Skip to content
Part 6 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

A haka na cigaba da risgar kukana, har ɓarawon bacci yayi awun gaba da ni, kuma tun daga wannan ranar ko ƙofan gida ban ƙara fita ba, balle kuma ayi maganan makarantar boko, ko kuma Tahfiz dan wannan abu da ya faru da kalaman mutumin nan ya dame ni ba kaɗan ba, nan dai na dinga salloli kawai ina karatun Alƙur’ani dan samun nistuwa, tsakanina da Mamina sai gaisuwa duk yanda ta so nayi magana naƙi yi, sai dai Umaima idan ta shigo mu yi magana sama-sama ita ma, amma bana iya dogon magana dan kuwa inajin ciwo a rai na, duk abinda ya faru kuwa ko kuka na kasa yi tun ranan alhamis da abun ya faru har yau da yake Lahadi.

Yau ma kaman ko yaushe ina cikin ɗakina, ina zaune a kan darduma da Alƙur’ani a hannuna, shigowa Umaima tayi ɗakin da sallama ta same ni da Qur’anin na buɗe na zuba masa ido amma ba karatun nake yi ba, har ta gama sallamanta ban ji ba, sai da ta taɓa ni kamun na ɗago firgit na zuba mata idanuwana da kana ganinsu za ka ga raman da nayi, cikin damuwa ta ce, “Masoyiya mene haka wai? Duk kin bi kin sauya, duba fa har ramewa kike yi, kuma na tambayeki kin ce ba komai, me yasa kike yin haka ne Banafsha? Ko kina so damuwa ya faɗar da Mami ne? Ke kin ƙi zuwa boko kuma kin ƙi zuwa tahfiz, kin sa hankalin Mami ya tashi, yanzu ke hakan ya miki?”

Lumshe idanuwana nayi kawai ba tare da na bata amsa ba, tunda na amsa sallaman da ta yi ban ce komai ba, ganin nayi shiru kuma tasan halina idan na yi hakan ba maganan zan yi ba, ko ya za’a yi da ni, sai ta girgiza kai kawai ta ce, “Allah ya kyauta! Idan kin gama shirun naki sai ki fito, Malam Abbo yana palour yana jiranki, kuma ya jima da zuwa.”

A ɗan razane na buɗe idanuwana na kalleta, na kuma maimaita sunan da ta faɗa “Malam Abbo!”, wani nauyayyan ajiyan zuciya na sauƙe wanda bansan nayo sa ba, a zuciyana na ce, “To me ya kawo sa gidanmu?”

Muryan Umaima na tsinkayo tana faɗin, “Idan kin fito ai zai faɗa miki abinda ya kawo sa gidanku, ni dai dan Allah ki fito dan ya jima da zuwa”, Umaima na gama faɗan haka ta fice a ɗakin.

Ni kuma da kallo na bita har ta fice ina mamaki, ashe maganan nawa a fili nayi ba’a zuciya ba, sai kuma gefe guda da nake tunanin abinda ya kawo sa gidanmu a irin wannan lokaci, kuma dai na ga ban wani jima da daina zuwa makarantar ba, share tunanin nayi na miƙe tare da rufe Qur’anin, na ajiye sa a wajan zamansa, ba tare da na tsaya yin komai ba na nufi hanyan palourn tunda daman ƙaton hijabi ne a jiki na, Umaima ta faɗa mini ya jima da zuwa, banson na tsaya ɓata lokaci ya ga kaman na renasa ina ɗalibarsa, kuma nima a maste nake naji abinda ya kawo sa.

Da sallama na shigo palourn namu, inda na same sa zaune a ɗaya daga cikin kujerun palourn, cikin shigansa ta alfarma da kamala kaman ko yaushe, Malam Abbo kyakkyawan gaske ne, sanye yake da jamfa dark-green mai ɗinkin da ake kira half-jamfa, da hulansa sannan ƙafan sa har da safa, agogo mai kyau ne a maƙale a hannunsa wanda idan ka gani za ka ɗauka ya kai na dubbanni saboda haɗuwan agogon.

Malam Abbo kenan saurayi matashin Malami mai ji da kyau da kuma ilimi boko da Arabic, namiji ne shi har namiji, duk inda ake neman namiji cikakke to ya kai.

Asalin sunan sa ALIYU HAIDAR haifaffen cikin garin Mubi ne, inda suke zaune da iyayensa a anguwan kwaccam amma ba kusa da gidajenmu ba, mahaifinsa da mahaifiyarsa duka malamai ne, shi mahaifin nasa limamin masallacin juma’a ne na ƴan shi’a a cikin Mubi.

Malam Abbo shi ne ɗan Auta a wajan iyayensa, yana da yayyu maza biyu da yayyu mata biyu, Malam Abbo ba zai wuce shekaru ishirin da shida zuwa da takwas ba, kuma kyakkyawa ne shi na bugawa a jarida, yana da ilimi sosai-sosai a boko ya karanci Islamic Education, yayi har degree biyu, a addini kuma yana da haddan Qur’an mai girma complete a kansa da tafseer nasa da komai, yana da littatafai a kansa ba adadi kuma har yanzun yana kan ƙara karatun ne, domin musabaƙan sa na ƙarshe anɗau nauyin karatunsa da komansa a Madina, kawai bai tafi bane, amma idan ya shirya ko yaushe komai nasa yana nan ready.

Cikin nistuwa na samu waje na zauna a ƙasa tare da sunkuyar da kai na, a hankali cike da ladabi na gaishe da Malam Abbo, shi kuma ya amsa mini yana murmushi.

Umaima da ke zaune can gefe da ni kaɗan, miƙewa tayi ta ce, “Banafsha na gudu gida Umma ta aike ni.”

Na ɗago kai zan ma Umaima magana, cikin rashin sa’a na haɗa ido da malam Abbo da ya zuba mini idanuwansa, wani iri naji a jikina nayi saurin yin ƙasa da kai na tare da cewa, “To sai kin dawo, ki gaishe da Ummu.”

Umaima ficewa tayi bayan ta yiwa Mamina da Malam Abbo sallama, sai da ta fice sannan Malam Abbo ya dubeni ya ce, “tashi a ƙasa Malama Faɗima.”

Kai na a duƙe ina wasa da yastuna na ce, “Nan ma yayi Malam.”

Malam Abbo yayi-yayi na koma saman kujera amma naƙi, ganin na dage sai ya ƙyaleni kawai yayi murmushi, tare da gyaran murya ya ce, “Malama faɗima kinga na biyoki har gida ko? Nasan kina mamakin me ya kawo ni ko?”

Murmushi kawai na yi kai na a ƙasa har yanzu, kuma ban ce komai ba, dan kuwa gani nayi Malam Abbo kaman ya karance zuciyata ne.

Shi kuma ganin murmushin nawa sai hakan ya wadatar da shi amsan da zan buɗe baki na basa, cikin nustuwa ya fara magana, “Malama Faɗima da farko dai zan tambaye ki abinda ya hanaki zuwa makaranta, duk da bai kamata na tambayeki har gida ba, kamata yayi kije makaranta ki faɗa mini dalili, idan ta kama ta hukunci kuma sai na miki, idan na yafiya ne kuma sai na miki afuwa, to yanzu bisa ga wani dalili ga ni har gida, kuma ina tambayarki me ya hanaki zuwa kwana biyu, bayan kinsan akwai maganan musabaƙa da ake staka da shi.”

Wani nauyayyan ajiyan zuciya na sauƙe jin tambayan Malam Abbo, wanda nasan da shekara za’a yi yana tambayana irin haka, to za’a kwashe wani shekaran nima ban basa amsa ba, balle na faɗa masa gaskiyan abinda ya faru ko ya hanani zuwa makarantar, kuma ga shi dai a rayuwata ni ban iya ƙarya ba, dole shirun dai shi zan yi, saboda wannan sirrinane ni da mahaifiyata, ko Umaima ba zan sanar da ita abinda ya faru ba balle wani a gefe, ban taɓa jin zan iya ɓoye wa Umaima wani abu ba sai wannan lokacin، a hankali na haɗiye wani mugun yawun da ya tokare mini maƙoshi na tuno abinda ya faru ranan, ɗago kai na nayi tare da kallon Malam Abbo, jin hawaye na neman zubo mini sai nayi saurin yin ƙasa da kai na ina haɗiye kukana da hawayena, dan basu da amfani tunda ko yaya za’a yi da ni ba faɗan dalilin zubansu zan yi ba.

Malam Abbo daman idanuwansa na kai na, kuma ko da na ɗago kai na idanuwanmu sun haɗu, kuma ina da tabbacin ya hango damuwan da ke cikinsu, ajiyan zuciya ya sauƙe kaman yanda ya ke a nawa ɓangaren, a karo na biyu ya tambaye ni me ya hanani zuwa makaranta, amma nan ɗin ma shirun na masa kawai tare da girgiza kai, ganin haka sai ya jinjina kai dan yana da tabbacin wani abun nake ɓoye masa, ko kuma ba zan iya faɗa masa ba, bai kawo komai a ransa ba kawai ya ce, “To shikkenan na fahimta Malama Faɗima, Allah rufa mana asiri duniya da lahira, Allah ya iya mana a lamuranmu, abu na gaba kuma da zan faɗa wanda shi ne babban dalilin zuwana, maganane akan musabaƙa, kinsan dai halin da ake ciki, ɗalibai masu gabatar da karatun musabaƙa anjima da zaɓansu, amma kuma da kuka same ni da maganan kuna son ku yi, sai na sama muku gurbi tunda makaranta gaba-ɗaya an sheda da irin ƙoƙarin ku da hazaƙan ku, to kina neman kawo tangarɗa a lamarin, ko kuma na ce kin riga da kin kawo, tunda hankalin hukaman makaranta ya dawo kanku, musamman ma dai ke, kuma maganan shiganku jerin masu musabaƙa anyi cancel nashi, kuma saboda rashin zuwanki, hukuman makaranta na batun sallamanki dan kina son basu kunya ko kawo musu wani naƙasu a tafiyansu, na zo ne in sanar da ke abinda ake ciki kuma makaranta ce da kanta ta turo ni, idan ba ki koma akan lokaci ba to komai na iya faruwa, da naso faɗa wa Malama Ummu-khultum ta isar miki da saƙon amma kuma sai makaranta ta bukaci da nazo da kai na.”

Wani irin bugawa ƙirji na ke yi zufa na ƙeto mini, jin wai an ciremu a masu yin musabaƙa kuma makaranta na son sallamana, mu da muke ƙoƙarin haɗawa a yayemu ba da jimawa ba in Allah ya yarda, kuma dai duk da ba dan abinda zan samu zan yi musabaƙa ba, amma na gama saka wa a raina in Allah ya yarda zan yi nasara, idan Allah ya ƙira mu muka samu zuwa ƙasa mai starki na samu na yi wa mahaifiyata addu’a, ai dole abin ya dame ni, kaman zan yi kuka na ɗago kai na, muryana na rawa na ce, “Malam dan Allah ka yi haƙuri, dan darajan Annabi SAW kada ku cire mu a masu yin musabaƙan.’

Malam Abbo ajiyan zuciya ya sauƙe ya kawar da kansa daga kallona ya ce, “Ni dai ban da yacce zan yi kuma a ƙara baku wata daman, wannan ku ne ya kamata ku ƙoƙarta ku samawa kanku wata damar.”

“Malam duk abinda ya kamata muyi za muyi in Allah ya yarda, amma ku yi haƙuri kada ku cire mu” ma faɗa hawaye na taruwa a idanuwana.

Numfasawa yayi ya ce, “To yanzu dai ni shawara guda zan baki, maganan zuwa makaranta duk rinsti duk wuya kada ki ce za ki aje karatu a gefe, ko me ya samu bawa ko kuma ya faru to muƙaddari ne daga Allah, ki dage da karatu sannan kije makaranta, ina tunanin hakan zai sa hukumar makaranta ta fasa abinda ta yi niya, idan aka ga kina zuwa kuma kin dage da karatun, to dole za su buƙaci yin tafiyan da ke.”

Lumshe idanuwana nayi, hawaye suka gangaro akan kumatuna, ba tare da na goge su ko na hana su gangarowa ba na sauƙe ajiyan zuciya da kuma hamdala, ko babu komai zan ji sanyi a rai na idan nayi hawayen, tun ranan na kasa kuka balle hawaye har yau, kuma zuwa makaranta ya zamo mini dole, sannan dagewa da karatu ya zamo mini dole shi ma, a hankali na buɗe baki da muryana da ke rawa na ce, “Malam zan je makarantar Insha Allah, kuma zan dage sosai, mun gode Allah saka da alkairi.”

Murmushi Malam Abbo ya saki wanda nima Uwar batoorl bansan na me bane, amma dai da alama da wani abun, cewa yayi, “ki mini magana da Umma zan tafi.”

Tashuwa nayi na nufi ɗakin Mamina, da sallama na tura ƙofan na shiga, bayan ta amsa mini, na faɗa mata Malaminmu na mata magana zai tafi, Mami ta amsa akan tana zuwa ni kuma na juya na koma palourn, samun Malam Abbo nayi har ya miƙe ma, kallo ɗaya na masa na ɗauke kai na faɗa masa tana zuwa, ban gama rufe baki ba sai ga Mamina ta iso, Malam Abbo durƙusawa yayi yana faɗa wa Mami zai tafi, ni kuma gaba nayi na fice ma a palourn gaba-ɗaya ina yabawa da girmama Mamina da Malam Abbo yayi, sosai naji daɗin yanda yayi ba tare da girman kai ba.

Mami ganin na fice a palourn sai ta buƙaci Malam Abbo ya tashi, tashuwa yayi ya zauna ita ma ta zauna, kansa a ƙasa cikin ládabi ya ce, “Umma mun gama magana da Malama Faɗima, kuma nayi duk abinda ya dace wanda nasan zai sa ta dawo normal, Insha Allah ina da tabbacin har makarantar bokon za taje.”

Mami farinciki kaman tayi yaya, tana murmushi da jinjina ƙoƙarin Malam Abbo ta ce, “Nagode sosai Malam, Allah saka da alkairi, Allah maka albarka, Nagode sosai.”

Malam Abbo miƙewa yayi bayan sun gana magana ya fice, Mami sai godiya take masa, ta miƙa masa kuɗi ma ya ƙi amsa, a stakar gidan suka same ni staye, Mami ta dubeni ta ce, “Banafsha sai ki takawa malamin naku ko.”

Amsawa Mami nayi, ita kuma ta juya ta koma cikin gida cike da farin ciki, ko ba komai yanzu ‘yar ta za ta saki ranta, ta daina saka damuwa a ranta.

Ni kuma kaman yanda Mamina ta faɗa hakan nayi, tare muka fice da Malam Abbo a gidanmu, yana min faɗa, cewa yayi, “Malama Faɗima, komai na rayuwa da kike gani haƙuri ake yi da shi, kuma ƙoƙari ake yi wajan ganin mutum ya cinye jarabawan mahaliccinsa, saboda samun gwaggwaɓan rabo da sakamako mai kyau a duniya da kuma ranan karɓan sakamako, ita kuma jarabawa a zagaye da mu take ko ta ina, a iya karatunki nasan kin sani, ayoyi da dama na ƙur’ani sun kawo hakan, sannan akwai wasu hadisan ma da suka kawo haka, Malama Faɗima hatta rayuwa da kike gani da Allah ya mana ya kuma azurtamu da lafiya to shi ma jarabawa ne, Allah ya jarabce mu da lafiya ne dan ya ga ya za mu yi da lafiyan, aljanna za mu nema da shi ko kuwa za mu dage wajan saɓa masa ne, rashin lafiya ma jarabta ce dan ya ga mutum zai yi haƙuri ya yarda da Allah ne ya ɗaura masa cutan ko kuwa zai dinga zargin mutane akan da saka hannunsu, haka zalika akan dukiya da rashin dukiya, akan haihuwa da rashin haihuwa, akan tashuwa ka rayu da iyayenka da kuma rayuwa ba tare da su ba, haka akan aure da rashin yin aure, komai da yake zagaye da ɗan Adam na jarabta ce daga mahaliccinsa, kuma Allah na so ne mu ci wannan jarabawan, ina fatan kin fahimta kuma za ki dage wajan ganin kema kin cinye naki jarabawan?” Faɗin Malam Abbo da ya dakata da tafiya ya zuba mini idanuwansa dai-dai mun shige ƙofan gidan su Umaima, kuma cikin rashin sa’a sai ga Ya Danish a waje shi da abokinsa kasancewan yau Lahadi yana gida bai koma ba tukunna.

Ya Danish yana zaune a bayan motansa, sai abokinsa ɗaya na zaune a plastic chair, da kuma Ya Farooq shima yana zaune a kujeran roba, ya Farooq ɗan farin Ummu ne, kuma kusan sa’a haka suke shi da Ya Danish, shiyasa suke yawan zama tare, muddin Ya Danish na gari to za ka gansu tare da wannan abokin nasu mai suna IB.

Ya Danish tun fitowanmu idanuwansa suka sauƙa a cikin nawa, wani irin kallon banza kallon tsana yake jifana da shi, ni kuwa ganin ya zuba mana ido sai na dinga sakarwa Malam Abbo murmushi, har dai muka tsaya ɗan gaba da su kaɗan, wani kallo na yiwa Ya Danish wanda shi kaɗai yasan fassaranshi ta ‘yar staman da ke tsakaninmu, sannan na mayar da hankalina kan Malam Abbo ina masa magana, Ya Danish kuwa a nasa ɓangaren wani wawan dogon staki ya ja, wanda sai da Ya Farooq da ya IB suka tambayesa menene, amma ya musu banza.

Idanuwana akan malam Abbo ina ƙayataccen murmushi na ce, “in Allah ya yarda Malam zan dage, wajan ganin na cinye tawa jarabawar, sannan na maka alƙawarin dagewa a karatu da zuwa makaranta, nagode sosai Malam, Allah ya biya ka da mafificin alkairi, Allah ya biya iyayenka da aljanna, Allah ya sa ka rabu da su lafiya nagode sosai.”

Tunda na fara magana Malam Abbo ya zuba mini idanuwansa masu ɗauke da sinadaran da ke saka ni jin kunya, amma duk da haka ban kawar da nawa idon ba sai ma wani murmushin da nake sakar masa, wanda duk saboda Ya Danish na daure nake yin hakan, shi kuwa Malam Abbo tuni ya susuce wajan kallona, inada tabbacin ya tafi wata duniya ta daban, ganin kaman hankalinsa ba ya wajan sai na ɗan mosta yastuna a gaban idanuwansa na ce, “Malam muje ko.”

Firgit Malam Abbo ya dawo daga duniyan da yake, yana mai dannewa dan kada na fahimta, ganin har yanzu da murmushi akan fiskana sai shi ma ya sakar mini tare da faɗin, “Malama Faɗima rakiyan ya isa haka, ki juya nagode ko.”

Ba tare da musu ba na gyaɗa kai tare da masa addu’an a koma lafiya na ƙara da godiya, ban juya ba sai da Malam Abbo ya juya ya fara tafiya, na ɗaga masa hannu sannan ganin ya ɓacewa ganina sai na juyo ina ta murmushi ni kaɗai, har na mance da abinda ke damuna domin kuwa nasihan Malam Abbo ya shiga jikina ba kaɗan ba.

Ina juyawa kuwa idanuwana karaf a cikin na Ya Danish, wani killer smile na sakar masa tare da cigaba da tafiya na, wannan karon ma ƙwafa Ya Danish yayi, wanda ya sanya su Ya Farooq bin inda yake kallo da idanuwansu, Ya Farooq suna ganin ni ce sai kawai suka yi dariya, daga Ya Farooq har Ya IB sun san za’a rina, Ya Farooq ne ya ƙwala mini ƙira tare da cewa Ya Danish, “Amma dai ka ji jiki wallahi, Allah taro ka Danish, ka saki ranka ka daina haushi da yarinya a banza, ita bata damu da tsabgarka ba amma ka bi ka azalzali yarinya.”

Ya Danish kallon banza ya yiwa ya Farooq tare da yin ƙwafa, ni kuwa ganin ya Farooq ne ya ƙira ni sai na taho cikin tafiyana ta nistuwa da ɗaukan hankali, har na iso inda suke zaune, ɗan rusunawa nayi na ce, “Ya Farooq ina wuni, Ya IB barka da yamma.”

Ya Farooq da Ya IB duk amsawa suka yi da murmushi, Ya Farooq ya ce, “Daga ina haka da yamman nan sistor?”

Langwaɓar da kai nayi gefe guda tare da kulle idona ina murmushi na ce, “saurayina ne ya zo zance, shi ne na rakasa.”

Tun kamun na rufe baki ya Danish ya ja wani dogon tsaki, daman shi kaɗai ya ganni basu ganni da saurayin ba, kuma ga haushin na gaida su ban gaishe sa ba saboda na renasa, Ya Farooq ko kallon Ya Danish bai yi ba duk da yasan yayi tsaki, murmushi ya sakar mini ya ce, “inye! Su sistor har an girma an yi saurayi, daman Umaima ta faɗa mini gobe za ku fara exam’s, ashe next year ana gama school sai biki kenan?”

Rufe fiskana nayi da tafin hannayena sannan na Jinjina kai alaman eh, Ya IB ne yayi dariya ya ce, “Yaran yanzu ba kunya, har da kai kike ɗagawa, shikkenan Allah nuna mana da rai da lafiya, Allah tabbatar da alkairi.”

Da “Ameen” na amsa ina yin ƙasa da kai na tare da wasa da yastu na, Ya Danish da ya cika ya gama cika, wani banzan tsawa ya mini ya ce, “Keeeeeeeeeeee! Dallah ɓace ma mutane a kai, ‘yar iska kawai, shashasha ƙwaila, mara tarbiyya.”

Duk da storon da stawan nasa ya bani amma hakan bai saka na tafi ba sai da na tsaya na sakar masa wani killer smile ɗin, na kashe masa ido guda na ce, “ai ba’a ɗan iska ɗaya, sai dai biyu, kaga kuwa ni kaɗai ba iya yin iskancin da kai na zan yi ba, dole tare da kai nake yi” Ina gama faɗan haka na juya na shige gidannasu, hankalina kwance.

Ya Farooq da Ya IB duk dariya suka kama yi, suna faɗin ai ga abinda suke guje masa kenan, ga shi tun ina storonsa amma ya saka na daina storonsa balle storon faɗa masa magana, na gaishe da kowa amma banda shi, kuma duk shi ya jawo ba kowa ba.

A tsakar gidan na haɗu da Umma Sabeera, ɗan rusunawa nayi na gaisheta amma ta aika mini da harara ta ce, “Ke dan uwarki karuwa ki fice mana a gida tunda ba gidan ubanki ba ne..”

Kamun ta ƙarisa maganan tuni muryan Abbaa ya dakatar da ita, ta hanyar cewa, “Sabeera ki fita a idanuwana na kulle, ke Faɗima maza zo ki shige inga gidan nawa ne ko nata, idan ta isa ta hana wanda na bari ya shiga gidan.”

Kai na a ƙasa ba tare da damuwa ko ɗigo a fiskana ba, na gaishe da Abbaa ya amsa, sannan na miƙe na shige gidan ina magana a zuciyata ni ɗaya, ba dan Umma Sabeera na cin albarkacin Umaima da Abbaa ba, ai da tuni ita ma na fara kasa mata hali na tasan banda sauƙi, ni ɗin do me i do you ce, back to back aradu, kana mini ina ramawa ba barin bashi kuma ba ruwana da girmanka.

Abbaa ya dubi Umma bayan shigewana ya ce, “Sabeera indai kina da kunya to kin ji shi, ƴar cikinki amma kike mata abu kaman sa’arki, yanzu da ta rama zagin fa? Ƙawar ƴar ki ce fa ba wai babbar mace ba ce, ki gyara halinki idan ba haka ba wallahi za ki sa nayi abinda ban yi niya ba, indai akan mahaifiyarta kike wannan abun, to sai na aure ta naga abinda za ki yi, ko kuwa na zama dadironta na ga ƙarshen rashin tunaninki da rashin hankalinki…” haka Abbaa ya dinga yiwa Umma Sabeera faɗa kaman wanda aka aiko sa da wahayin faɗan, ita kuwa Umma wani irin stanata ne ya ƙara rufeta, tana jin za ta iya kasheni ma akan abinda Abbaa ya faɗa, na ya haɗa alaƙa da Mamina.

Ni kuwa ina shigewa ciki na gaishe da Ummu sama-sama, da yake nasan abinda na shuka a waje da wuri na fito na ce Umaima ta zo ta rakani, so nake kamun Abbaa ya fita na gudu gida, idan ta Ya Danish ne banda mastala zan iya tsayuwa mu daku ma, amma kuma Umma ita nake shakka saboda mijinta da ‘yar ta, kada ta ce za ta taɓa ni kuma ba iya ƙyalewa zan yi ba.

Umaima sai mita take daga zuwana zan tafi, ko labarta mata yanda muka yi da Malam Abbo ban yi ba, haka dai na yafito ta muka fito, Allah ya taimaka lokacin Umma ta shige ɗakin Abbaa da ke ta cikin gidan, hamdala nayi muka nufi waje, muna ficewa a gidan kuwa muka kusa yin karo da Ya Danish, wani mugun kallo ya aikawa Umaima amma ta kawar da kai kaman bata ga ni ba, tsawa ya daka mata da mugun ƙarfi ya ce, “kin juya kin koma gida ne ko sai na iso wajan na ɓaɓɓallaki? Ban hanaki haɗa hanya da yarinyar nan ba?”

Kamun mu yi wani mosti sai muka kuma jiyo muryan Abbaa, ashe yana bayanmu bai fita ba, dan-ƙwalo ya aika wa Ya Danish, sannan ya ce, “ke Umaima wuce ku tafi, idan kun je ki kwana a can, sai naga ko akwai wanda ya haifa mini ke, da zai mini iko da yarinya.”

Fakan idon Abbaa nayi na murguɗa wa ya Danish baki tare da gwalo, na kuma masa magana da ido wanda na tabbata ya fahimci abinda nake nufi, daga kallon da ya mini, jan hannun Umaima nayi muka yi wa Abbaa sai da safe muka wuce gidanmu, shi kuma ya Danish fasa shiga gidan yayi daga wajan ya shige motansa yayi gaba saboda Ya Danish akwai zuciya, Abbaa ma wucews inda zai tafi yayi.

Malam Abbo tun da ya juya ya tafi babu abinda yake tinanowa sai murmushin da Banafsha ke sakar masa, da kuma kallon da take masa, tuni ya ƙara matowa a kanta, nan ya ci alwashin ya kusa bayyanar mata da saƙon zuciyarsa.

Muna shiga gidanmu Umaima ta dinga dariya kaman ba lafiya ba, kallonta nayi na ce, “an fara sanyi kuma ai, hauka ta fara mostawa.”

Tana dariyan ta ce, “Masoyiya ba za ki fahimta ba, ni ba haukar ce ta mosta ba, abinda Abbaa yayi ne ya mini sweet, ga shi Ya Danish ya ja an ce na kwana anan, wayyo mi farinciki kashe ni, yau za mu kwana karatu saboda peppernmu na gobe, Allah ya yiwa Ya Danish albarka, Allah ya sa watarana Umma ma tayi a gaban Abbaa, ya ce ya bawa Maminmu ni kyauta, heee!hu!hu!”

Hararan Umaima kawai na yi muka shige palourn namu, ban sanar mata abinda ya faru stakanina da Umma ba ɗazu, domin duk son da Umaima ke mini to fa uwa-uwace, kuma wannan ba baƙon abu bane, hantara daga wajan Umma da Ya Danish ba sabo bane a wajena.

Da sallama muka shiga palourn amma ba kowa shiru, ɗakina muka wuce direct muka yi alwala tare da yin sallah, mun idar muka fito palour muka samu Mamina zaune tana cin abinci, ganina da Umaima bata yi mamaki ba, kuma bata tambaya ba, domin ba wannan ne karo na farko da Umaima ke kwana a gidanmu ba, ni ce kawai Mamina bata barina na kwana a gidan su Umaima saboda wai gidanmu ya mata girma ita kaɗai, ta fi son tana jin mostina.

Mami ta sani na ɗebo mana namu abincin, muka ci muna kallo hankali kwance, hira muka ɗan taɓa da Mami sannan nake faɗa mata ma yanda muka yi da Malam Abbo akan maganan musabaƙa da hukuncin makaranta, da mamaki dai na kalli Umaima hankalinta kwance bata tashi hankali ba, Mami ce dai ta nuna ɗan damuwanta sannan ta mana faɗa sosai akan mu dage mu mayar da hankali, ta kuma ƙara mana da nafilfilu da kuma addu’oe da za muyi saboda exam’s da za mu fara gobe da yardan Allah, ba mu wani jima ba na tashi na shige ɗaki bayan na yiwa Mamina sai da safe, ina shigewa Mami ta dubi Umaima ta ce, “yarinyar Mami kada ki sanar da ita gaskiyan abinda ake ciki, ki ƙyaleta dai ku dage ku mayar da hankali, kinga yanzu ta saki ranta, nasan idan ba ta haka aka ɓullo aka mata wayo ba, to Banafsha ta dinga cin rai kenan.”

Murmushi Umaima tayi ta ce, “Insha Allah! Mami ba zan sanar mata ba, zan dai nuna mata nima na damu mu ƙara mayar da hankali.”

“Yauwa ƴar kirki, Allah muku albarka duka ya ba ku sa’a ku ciyo na ɗaya a musabaƙa, flying color result a boko” cewan Mami tana murmushi.

Umaima amsawa ta yi da, “Ameen” sannan ta yiwa Mami sai da safe ta shige ɗakin Banafsha, Mami ma hamdala tayi sannan ta kashe kayan kallon ta koma nata ɗakin, sai da ta gabatar da shafa’i da wuturi da wasu nafilfilun sannan ta kwanta.

Na fito wanka ina ƙoƙarin shumfiɗa darduma Umaima ta shigo, kallon yanayin fiskanta ya sa na tambayeta ki lafiya, cikin damuwa Umaima ta ce, “Masoyiya maganan musabaƙan nan ne ya dame ni.”

Kwantar mata da hankali nayi, na ce mu dage da addu’a da kuma karatu, sannan in Allah ya yarda ni ma daga yau ba zan sake irin wannan dena zuwa makarantar ba, da ƙyar na shawo kan Umaima ta shige wanka, tana fitowa ta saka kayana muka yi nafilfilunmu da addu’oe sosai, sannan muka kwanta, da asuba kuwa muka tashi muka hau karatu saboda exam’s.

Ya Danish taƙaici da ya cika sa ya masa dama-dama, ko gidan bai koma ba daga nan ya yiwa motansa key ya wuce wajan aikinsa da ke Camaroon, idan ya koma Sunday da yamma sai Friday da yamma yake zuwa, weekend kawai yake zuwa yi a mubi.

<< Yar Karuwa 5Yar Karuwa 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×