Skip to content
Part 7 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Washe-gari Abbaa da kansa ya saka Nana ta kawo wa Umaima uniform nata gidanmu, Umma sai cin rai take yi tana ta fushi akan Umaima ta kwana a gidanmu, amma Abbaa ko a jikinsa, Umma haushi kaman ya kasheta ga shi Ya Danish ba ya gida, kuma babban yaya ba ruwansa, ya mus’ab da ke Camaroon ma ko yana nan ba ruwansa, Ya Danish ne daman mai biye mata.

Mun yi wanka mun shirya tsaff muka fito, abin karyawanmu da komai muka samu Mami ta jera mana a kan centre carpet na palourn, zama muka yi muka cika cikinmu yanda ya kamata, sannan muka yiwa Mami sallama ta ba mu kuɗin mashine da na kashewa muka fice, cikin sa’a muka samu mashine kuwa da wuri, ya ajiye mu a makaranta muka shige hall na exam.

Haka rayuwa ta dinga tafiya da daɗi da babu daɗi dai sai haƙuri, mastalolin rayuwa da ƙalubalen rayuwa gare ni kullum ƙara gaba suke yi, saboda daga halayyan Mamina babu wanda ya canja kullum gaba-gaba abun yake yi, ni a tunanina abinda wancan stohon ya mini zai sanya Mamina gyara kura-kuranta, amma ina Mamina ci-gaba tayi da harkokinta, sam-sam Mamina bata jin ƙira dan ta riga da tayi nisa, kullum dai magana guda ne, idan na ce ta dena wannan rayuwa, sai ta mammakeni kuma ta ce sana’a ce dan ta rufa mana asiri,nidai wannan sana’a banga alfanunta ba, sai dai ban da yacce zan yi idan ba addu’a ba.

Maganan makaranta kuwa na dage sosai na mayar da hankali muna exam’s namu hankali kwance, sannan a tahfiz ma ina ƙoƙari yanda ya kamata, tsakanina da Malam Abbo kuwa yanzu ya zama kaman yayana dan yana yawan mini faɗa da nasiha, sannan wani irin shaƙuwa na neman shigowa tsakaninmu wanda ni dai ban farga da hakan ba sai da shaƙuwan tayi nisa.

Sati biyu muka kwashe muna exam’s, sai ranan Alhamis muka kammala, daga ranan kuma muka yi wa makaranta bye-bye, saboda musabaƙan namu week da za’a shiga ne.

Kaman ko wanne weekend, yau ma da yake Saturday da wuri muka je tahfiz muka dawo, tun daga compound na gidanmu da na shigo na ga wata dalleliyar haɗɗaɗɗiyar Mota, lumshe ido nayi kawai ina ambaton sunan Allah dan nasan ba zai wuce wani baƙon Mamina tayi ba, taɓe baki nayi ina faɗin ko wani jarababben ne da sanyin safiya haka oho, sai da na seta zuciyata na shanye taƙaicin da zan tarar a ciki tun ban shiga ba, sannan na tura ƙofan palourn na shiga da sallama, daga muryan wanda ya amsa mini sallaman na sheda baƙon da Mami ta yi da sassafen.

Ƙarisa shiga palourn nayi kai na a sunkuye, durƙusawa nayi har ƙasa na ce, “Sannu da zuwa Alhaji.”

Alhaji Mukhtar na washe baki ya ce, “Sannu ƴar albarka, sannunku da dawowa ko.”

Amsawa na yi har yanzu ban ɗago ba balle mu haɗa ido, a haka na gaishe sa ya amsa, ya ce na je na huta na karya zuwa anjuma zai ji karatun nawa, ba musu na amsa na miƙe na shige ɗakina, ina shiga na faɗa kan gado tare da ɗaga hannayena sama na ce, “Ya Rabbi ga bayinka nan, ka fi ni sanin abinda suke ciki, ya Rabbi ka shirya su ka gyara rayuwansu, ya Rabbi kada ka kama zuri’arsu da laifin da basu ji ba, ba su gani ba, don kuwa ƙur’ani mai girma ya ce “az- zina dailun (zina bashi ce)”, Allah ka shiryamu duka, ka shiga stakaninmu da biyan bashin da ba mu ci ba”, ina ƙarishe addu’ana na miƙe na cire uniform nawa, ina ƙoƙarin fita sai Mamina ta shigo, murmushi ta sakar mini ta ce, “Sayyada Faɗimah a zo a karya, kada ulcer ta kama mini ‘yar fari, ‘yar auta.”

Murmushin nima na yiwa Mamina ban ce komai ba, na bi bayanta muka fice, abin karyawa na samu ta zubo mana ni da ita, zama nayi amma na kasa cin abincin, kasancewan Alhaji Mukhtar na palourn duk da dai hankalinsa na kan wayansa ne, Mamina ganin naƙi ci sai ta gusturo sinasir ɗin ta kai mini baki, ni kuma na buɗe bakina a hankali ina karɓa, a haka ta dinga bani a baki har na ƙoshi, sannan ta cigaba da cin nata, Alhaji Mukhtar da ke kallonmu sai yayi murmushi ya ce, “Lallai Ramlah kin shagwaɓa mini yarinya da yawa, budurwa da ita kina mai da ta ‘yar goye, yarinyar kirki kar ki biyewa Maminki fa, ke babba ce yanzu.”

Ƙasa nayi da kai na ina murmushi, Mamina kuwa kallon soyaya ta yiwa Alhajin nata ta ce, “wannan jaririyar ce babba? Banafsha ta wuce na sa zani n goya ta ne Alhaji? Ita ce fa ‘yar fari kuma ‘yar autan Maminta.”

Alhaji Mukhtar ma yana murmushin ya ce, “Amma dai wasa kike yi, Banafsha kar ki yarda fa ta ce miki auta, ƙannenki na zuwa.”

Mamina ta ce, “bayan ita ba kowa, daga ita ba ƙari, tal ɗin Maminta, shalele gudan stokar miya.”

Alhaji idanuwansa akan wayansa ya ce, “yarinya ɗaya bata ishe mu ba, dole ki haifo mini wasu.”

Kai na a ƙasa ina sauraran maganan su Mamina, jin abinda Alhaji ya ce sai nayi saurin ɗagowa dan na kalli yanayin Mamina, a tunanina zan ga tayi murmushi dan ita ma tana son haifa mini ƙanne, amma sai saɓanin hakan na gani, Mamina ta haɗe fiskanta ta yi kicin-kicin da shi, Alhaji Mukhtar kuwa hankalinsa kwance yana lasta wayarsa sai ma murmushin da yake yi, dan yasan ya stokano masoyiyarsa Mami kuma shi daman burinsa kenan, saboda wani shiri da yake yi na daban.

Mamina ganin ma yana murmushinsa ya manna mata hauka, sai ta miƙe ta wuce ɗakinta, ni kuma na tattare kwanukan na mayar kitchen, har da wanda Alhaji ya ci abinci a ciki, na Juyo zan shige ɗaki sai Alhaji ya dakatar da ni ya ce na zo, dawowa nayi na samu waje a nesa da shi na zauna a ƙasa, yana murmushi ya ce, “Yarinyata Banafsha ya karatun? Fatan kun gama exam’s lafiya?”

Kai na a ƙasa na ce, “Lafiya Alhamdulillahi, Alhaji.”

“To Masha Allah! Allah sa result tayi kyau, Ya karatun musabaƙan kuma? Yaushe za ku yi?”

Kai na a ƙasa har yanzu na basa amsa da ranan da za mu yi, jinjina kai yayi ya ce, “To shikkenan, zuwa dare Insha Allah za mu duba karatun, yanzu je ki huta, zuwa anjima za mu je anguwa Insha Allah.”

Miƙewa nayi na masa a huta gajiya na shige ɗaki na, shi ma miƙewa yayi ya shige ɗaya ɗakin, ruwa ya wasta ya kwanta tare da jawo wayansa yayi dialing wani number da sunan “My Son” ya ke ɓaro-ɓato, ba jimawa aka ɗauka, Alhaji Mukhtar yana murmushi ya ce, “Chief of the air staff.”

Wani haɗaɗɗen murya ne ya murmusa yanda sai da sound na murmushin ya fito, sannan cikin yanga ya ce, ” morning Sir.”

Alhaji Mukhtar murmushi yayi tare da girgiza kai ya ce, “BUNAYD Allah ya shiryeka.”

A hankali kaman mai raɗa ya ce, “Ameen Papi.”

“Ya General?”

“General yana gidansa Sir.”

Girgiza kai Alhaji ya kuma yi ya ce, “zan saɓa maka Bunayd, ina ubanka kana ce mini wani Sir.”

Murmushi ya kuma yi ya ce, “sorry Sir!”

Alhaji ya ce, “Ubanka General ne Sir, yaushe za ka shigo Kano?”

“Soon zan shigo, kasan za’a yi bikin Abeed in next 3 months.”

Alhaji ya ce, “Masha Allah! Ya fi masa ai yayi aurensa, kada ya biyewa duniya wai sai yayi iyayi, yanzu mutuwa araha take, kar mutum yaga kullum yana sama kaman stunstu ya ɗauka shi ba mutuwan zai yi ba, to azara’ilu ko a duniyar wata kake lokacinka na cika zai zare ranka, balle jirgi da nawa aka yi, idan akwai mai ƙararren kwana a ciki ai hastari jirgi ke yi, to gwanda tun wuri kasan abinda ka adana kamun ka wuce babu masu maka addu’a.”

Bunayd a ɗaya ɓangaren murmushi yayi bai ce komai ba dan yasan da shi Papi ke yi, Alhaji ya kuma cewa, “ko ka fito da mata ko kuma daga kai har ubanka General ku ji anbada ka sadaka, sadaka yalla zan ba da kai a masallaci, in ana ƙiran macen sadaka ta Annabi, to kai za ka zama na Annabi, bari lokacin da na ɗiba maka su cika.”

“Byee Sir, my regards to Adamawa” yana gama faɗa kitt ya daste ƙiran.

Alhaji murmushi yayi tare da cewa, “Allah ya muku albarka” yana gama faɗa ya gyara kwanciyansa ba jimawa bacci tayi gaba da shi.

Ɓangaren Mami ma tana barin palourn ta bi lafiyar gado ta koma baccinta, cike da taƙaicin Alhaji Mukhtar, maganansa ya wuce stakaninsu ga shi har a gaban yarinyarta yana faɗa mata maganan aure, ita kuma ga shi duk abinda zai mata ta kasa rabuwa da shi, a rayuwanta gaba-ɗaya wannan ne karo na biyu da taji tana matuƙar son wani har tana jin ba za ta iya rabuwa da shi ha, Alhaji Mukhtar na cin albarkacin wannan soyayyan idan ba haka ba, da tuni ba wannan maganan ake yi ba.

Ɓangarena ma baccin ne yayi gaba da ni, sai wajan azahar na tashi, fitowa nayi naji gidan shiru alaman duk basu tashi baccin ba, sai na shige kitchen na kunna gass na hau haɗa mana abincin rana, fried rice da yaji ice fish da haɗin coslow na mana, sai da na gama sannan na koma ɗakina lokacin ana ƙoƙarin shiga sallah, wanka nayi na ɗaura alwala na gabatar da sallah na sannan na fito dan tashin Mamina, amma sai na same ta zaune a palourn ta sha kyau, ina isa wajanta da murmushi sai kuma ga Alhaji ya shigo, alama daga masallaci yake, ƙasa nayi da kai na, Mamina ta ce, “je ki kawo mana abincin mu ci, mu yi la’asar za mu fita duka da Alhaji.”

Miƙewa nayi na haɗo mana abincin, na Alhaji na ajiye masa, na ajiyewa Mamina nata, sannan na juya, nawa na ɗebo na shige ɗaki, ina ci ina game a wayan Mamina da na ɗauko, binciken da na saba yi ko zan ci karo da layin wani ɗan uwan Mamina a wayanta na yi, amma ba ko alaman abinda ya shafi layin wani nata, ganin haka sai na dinga game kawai ina cin abinci, har aka ƙira la’asar, sannan nayi sallah na kuma wanka na sanya riga da skirt na swiss-less, ba ƙaramin kyau kayan ya mini ba, kuma ya zauna a jikina ɗamas, mayafina na yafa na fito, lokacin Alhaji da Mamina ma sun shirya, Mami kallo ɗaya ta mini ta ce na koma na sako hijabi, cunna baki nayi ina shagwaɓe fiska na ce tayi haƙuri, amma ta dage sai na sako hijabi, Alhaji ne ya bata haƙuri tunda a mota ne ta kyale ni da mayafin tunda ba ƙarami bane, Mamina da ƙyar ta ƙyale ni tana wasta mini mugun kallo, wanda nasan nufinsa bai wuce ta ce nasan halittan da Allah ya mini ko ina a cike amma bana son hijabi, ni abun har ɗaure mini kai yake yi, Mamina kaman wacce ta fito a jikin bishiya ba iyayene suka haifeta ba, ko kaɗan bata damu da kanta ba, burinta a rayuwanta komai nine, bata damu da mutuncinta ba tana kule-kulen maza, amma ni ko saurayi har yau bani da kuma ta hanani waya ma, ajiyan zuciya kawai na sauƙe tunda ta bar ni naje hakan ba komai, Allah dai shi ne mai starewa.

Tare muka fito duka, Alhaji ya shiga mazaunin driver, Mami ta zauna a gefensa kujeran mai zaman banza, ni kuma na buɗe gate, sai da motan ta fita sannan na kulle gidan gaba-ɗaya na nufi motan, a ƙofan gidan su Umaima na hango ya Danish da yake shigewa gidan bai ma kalleni ba shi, murmushi na sake na abinda na rashin mutuncin da na shirya masa, gidan baya na shige Alhaji ya ja mota muka shige gari, Japsal Shopping-mall muka fara zuwa, waje ne na sayayya kuma kayaki ne masu kyau da kuɗi a can, sayayya Alhaji ya mana ba kaɗan ba, kama daga dangin kayan sawa, kayan kwalliya, kayan abinci, kayan abun sha da su snacks, muna gamawa da sayayya kuma ya wuce da mu ADU, nan ma sai da ya mana ordern abinda za mu ci, kowa aka kawo masa abinda yake so, muka cika ciki, muka yi takeaway, ƙara zaga gari yayi da mu, yawo muka yi sosai kaman ba gobe, idan ka ganmu za ka ɗauka Mami da Alhaji, mata da miji ne da kuma ni ƴar su.

Sai da yamma tayi liss muka dawo da kaya niƙi-niƙi, Alhaji ya kashe kuɗi ba kaɗan ba, kuma ya ce kada Mami ta yi girkin dare, wannan takeaway ya ishe mu, idan da wani abin ma zai fita ya nemo, ni kuwa daman na jidowa Umaimata nata tunda nasan mayyar ice cream ce ita da naman kaza, muna iso wa, na sauƙa na buɗe ƙofa Alhaji ya shige da motansa, kayan da na jidowa Umaima na ɗauka na ce, “Mamina bari na bawa Umaima nata”, kamun Mami tayi magana tuni na fice a gidan da sauri saboda kada ta dakatar da ni, ai kuwa hakan aka yi, ƙwala mini ƙira ta dinga yi amma na gudu, Alhaji murmushi yayi tare da riƙo hannun Mami ya ce, “Amarya ta mu shiga ciki ko.”

Wani kallo Mami ta masa tare da ƙwace hannunta ta shige fuuuu! Ga haushin Alhaji ga haushin Banafsha ta fita ba hijabi.

Ni kuwa ina shiga gidan su Umaima na dinga leƙe-leƙen Ya Danish, amma ban gansa ba, kuma dai motansa na gida, nasan ba zai wuce yana part nasu ba, shigewa cikin gidan nayi ba kowa a palourn, sallama nayi na nufi ɗakin su Umaima, samunta nayi tana guga, murmushi na sakar mata, ta ce, “Masoyiya irin wannan kyau haka, komai Masha Allah! Daga ina?”

Ledan hannuna na miƙa mata na ce, “Ga tsaraba tawan.”

Umaima kaman za ta fire ta ce, “Wayyo! Allah bar mini ke Banafsha, Mamina Allah ƙara buɗi, wayyo naman kaza da ice cream, kutt har da shawarma, oyoyo chocolate” faɗin Umaima tana dariya.

Zama nayi a gefen gadonta na ce, “Mun godewa Allah da ba’a ƙauye kike ba, ko gidan talakawa da abin ya fi haka, Abbaa yana da kuɗinsa, yayyunki ma haka, kuma Umma na business, Ummu ma ba’a bar ta a baya ba, kuma babu wanda ba ya saya miki, amma idan kika ga kaza da ice cream kaman me, gaskiya idan Allah ya kai mu Abuja za ki ba da mu, muna zuwa saudi kuwa nasan sai na dinga riƙe ki, saboda kada a samu masu jan ki da dajaja(kaza da larabci), kinsan larabawan Makkah wasu yan albarka ne, wasunsu iskanci suke da mutane.”

Hararana Umaima tayi ta ce, “To zabiya, kanki ake ji, ki bari idan munje makkan sai mu tabbatar, ba kyau shedan zurrr.”

Nima rama hararan nayi ma miƙe na ce, “sai anjuma bari na shirya ki same ni a ƙofa mu wuce tahfiz.”

Amsawa Umaima tayi, na fice na shige ɗakin Ummu na gaisheta, sannan na fito ina ta kan leƙe-leƙe ban hango sa ba, yaya babba ne ya shigo gidan, da murmushi na ɗan rusuna na ce, “Sai babban yaya! Allah taimaki babban yaya.”

Dariya yaya babba yayi, ya ce, “sistor ba’a raba ki da abin dariya, kun gama exam’s lafiya?”

“Alhamdulillahi babban yaya, ya Auntynmu.”

“Tana lafiya, tunda kun ƙi zuwa gidan mu, ga baki ga hanci amma bakwa son shiga, daga ke har Umaima, bealkysou ce kawai ke shiga.”

Murmushi nayi na ɗan sosa kai, dariya yayi ya ce, “Allah shiryaki sistor, wannan kyau haka daga ina zuwa ina?”

Na buɗe baki zan basa amsa cikin kunya, sai muka jiyo muryan Umma tana masifa wai ta ƙirasa ya tsaya magana da fistararriyar yarinyar nan ƴar karuwa, yaya babba haƙuri ya bani da ido kawai ya wuce, ni kuwa fakan idon sa nayi ganin ya juya na aikawa Umma da murguɗa baki, juyawa nayi ina tafiya na, kaman daga sama kawai naji an zuba mini ranƙwashi aka ce, “Dan uwarki, fistararriya uwar tawa kike wa gastine da baki?”

Ina ɗagowa, idanuwana suka sauƙa akan Ya Danish, cikin zafin ranƙwashin na ɗaga hannu zan maresa, amma sai ya riƙe hannun nawa ƙam na kasa mosta sa balle ƙwace sa, wani kallo ya wasta mini ya ce, “mara tarbiyya kawai, dube ki haka kike yawo, uban wa za ki ja hankalinsa da wannan ƙazamin jikin naki, mai rijiyan kasuwa kowa zura gugansa yake, mara aji kawai.”

Taƙaici ne ya rufe ni na maganganun sa, na ma rasa da me zan rama ga shi har yanzu ya ƙi sake mini hannuna, idanuwana ne ke ƙoƙarin kawo ƙwalla, amma ƙoƙari nake wajan maida su, cikin dakewar zuciya na ce, “sake mini hannuna ni ba sa’ar yinka ba ce, wanda bai san darajar uwar wani ba balle a kai ga tasa” ina faɗa na ƙwace da ƙarfi, sai da na staya na ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan naja staki na ce, “Ni ko iskancin nake yi ai kasan na wuce wa irinka, na wuce yinka, na fi ƙarfinka, ba ka da abinda za ka isar da ni, ka yi kaɗan abinka yayi kaɗan, ka je a sake maka kaciya tukunna, riƙe hannuna ba zai sa naji komai a kanka ba, saboda kallon jariri nake maka, abinka kuɓewa ma ta fi sa a waje na, mtsww!” Ina gama faɗan haka na juya da sauri-sauri na bar sa a wajan tsaye da buhun mamaki, ni ko ina ficewa na juya na harari gidan, sannan na murmusa dan nasan ko banza na faɗa masa magana, ina dariya kaman ba ƙalau ba na shige gidanmu.

Ya Danish mutuwan tsaye yayi, jin abinda yarinya ƙarama ke faɗa masa, haushinta da stananta suka ƙara cika sa, ƙwafa yayi ya ce, “ko na fi karfin zura gugana a rijiyar mutane da yawa, to tabbas sai na gwada miki karatuna ya fi ƙarfin na ‘yan iskan abokan iskancinki” yana gama faɗa shi kaɗansa ya shige sashinsu ya fasa shiga cikin gidan ma, saboda taƙaicin Banafsha.

Ni kuwa ina shiga tun ba’a faɗa mini ba na buɗe motan Alhaji na dinga jidan kayan ina kai wa ciki, sai da na gama sannan na kalli Mamina a sace na wuce ɗakina, shiryawa nayi na fito na ce, “Mami sai na dawo.”

“A dawo lafiya” Mamina ta faɗa a taƙaice, na fice a gidan, a ƙofa muka haɗu da Umaima muka wuce tahfiz, sai da aka tashe mu sannan muka kamo hanya muna hira, na faɗa wa Umaima yau Malam Abbo bai zo ba Allah ya sa lafiya, amsawa tayi da Ameen tana kallona tana murmushi, saboda Umaima ta gama fahimtan akwai abu a zuciyan Malam Abbo game da Banafsha.

Tun daga hanya muka raba tasha ta yi gidansu, nayi namu dan kar Ya Danish ya ganta, ina isa gida na yi sallah na je kitchen na ɗauko rabona na ci, sai da muka yi isha’i, sannan muka zauna dukanmu, Alhaji yana ja mini aya ina ƙarisawa, haka muka dinga yi har dai muka yi iya dai-dai izu arba’in ɗin da za muyi musabaƙan a kai, ko ina ya canko ina idawa dai-dai, kuma yana tambaya ina basa amsa dai-dai, gyara biyu kawai ya mini, sai da muka yi sosai sannan ya kulle ƙur’anin ya sa na mayar da shi, muka zauna muna kallo, ba jimawa na musu sai da safe, sai da nayi karatu sosai na yi nafila da shafa’i da wuturi, sannan nabi lafiyan gadona na kwanta bayan nayi addu’an bacci.

Mami da Alhaji ba laifi yau ba’a yi faɗa ba, amma ko da suka shiga ɗaki Alhaji nafilfilu kawai ya dinga yi har Mami tayi bacci, shi kuma ya tattara ya koma ɗaya ɗakinss ya kwanta, bayan yayi waya da matarsa Hajiya Sa’adatu.

Washe-gari haka muka je tahfiz muka dawo, nan ma dai Malam Abbo bai zo ba, ya Danish dai ya gama haɗa irin muguntan da zai mini, sai dai cikin rashin sa’a kuwa ba mu haɗu ba har ya koma da yamma, haushi kaman ya kashe sa, amma ya gama cin alwashin wata satin zai gyara mini zama, Alhaji Mukhtar kuwa sai washe-gari Monday sannan ya sallami Mamina, ni kuma ya mini faɗa sosai akan na dage, idan nayi ƙoƙari shi ma zai mini kyauta duk abinda nake so, sannan ya ƙara ƙarfafa mini guiwa sosai, sai ya kama hanyan Yola, yana isa ya wuce airport jirginsa ta ɗaga sai garin kano kanawan dabo.

Ranan Monday munje tahfiz amma boko kam mun ƙyale sa sai result ta fito kuma next semester, a ranan aka gama komai da komai a tahfiz na shirin musabaƙa saboda daga ranan Laraba za’a fara kuma har sai asabar a gama saboda makarantu da yawa ne za su yi musabaƙan, an tashe mu akan ranan talata kada muje kowa ya huta kuma yayi karatu yayi addu’a, ni da Umaima kuwa washe-gari talata maimakon karatu sai muka shirya abinmu muka tafi gidan yaya babba duk da kusa-kusa ne amma yini muka kai masa tunda ya ce bama zuwa, kuma zai yi fushi, munje gwanin daɗi-daɗi Amaryan sa mai ɗan matashin juna biyunta ta amshe mu da fara’a, amma tunda yaya babba ya dawo taga yanda muke wasa da dariya da shi, musamman ni sai ta fara haɗe fiska tana hararata, kamun ka ce me ta tsawwalawa kanta wai kishi take da ni, amma daga ni har Umaima har yaya babba babu wanda ya hararo jirginta, abinda ya dame mu muke yi.

Sai da yamma tayi liss, sannan muka ma Amarya Hindatu sallama, amma sai wani cin magani take yi, ba mu damu ba yaya babba ya sako mu gaba muna tafiya muna hira har gida, kallona yayi yana murmushi ya ce, “su sistor an kusa zama graduate, ga kuma za’a ciyo mana kyauta a musabaƙa, sannan kuma za’a amarce.”

Ina dariya na ce, “wa ya faɗa maka haka babban yaya? Amarci kuma?”

Ya kabeer (babban yaya), yana dariya ya ce, “Faruq ne ya faɗa mini ai, wai haka kika faɗa musu, kuna zama graduate sai aure, inyee! Waye wannan mai sa’an? Ni na ɗauka ma da Danish za’a yi, irin wannan stamar tsakanin naku ai ta love ce, gaskiya koma waye a basa haƙuri muyi tuwo na mai na.”

Haɗe fiska naayi, girar sama da ƙasa duk na haɗe su, na tura baki tare da bankawa Umaima harara kaman ita tayi maganan na ce, “Ni na tafi gidanmu sai gobe.”

Yaya babba yana ta ƙira na amma naƙi juyowa, dan sosai ya ɓata mini rai, ni ba aure ne a gabana ba, ba zan je a dinga wulaƙantani ba, kuma ko auren zan yi har abada babu abinda zan yi da Ya Danish, ni ban taɓa jin na tsani mutum a duniya yanda na tsani ya Danish ba, a haka rai a haɗe na shige gida, Mami ta kalle ni kawai ta girgiza kai, cikin sigan rarràshi ta ce, “Wa ya taɓa fitilar Maminta? Shalelena, Sayyada Faɗimah, autar mata, shugabar mata, gudalliyan Maminta.”

Tura baki nayi, kaman zan yi kuka na ce, “Mami ba kina ganin babban yaya ba, wai ai…wai… wai ai..uhmñ!”

Mami murmushi tayi ta ce, “kina ta cewa wai wai kin kasa faɗan abinda ya faɗan, wai me?”

Langwaɓar da kai nayi na tura baki na ce, “uhmñ! Ni dai ba ruwana kada ma yan Ameen su amsa magana ya wuce.”

Mami taɓe baki tayi ta ce, “Idan tayi tsami zan ji, in kuma sun riga sun amsa, shikkenan ko mutuwa za kiyi yess ne, indai alkairi ne.”

Tashuwa nayi kawai na wuce ɗakina, jin Mamina za ta ƙara nata akan na babban yaya.

Babban yaya kuwa dariya ya dinga yi, Umaima tana taya shi ta ce, “yaya ka kora mini Masoyiya kuma kasan ba wannan maganan tsakaninta da ya Danish, ranan ina laɓe ina ganin su har da ranƙwashinta yayi, ranan da ka zo da yamma.”

Murmushi yaya babba yayi ya ce, “Nima na gani ai, na sani Umaima, da gangan na faɗa, amma na sani Danish da Banafsha ba wannan magana, mutane kaman masu ganin hanjin junansu,ya riga ma da ya ɓata rawansa da stalle babu ta yanda za’a yi ta ƙaunace sa.”

Umaima dai murmushi tayi ta shige gida yaya babba kuma ya juya ya koma gidansa, yana shigowa ya kalli matarsa ta haɗe nata giran sama da na ƙasa, fiska kaman an haɗo mummunan hadari, cikin mamaki ya dubeta ya ce, “my love me ya faru? Ko baby ne ya naushe ki? Ya faɗa yana murmushi tare da zama a gefenta.

Stam! Hindatu ta miƙe ta koma gefe ta zauna, tare da juyar da kai, yaya babba bai kawo komai a ransa ba akan su Banafsha, kawai ya ɗau abun akan ko fushin masu ciki ne, haka ya dinga lallaɓata, da ƙyar ta haƙura sannan ta ce ya shiga tsakanin Banafsha da zuwa gidanta bata so, babban yaya kam mamaki ne ya kashe sa a zaune, wato daman abinda ya sanya ta sauya fiska tun ɗaxu kenan, girgiza kai kawai yayi ya lallaɓata komai ya wuce.

Banafsha duk da tasan gobe ba lallai a fara da su ba, amma ta dage da karatu da addu’a, duk da gefe guda na zuciyarta tunanin rashin zuwan Malam Abbo kwana biyu ne cike fam a ciki, haka kawai take kewansa sam bata jin daɗin rashin ganinsa.

Ɓangaren Umaima ma karatun da addu’an tayi sosai, Nana ce ta shigo ta ce, “yaya Umaima wai inji Umma ki zo.”

Miƙewa tayi ta fice, ɗakin Umma ta shiga da sallama, bayan ta zauna a gefe ta ce, “Umma gani nan.”

Rai a ɓace Umma ta dubi Umaima ta ce, “Umaima! Umaima! Umaima! Sau nawa na ƙira sunanki?”

Umaima ta ce, “sau uku Umma.”

“Umaima kinsan dai ni ce uwarki ko? Ni na stugunna na haifeki ba wata banza ba ce ta haifa mini ke, kibar ganin ansaka miki sunanta tana nuna tana sonki, to duk soyayyan munafurci ce ba ta gaskiya ba, Umaima ki nistu ki shiga hankalinki da ni, kada ki bari rai na ya ɓaci kiga fushina, ko kuwa na miki baki akan wasu mutane daban, Umaima uban wa ya ce kije gidan kabeeru da wancan fitsaratun yarinyar?”

Umaima tura baki tayi ta ce, “Umma kiyi haƙuri, wallahi ni ba ruwana babban yaya ne ya ce muje da ita.”

Umma hararan Umaima tayi ta ce, “Dan ubanki rufe mini baki, munafuka kawai, ƙarya za ki mini? Bansan halinki ba ne ko me? Sau nawa ina faɗin ki fita harkan yarinyar nan bana so, bana so amma kin mini kunnen uwar shegu kinƙi ji, to kada ki bari rai na ya ɓaci.”

Tura baki Umaima tayi ta ce, “ki yi haƙuri Umma.”

“Tashi ki bani waje kamun na karya ki yanzun nan, mara zuciya kawai wacce bata gaji uwatta ba.” Faɗin Umma kaman za ta kifawa yarinyar tata mari.

A ɗari Umaima ta tashi ta fice, ta koma ɗakinsu tana faɗin, “Allah huci zuciyanki Umma, Allah shirya mana ku iyayenmu.”

Washegari Umaima da Banafsha suka shirya staff suka tafi tahfiz, Banafsha da Malam Abbo ta fara yin tozali, farinciki kaman ya kasheta, har Malam Abbo sai da ya kusa fahimtan hakan saboda ya ga wani irin murmushi da take sakar masa, abubuwan da ya kamata suka yi sannan aka ɗauki ɗalibai aka tafi wajan gabatar da musabaƙa, makarantu ne kusan nawa, haka aka fara gabatar da musabaƙa, ɗalibai kowa na iya ƙoƙarinsa, amma har aka tashi na yau ba’a taɓo ɗaliban makarantan su Banafsha ba, sai da suka dawo sannan Banafsha ta sa Malam Abbo a gaba da shwagaɓa wai me ya sa kwana biyu bai zo ba, Malam Abbo murmushi kawai ya mata ya ce su tafi gida ta ci-gaba da dagewa da karatu.

washe-gari ma haka aka yi musabaƙa lafiya-lafiya kuma dai ba’a iso su Banafsha ba, Laraba, Alhamis, juma’a duka ba’a iso su Banafsha ba, kuma abu na ta kan tafiya, ɗalibai masu ƙoƙari suna yi, wasu kuwa ana musu gyara, wasu kam ma dismiss nasu ake yi saboda they’re not fit and compited, ɗalibai da dama wasu akwai ilimin, akwai kuma ƙoƙarin, amma ba su da confidence na tsayuwa a gaban dubban jama’a su gabatar da abu, wanda kuma wannan confidence ɗin shi ake buƙata a wajan ɗalibi, wani sa’in ma shi aka fi buƙata fiye da ƙoƙarinsa ko iliminsa, so dan haka yaranmu students ku dage, ku sa a ranku kuna da ƙwarin guiwan stayuwa a gaban duniya kuyi magana, just feel you can stand and talk for whole world, wannan courage shi ake buƙata, Allah ya taimaka wa yaranmu masu karatu da mu kanmu, Allah buɗa basira ya dafa mana a ko wanni hali da juyin rayuwa.

<< Yar Karuwa 6Yar Karuwa 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×