Skip to content
Part 4 of 4 in the Series Yasmeenah by Deejasmaah

Cikin k’unar rai yake driving lallai ma Meenah yana mata kallon mai hankali ashe irin wainnan yaran take kulawa? har da wani ce mata taje gida, dukan steering wheel d’in yayi yana tuna kamota da ya kusa yi. Lallai a yau zata san shi waye, don ta kiyaye ko don gaba. Tsaki ya sake a karo na ba adadi, cikin ikon Allah ya kawo gida.

A bakin wani had’add’en gida yayi horn, tun daga waje zaka iya shaida tsari da haduwar gidan. Balle kuma sanda security guard ya bud’e gate, tsayawa labarin gidan b’ata baki ne ainun amma ka kwatanta had’uwa da kyan gida irin na y’an gayu. Though ba wata k’awa akayi wa gidan ba tsabar tsari da yanayin tsarin ginin da yafi kama da gine-ginen Turkiya shi zai ja hankalinka.

Shigar da motar yayi yana mai parking a inda aka ajiye takwarorinta, lumshe idanu yayi ba zai iya shiga wurin Mamie a yanda yake ba. Don tabbas zata tambaye shi abinda ya b’ata masa rai, and he’s not ready to discuss that with anyone don haka ya nufi part d’in shi cikeda b’acin rai.

Yanda ya b’ule shi da hayak’i ba k’aramin sake hargitsa shi yayi ba, wato shi zasu wulak’anta su tafi su bar shi kamar mahaukaci. Bakin shi ya ciza yana mai ciro wayarshi numb Meenah da yayi saving as “LOML” da emojin heart da lock ya fara dialing. Har ta katse bata d’aga ba, sake kira ya kuma shi ma same thing a na ukun ma sai yaji switch off.

Wani k’ululun bak’in ciki ne ya sake zuwa mai k’irji, k’arasawa yayi jikin gate ya fara knocking a d’an zafafe kamar zai b’alla. Ai ko nan take yara suka d’an fara zagaye wurin suna masu kallon shi, a take aka bud’e gidan Zuu ce cikin kallon k’ask’anci tace ” lafiya Malam kake shirin b’alla mana k’ofa, bashinka muka ci ne halan?”

Kallon tsana yayi mata don duk da kasancewarta ‘yaruwar Meenah amma yayi masifar tsanarta yadda baka tsammani, yace ” Dallah ba wurin ki nazo ba, kin zo kin tsareni da wata kod’ad’diyar fuskar ki sai ki koma ai.” Ware idanunta tayi a kan shi jin yadda ya kira fuskarta da kod’ad’diya, kafin cikin dariyar rainin hankali tace ” ohhh haka ne fa ba wurina kazo ba, amma ina son ka sani ita wacce kazo wurin nata ba zata fito ba zaka iya jan tsumman k’afafunka ka tafi ko in sa yara suyi maka watsin kasa.”

Ya san kanun rashin mutuncin ta ya kuma san wannan k’arami ne daga abunda zata iya, da ko yara suyi masa watsin k’asa da ihu gwara ya wuce. Wulak’ancin da akayi masa ma ya ishe shi ba sai an k’ara masa da wani ba, sai ji yayi tace ” auuu, ba zaka tafi ba?, kaiii Shamwilu kuzo in saku aiki….” Kafin ta k’arasa yaran suka iso yuuuu kamar dama abinda suke jira kenan.

Murmushin nasara tayi tana kallon shi, shima kallonta yayi dead in the eyes yana cewa ” ai shiyasa har yanzu kika rasa mashinshini, toh wani sakaran ne zai d’auki mai mugun hali irinki ai sai dai kara da kiyashi ‘ d’aukar marar sani’ zan tafi ba wai don ina tsoro ko shakkar abinda kike k’ok’arin sawa a min ba Aa sai don saboda ba zan iya zama muna shak’ar iska d’aya da worthless piece like you ba. Shegiya mai bak’in jini kawai.”

Yana gama fad’in haka ya juya, yana mai jin dad’in rage fushin shi a kanta. Ita ko tsayawa tayi k’ik’am tana mai jin d’aci a ranta, lallai ma Nazeem har shi zai mata gorin samari. Toh ai da saurayi irin shi gwara ace bata da kowa, sai dai kuma abun ya mata dukan da baka yi zata ba. A take ta runtse idanunta hawaye suna gangarowa, juyawa tayi ta koma tana mai banging gate d’in har ta manta da yaran jama’a da ta tattaro. Tana tura gate d’in ta duk’a a k’asa tana mai sanya kuka mara sauti, ta d’an dad’e a wajen sai da taji d’an sukuni a zuciyarta kafin ta nufi parlor.

Mama dake zaune ne tace ” ke daga cewa ki dubo wake buga k’ofa zaki je ki dad’e kamar an aiki bawa garinsu?”. Dariyar yak’e tayi tana cewa ” wancan mahaukacin ne Nazeem, da alamu fad’a sukayi da mutumiyar shine yake shirin huce haushin shi a kan k’ofar mu.” Mama ce tace ” kul kika kuma ce masa mahaukaci, saan ki ne? Ko dan yana son k’anwarki shine kike ganin shi a abun wulak’antawa?”

Tura baki tayi tana mai kauda kanta gefe, Mama ko ta cigaba da sababinta ta silleta tas sai da Meenah ta fito ta bata hak’uri kafin ta tsagaita amma ita Zuun ko ci kan ki bata ce ba balle ta bata hak’uri sai k’iyasta tsananta da Maman tayi a cikin zuciyarta da take yi. Ba tun yau ba ta san an fi son ta a cikin gidan hakan yasa ba a son tab’a duk abinda ya kasance nata ne. Ita ko Meenahn wayarta da ta bari a wajen ta d’auka ta tabbatar ko kowa bai nemeta ba toh Nazeem will, musamman yanda yayita Buga gidan Zuu ta fita.

Ta tabbatar ba abun alkhairi zai faru a tsakaninsu ba, tunda dukan su sun tsani juna ko ga maciji basa yi. Though ita Zuun ta kan bata shawara akan shi, yau kuma bata san mai ya wanzu tsakaninsu da har take kiran shi da mahaukaci ba. Sunan da ya zafe zuciyarta ba k’arami ba, ba dai ta nuna ba wucewarta tayi ciki don ta shirya kasancewar daga wanka ta fito.

Har dare babu wanda ya nemeta a cikin su, tun tana d’an damuwa har ta cire abun a ranta. Sai bayan ishai da ta fara k’ok’arin kunna data kafin ta lura da ashe wayar a flight mode take. Dafe kanta tayi don bata san yaushe ta sata ba, cirewa kawai tayi.

Wayar na gama dawowa dai-dai kiran shi na shigowa, sabuwar number ce. Ba kuma wanda Nazeem ke kiranta dashi bane picking tayi tana karawa a kunne, cikin muryar shi mai taushi yet masculine amma har lokacin da d’and’anon b’acin rai a ciki yayi mata sallama. Amsawa tayi cikin son dakewa tana mai gaishe shi, ai ko kamar jira yake tayi gaisuwa ya fara fad’a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.

Shiru tayi tana sauraron shi ba tare da ta tanka ba, mamaki da taajjubi take yi ita kuma tata kad’darar kenan yin samari masifaffu toh Allah yasa ba mai irin halin zata aura ba don ita bata iya tashin hankali ba. Bata san fad’a da tsawa hakan ne ma ya sa take zama lafiya da kowa gudun abinda zai yi leading to fad’a, jin tayi shiru ne ya sa shi cewa.

“Auu shiru kikayi kika kyal’eni ina magana tunda ga mahaukaci ko?” tallafe hab’arta tayi tana mai cewa ” I’m sorry” cewa yayi ” I’m not asking for that, bada hak’urin ki won’t change anything I’ll come back to that later, shi wancan shegen waye?” Runtse idanu tayi cikin d’an jin zafi tace ” Nazeem “.

“Shi kad’ai ne ko da wasu?” ya sake tambayarta cikeda kishi. Shiru tayi don bata iya k’arya ba, ba kuma zata iya sanar masa gaskiyan ba. Shirunta ya tabbatar masa da zargin shi don haka yace ” your silence says it all, but ina so ki sani Meenah ba zan iya d’auka ba gaskiya ni mutum ne mai kishi akan abinda yake so ba kuma zan iya zuba ido samari suna dabdala a gidan wacce nake da burin aure ba,,,,,so zan turo kawai don hankalina ya kwanta”.

Zare idanu tayi tana mai cewa ” so soon?” Da sigar tambaya shi ma yace ” soon?” Lumshe idanu tayi tana adduar Allah yasa ta fad’i abinda zai fahimceta tace ” ba ina nufin yayi kurkusa ba, but kaga we barely know each other bamu fahimci juna ba kaga shi aure abu ne bana wasa ba yin gaggawa a cikin lamarin shi bai da faida.”

Shiru ne ya d’an biyo baya kafin yayi ajiyar zuciya yace ” look Babe ba wai ban fahimce ki bane or ban yarda dake ba, but ni ba yaro bane da zan na zarya gidanku ba tare da k’wak’kwaran magana bane and ba ina nufin daga na turo shikenan aure za a yi ba no ina so ne gidanku su san da zamana a matsayin wanda ke neman aurenki ko hakan zai sa ki daina kula wasu tunda kin san an miki miji.”

Murmushi tayi da alamu zai yi daru kam amma kuma yana da tunani da hangen nesa ainun. Tun da take babu wanda ya tab’a proposing mata a time d’in da wasu suke kira da talking stage, hakan ya nuna he’s real about her and his intentions are pure. Katse tunaninta yayi da cewa ” ko dai ba a sona ne?”.

K’aramar dariya tayi tana cewa ” zan gayawa Mama, duk yanda mukayi I’ll let you know.” Murmushi yayi kafin yace ” will be expecting you, and abu na gaba…” Dafe kanta tayi ba dai wani laifin zai kuma cewa tayi ba, amsawa tayi da ” what’s that” a d’an marairaice murya ” kin sa raina ya b’aci now you should cheer me up”. Rufe idanu tayi a shagwab’e tace ” ba na bala hak’uri ba?”  yace ” uhmm amma ai ban hak’ura ba.”

D’an tale baki tayi kamar zatayi kuka tace ” ba kyau fa a bawa mutum hak’uri bai hak’ura ba.” K’aramar dariya ya sanya jin tone d’in da tayi maganar yana mai cewa ” yanzu kam na hak’ura amma kar a sake”. Tab’din wannan abune da ba zata iya alk’awari ba, don idan kagan Nazeem bai rab’i inda take ba toh aure aka d’aura mata shi ma she’s not sure tunda ta san halin kayanta inda a kanta ne. Sai dai kawai ta furta ” in shaa Allah ” yaji dad’in yanda ta girmama request d’in shi don haka ya k’ara mata matsayi a rai da zuciyar shi, nan ya zage ya fara mata hirar cikin soyayya.

Abinda ya sata ajiye kowani tunani kenan at that time ba kowa a gabanta sai shi d’in don sosai ya iya soyayya. Wayar ta d’auke su lokaci mai tsayi don har Zuu tazo ta kwanta basu gama ba, sai shi ne ya lura da tafiyar lokaci yace mata ” sai da safe I know kina da school gobe ” yes ta amsa tana mai jin kamar kar su rabu ” I love you!,” ya fad’a cikeda jaddadawa a kunyance tace ” I love you too, good night ” ta katse wayar kamar wacce tayi wani laifi, ta gefen shi dariya yayi yana mai jin k’arin sonta a ran shi tarbiyyarta, halayarta, d’abiu da yanda take magana uwa uba kunyarta suna cikin abinda ya sa shi fad’awa k’aunarta tsamo-tsamo.

Duk da ya san har yanzu bata san yaushe ya ganta ba, amma ya kai a k’alla shekaru biyu don tun tana neman admission ya fara ganinta shima time d’in yaje neman ma k’anwar shi admission. Tun daga nan yake bibiye da rayuwarta, muamalarta a ciki da wajen makaranta hatta da adadin samarin da ta rabu dasu ya sani, Nazeem ma ya san da zaman shi abinda bai sani ba shine tana son shi. Amma yanda tayi reacting da ta ganshi ya nuna tana son shi tana kuma gudun b’acin ran shi, shine ma abinda ya assasa b’acin ran nashi shi.

Shiyasa ya k’udura tura magabatanshi a kan maganar don bai shirya rasa ta ba. Ya dad’e yana lissafe-lissafen shi har bacci ya kwashe shi.

Tana ajiye wayar ne taga messages rututu daga Nazeem, zare idanu tayi don ta san ta kuma wani laifin. Kafin ta bud’e ya danno wata kiran, d’an natsawa tayi ta d’auka a jirance yace ” saboda gani d’an iska ko Meenah? in kiraki d’azu baki d’aga ba sai ma kashe min waya da kikayi shine yanzu ina kira yafi sau 10 kin k’i katse wayar da kikeyi saboda kin samu wanda ya fini a komai ko?”

Runtse idanu tayi na farko bacci take ji, na biyu kuma bata shirya jin masifar shi ba ta gama da ta Sarham ta kuma fad’a tashi. Tunda gata cibiyar k’orafe-k’orafe ta samari ko? Yanda tayi ya sashi cigaba da masifar tashi kamar ya ari baki ” au ga mahaukaci ko? Dole ai kiyi banza dani tunda ban k’ararki da komai ba saboda kin daina so na ko?”

A hankali tace “ban cika son kana d’aga hankalinka ba Zeem, kasan kud’i ko mulki ba zasu tab’a jan ra’ayina ba maganar so kuma ba sai na ta jaddadawa ba ko mahallicinmu ya san hakan kaima kuma shaida ne, ko a yanzu ka shirya aurena toh na shirya amma abinda zai sare min gwuiwa da lamarinka shine halayyarka yanzu d’azu wace riba kaci?”

Lumshe idanunshi yayi yana mai gyara kwanciyarshi akan katifar shi, ya na son ta maganganunta kuna sun sa shi samun natsuwa yace ” na kasa controlling kai na ne shiyasa, amma ki kore shi kar ya sake dawowa tunda dai ni kike so.” Lallai ma wato ya sata tayi saki-na-dafe kamar yadda ta saba a soyayyar baya ko? Toh a wannan karan ba zata sake ba, tace ” in ka ga na kori wani toh ka fito ne, in ko baka fito nan da k’arshen watan nan ba wallahi zan ba shi damar ya turo ko da son da nake maka zai zama ajalina.”

Wara idanu yayi lallai ma Meenah lallai zata sa ayi kisan kai, don ba zai yarda wani ya mallaketa ba shi ba don haka yace ” ba zan yi k’arya ba, ko a gidanmu ban isa in tunkari Babudi da maganar aure ban da aikin yi ba ki dai k’ara min time kin ai ba zaune nake ba har yanzu aiki nake nema”. Tab’e baki tayi tana cewa ” toh Allah ya taimaka, ni zan kwanta ina da test gobe” da sauri yace ” Allah ya taimaka, I love you ” Ameen ta iya cewa don haka nan taji kunyar ce masa she love him too, ba don bata son shi ba sai dan bata dad’e da shaida ma wanin sa ba cije bakinta tayi wai ya mata masu double date suke ji? Wasu fa normal ne ko a jikinsu ko. Shi ma bai damu da sai ta amsa ba kashe wayar yayi yana mai kwanciya dole gobe ya sake fita neman aikin nan ko Allah zai sa a dace.

Nazeem Suleiman Anchau graduate ne, ya kammala makarantar shi shekaru biyu baya. Iyayenshi masu matsakaitan k’arfi ne amma shi kuma irin yaran nan me masu tsananin buri a rayuwa, ko sanaar kirki bai dashi sai bin inuwa da kwanciya a d’aki kamar ruwa.

Sun dad’e da Yasmeenah tun tana JS3 wannan halin rashin sanaar ba k’aramin rikici ya haifar tsakanin su, sanda ya kammala jamia ko ce masa tayi yayi applying NDA ko NPF yayi short service amma yak’i. Duk wani form da zaa fitar wani lokacin ita take cire kud’i ta siyan mai amma abu d’aya ne bai so, don shi duk wani aikin wahala bai so. Burin shi ya samu aikin da zai zauna a office AC tana bugunshi ba wai yaje inda zai sha wuya wai don neman kud’i ba. Yana tsananin son Meenah bai k’aunar ta sha wahala bayan nan ma Babanshi da Suke kira da Babudi ba zai tab’a amincewa neman auren shi ba don ya kafa mai sharad’i akan ya nemi aikin yi har loan ya ci a wajen aiki ya kama mai shago akan ya fara POS sai dai a banza yak’i zama sai k’annnenshi suke zama, in ka ganshi a wajen toh baida kud’i ne yaje ya amshi 1k ko 2k in suka hana ya daki kayan banza hakan yasa suka daina hanawa sai dai su rubuta Babudi bai iya masa fad’a balle Mamani da bata k’aunar laifinshi . Haka yasa suka dage wajen neman mai aikin gwamnati sai dai duk wanda aka d’an samu sai yace yayi masa k’arami shi da first class honor ya fita yafi k’arfin aikin, in Babudin yace ba sai a hankali bane ake samun babban matsayin sai yace shi fa bai san wannan ba, shiyasa suka taru suka zurawa sarautar Allah idanu don basu san kalar shi ba……

Deejasmah

<< Yasmeenah 3

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×