena tana bubbuga bayana cikin sigan rarràshi tana faɗin, “Banafshaty dan Allah kiyi haƙuri hakanan ki daina kukan nan, kanki zai yi ciwo fa.” 

Cikin kuka wanda har ya dishar min da murya na ce, “Haba Umaima! Haba Umaima! Yanzu ke hakan ya miki? Kullum haƙuri kawai kullum abu ɗaya haƙuri kawai? Ba za ki ce mini wani abun ba?” 

Umaima ta ce, “Banafshaty bayan haƙuri me kike so? Ko akwai kalman da kike buƙata na faɗa miki wacce ta fi haƙuri ne a halin da muke ciki yanzu?” 

Tsaya nayi ina kallon idon Umaima na ce, “Dan Allah ko sau ɗaya ku ce mini na shiga duniya, ko kuma na kashe kai na, dan Allah Umaima ki ce na kashe kai na zan huta” na faɗa ina haɗa hannayena tare da sakin kuka mai matuƙar cin zuciyan duk mai saurarona, dan ni kaɗai nasan zafin da nake ji a zuciyata, duniyan gaba-ɗaya bata mini daɗi, ji nake kaman na hau kwalta mota ya take ni ko zan huta, ana storon mutuwa amma ni a halin da nake ciki nafi ƙaunar mutuwa fiye da rayuwata, abin ya koma har ƴar shege ana ƙira na, tuna abinda Garba ya faɗa mini da abinda na yi tozali da shi a gidan Mamina sai na kuma fashewa da kuka mai tsanani, tun kamun Umaima ta yi magana na tari numfashinta na kuma cewa, “Dan Allah ke ma kiyi haƙuri, kar ki ce mun a’a kinji Umaima, Please ki ce na kashe kai na dan Allah.” 

Umaima kallona tayi cikin karaya da matuƙar tausayina ta ce, “Banafshaty naji roƙon ki, amma kamun nan dan Allah ki saurareni.” 

Zuba mata idanuwana da suka jiƙe da hawaye nayi, wanda kana ganinsu kaga tsantsar damuwa da raɗaɗin da nake ciki ko ban faɗa maka ba, ka kalli idona kasan ina fatan mutuwa wa kaina akan wannan rayuwa. 

Numfasawa Umaima tayi, idanuwanta sun cicciko da ƙwalla ta ce, “A cikin shika-shikan Musulunci guda biyar 5, na huɗunsu shi ne Zakka, nasan kinsan da wannan Banafshaty, Zakka ba yana nufin iya na dukiya ko dabbobi ne Zakka ba, ki sani a cikin halayyanmu akwai Zakkan da za mu dinga fitarwa wanda yake a matsayin haƙuri, haƙuri kuma halin Manzon Allah SAW ne,halin da Allah da Manzon sa suka fi so, to tabbas har abada in baka mutu ba sai andinga binka da kalman haquri dan tunatar da kai ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci kuma guda daga halayen fiyayyen halitta Rasulullahi SAW, a cikin ƙur’ani mai girma, Allah ya ambaci haƙuri ba adadi, ga Annabi SAW, da kuma mu al’umman Annabi SAW, akwai inda Allah ya ke faɗa wa Rasulullahi cewa “ka yi haƙuri kaman yanda manzannin da suka gabata kamun kai suka yi” bawai Annabi baya haƙurin bane, a’a tunatarwa ce Allah ya ke yiwa habibinsa da kansa, sannan muma al’umman Annabi SAW wajaje da dama Allah yana faɗa mana mu yi haƙuri da kuma fa’idan haƙuri, “Allah yana tare da mai haƙuri (innallaha ma’assabirin), Allah yana son mai haƙuri(innallaha yuhibbul sabirin)….” Wajaje da yawa dai, har ma akwai inda ya ke faɗin, “wa jaza hum bima sabaru jannatan wa hareerah”, Banafsha mai haƙuri baya taɓa faɗuwa domin hali ne da Allah ya ke so kuma yake horar da bawa akan ya yi halin.” 

Ajiyan zuciya Umaima ta sauƙe, sannan ta riƙo hannayen Banafsha ta cigaba da magana, “Banafshaty bayan wannan a cikin shika-shikan Imani guda 6, wanda yake na shida a rukuni kuma na qarshen shi ne IMANI DA ƘADDARA WALAU KAIRUN WALAU SHARRUN, kaman yanda ya faɗa a aya ta farko a cikin TABARAKHALLAZHI BI YADIHIL MULKU WA HUWA ALA KULLI SHAI’IN ƘADIR, wannan kalma ta ƙarshe a ayar to tana nufin ƙaddara ce da kuma jarabawan Allah akan bawansa, inason ki sani Banafsha, rayuwanmu gaba-ɗaya akan jarrabawa da kuma ƙaddara take tafiya har mu riske ramin kabarinmu, a cikin SURATUL MULK aya ta 2 Allah subhanahu wata’ala yace :- 

[Al-Mulk, Verse 2] 

ألذى خلق الموت والحياة ليبلوكم ايكم احسن عملا و هو العزيز الغفور 

Allah ya halicci Rayuwa da kuma mutuwa dan ya jarabce mu, a cikin wannan rayuwa akwai abubuwa da yawa waɗanda ya ɓoyesu akan gaibu gare mu, dan sanin su ba ƙaramin masifa bane gare mu, akwai farinciki kuma akwai baƙin ciki, akwai aure kuma akwai mutuwan aure ko rashin aure, akwai samu kuma akwai rashi, akwai haihuwa kuma akwai rashin haihuwan, abubuwa da yawa da Allah ya halitto su yayo kishiyoyinsu dan jarabtar mu, kaman dai yanda yayi mace Nana Hauwa’u kuma yayo namiji Annabi Adamu AS, a wannan lokacin kuma ya sanya wa Annabi Adamu AS kwaɗaituwar keɓancewa da Nana Hauwa’u, wannan ma jarabawa ne tsakanin mace da namiji, Acikin mutuwa kuma Allah yayi jarabawa da yawa wanda shi ma duk imaninka zai jarabce ka, akwai zafin fitan rai, akwai kwanciyan kabari, akwai tambayan kabari, akwai tashuwa bayan Mala’ika Israfil ya busa ƙaho, akwai tsayuwan hisabi, akwai bawa Kowa littafinsa, akwai duba ayyukan kowa, akwai hawa siraɗi da dai sauransu, abubuwa da yawa dan mu sani mu gaba ɗaya a kewaye muke da jarabawa, har sai munyi haƙuri mun kuma aikata dai-dai tare da ƙaunar Manzon Allah SAW, in muka shiga aljanna nan kuma sai Allah da kansa yace ga gidan da ya mana sakamako na haƙurin da muka yi da jarabobin sa akanmu, to sai fa nan ne ba jarrabawa in an shiga aljanna dan kuwa magana ta ƙare, tunda idan aka shiga aljanna ba wani abu da za’a yi mai siga da ibada, to jarabawar da Allah ke jarabtar mu da shi ai idan muka yi haƙuri duk cikin ibada ne, ki amshi ƙaddaranki hannu bibbiyu masoyiya,

Banafshaty ba ta inda Allah baya jarabtan bawan sa, wani akan mahaifa, wani akan ‘ya’ya, wani akan matan auren sa, wani akan kasuwancin sa, wani ciwo, wani kuma Allah ya bawa wani bawansa daman yin mugun nufi akan ɗayan bawan dan jarabtan su dukan su biyun, wani kuma akan maƙwabtansa, wani kuma akan abokanansa..etc

Duk wanda bai yarda da abu biyunnan ba, waɗanda ke ƙidaye a sharruɗan Addini da kuma Imani, to kina tunanin ya cika musulmi kuma mai son Rahamar Ubangiji?

Banafshaty wannan ita ce jarabawan ki kuma ƙaddaranki, sannan haƙurin da zaki yi shi ne Zakkan ki, a ko da yaushe kalman haƙuri ita ce kowa zai faɗa miki dan kuwa ansan kina kan stakiyan dandamalin gadon jarabawa, kuma duk wanda aka cewa KAYI/KIYI HAƘURI to tabbas ki sani wannan bawan Allah ko baiwar Allahn ansan ya/ta taka wuta, yanda haƙuri ke kai mu aljanna to haka tun a duniya haƙuri ke kai mu stibirin farin ciki da ɗimbin nasarori wanda bamu taɓa zato ko tsammani ba a rayuwa.

Duk wanda ya faɗa miki wata kalma a rayuwanki bayan kiyi haƙuri da kuma ki ci gaba da addu’a, to ki binciki wannan wanda ya faɗa miki kalma saɓanin biyun nan, dan kuwa baya miki kwaɗayin shiga rahamar Ubangiji, ya tabbata ba mai sonki da ƙaunarki ba, domin kuwa addu’a da haƙuri sun isa su miki maganin ko wacce iriyar jarabawa ta rayuwa, duk tsanani yana tare da sauƙi muddin ba wai ka riske makwancinka a wannan halin ba ne, kuma ko da ka riske makwancinka a wannan halin jarabawan bai wuce ba, to shi ɗin ma wani babban nasara ne dan baka san abinda Allah ya shirya maka ba idan ka koma gare sa. 

Banafsha ki dage da addu’a, duk da dai na sani kina yi, amma ki ƙara dagewa kuma ki duƙufa sosai ki kai kukanki ga mahaliccinki, musamman cikin sujjadanki, a wajan kina tasbihi ga Allah tasbihi ne na yabo, kuma babu mai son yabo irin Allah, kina tasbihinki ki karanto kukanki Insha Allahu komin nisan rayuwa Allah zai amsa miki, don babu inda bawa ya fi kusanci da mahaliccinsa irin sujjada, dan haka ki dage sosai, in Allah ya hukunta ya yarje ya ƙiramu ɗakinsa mai starki sai mu baje dukkan tulin addu’oenmu ga mai amsawa, in kuma Allah bai nufa ba, to daga nan ɗin ma Alhamdulillahi, don kuwa muddim bawa zai tsarkake zuciyansa da jikinsa sannan ya tunkari mahaliccinsa da buƙata, to ko da kuwa a kwance a gadonsa yayi wannan addu’an Insha Allah sai Ubangiji ya amsa, kiyi haƙuri Banafshaty komai zai wuce kuma zai zama labari kaman ba’a yi ba.

Batun ki shiga duniya ma wannan butulci ne da kuma rashin nuna amincewa da ƙaddaran Allah, dan kuwa na tabbata duk iya yawan starewanki da kamewanki muddin kika shiga duniya to abinda kika tsana kika sa damuwa a ranki dan shi tom ke ma shi za ki jarabtu da shi ko da kuwa bakya so ne, mutanen duniya ba duka ne na kirki ba, kuma ko da kika ce za ki kashe kanki, to ki sani wannan ya fi komai muni dan kuwa duk storon Allahnki, Addininki, iliminki, soyayyan ki ga Manzon Allah SAW, to duk sun tafi a iska domin duk wanda ya kashe kansa to ya mutu kafiri, wanda direct makomansa wuta ne, mu kuma bamu fatan hakan, muna al’umman Annabi SAW wuta ba namu bane, dan girman Allah Banafshaty kiyi haƙuri ki kuma ƙara haƙuri ki duba maganana kin ji masoyiya” Umaima ta gama maganan tana hawaye. 

Jikinane yayi mugun sanyi, dan zuwa yanzu ko banu komai to naji sassauci da kuma sanyi a zuciya ta fiye da tunanin mai tunani, kukan ma na neme shi na rasa, dan kuwa duk abinda na sani ƙawata Umaima ta tunatar da ni wanda dama Allah subhanahu wata’ala yace:- Ka tunatar domin tunatar wa yana amfanan mumini. 

Ajiyan zuciya na sauƙe na dubi Umaima cikin ƙaunanta da naji ya ninku a zuciyata na ce, “Nagode sosai Umaima, Allah ya saka miki da alheri, Allah ya kuma bar mu tare, in Allah ya yarda zan yi haƙuri, zan ci gaba da addu’a, kuma zan rungumi ƙaddarata hannu bibbiyu domin kuwa kasancewa ‘𝗬𝗔𝗥 𝗞𝗔𝗥𝗨𝗪𝗔 shi ne babban ƙaddaranta, Alhamdulillahi! Na gode Allah na yabi Annabi, kuma na amsa ƙaddarata Insha Allahu ya Rabbi. 

Murmushi na sakar wa Umaima na ce, “Masoyiya Umaima dole na dage da karatun musabaƙan nan, dan nima ina kwaɗaice da zuwa ƙasa mai tsarki, mahaifina tun da nake ba’a taɓa bani labarin sa ba sai kawai ni marainiya ce abinda Mami ke faɗamun kenan, ga shi yau har an buɗe baki ance mun ƴar cikin shege, bayan sunan ƴar karuwa, to Alhamdulillahi ni dai ina yiwa mahaifina addu’a, amma ina da buƙatan ƙarawa in ba shi da rai Allah ya masa rahama, idan kuma yana raye to Allah ya haɗa fuskokinmu ko da kuwa gaskiya ne ba ta hanyan halal aka same ni ba, to na yafe musu Duniya da lahira Allah ya yafe mu duka. 

Ƙiran sallahn Magrib da aka yi shi ya kaste mu muka miƙe duka muka ɗauro alwala muka koma ciki muka bi masallaci sallah, Ummu na ganinmu taji sanyi a ranta ganin damuwan dake kwance a fiska na ya dai-daita. 

Muna idar da Sallah Umaima ta miƙe ta fice, ni kuma karatun Alkur’ani nake yi har dai aka ƙira isha’i, Umaima ta shigo muka ƙara gabatar wa muna idar wa muka yi lazumin mu muka shafa addu’a sannan muka fito duka. 

Ummu ta ce, “yauwá yaran albarka ga abinci nan ku zauna kuci ko.” 

Zama muka yi muna ci muna kallo, duk da dai nikam hannu kawai na saka dan kar Ummu tayi magana, amma Umaima duk tana sane da abinda nake yi, sanin halinane na rashin cin abinci ya sanya bata ce mun kala ba. 

Can muna zaune sai ga kuma sallaman Abba da Umma sun shigo, wani irin bugawa zuciyata tayi da na tuna halin Umma Sabeera ga kuma ya Danish a gida.

*****

<< Yar Karuwa 3Yar Karuwa 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×