Skip to content
Part 8 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

 KANO STATE

A babban filin sauƙan jirgi na garin Kano, jirgin su Alhaji Mukhtar yayi landing, yana sauƙa ya samu already driver na jiransa, yana isowa wajan motan sai driver ya buɗe masa gidan baya ya shiga, sannan ya kulle ya koma ya shige ya ja motan suka nufi Railway estate, anguwan manyan ƙwari kenan a Kano, daga sunan kunsan ba wajan cin miyan lami bane.

A gaban wani katafaren, shirgegen, haɗaɗɗen gida wacce ke ɗauke da wata arniyar gate ga sojoji ko ta ina, driver na horn aka buɗe musu suka danna hancin motan cikin gidan, subhanallahi! Wata munafukar estate ce, upstairs guda biyu, sai haɗaɗɗun plat guda biyu su ma, ga motoci sun kai goma manya-manya masu shegun kuɗi, upstairs na farko Alhaji Mukhtar ya nufa fiskansa ɗauke da murmushi, yana tura ƙofan ya shiga da sallama, da wata kyakkyawar matashiyar budurwa wacce ba za ta wuce sa’ar Banafsha ba ya fara karo, murmushi ya sakar mata tana masa oyoyo, hugging nata yayi ya ce, “Maman babanta sannu ko.”

Murmushi budurwan ta saki ta ce, “Papi staraban Adamawa.”

Alhaji shafa kan ‘yar budurwan yayi ya ce, “Majeeder tun ban huta ba?”

Murmushi kawai tayi, Alhaji ya riƙo hannunta suka ƙarisa shigewa palourn, har suka haura sama da yake part na Alhaji, suna haurawa kuwa sai ga wata hamshaƙiyar mata kyakkyawa, wacce kana ganinta kasan ita ce mahaifiyar Majeeder, Hajiya Sa’adatu kenan uwargida ga Alhaji Mukhtar, harara Hajiya ta bi Majeeder da shi ta ce, “Jeedderh ban aike ki ba ne, me kika tsaya yi?”

Majeeder tura baki tayi ta juya, Alhaji Mukhtar murmushi kawai yayi bai ce komai ba, shi ne ya ce, “Hajiya Barka da gida.”

A gadarance Hajiya ta ce, “Sannu da dawowa Alhaji.”

Amsawa yayi kawai ya shigeta ya wuce ɗakinsa, sai da ya rage kayan jikinsa ya zauna bakin gado tare da sakin murmushi ya ce, “Allah Sarki duniya, ba dole mu bi mata ba, ai dole maza su nemi matan banza, mace ce a gidan sunna wai bata san yanda za ta kula da mijinta ba, sai ka je wani wajan sai a dinga tarairayarka, ga shi dai saɓon Allah ne a wajen, Astagfirullah! Allah na tuba, Allah ka mallaka mini Ramlah idan ita alkairi ce a gare ni, ba dan halina ba ya Rabbi.”

Yana gama magana ya miƙe ya shige toilet ya wasta ruwa sannan ya zo yayi sallolinsa ya jawo system nasa ya fara duba ayyukansa, yana gamawa ya bi lafiyan gado ya kwanta, yana son ya huta saboda nan da kwana biyu zai tafi Russia akan business nasa da wani abun gaggawa ya taso.

Hajiya Sa’adatu tana ganin Alhaji ya shiga ɗakinsa ta juya ta koma nata, tare da fidda waya tana ta magana akan nata business ɗin ita ma.

Mata mu gyara, abun haushi da iya matan masu kuɗi ke kasa kula da mazajensu, saboda boko ta jiƙa su ko issuen harkokinsu to da sauƙi, amma baiwar Allah kina salamatu ‘yar malam muhammadu ke ba juya dubu ba balle ya koma dollar, aikin me kike da za ki kasa kula da miji ki tarairayesa? Maza dai ƴan haƙuri ne, balle ma a wannan zamani da muke ciki suke ganin mun fi su yawa, to ki kula ƴar uwa, aure ya fi gaban wasa, idan mijinki ya bi matan banza ke kika nema, idan mijinki ya miki kishiya babu niya wannan ma ke kika jajuɓo ma kanki, Aradu mata iyayenmu da mu kanmu da kuma ƙannenmu kowa ya gyara halinsa.

Majeeder tana tura baki ta shige ɗakinta da ke nan a ƙasa ta sanya after dress ta fito, mota guda ta ɗauka da kanta ba driver tayi driving ta je ta amsawo Hajiya saƙonta, hankali kwance duk da tasan Papi ya hanata driving da kanta, Majeeder Hauwa’u Mukhtar Sule Kwalli, ɗiya ta biyu kuma ‘yar Auta ga Hajiya Sa’adatu, da Alhaji Mukhtar, Majeeder kyakkyawar gaske ce, bata da haske sosai, tana nan kalar stamiya haka, tana da hanci mai stayi da ƙaramin lip’s nata ja da shi, tana da idanuwa ‘yan dai-dai, bata da stayi sosai haka ma jiki, ƴar dai-dai ce ita, tana da gashinta mai tsayin gaske baƙi wuluk da shi.

Tana dawowa ta hauro sama ta kawo wa Hajiya Sa’adatu aikanta, sannan Hajiya ta ce ta koma ta cewa masu aiki a ɗaura girki kamun Alhaji ya tashi a bacci, a haka ta juya ta kuma faɗa musu, sannan ta shige ɗakinta ta cire kayan jikinta ta wasto ruwa ta zo ta ɗau wayanta tana lastawa, Majeeder maƙura ce a kyau da kuma sura.

Alhaji sai da ya huta sosai sannan ya tashi ya wasta ruwa, palourn ƙasa ya dawo ya zauna yana kallon labarai, ƙiran layin Mami yayi suka sha firansu, yana gamawa Hajiya ta shigo palourn, waje ta samu ta zauna ta ce, “Alhaji ka faɗawa yaronka ya cire layina a blacklist, ya ɗau ƙirana ko na saɓa masa, yaro kaman ba nice uwarsa ba duk an bi an kanainaye sa, baya girmamani balle mutunta ni ko yaji tausayina.”

Alhaji Mukhtar murmushi yayi ya ce, “Hajiya ke ɗin ce kika nuna masa haka ai, yanzu ma idan ba ki daina wasu yawo-yawon nan ba, zan tattara Majeeder ita ma na mayar da ita gidan General tun da shi matarsa mai zama ce, tasan mutuncin aure, ko kuwa na auro wata sai ki ci-gaba da halinki.”

Baki na kumfa Hajiya ta yunƙuro cikin haushi da kishi ta ce, “Babu ubanda ya isa ya ɗauka mini yarinya, idan wancan nayi shiru to wannan ba zan yi ba, kuma ba’a haifi uwar shegiyar da za ta haifa mini kishiya ba, baka isa ba, kuma ni halina lafiya lau yake atou.”

Murmushi kawai Alhaji yayi ya ci-gaba da kallonsa, shi Alhaji haka yanayinsa yake, shi mutum ne da kamun kaga fushi a fiskansa to za’a ɗau dogon zango, yanayinsa ke sanya Hajiya Sa’adatu yaudaran kan ta tana tunanin ko ta mallakesa ne.

Hajiya kuma cigaba da yin nata surutun tayi kaman wacce aka kunnata, har dai ta gama ta gaji tayi shiru, Hajiya Sa’adatu irin matan nan ne masu kuɗi, marassa mutunci, masu wulaƙanci, ita ko yaranta ba su da lokacinta balle mijinta, gaba-ɗaya tunaninta akan business nata ne, kuma saboda haka ne ta stayar da haihuwanta wai yara biyu sun ishe su, kada ta stufe ko su hanata kula da harkokinta, karshe ma zuwa tayi aka cire mata mahaifa Alhaji bai sani ba

Kwana biyu tsakani, Alhaji ya shirya ya tafi Russia kuma zai yi sati biyu kamun ya dawo, yana tafiya washe-gari Hajiya Sa’adatu ta ɗaga ƙafafuwanta ta tafi Dubai, sai da ta yi kwana uku sannan ta dawo, kuma bata sanar da Alhaji ba, Majeeder dai tana gida, daga ɗaki sai ɗaki, sai kuma driver ya kai ta makaranta idan ta dawo ya kuma kai ta islamiyya, inda a can ne ma suka yi musabaƙa, har Alhaji Mukhtar ke bawa Banafsha labari lokacin da ya kai ta school.

Alhaji sai da ya kwashe sati biyu casss, sannan ya dawo, ranan ya samu Hajiya Sa’adatu sun fita da wata ƙawarta, Hajiya bushira sun je akan batun siyasar da Hajiya bushira ke ƙoƙarin stayawa takara, Alhaji ya riga ya saba da halin abarsa, shiyasa kawai ya share ya zauna, ko da ta dawo bai ce mata komai ba.

LAGOS

Banana Island

Anguwa ne na shegun ƙasa, manyan a ƙasa ba iya Lagos ba, anguwan sai wane da wance, ba ko wani laga-lagan me kuɗi ke mallakan gida a wajan ba, sai wanda ya cika cikakken babban ƙusa, fili mai araha a wajan, iya fili babu gini, arahansa shi ne 10billion, a hakanma da ne lokacin da duniya ke zaune shiru ba yanzu da komai ya tsaya da ƙafafuwansa ba.

Wani gida ne wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa, kusan a street ɗin babu irinsa wajan haɗewa, Arnen haɗaɗɗen gida ne na gani na faɗa, kana ganin gidan kasan da starinsa da komai daga ƙasar waje ne, sai dai masu ginawan dole yan Nija ne, domin idan ana neman ‘yan baiwa waɗanda suka san kan gini duk iya staruwansa to sai baƙaƙen fata, turawa masu jan kunne barsu dai kawai da iyayi, Nigeria my country.

Tsayawa tsara yanda wannan haɗaɗɗen Arnen gidan yake, to tabbas ɓata baki ne da cin lokaci, dan sai mu cinye page’s a abu ɗaya, tun daga wajen gidan har ciki sojoji ne kaman wanda gidan barikin sojijine ba gidan mutum ba, kai kawo sojojin ke yi kaman masu yin Safa da Marwa, Uwar batoorl ta nufi cikin haɗaɗɗen ginin dan kwaso labari sai taji iska na neman ka da alƙalaminta, a ɗari ta ɗago, da mamaki nake kallon jirgi ne na sojoji ke shawagi a saman gidan, can kuma sai ga wani ya fito a jirgin kaman zai diro, amma hannunsa riƙe da igiya har sai da ya sauƙa a cikin gidan, sannan ya sake igiyan, masu jirgin suka janye suka yi gaba, wannan bawan Allah na juyowa sai da Uwar batoorl tayi suman wucen gadi.

Starki da godiya su tabbata ga Ubangijin kowa da komai, wanda ba ya gyangyaɗi balle barci, Sarkin da mutuwa ta koru gare sa, Sarki mai stara halittan bawa yanda ya so, Wani haɗaɗɗen guy ne wanda a ƙalla zai kai shekaru 34 da haihuwa, kyawunsa har ya wuce misali, idan aka ƙirasa kyakkyawa ma to an mai da sa baya ne, saboda irin haɗuwansa, gaskiya Allah yayi halitta a wajan.

Jikinsa ɗan dai-dai, yana da ɗan stayi da ya tafi da yanayin jikinsa, fari ne tasss ma kuwa kaman Balarabe, duk yanda ma aka yi ya haɗa jini da ‘yan wata ƙasar bayan Nigeria, idanuwansa dara-dara kaman na mace, wanda na tabbata duk wanda ya gansa zai so ƙara ganinsa ko dan idanuwansa, daga gani ba ƙaramin rububi mata ke yi akan idanuwan nan ba, yana da hanci mai stayin gaske kaman na Majeeder, yana da ɗan ƙaramin baki, lip’s nasa ja kaman na Majeeder, matuƙar kama suke yi da ita, banbancinsu kawai launin fata, da ɗan gemunsa dai-dai kaɗan, da sajensa dai-dai, sannan ga wani irin arnen kisto a kansa, da gashin sa da yayi kama da na larabawa, da aka kista kuma yayi kaman na turawa masu baƙin gashi, wata kafurar aski aka masa sannan aka kista gashin nasa, mai tsayin gaske, sanye yake cikin kaya mai kama da up&down, wanda zip ake buɗewa a gaban daga sama har ƙasa a saka, rigan haɗe yake da wando, kuma kayan irin na sojojin sama ne, ƙafansa kuwa sanye yake cikin sandal’s wanda shi ɗin ma na sojoji ne, ga wani uban headphone a kunnensa shi ɗin ma irin kakin sojojin sama ne kalansa.

Tunda wannan haɗaɗden guy ɗin ya sauƙo daga jirgi ta sama, shikkenan duk sojojin cikin gidan suka sha nistojin, suka nistu sai zuru-zuru kawai suke yi, amma tun sauƙansa duk suka sara masa suna faɗin, “Welcome Sir.”

Wannan gayen bai ko ɗaga idanuwansa ya kalli mutum ɗaya a cikinsu ba, cikin isa da ji da kai yake tafiyarsa ta jarumai har ya shige katafaren gidan nasa, ya

Ilahi! Fan’s ga wata dalleliyar palourn ma wacce koman cikinta ordern waje ne, colorn komai na babban palourn blue black ne da kuma light arsh, komai yaji zam-zam, komai ya haɗu ya gaji da haɗuwa, cikin isa yake tafiya har yanzu headphone ɗin na kunnensa, sai gyaɗa kai yake yi har ya haura ɗan step’s ɗin, ya tura wani kyakkyawan ƙofan glass ya shige ciki, da wani makeken gado na fara tozali, gado ne wanda mutum goma ma sai su kwanta lumui lafiya, ba dan irin starin gidansu na can ba, a nan arewa kam babu irin ɗakin.

Yana shiga ya cire kayakin jikinsa duka ya bar boxers kawai, ya tura bathroom ya shige, sai da ya wásta ruwa ya fito ɗaure da guntun towel sannan na kuma ganin irin haɗewansa, jikinsa daga bayansa zuwa hannayensa duk tatoo ne, ƙirjinsa mai cike da gashi ne kawai babu tattoo, kuma ba ƙaramin kyau zanen ya masa ba, gaban mirror ya je ya danna wani abu, sai ga mayukan shafawa iri da kala, yana shafawa ya maida, ya kuma danna wani turarukansa suka fito, sai da ya gama shafe-shafensa staff ya yiwa wannan kiston kan nasa mugun gata, sannan ya wuce wajan kayakinsa ya ciro 3quater da armless duka na sojoji ya saka abinsa, ya kuma feshe kansa da turare kaman ba lau ba, sannan ya ɗau wayoyinsa ya fito a ɗakin, da kansa ya shiga kitchen ya haɗa dan abu dai-dai mara nauyi, wanda zai iya ci ya kawo dinning da kansa ya ci, yana gamawa ya tashi ya koma palourn sa ya kwanta tare da kunna TV ya kamo tashar turawa da ake romantic films, wanda matan suke yawo kusan tsirara, bai wani mai da hankali sosai akan TV din ba, ya fidda wayarsa ya shiga dialing layin abokinsa.

Ana ɗauka a ɗaya ɓangaren aka ce, “Assalamu’alaikum! Kunga ƴan iskan gari, manyan gari, arnan gari, masu certificate a Nigeria da ƙetaren Nigeria.”

Murmushinsa mai tsada ya saki tare da shafa kiston kansa ya amsa sallaman, sannan ya ce, “Abeed ka daina kafurta ni, ina musulmi ɗan musulmi, jikan musulmi, haihuwan musulunci.”

Abeed ma a nasa ɓangaren murmusawa yayi ya ce, “Chief of the air staff Bunayd (CAS bunayd), manyan ƙasa ya aka yi? Da alama kana Lagos, yaushe ka dawo daga New York ɗin?”

“Ko 1 hour ban fi da dawowa ba, ya kake ya kowa da kowa? Ya kamilarka?”

Dariya Abeed yayi ya ce, “ka ce kada a ce maka arnen ƙasa, ga shi kana cewa wai ina kamila ta, kai fa kaƙi ganewa CAS, hadisi ne fa guda ya ce Adduniya mata’un wa….”

Bunayd dakatar da shi yayi ya ce, “wa khairu mata’u ha, mar’atussaliha.”

Abeed ya ce, “ɗan iska, ai nasan ka sani, take saninka kake yi, wai kai ka dage baka son kamilar mace, to kai baka son mar’atussaliha ɗin kenan? Ka fi son wacce za ta kashe ka a tsaye ko.”

Murmushi mai tsada Bunayd ya saki ya ce, “Kai baƙon duniya ne tukunna har yanzu, baka san rayuwa ba Abeed, kaƙi wayewa kwata-kwata sam, ga ka dai ka zaga duniya amma shiru kakeji, diɗim kaman an shuka dusa”, ni dai Uwar batoorl da mamaki nake kallon wanga haɗaɗɗen gayen, ganin har da ƙarin hausa ya iya, ba iya hausan ba, mutumin da idan ka kallesa ka ɗauka ko kunnen uwarsa aka ce da hausa ba zai ji ba.

Abeed a ɗaya ɓangaren ya ce, “To nidai bana fatan shigowa wannan irin taka rayuwan, ina cikin rayuwa kana faɗin bansan rayuwa ba, to kai ba ka son kamammiyar mace saliha, me mastalanka? kaƙi maganan aure gida da waje, ko ƴan iskan turawan da suke maƙale maka kaƙi su wai iskancinsu yayi kaɗan, su ma basu san rayuwa ba tukunna, duk irin fitsarar su ai dai kasan ko karuwa bata kai matan turawa iya iskanci ba, mutanen da suke yin BF kuma me ya rage musu.”

Bunayd taɓe baki yayi ya ce, “Ba za ka gane ba Abeed, ka riƙe kamilarka, sunan wani wai saliha, to riƙe abarka, ni tsagerar ƴar iska cikakkiyar nake son na samu tukunna, idan na jarrabata naga ta gane rayuwa tasan ta kan harkan caja Palace, da kuma cinikin ka saya ɗaya a baka biyu kyauta, to normal ne ba mai hanani aurenta sai Assamadu.”

Abeed guntun tsaki ya ja ya ce, “Yanzu haka ga shi ina jiyo screaming na mace da alama dai film ɗin naka kake kallo na yan iska, kai kaƙi kallon Blue Film amma kana ganin irin waɗannan, kaƙi cin biri ka ci dila, wai ba cinyar ba ƙafan baya, to me marabin dambe da faɗa?”

Murmushi Bunayd yayi ya ce, “Kai yaro ne, kanka yayi kaɗan ko na banbanta maka ba za ka gane ba, anyway ni dai tantiriya wacce ta san ta kan harkar caje Palace nake nema, ina samu kuwa wuff da ita zan yi, kullum cikin kwaso shoki a Palace zan kasance, amma kaga kamilallun nan, daga first night sai a ce sai ka yi week kana barinsu su huta, kuma a na ɗan stallake kwanaki, amma kaga ina samun stagera, tantiriya wacce tasan rayuwa tasan duniya, wacce za ta iya laying nawa a down ta mini full cherge to komai dai-dai, ni ina ƙulla abota da Palace to ko period haka zai ganni ya bar ni, saboda ba ma ƙyamar jinin nake ba, a haka sai na caje Palace hankali kwance, duk normal ne, saboda mugun yin Palace da nake to wannan jininma yinsa nake irin overn nan hundred percent ma kuwa.”

Dariya Abeed ya kwashe da shi kaman mai ƙaramin hauka, ya ce, “daɗina da kai ka iya surutu akan wannan Palace-palace da ka addabi mutane da shi, in iskancin kake ji da tantiranci na tantiraye cikakkun ƴan iska, ai sai ka ƙira sa da asalin sunansa.”

Murmushi Bunayd yayi ya ce, “Man baka san rayuwa ba, ai yanzu an waye, duk dirty talks ɗin nan shirme ne, idan ka ce Palace ya kaji yanda abin ya bada citta? Ai normal kawai ako ina a bajeta kawai duk wanda ya gane normal, wanda bai gane ba ma can da yawarsa.”

Dariya Abeed ya dinga yi, shi dai Bunayd sai dai murmushi mai shegen zafi kawai, maganganun ma kaman ba shi ya ke furta su ba, a haka suka dinga wayarsu cikin nishaɗi har suka yi sallama, Bunayd ya kashe wayansa ya kalli TV dai-dai lokacin wani bature na sucking Palace na wata babe tasa, murmushi Bunayd yayi ya ce, “ai ku ne duniya, ku ne sanin duniya, Allah nima ka bani tantiriya ta wacce zan wanke mata Palace na ɗauraye shi, na lashe shi, na busar da shi, na masa full cherge.”

Alwala yayi tare da yin Sallah sannan ya kwanta a makeken gadonsa, ba jimawa bacci yayi gaba da shi, da mamaki dai nake kuma kallon CAS Bunayd, ganin namiji da shi amma birgima yake yana juyi a ƙaton gadonsa, sai tale ƙafa kuma yake kaman abin ba dama.

Shi ne bai tashi bacci ba sai can yamma, yana tashuwa da addu’an bacci a bakinsa ya ɗaura alwala, karatun Alkur’ani mai girma yake rerawa, subhanallahi fan’s wannan CAS ɗin da abin mamaki yake, kunji kira’a kuwa kaman limamin Saudi ke rerota, sai da lokacin Magrib tayi sannan ya aje ƙur’anin, ya tashi yayi sallahnsa, nan ma komawa yayi ya zauna yana azkar yana jan carbi, shi ne bai tashi a wajan ba sai da yayi isha’i, yana idarwa ya miƙe tare da fitowa cikin gidan nasa, wanda yake da haske tarr ko ta ina kaman da rana ne, ga kuma sojoji na kai komo kaman masu jiran ko ta kwana, yana tsaye yana shan fresh air ƙira ya shigo wayansa, ɗauka yayi ganin General ne, cikin yanga yayi sallama, General ya amsa tare da cewa, “kana gidanka ko?”

“Yes General.”

Jinjina kai General yayi a nasa ɓangaren ya ce, “Okay! Ka zo gida yanzun nan.”

Ɓata fiska CAS yayi kaman wani ƙaramin yaro ya ce, “Toooo! An coming.”

General murmushi yayi tare da kashe wayansa, CAS Bunayd kuwa cikin gidansa ya koma, wanka ya kuma fesawa ya saka wani armless ɗin da 3qauter, feshe turarensa yayi ko ta ina sai ƙamshi kawai yake yi na fitan hankali, yana fitowa wasu sojoji da gudu-gudu suka ɗauko motoci kusan guda goma, CAS Bunayd kallonsu yayi ya taɓe baki fiskan nan a haɗe, kaman an haɗo baƙar hadari, da mamaki na ce ashe dai mutuncin da fara’an wa iya abokinsa ne, waɗannan sojoji Aradu suna ganin rashin mutunci wajan wannan Bunayd ɗin, cikin isa ya ce su ƙyalesa zai je shi ɗaya, amma suka ce ina, saboda baya son dogon magana da su, motan da ke tsakiya wanda ya fi ko wanne haɗuwa suka buɗe masa ya shiga, duk da gudu-gudu suka shige nasu motocin, a saba’in suka bar cikin gidan, motoci biyar a gaban nasa, biyar a bayan nasa, sai stula gudu suke a cikin garin Lagos, gudu na Allah stine uwar mai ƙarya, domin ba laifi su ma sojojin, suna fesa rashin mutuncinsu a kan kwalta, idan ka sake ka kusto gabansu to rip gare ka, dan kaman ba su da birki, ga mugun gudun stiya, shi dai CAS Bunayd yana hakimce a bayan haɗaɗdiyar motansa, sai lasta wayansa yake hankali kwance ko ɗago kai baya yi, kuma daman wannan al’adansa ne, shi abinda yake gabansa kawai yake yi, in za ka shekara staye a kansa ko a gefensa, sai ya shekara bai dago ya kalleka ba, ko kuma bai juyo ba.

Victoria Island suka nufa, nan ɗin ma anguwan wasu manyan kusoshin ƙasa ne, anguwan manyan yan kasuwa, manyan masu kuɗin ƙasa, da kuma sojoji da ƴan siyasa.

A gaban wani katafaren kantamemen gida suka buga wata mahaukaciyar horn, kaman za su tashi garin Lagos da bala’i, wannan gidan ma sojojin ne ko ta ina kaman kayan banza, ana buɗe musu, suka danna hancin motocinsu ciki, Masha Allah! Wannan gida ma ta haɗu ta tafi da zuciyata, ba dan gidan manya ba ne to da tabbas motocin CAS Bunayd ba za su samu mastugunni ba, amma da yake wannan gidan ma ya amsa sunansa, to kaman ba motoci goma sha bane suka shigo, kuma akwai wasu arnun motocin a gidan ma, waɗanda suke mallakin mai gidan.

Suna gama parking, wani soja ya zo da gudu ya buɗewa CAS Bunayd ƙofa tare da ƙamewa ya sara masa, amma bawan Allah sai da ya kusa mintuna biyar a cikin mota sannan ya jeho ƙafa guda a waje, can da ya gama iyayinsa sai ya fito gaba-ɗaya, wannan karon har da glass ya maƙalawa fiskansa da babu annuri, cikin isa yake takunsa na ƙasaita, hannu guda a aljihu hannu ɗaya riƙe da wayansa mai stadan gaske na yayi, ga kuma uban headphone a kunnensa, a haka ya shiga gidan da sallama kansa akan wayansa, ba ruwansa da an amsa sallaman ko ba’a amsa ba ya haura sama direct, a palourn sama ya samu General a kwance Matarsa Hajiya Huraira tana masa tausa, duk da shigowan CAS Bunayd bata bari ba, ci-gaba tayi ta aikinta tana sakarwa yaron nasu murmushi.

Waje CAS Bunayd ya samu ya zauna, cire glass nasa yayi, sannan cikin girmamawa da maganarsa ta yanga ya ce, “General barka da gida, Momsee sannu da aiki.”

Hajiya Huraira wacce suke ƙira da Momsee, tana murmushi ta ce, “Yauwá, sannu Bunayd, fatan ka dawo lafiya?”

“Alhamdulillahi Momsee” ya faɗa yana mai ɗan kishingiɗa.

General ya ce, “My Man, yaushe ne ka dawo?”

Cikin shagwaɓa kaman ƙaramin yaro ya ce, “Yau na dawo.”

“Good! Sannu da hanya Man, wai me yasa baka son zama anan gidan ne? Ka yi gida a gefe ka koma can da zama menene damuwanka? Ko dai rashin ji kake shukawa?” Faɗin General idanuwansa akan Bunayd.

CAS Bunayd shafa kiston kansa yayi dan ya fahimci nufin General na cewa wai ko rashin ji yake shukawa, murmushi yayi mai stadan gaske ya ce, “General ni ba wani abinda nake shukawa, just small boy like me ai babu abinda zan iya yi, ba mace ko ɗaya a gidana, kuma wasu ayyuka nake yi, amma zan dawo, nima ba daɗin zaman can ɗin nake ji ba.”

General yana kallon Bunayd cikin soyayyan da yake masa ya ce, “Kai ne small boy? Anyway shikkenan, I trust you, nasan ba za ka shuka rashin ji ba, yanzu dai ko baka kammala aikin ba, ba inda za ka koma, ka dawo kenan, bana son zamanka kai kaɗai a gida.”

Haka ya ƙara marairaicewa kaman ɗan goye ya ce, “General zan dawo da gaske fa”, magiya Bunayd ya dinga yi da gaske, sannan General ya amince akan idan ya gama ya dawo, sosai General yake ƙaunan Bunayd, shi ya sakalta shi, ya shagwaɓa shi.

General ya ce, “To kai ka ce small boy ne kai, yaya kuma ya ce aure za kayi, dan kada ka shuka rashin ji, dan nasan dai ba lalacewa za ka yi ba, sai dai shuka rashin ji ɗin.”

Murmushi CAS Bunayd yayi ya ce, “General ka ƙyale Sir, ni har yanzu gaskiya banga wacce ta mini ba.”

General ya ce, “Amma dai kasan halin yaya ba, staff zai aura maka wata, gwanda kawai ka nemi nistasttiya tun wuri ku dai-daita, ni bana son a maka abinda baka so.”

CAS Bunayd ɓata fiska yayi ya ce, “General to gaskiya da ace Sir yasan irin macen da nake so, ai ba mastala ya zaɓa mini, amma ga shi kai ma da muke tare kana cewa nistasttiya balle kuma Sir, ai sai ya ce shi kuma kamila mai kwana da hijabi tana guma Palace zai nema mini, gaskiya a barni na nemi irin wacce nake so.”

General cikin soyayya da lallashi ya ce, “To wacce irin mace kake so my Man? Ka ce ba nistasttiya ba, kuma ba kamila ba, Ustaziya kake so kenan?”

CAS Bunayd ji yake kaman ya ƙwala ihu dan taƙaici, kaman zai yi kuka ya ce, “General ni ko ɗaya ba su nake so ba.”

“To wai wacce irin mace kake so?”

“Gaskiya General ni bana son mata masu saka hijabin nan, ƴan ƙauye ne, gaskiya ni banason nistasttiyan mace.”

Da mamaki General da Hajiya Huraira (Momsee), suke kallon Bunayd, Momsee ce ta ce, “To Bunayd wace irin mace kake so? Kowa na fatan samun nistasttiyan mace amma ka ce ba haka ba.”

“Momsee ni nafison mace wacce ta waye tasan rayuwa, tasan duniya, amma nistatststun nan basu san kan rayuwa ba, basa bada Palace yanda ya kamata.”

General ya ce, “shi kuma Palace ɗin menene? Ai mace nistasttiya ita ce jin daɗin duniya.”

“General ni nafison wacce take nan tantiriya-tantiriya, ko gantalalliya-gantalalliya haka nan, ko stagera-tsagera ko kuma wayayyiya wacce dai ba kamila ba, wacce dai tasan rayuwa, nistasttiyan nan cutan ta zan yi, kaga ni ba nistastte bane, kuma ni Soja ne, nistasttiya ai sai malamin islamiyya, ustazu.”

Momsee dariya kawai ta yi, shi kuwa General sake baki yayi ganin ikon Allah, ganin da gaske CAS Bunayd ya dage shi iya gaskiyansa yake faɗa, abinda yake so yake faɗa, ikon Allah, da mamaki ya ce, “ubanwa ya ce maka kai ba nistastte bane?”

Bunayd ya ce, “Abeed ne ya faɗa General.”

Girgiza kai kawai General yayi, tunda yasan Abeed kuma ya san waye Bunayd ɗin da rashin jin sa, kawai soyayyan da yake masa ya saka yake lallaɓasa, rarrashinsa ya dinga yi amma ya dage firr shi baya son nistasttiya, in kuma Alhaji zai sama masa wacce yake so, to ya basa zaɓi, shi normal ne kawai, ai damuwansu yayi aure ne, to zai yi kawai a samu kalar wacce yake so, General dai kama haɓa yayi yana ganin ikon Allah, amma tunda dai ya amince zai yi auren da sauƙi, kuma daman hakan na ɗaya daga cikin abinda yasa yake son sa sosai, Bunayd baya musu da su ko kaɗan, kuma yana jin maganansu yana musu biyayya, halayyansa masu kyau ne, dan ya fi ƙannensa har da matan jin magana, shi dai bar shi da abin raha, ita kuwa Momsee ba abinda take yi sai dariya, ganin Bunayd ya girma da gaske amma kuma ƙuruciya na damunsa, dan idan ba ƙuruciya ba mutun ya dage baya son kamilar mace saliha, ya ce sai gantalalliya.

General ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce, “To daman ma babban abinda ya sa na ƙira ka, ba akan ka dawo bane, dan nasan muddin baka yi niyan dawowa ba tuni ka kanainaye ni da magana na ƙyaleka, ga shi kuma na haƙura dan dole, Man kai kam ai mace bata isa ta maka daɗin baki ba, Allah shirya mana kai.”

CAS Bunayd na murmushi ya ce, “Ameen Ya Rabbi my General.”

General sai da ya dara kawai ya girgiza kai ya ce, “akan maganan ƙannenka ne, da farko Suhail na kai sa makarantar sojoji shi ma ya gado ni, amma yaron nan ya gudo haka na kylesa, aka tura sa Turkish ɗin da yake so, ya karanto duk shirmen da yaga dama, yanzu kuma Nabeel ya ɗau ƙafansa, dan tsabar yaran nan duk sun mai da ni abin wasansu wai shi ɗin ma yaro da shi yana cewa ba zai je ba, baya so, bansan mene mastalansu da aikin Soja ba, yara duk basa kishin kansu balle ƙasar su, ba za su tsaya su kare ƙasar su yanda muke fafatawa ba.”

Bunayd murmushi kawai yayi ya ce, “General wallahi ba ko kaffara, Suhail ne ya zuga Nabeel wai wahala ake, amma ba komai zan yi wa Nabeel ɗin magana.”

“Good boy! Allah muku albarka duka my Man, idan kuma yaƙi ji ka kai sa guard room ba ruwana” faɗin General yana murmushi.

CAS Bunayd ya ce, “Ba za’a je ga guard room ba ma General.”

Dariya General yayi ya ce, “Daman nasan haka za ka ce ai, tunda ka fi kowa son ƙanne a duniya, duk kai ma ka sakalta yaran nan, amma dai tunda suna jin magananka da sauƙi, ni na rasa ya ake suke storonka ma yanda kake buɗe musu haƙorankan nan.”

Murmushi kawai CAS Bunayd yayi bai ce komai ba, ya shafa kistonsa yana lumshe idanuwansa kaman mai jin bacci.

Momsee ganin Bunayd na ƙoƙarin yin bacci sai tayi murmushi ta ce, “To muje a ci abinci dama kai muke jira.”

Duk miƙewa suka yi suka sauƙo dinning na ƙasa, kowa ya samu waje ya zauna, yaran mata ne guda uku suka fito, kyawawa da su masu kama da General, kuma daman Bunayd da General yake kama shi ma, ɗaya a cikinsu ba za ta haura shekara sha tara ba 19 mai suna Ramla, sai ɗaya ba za ta haura 17 ba ita kuma sunanta Suhaila, sai kuma autar cikinsu da ba za ta haura 14 ba mai suna Nabeela, duk a niste suka gaishe da Bunayd ya amsa fiskan nan a sake yana musu murmushi, General ne yayi magana ya ce, “table manners, kowa ya ci abinci ayi shiru.”

Duk stitt suka yi baka jin ƙaran komai, sai na spoon da plate da suke karo, yayin da CAS Bunayd kuwa rabin hankalinsa ke kan wayansa yana sakin murmushi.

Banafsha suna dawowa daga wajan musabaƙa aka sallami kowa ya koma gida bayan an ƙara ƙarfafa musu guiwa su dage, tunda sun ga yacce rashin ƙwarin guiwa ke sa wasu faɗuwa, babu confidence.

Malam Abbo ne ya biyo su Banafsha yana taka musu, yana ƙara basu shawarwari yanda za su yi karatunsu hankali kwance ba tare da yawan idanuwan jama’a a kansu ya dame su ba, ko ya hana su yin nasara, su Umaima dai suna ta sauraronsa har ba su ankare ba suka fara hango gida, Malam Abbo ma na farga ba ashe ya biyo su har gida, kuma tun daga nesa Umaima da Banafsha suka hangi Ya Danish a ƙofan gida kuma ya kallesu.

Malam Abbo sallama ya musu zai juya, sai Banafsha ta langwaɓar da kai ta ce, “Malam ba ka faɗa mana abinda ya hanaka zuwa ba, in rashin lafiya ne ai sai mu dage da addu’a, Allah bawa malaminmu lafiya.”

Umaima duk ta sture ko sauraran su Banafsha bata yi, kuma ta kasa tafiya tabar Banafsha, ga shi Ya Danish ya zuba musu na mujiya ko ƙiftawa ba ya yi, kuma fiskan nan a haɗe, kana gani kasan yau akwai bala’i.

Malam Abbo yana murmushi ya ce, “Na ɗan yi tafiya ne urgent zuwa Borno, afuwan ko Malama Faɗima.”

Banafsha murmushi ta sakar masa mai rikitasa ta ce, “tunda Malam ya dawo lafiya Alhamdulillahi, sannu da gajiyan hanya, gobe kada a mance mana tsarabanmu Malam”, ita fa Banafsha duk saboda Ya Danish ya ƙulu take yi.

Malam Abbo da ya susuce, murmushi kawai yake sakarwa Banafsha kaman ba lafiya ba, har ya buɗe baki dan faɗa mata akwai maganan da yake son faɗa mata, amma sai ya fasa kawai ya dake, ya musu sallama ya juya, zuciyansa cike da wani irin ƙaunar ɗalibarsa Faɗima.

Banafsha da gangan ta staya tana yiwa Malam Abbo bye-bye, duk da ya riga ya juya, amma yi take dan Ya Danish, har da ɗaga hannu sama ta yi alaman love, Umaima da ta gaji da haukan Banafsha sai wucewa tayi ta ce, “Sai kin iso, tunda ba ki san ruwan da ke gaban mu yana jiranmu ba, yau nasan nidai na gama yawo na kaɗe, Ya Danish zai targaɗa ni.

Banafsha na murmushi ta juyo, daga inda take ta harari Ya Danish sannan ta bi Umaima da sauri tana faɗin, “jirani Umaimaty, zan je wajan Ummu.”

<< Yar Karuwa 7Yar Karuwa 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×