TUNAWA
Iyayenmu da suka rigayemu gidan gaskiya, da sauran ‘yan’uwa Musulmi bakidaya, Allah ya ji kansu, ya gafarta musu, amin summa amin.
DOMIN
‘Ya’yanmu
YABAWA
Malamaina, abokaina da ‘yan’uwana.
A KARKASHIN
Inuwar Marubuta Littattafan Hausa (Hausa Authors Forum)
*****
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.
Idan ka duba kan gwadaben, babu abin da za ka gani sai yuyar yara suna biye da dan biri da majayin birin. Idan majayin birin ya tsaya don yin wasa a gaban mutane, yaran ma sai su tsaya suna tsalle-tsalle, suna shewa, suna amshin wakar da majayin birin ke bayarwa.
Da yawan yaran ba su zarce shekara goma sha biyu a raye ba. Sun fari rayuwarsu daga hudu zuwa sha daya ko sha biyun. Maza da mata, wasu almajirai ne don suna dauke da koko ko roba ko tasa na bara, kuma cikin dauda. Kodayake su ma ragowar yaran da ba almajiran ba kusan mafi yawansu haka suke cikin datti, akwai masu dauke da kayan talla, akwai kuma wadanda da alama aiken su aka yi, amma suka tsaya yin aikin baban-giwa.
Bakin mutumin da ke rike da dan birin mai sanye da riga da wando, gajere ne abin kifewa da kwando saboda gajarta, mummuna zubin farko, katon kansa kamar shi ya dora shi, ya zuba masa burmemen hanci da jajayen idanu gami da wawakeken baki mai rikon wani shaci-fadin wawulo da ke tsakanin dafaffun hakoransa, abin gwanin kallo fiye da birin.
Akwai wadanda suke cewa birin na matukar yi masa biyayya ne saboda tsoron muninsa da yake ji. Wasu kuma sukan ce wasu lokutan yara da manyan mutane sun fi kallon shi a matsayin wata halitta abar kallo fiye da dan birnin.
Wadanda suka san shi, suna kiran sa da suna Waske, su kuwa yara da yake riska a hanya kan kira shi ‘Danbaki mai biri’ ko ‘Gajere mai biri’.
Daidai lokacin da Waske ya wage baki ya fara rera waka, shi ya yi daidai da karasowa ta gurin.
‘Dan taka…kai juya…juya…juya.’
Idan Waske ya rera wannan baiti da muryar gurnani. Sai ka ga ya yi tsalle. Yara ko sai su dauki shewa suna amsa masa.
Ni kaina, na lura idan aka yi mafarki da Waske, to mafarkin nan sai addu’a. Ba ni kadai ba, na san duk mai hankali idan ya ga yadda yaran suka yayume Waske, suka mayar da lamuransu gare shi dari bisa dari, ba zai ji dadi ba.
Na matsa kusa da shi, na ce “Dakata Malam.”
Ya dakata din, yana kallo na da alama tunani yake a ransa ko ni dansanda ne ko soja ko dai wani mai aikin damara, ya ce “Yallabai lafiya ko? Ka san da lafiya ake zama lafiya ake samun rufin asiri da yin sana’a.” Ya yi min irin maganar su ta ‘yan kwararo.
“To, lafiyar kenan. Amma yaran nan da ka tara sam bai dace ba, kuma kamata ya yi idan suka zo ka kore su.”
“Babbar magana, dansanda ya ga gawar soja, malam ai ba a raba kaska da jini, kuma shi kare ai ba sai an gaya masa gidan biki ba. Ba ni na kawo su ba, kuma ban kira su ba, don duk taron nan nasu babu mai ban ko ranyo bare ainini, su suke bi na, ba ni na bi su ba, bare a ce in rabu da su. Haba Malam ina gamin kura da kashin dutse?” In ji Waske.
Na kalle shi kawai, kafin in kara yin magana ya janye birinsa, ya yi gaba yana waka.
“Kai dan taka…
kowa ya ganka.
Sai dai kallo.
Kai juya…
ba ni rawar ‘yan sa ido a gari.”
Dan birin nan ya yi rawa da kai, ya wurkila idanunsa, alamun ya ji habaicin da maigidansa ya yi mini.
Ban farga ba na ga yaran sun rufa masa baya, amma ban yi kasa a guiwa ba, na daka musu tsawa, na ce “Kai ku zo nan!”
Masu kunnen kashi a cikinsu suka yi kunnen-uwar-shegu da ni ko a jikinsu an yakushi kakkausa, wasu kuma suka tarwatse suka yi nasu wuri. Allah ya sa wasu kalilan suka yo wajena.
Nakan damu da halin da yara suke ciki a wannan lokaci, musamman mu da muka taso talakawa, a rayuwar talauci, amma duk da haka ba haka ya kamata rayuwar tamu da ta ‘ya’yanmu ta gudana ba.
Duk talaucin mutum akwai hanyar inganta rayuwar ‘ya’yansa. Idan hakan ba ta samu ba to za a kyankyashi miyagun ‘ya’ya da shugabanni nan gaba, za a haifar da wata gurbatacciyar al’umma da za ta gurbata kasa da duniya bakidaya.
Wadannan dalilai ne suka sa nake kokarin bibiyar rayuwa irin tamu da ta ‘ya’yanmu don mu gano yadda take da yadda ta gudana da mafitarmu, da yadda za a gyara ta.
Yaran da suka saurare ni sun ba ni damar jin yadda suke a haka; a halin rashin tsafta da rashin kamewa da rashin tarbiyya da sauran abubuwan ki.
Yaran za su ba ku mamaki da tausayi matuka, idan ka dubi halin da suke ciki da kuma yadda su kansu suke neman mafita daga kangin rayuwar da suke ciki.
Bari ku ji labarin rayuwar ire-irensu da yadda suke gudana.
Babi Na Farko
KURMAN AMO…
Labarin Dan’amadu da Bala da Lalo
Karfe bakwai na safe zuwa bakwai da rabi har karfe takwas lokuta ne na tafiyar yara dalibai zuwa makarantun Islamiyya ko allo ko kuma boko, amma a lokacin idan ka dubi cikin unguwar Hayin Talaka za ka tarar da yara reras suna sha’aninsu na wasanni, wannan ne ya nuna ba duka aka taru aka zama daya ba, domin ‘yan kalilan ne suke kokarin tafiya makarantun. Amma mafi yawansu ba sa zuwa.
Akwai wasu yara masu yawa a kofar wani tsohon gida, gindin wata bishiya, sun yi cunkus a wurin suna wasanninsu, wasu wasan ranwa suke yi (wato katantanwa), wasu wasan ‘yar gala-gala, wasu kuma kartar kwalin ashana suke yi.
Yara ne da suka fari shekarunsu daga biyar zuwa goma sha daya. Da yawansu ba su dade daga tashi daga barci ba, wasu akwai yawun barci bushe a bakunansu, duk da ‘ya’yan Musulmai ne amma ba su yi alwala ba, bare sallar Asuba.
Kusan dukkaninsu sun yi dukun-dukun kamar an tono su daga bola, sai ka dauka ba su da iyaye a kusa.
Daga wani bangare na cikin layin, wasu yara ne su uku, guda biyu masu shekaru biyu da rabi-rabi sai kuma daya mai shekara uku zuwa hudu a raye. ‘Yan shekaru biyu da rabin mace da namiji, macen tana sanye da wando fatari babu riga, shi kuma namijin babu riga babu wando a jikinsa, timbir yake – Dukkaninsu su biyun kuka suke yi, ga majina a hancinsu, cakal-cakal cikin gudu suke bin dan shekara ukun da gudu, da alama wani abu suke so ya ba su da ke hannunsa shi kuma ya ki, haka suke gudun cal-cal-cal kamar ‘ya’yan barbelu.
Wani yaro mai shekaru biyar, sanye da riga da wando masu dan kyau, amma cikin datti, yana gara gare-gare, hannunsa daya rike da kwalin ashana da aka aike shi ya sayo. Bai lura ba, yana wannan falfala gudun nasa ne suka yi taho-mu-gama da dan yaron nan da yara biyu suka biyo, gabadayansu suka yi sama, sannan suka dawo suka zube a kasa, sai kuka, wi-wi-wi!
Wasu almajirai su hudu masu shekaru biyar da shida-shida, da suke yawon barar safe a wurin suka kai musu dauki don su daga su.
Kowa da kiwon da ya karbe shi makobcin mai akuya ya sayo kura, shi kuwa wani yaro mai shekaru hudu da ke can gefe bai damu da wadannan yara da suka yi taho-mu-gama ba, ta kansa yake yi, yana kokarin kwatar kansa daga wurin wata tunkiya da ta ritsa shi, tana kokarin yi masa kwacen kosan da aka aike shi ya siyo a gidan Tabawa mai kosai.
A daidai lokacin Dan’amadu ya fito daga cikin gida, ya hango yaron nan da tunkiya ke neman yi wa fashin kosai, ya isa da gudu ya kore ta, kana ya kama hkannun yaron, ya dora shi a kan hanya don ya tafi gida, tare da nuna masa babu matsala.
Unguwar Hayin Talaka, daya ce daga cikin unguwannin dake cikin birnin Kano, unguwa ce ta Yaku-bayi, ma’ana mafi yawan mazaunan cikinta talakawa ne na sosai. Unguwa ce da a kiyasi take da yawan jama’a, kusan tana cikin manyan unguwanni masu tarin al’umma.
Rayuwar da ke gudana a Hayin Talaka, rayuwa ce da ta isa misali a duk duniya in dai za a yi maganar rayuwar talakawa, to la-budda za a yi kwatancen Hayin Talaka.
Bayan da Dan’amadu ya sallami yaro mai kosai, sai ya kada zuwa inda ya nufa. Tafe yake yana ‘yan tsalle-tsalle da wasa da kuma ‘yan wakoki irin nasu na yara. A haka har ya isa inda ya nufa din. Za ka dauka aiken shi aka yi, to ko kadan kuma ko alama shi ya aiki kansa, kofar gidan su Bala ya isa, ya taki sa’a Balan da ya je nema yana kofar gidan yana wasan yin motar gwangwani.
Allah mai hikima, shi ya bai wa yaran hikima da basirar samo gwangwanin madarar da mafiya yawansu ba su taba shan ta ba, ka ga sun samo dutse da kusa, su sami kan siminti musamman mai kurji-kurji, sannu a hankali su fafake gwangwanayen, su molaka su, su juya su, su motsa su yadda suke so, sai ka ga sun sarrafa su yadda suke so, su yi motar gwangwani ta wasan yara.
Ikon Allah kenan, su, su ja motar gwangwani, ‘ya’yan masu kudi su ja mota ‘yar kanti, kirar Turai.
Dan’amadu ya zauna a gabansa, ya dauki wani gwangwanin madara da ke gaban shi, ya ce “Bala ba za ka je ba?”
Bala dan shekara goma, yana da tsamin baki, ya ce “Ai tun daju kai na ce jiya ba ka jo ba. Bari in taci mu tafi.” Ya mike, ya kwashe kayayyakinsa, ya shiga gida da su, sannan da ya tashi dawowa sai ya dawo da wani buhun algarara da leda a hannunsa, ya mika wa Dan’amadu buhun, shi kuma ya rike ledar suka rankaya.
Bola suka nufa, inda suke neman kudi, kamar yadda suka saba a kullum, iyayensu ma sun san da haka, a ganin su ma yaran masu zuciyar nema ne, don haka sun yi dace da ‘ya’ya. Batun zuwa makaranta fa? Wannan ko a jikinsu an tsikari kakkausa.
*****
Bola ce da ta munana, muni da kazanta mai tarin yawa, cunkushe da yama da dagwalon cututtuka. Bola ce da dukkanin bololin da aka kwaso daga cikin gari da unguwanni nan ake kawowa a jibge. An ce abokin damo, guza, daga can karshen bolar kuwa wani rubabben kududdufi ne da ake zuba kashin da ake debowa daga gidajen mutane na cikin gari.
Don haka ilahirin gurin ke dauke da tsananin doyi da warin da ya gagari jama’a zama a kusa da gurin. Masu wucewa da ababen hawa ta gurin sukan wahaltu idan har ba su rufe hancinansu da bakunansu ba. Su kansu masu kawo sharar da bayan-gidan sukan rufe bakunansu da hancinansu. Duk da haka sukan sha wuya wajen shaka ko fitar da numfashi.
Daidan wani karkataccen wani, kuma idan wani ya gaza hawa bishiyar kuka, wani yana can samanta. A can cikin bolar, idan idanunka za su iya gano maka, to za ka hango Bala da Dan’amadu. Gumi suke yi da naso da daudar da zafin rana ke haddasa musu.
Yaran suna rike da karafunan tono, Dan’amadu da buhunsa na algarara, Bala kuma da leda, kamar yadda suka baro gida.
Karfe, danko ko kashi ko kuma robobi da sauran ‘yan abubuwan da ‘yan jari-bola ke tsinta, su suke tono su tsinta. Idan mutum ya so yakan iya kiran su ‘yan-bola ko Baban-bola idan daya ne.
Ana zaune lafiya, idan aka ce yaran nan za su shiga bolar nan to kowa ma na iya musawa, saboda barazana ga lafiyarsu, amma ga su tsamo-tsamo a ciki. Haka suka kasance tsawon lokaci, kafin Dan’amadu ya juya, ya kalli Bala bayan ya dago daga dukawar da ya yi, ya ce.
“Ni fa na gaji, Bala.”
Bala ya amsa “Wayyayi (wallahi) ni ma na gaji, ka camu da yawa kuwa?”
Dan’amadu ya ce “Zo mu duba.”
Suka sami wani wuri a cikin bolar da suke ganin yana da dan dama-dama a tsafta, suka zauna a kan wasu kwalaye da suka shimfida.
“Ni ban camu (samu) da yawa ba.” Bala ya ce bayan ya gama kallon cikin buhun nasa “Babu yefi (laifi).”
Bayan da su Dan’amadu suka huta, sai suka tashi, suka ci gaba da tone-tonensu a cikin bolar. Tsawon lokaci suna lakatar abin da za su iya lakata, suna jefawa cikin buhunan nasu. Har zuwa lokacin da suka gaji, sannan suka fita daga bolar domin tafiya inda za su sayar.
Suna tafe, suna dudduba gefe da gefe don ko za su yi karo da abubuwan da suke nema kafin su isa inda za su sayar.
Haka rayuwar yaran take. Dan’amadu da Bala idan suka wayi gari a gaban iyayen su to sun yi mai wuyar, daga haka babu batun hakkin uba, misali ya tura diyansa makaranta, ko ya kula wajen ci da shan su ko sutura, ko kuma lura da abokan huldarsu da tarbiyyarsu. An haife su, an yasar, don haka batun inganta rayuwar su daga iyayensu ya zama shurin iskar damina kenan, idan ta kada, ta wuce, ta wuce kenan.
*****
Dandazon yara ne jingim kamar fari a harabar gidan karfen Alhaji Mudi Amu. Gidan karfen, waje ne da ake harkokin kasuwancin sayen karfuna da robobi da takalman rafta da sauran irin wadanda ‘yan jari-bola ke samowa. Kowane bangare dai yaran ne da manya dauke da ‘yan buhunhunansu na algarara ko na leda da makamantansu suna tsumayin layi ya zo kansu a auni abin da suka kawo, a siya, su siyar, su samu kudin sayen abinci ko makamancin haka.
Akwai wasu yaran da za ka ga bakunansu da ledojin ruwan sha (fiya-wata) za ka yi tsammanin ruwan suke sha, amma a zahiri ba ruwan suke sha ba, sholisho suke zuka kamar yadda wasu masu tsumma a bakunan su ma suke zuka kai tsaye. Zamani riga, wato su masu ledar suna yin haka ne don su bagarar da mutane wai ba za a gane abin da suke sha ba.
A wani bangaren kuwa, wasu yaran suna ta fadace-fadace, wasu bisa dalilin bin jerin gwano (layi) wasu kuma saboda daya ya daukar wa daya wani abu, ko kuma kokarin kwace ko sata. Ga su nan birjik, yara da samari biji-biji.
Dan’amadu da Bala a gefe guda rakube da su ma, suna jira. Su Allah ya kiyaye lamuransu, ba su fara shaye-shaye ko shiga sabgogin rikici ko daru da nuna kwanji ko tashin hankali ba. Ire-iren su ba su da yawa a wurin.
Akwai wani yaro dan lagai-lagai da shi kamar shamuwa abin tausayi a rabe ba tare da hayaniya ba, alamunsa ma ba su nuna zai iya yin wata rigima ba, tun da shi alamun karfi yana ga mai kiba.
Lokaci-lokaci Dan’amadu yakan kalle shi da fuskar tausayi. Can dai ya yi magana yana kallon Bala.
“Gaskiya da a ce akwai wani gurin sayar da kayan nan da can za mu rinka zuwa.”
Bala ya ce “Akwai mana, kawai dai ka can (san) nan ya fi ciye (siye) da tsada ne.”
Dan’amadu ya ce “E to haka ne.”
Haka suka yi wujiga-wujiga a cikin rana har sai da idanunsu suka yi kwalla, kana daga bisani aka sayi kayan nasu. Sai dai sun yi rashin sa’a domin kafin layi ya zo kan su, Alhaji Mudin ya tashi daga aiki, sai yaransa, wadanda suke ci gaba da harkokin, su kuma yaran azzalumai ne, don idan Alhaji Mudi yana siyen kilo daya a Naira goma, su a Naira biyar suke siye, wai sai sun ci riba. Ko ka sayar ko kuma ka kara gaba, wannan ko a jikinsu an yakushi kakkausa.
Bala da Dan’amadu suna tafe jiki babu kwari, yanayi ba dadi. Sun sayar da jari-bolar su cikin rashin sa’a da wulakanci ba kamar yadda suka so ba. Babu daya daga cikinsu da ya iya magana, domin a kufule suke, gida suka nufa.
Daf da isar su cikin unguwarsu, Bala ya bude baki yana fadin, “Dan’amadu ja ka je fili yau?”
Dan’amadu ya ce “I mana, zan je, kai fa?”
“Ni dai na gaji.” In ji Bala. Daga haka sai suka yi shiru, suka ci gaba da tafiya zuwa gida.
Malam Kasimu Danhaya, shi ne mahaifin Dan’amadu, dattijo ne da ya juyawa shekaru sittin da shida baya, amma saboda jakale-jakalen duniya idan ka gan shi za ka dauka ya sa kafa ya shure shekaru casa’in a raye. A da fari ne, lokacin yana yaro, kafin ya rungumi wahalar duniya, amma yanzu ya zama bakikirin. A fuskarsa akwai wata kasumba da ake kira taskar-talauci. Za ka iya gane shi da wata jar dara da ta zama ruwan toka a kansa, da kuma riga da wandon kufta da suka zama ruwan gawasa-gawasa saboda su ya fi sawa a yau da kullum. Yakan saka wata riga da wando na waganbari musamman idan wani biki ko sha’ani na zuwa wani guri ya taso, ko kuma zuwa ganin gida, don haka wasu suke ganin iya kayansa kenan a duniya.
Asalin iyayen Malam Kasimu mutanen Zariya ne, amma shi a Kano aka haife shi, tun yana yaro, bai sami yin karatun addini sosai da ya wuce doraya ba, wato daga Fatiha zuwa Alam-tarakaifa, a boko kuwa bai kammala firamaren da ya fara ba. Haka ya yanki tikitin yin rayuwar ba bisa tsari ba, ya yi wa talauci masauki a zuciyarsa.
Bayan yawace-yawacen gidajen dambe da wuraren caca da karta da dandaloli da yin zaman zuru, ya fara sana’ar sayar da goro da taba a ire-iren wuraren da yake zuwa, don haka ya iya zukar sigari da cin goro.
Yana da shekaru sha tara ya fara sana’ar, ya tara kudi gwargwado, shekaru biyu a tsakani ya yi aure. Da karma-karma da dabaru ya kama haya a wani gidan haya. Daga baya ya sauya sana’a zuwa sayar da ruwan garwa wanda ake dauka a kafada, kafin ya samu kudin sayen kananan kekuna guda biyu, ya fara bayar da haya ga yara, har kuma ya fara gyara da yin facin kekunan, inda ya sami sunan Danhaya.
Malam Kasimu ya shure shekaru arba’in da wani abu a gidan haya. Idan za a yi bayanin irin yadda ya sha wahala ko yake kan sha a rayuwar gidan haya to wannan ma babbar magana ce mai dogon labari.
Ya dace mai aure ya san dokoki da ka’idojin zaman aure, shi kam Malam Kasimu bai sani ba, bai damu ya sani ba. Haka nan ya kamata uba ya san yadda zai tarbiyantar da ‘ya’yansa, ya tsara rayuwarsu, shi bai sani ba. Bai san ta yaya zai samar musu abinci ba, yana da kyau ya sa dansa ko ‘ya’yansa a makaranta, bai yi hakan ba.
“Abubuwan ne da yawa, mutuwa ta shiga kasuwa, ka ganni nan sai in wuni ban samu Naira saba’in ba, idan babu sa’a ko sisi ba na yi. Raneku da yawa ba ma cin abinci sau biyu ni da mai dakina Larai, sai dai ko sau daya. Gara shi takan tura shi bara ko kuma idan wani mai tausayi ya gan shi ya ba shi ya ci.” Malam Kasimu ya ce da wani makocinsa, a lokacin da ya nemi da ya sa Dan’amadu a makaranta.
Ita ma Larai, mahaifiyar Dan’amadu, wata mata ce da dole ta zama kazama, dole ta zama gajiyayyiya, ta zama mai duhun kwakwalwa, wadda a kullum tunaninta shi ne yadda za su sami na sawa a baki. Saboda tsananin yawon haya da zaman dabaron da suka yi wa gidan haya ya sa ta iya abubuwa da yawa, idan tana zagi ko fada sai ka rantse ‘yar Maguzawa, idan tana habaici kamar ‘yar mahauta, idan tana zukar sigari kamar kanwar Kabusu, wanda a da sam ba ta iya ba, ta koya ne a yawon haya.
Don haka rayuwar Dan’amadu ta kasance cikin hatsari, hatsarin rashin samun rayuwa tagari, hatsarin yi wa duniya zuwan zomo kasuwa, zuwa da gudu, komawa a guje.
To idan ka dauki rayuwar iyayen Dan’amadu ka dora a ta iyayen Bala, su Malam Sabo, za ka tarar dan bambancin kadan ne, wannan dalilin ne ya sa ‘ya’yan suka zama abokan juna, dama sai hali ya zo daya, abota kan kullu. Kuma dolen su, matsin rayuwa ya sa suke neman matsera, ta yin kwadayi ko bara a wani lokaci ko kuma yawon bola, ko dai wasu abubuwan da suka kauce hanya. Kuma ire-iren su suna da yawa a unguwar nan.
*****
Wasu yara kusan su ashirin, dauke da likidirai na roba da na karfe, wasu jarkoki, wasu kuma garewani sun yo jere (layi) don zuwa diban ruwa. Idan ka duba, za ka ga Bala a cikinsu da wani likidiri na roba, ja, yana tafe kafa babu takalmi.
Wani dattijo a bisa keke ya zo zai wuce su yana ta kada musu kararrawa, da kyar ya samu suka ba shi hanya, ya wuce yana fadin “Allah Sarki ‘ya’yanmu, ku an bar ku da jelen diban ruwa da bin layi, mu an kakaba mana dawainiyar neman kalanzir ko man fetur da bin layi.” Ya wuce.
A daidai lokacin Dan’amadu ya rasgo a guje dauke da garwarsa ta diban ruwa a hannu, da nufin ya tsinkayi su Bala don su tafi tare. Yana zuwa bai tsaya a ko’ina ba sai kusa da Bala yana nishi yana fadin. “Bala sawunka nawa?”
“Cawuna biyu na Babata. Yanju na cedawa ne zan kai wa Cahura mai dan wake.” In ji Bala.
Dan’amadu ya ce “Ni ma daga wannan na gama, sai in debo wa Tanimu mai shayi sahu biyu zai saya.”
A haka kowanne yaro da irin hirar da yake, suka ci gaba da tafiya, suna karya kusurwa, sai ga wani mahaukaci da suka saba tsokana mai suna Danballolo, ai kuwa sai yaran nan suka tarwatse, wasu suka fara kida da garewaninsu da likidirai, wasu suna waka suna tsalle suna cewa.
“Ga Danballolo a gari!”
Masu amsawa na cewa “To.
“Kowa ya gudu gida.”
“To.”
“Kowa ya rufe gida.”
“Mata su shige daki.”
“To.”
“Yara a shiga karkashin gado.”
“To.”
“Manya a baje da gudu.”
“To.”
“In ba haka ba ya yo barna.”
“To.”
Sai su hada baki “Ga Danballolo a gari!”
Haka suka yi ta yi, shi kuma sai ya bi su nan a guje, ya yi can a guje a wani lokacin ya tsaya yana taka rawa, inda su kuma yaran za su kara cashewa da waka, suna tsalle.
Sun bata lokaci sosai kafin wasu su gaji, su kyale shi, su tafi, wasu kuma suka ci gaba da bin shi.
Abin da zai ba ka mamaki shi ne, duk mutanen da ke tarar da yaran babu mai tsawatar musu, face wasu ka ji sun ce.
“Kai Allah wadaran yaran nan!”
Wasu kuma dariya suke yi.
Rayuwar zaman marina ake yi, kowa da da inda ya sa gaba. Wani bai damu da ya kwabi ko ya dora dan wani a kan hanya madaidaiciya ba, mai kokarin yin hakan akan kira shi da dan sa-ido ko kimina (wato munafuki).
Wadanda suka wuce din sun hadar da Dan’amadu da Bala, suka je, suka debo ruwan.
*****
Wasu yara suna ta wasanninsu a cikin hasken farin watan. Sam babu maganar samun wutar lantarki a unguwar Hayin Talaka, kamar yadda ruwan famfo ya kafe haka wutar lantarkin ta dusashe. Idan ka ga an kyallo wutar lantarki a unguwar to tabbatar da akwai dalili, ko dai masu lura da wutar na gundumar sun zo karbar kudin wuta, ko kuma wani mai mukamin siyasa zai kawo ziyara unguwar.
Dalilai da yawa sun tabbatar a fadin jihar Kano in dai unguwa irin Hayin Talaka ce, to dan ragowar jin dadin rayuwar an kwakule. Ina ruwan shugabannin Nijeriya da talaka, in ba zabe ba?
Don haka mazauna unguwar sun saba da wannan zaman kunci, sun kawar da kansu daga batun lantarki bare su sa ran amfana da ita, idan wata ya fito yaran unguwar sukan hada dandalolin wasanninsu, kamar yadda yake wakana a wannan lokaci.
Wasu kuma, ga su nan zube kamar yayi, kwankwance rututu suna barci a bisa tabarmi, wasu a bisa ledoji, wasu a kwalaye, wasu ma a kasa.
Wasu kuma zirga-zirgar su suke yi, na aike ko na yawo. Dan’amadu ne tafe, shi da wani abokinsa mai suna Lalo, suna tafiya don zuwa gidan kallo, hira suke yi.
Lalo ya ce, “Allah ya sa Canis za a yi yau, ni na fi son kallon Canis, ko kuma Amerika.”
Dan’amadu ya kalle shi “Tab, Allah ya sa Indiya a ke yi.”
Lalo ya yi dariya “To Amita mai-kaho.” Wata sara ce suke da ita, idan mutum yana wakar Indiya ko yana yin maganar Indiya ko yana yin rawar Indiya, ko ya yi zance a kan Indiya, sai a yi dariya a ce “Amita mai-kaho.” Wai shi mayen Indiya ne.
Suka karasa gidan kallon, kowanne da fatan a ce abin da yake so ake yi. A bakin kofar shiga gidan suka biya kudin shiga, kowannensu ya biya Naira talatin-talatin.
A cikin kangon gidan kallon yara ne kanana damkar masu kananun shekaru, saboda yawansu, ba za ka iya shakar kyakkyawar iska ba, sai iska mai dumi ta numfashi, da warin rana da gumuwar dauda da dauda za ka ji.
Akwai matasa a gidan, amma ba su kai kananun yaran yawa ba.
Idan son samu ne, wadannan yaran a ce a wannan lokacin suna makarantun allo ko Islamiyya ta dare, ko suna darasi a gida, ko suna sauraren nasihohi da karatun hikayoyin kaifafa zukata ko fadakarwa, ko kuma a ce wasun su sun kwanta barci don tashi da wuri. Amma ga su a gidan kallo suna kallon abu mara muhimmanci.
A unguwar Hayin Talaka, kamar babu manya, wato iyaye da malamai, kuma babu shugabanni nagari a unguwar.
Burin Lalo ne ya cika, domin fim din Amurka ake nunawa na fadace-fadace da harbe-harben bindigogi. Lalo ya yi murna yana kallon Dan’amadu “Yauwa, Amurka ake yi.”
Dan’amadu ya yi tsaki, ya nemi wuri kusa da Lalo ya zauna, ya ce “Su gidan nan sun fiye yin Amurka.”
Lalo bai ce masa komai ba, sai da dariya da yake yi.
Fim din ya ci gaba da gudana ana ta bata-kashi, yara suna ta yin ihu, da sowa, wasu suna fadin “doke shi,” wasu na cewa “harbe shi,” ko “fasa masa hanci,” ko kuma ka ji sun ce “kusha!” haka dai.
Idan aka zo wurin da ake nuna batsa kuwa sai ka ji gidan kallon ya yi tsit, masu tunani na yi, haka nan masu nutsuwa ma suna yi. Can kuma sai ka ji sun yi sowa, suna fadin wata sara ta “Lagwada! Lagwada!!”
Munin abin yana da yawa, karamin yaron da tunaninsa da hankalinsa ba su nuna ba, ga shi yana kallon mu’amalar mace da namiji, wanda hakan yake gina musu mummunan tunani.
Bayan an gama, a ka’ida finafinai biyu suke gani, ko na Amurka duka biyun ko na Canis, ko kuma a gauraya musu Amurka da Canis ko kuma da Indiya.
Haka yaran suka shure sama da sa’o’i uku suna kallon kafin kuma a gama su fita daga cikin gidan kallon.
Bayan sun fita ne, wasu mutanen suka rinka shiga, wadanda suka hadar har da masu baburan haya da Napep. Za ka yi tunanin wani sabon kallon za a kuma yi, to ko kadan ba haka ba ne, su masu shiga a yanzu, suna shiga ne don kwana, wurin makwancinsu ne, kashi daya cikin uku daga cikinsu ‘yan unguwar ne wadanda ba su da makwanci a gidajen iyayensu. Kashi biyu kuwa baki ne, wadanda babu wanda zai ce ya sansu ko ya san daga inda suke. Wasunsu ‘yan acaba ko ‘yan Napep ne, wasu masu sayar da ruwan leda (fiya wata), wasu kuma masu sayar da goba ne ko yalo, ko kuma maganin Turawa da ake sayar wa a kwali ko magungunan gargajiya, kawai suke zuwa su bayar da hasafi don su kwana a kangon gidan kallon, idan an tashi daga kallo, da safe su tashi su kama gabansu, idan ta kaya su dawo, idan kuma ba ta kaya ba su kara gaba, duk inda ta fadi sha ne a gurinsu, cirani suka zo.
*****
Dan’amadu da Lalo suka dawo gida daga gidan kallo, Dan’amadu ya tsaya a inda yake kwanciya, shi kuwa Lalo ya kara gaba. Dan’amadu ya dubi inda ya ajiye guntuwar yagaggiyar tabarmarsa, wasu yara ya gani kwance a kai sun yi masa kaka-gida, ya yi tsaki.
“‘Yan banzan yara, ku ba za ku sami abin kwanciya ba, sai mutum ya ajiye nasa ku zo, ku kwanta masa a kai.” Ya finciki gefen tabarmar, wanda da ya sani bai yi hakan ba, domin a rabe ta zo masa, guntuwa a hannunsa, guntuwar a kasan yaran da suke kwance a kai.
Ransa ya baci, a fusace ya mirgine su kasa, ya dauke guntuwar tabarmar, yana ta tsaki. Su kuwa ko farkawa ba su yi ba, kansa ake ji, wai mahaukaci ya fada rijiya, barcinsu kawai suke yi.
Ya dubi guntayen tabarmar tasa a kufule, bai hakura ba sai da ya tattaka su da kafa, amma kamar dai kasan wurin yake takawa, yadda idan ya yi hakan ba za ta ji ba, su ma ba su ji ba, barcinsu kawai suke yi.
A bainar masu barcin, minshari da gurnanin da ke tashi kamar ana musayar wuta ne tsakanin zaki da namijin damisa wato damishere. Ji kake “Karr, karr!…Girr…girr!!…. Kyayyy… Kiyyyy!!
Can gefe guda Dan’amadu ya koma, ya shimfida guntattakin tabarmar wuri guda, ya haye bisanta yana fadin “Wush! Na gaji.” Bai san yadda ake yin addu’a yayin kwanciya barci ba, haka yake kwanciya.
Da karfe biyun dare ta gota, ilahirin cikin unguwar ya yi tsit. Ba fa tsit na yin kurum ba, a’a tsit na kasancewar mutane sun yi barci.
Amma a farkon unguwar akwai wani mai sayar da shayi da wasu samari, su biyu da suke hira a wajen, kusan al’adar su kenan, su zauna su yi ta hira tsawon dare suna bayar da labarin kanzon kurege, ko hirar kwallon kafa. Shi ma mai shayin yakan yi kuru a zaune wai yana jiran mai zuwa siyen shayi.
Ta wani bangaren, zaman nasa ya samo asali ne da wani labari da ya taba ji cewar, wai wani mai shayi ne a Ikko ya kai tsakar dare yana sayar da shayi, wasu aljanu suka zo suka siyi moda biyu, suka ba shi miliyan goma, ya zama mai kudi. To shi ma Malam Zubairu mai shayi wannan dalilin ne ya sa, yake raba dare yana zaman tsammanin wa rabbuka.
Sau tari idan ya zauna yakan raya a ransa cewar idan har suka zo duka kwallar shayin zai zuba musu, ya karbi miliyoyin da za su ba shi ko da ba su kai goma ba.
To idan ka dauke hirar samarin nan wanda Malam Zubairu ke dan tsurma musu baki, sai gurnanin minsharan masu barci da ke wurin.
Lokacin da karfe uku ta rage saura ‘yan dakikoki, wani hasken fitilar mota ya wadaci cikin layin, hasken kamar ketowar alfijir. Samarin nan biyu suka yi dif, suka daina hirar, alamun tsoro a tare da su, kafin motar ta kara sulalowa inda suke, sun gama mikewa tsaye, daya daga cikin su ya ce “Kai ni dai barci nake ji.”
“Ni ma haka.” In ji dayan da saurin baki. Kafin ka ce mene ne wannan, sun bace kamar walkiya.
Malam Zubairu kuwa tuni ya jera kofuna, kafin motar ta gama tsayawa a kusa da teburin shayin nasa ya gama cika su da madara da sauran kayan hadin shayi, ya fara dagawa cike da murna, a tsammaninsa ya sami aljanu masu saye, zai yi kudi.
Mutane hudu ne a cikin motar, gaba da baya, bayan da suka tsaya, uku daga ciki suka fito, direban motar kawai suka bari, suka nufi wurin Malam Zubairu. Shi kuwa, sai fama yake da daga shayi domin ya sanyaya shi, yana fadin.
“Lale marhabin, sannun ku da zuwa fararen aljanu, ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba. Na san za ku iya shanyewa duka, mu dai arzikinku muke nema a ba mu, mu ma, mu samu.”
Kallon sa kawai suke yi, suna tunanin ko gamo ya yi? To amma bai dame su ba, su abin da ya kawo su suka zo yi. Biyu suka kewaya inda yake.
“Malam mai shayi ba ka san an hana kai wa dare ba?” Wani mai magana da Hausar da ba ta ishe shi ba ne ya yi maganar.
A yanzu Malam Zubairu ya fara zargin ba gamo ya yi da fararen aljanu ba, gamo ya yi da bakaken mutane. Ya ce “Ban shina ba, wane ne ya sanya wagga doka kuma?”
Daya ya ce, “Mu ne.” Ba su yi wata-wata ba suka rarumi Malam Zubairu suna fadin “Sai mun tafi da kai, kuma idan ka yi mana kwakwazo sai jikinka ya gaya maka.”
Suka yi sama da shi, gami da rufe masa baki, yana wantsal-wantsal da kafafunsa. Ya makuru iyakar makurawa. Da ya tabbatar akwai matsala, sai ya yunkura iya karfinsa yana fizge-fizge da yamutse-yamutse, har sai da ya samu ya fincike, bai yi kwakwazon ba kamar yadda suka ja masa kunne, amma ya kwaci kansa, ya ranta a na kare, babu ko waiwaye.
Mutanen da suka ga sun rasa wannan, sai suka laluba daga cikin yara da almajirai da mutanen da ke kwankwance suka dauki na dauka, suka yi tafiyar su.
A da ne masu amfani da sassan mutane wajen yin tsafi suke wahala wajen samo mutanen da za su yi tsafin da su, amma a yanzu suna samun su ne a bagas, domin idan suka bi kwararo ko bakin kasuwanni, ko cikin unguwanni irin su Hayin Talaka, sai ka ga cikin sauki sun samu abin da suke nema.
*****
Da safe, a nan unguwar Hayin Talaka, an farka ba a ga yara uku ba, gami da Malam Zubairu mai shayi. Cikin yaran da aka sace har da Bala, abokin Dan’amadu.
Samari biyu masu hirar dare ne suka shaida wa jama’ar unguwa cewar barayin mutane (‘yan yankan kai) ne suka zo, suka sace su, su ma wai da kyar suka kwaci kansu. Al’amarin ya tsorata mutanen unguwar, inda ko ina ka je, ciki da waje na gidaje, yara da manya, mata da maza, zancen da suke yi kenan. Wato abin nema ne ya samu matar falke ta haifi jaki, gwanaye ne wajen surutu a kan abu idan ya faru, ko zagi ga shugabanni, ko zantuka a kan matsaloli, amma babu kokarin magance su, ko samar da mafita.
“Rabon da a yi irin wannan satar ta yara an shude shekara fa.” Malam Ado Makeri yake gaya wa abokin sa Sale a hirar da suke yi.
“Yau su Sabitu ba za su kwana a waje ba, gara mu je can cikin daki, mu cunkusa mu kwana. Allah ya kiyaye mu daga sankarau.” In ji Malam Sale.
Malam Ado Makeri ya yi murmushin takaici, ya ce “Ai gara kai dakinka da dan fadi, ni da dakina yake kamar akurki fa? Ga yara bakwai, na zarta ka da yaro daya, to a haka za mu cusu, mu kwana.”
Irin wannan ne ke faruwa a wannan unguwa, duk lokacin da aka samu kwatankwacin haka, ko wani hargitsi ya faru, na rigima ko sumamen ‘yandaba, to sai ka ga magidanta suna cusuwa a tsukakkun dakunansu suna kwanciya. Idan ka ga dakunan; ‘yan tsugul, wanda daya ya yi wa mutum biyu kadan saboda kankantarsa da tarin cunkuson shirgi, to amma sai ka ga maigida da matarsa da ‘ya’yansa hudu ko biyar ko shida zuwa sama sun cunkusu, sun kwanta a ciki, wai ana tsoron wani abu ya faru da yaro ko a sace shi, alamun wai ana son yaron, wanda son rakumin yara kenan.
*****
Tun daga waje, duk wanda ya ga gidan zai san kamar kumbo kamar katanta, gida ne gamin-gambiza a bangare gininsa, asalin gidan ginin kasa ne, amma da wani bangare ya rushe sai aka yi gyara da tsoffin bulon siminti da aka tsinto. A wani bangare na gidan an yi masa yabe a wani bangaren kuma ko oho, ga bulullukan kasa nan da na siminti a tsirara.
Kofar gidan babu dabe, kasa ce. Akwai wata kazamar bishiyar maina a kofar gidan, wadda ta sha sara, ta sha karta da kwarzani daga yaran da suke dabdalar wasanni a kasanta ko a bisanta.
Akwai cakwalkwalalliyar kwatar da ta fito daga cikin gidan, kwata-kwata ba a kwashe kwatamin, ba a share ta, babban kokarin da ake a kanta shi ne a bai wa ruwa wuri ya wuce, amma a cakwale take, kuma babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da yara biyu ko uku ko sama da haka sun fada cikinta ba.
Gidan yana da zaure, a zauren babu yabe, bulo ne a tsirara, akwai shimigin ledoji, da kwalaye, da buhuna da tabarmun kwanciyar yara. A gefe kuma akwai jerin kwandunan shara kusan guda bakwai, sai tsami da doyi suke yi, kudaje na bin sharar suna wata kara “yuuuy!”
Kana lekawa cikin gidan za ka tabbatar gida ne na kazamai. Gidan yana da zurfi, mai dauke da jerin gwanon dakuna ashirin da uku, a gabas guda goma sha daya, a yamma guda goma sha daya, a can kuryar gidan kuma daki daya ne, na mamallakiyar gidan, tsohuwa Yabi Buhun Bala’i.
Kwatar gidan, ta taso ne tun daga kuryar gidan kusa da rijiya ta ratso tsakar gidan, ta wuce zuwa waje. Kowanne kofar daki akwai murhu daya ko biyu har zuwa uku, da yake akwai masu sayar da abincin sayarwa, ire-iren su koko, kunu ko gyada ko gurjiya, abubuwan sayarwa dai an ce babu wanda ba a sayarwa a gidan; shinkafa, shinkafa da wake, doya, dashishi, alkubus, taliya, awara, tuwo (na masara ko dawa ko gero ko shinkafa), waina ko fanke ko funkaso ko gurasa ko dan-bagalaje ko danmalele da sauransu.
A wani bangaren kuma gyada, gurjiya, masara gasasshiya da sauransu. Gidan kamar gidan masana’antar saye da sayarwa ta abubuwan tallan yara.
Bayan murhuna, a kowanne kofar daki akwai shirgunan kaya, irin su kejinan kaji da tantabaru da agwagi, akwai buhunan kayan sawa da suka yi dauda, akwai kwandunan kwanuka da sauransu.
Bandakin gidan guda daya ne, yana can daf da kofar fita daga gidan, a nan ne za ka tarar da matattarar kazanta, ta jerin faretin fo-fo (mazubin kashi) na yara, wasu da kashin a ciki, wasu kuma an zubar ba a wanke fo din ba, ga kashin nan yababa a ciki. Wadanda babu kashi an kife su. Idan ka ji an ce harbutsalle-cunkus, to sunan gidan ne.
Mata ne da yara yanyame a gidan, amma a wannan loton sun fi taruwa a kofar dakin mahaifiyar Bala, wadda ake yi wa jajen sace shi da aka yi a daren jiya. Irin wannan al’ada ce ke faruwa a gidan, idan wani abu ya faru na asara, ko batan yaro sai ka ga mutanen gidan musamman mata da yara sun yi cirko-cirko a kofar dakin wadda abin ya faru a kanta kamar gaske ana jajanta mata, ana ta magana a kai, amma dan lokaci na ja, sai ka ga kowa ya kama harkar gabansa, wasu har da shewa sun manta da abin da ya faru a dazu ko a jiya. Kamar yadda gidan yake babu tsari, haka zaman gidan yake.
Uwale, mahaifiyar Bala, kuka take yi, su ma wadanda ke kusa da ita, akwai masu taya ta kukan.
“Don rashin imani a sace yaro karami, za a yanke masa kai.” Uwale ta fadi haka, da shisshikar kuka.
“Hakuri za ki yi, in Allah ya yarda za a gan su.” Wata mata mai suna Atuwa ta ce da ita.
Kwanaki biyu suka wuce, watanni da shekara suka zo, suka gifta amma ba a gano su Balan ba, har ma iyaye sun hakura da shi, sun ci gaba da sabgar gabansu.
*****
Tuni Dan’amadu ya canja manyan abokai har guda biyu, wadanda suke tafiya yawon bola tare, wato Sule da Lalo. Lalo a unguwar Rafin Shara yake, kusa da unguwar Hayin Talaka. Ba shi da wayo sosai kamar Dan’amadu.
Sule kuwa asalinsa almajiri ne, yana da wayo, don ya dan girmi su Dan’amadu, fitinanne ne, kullum cikin rigima da daru yake, idonsa a bude yake. Kai hatta ma yadda aka kawo shi cikin birni daban yake da sauran.
AN KAWO SULE BIRNI YIN BARA
Tsahare tana zaune ita da danta Sule mai shekaru uku da ‘yan kai yana ta callara kuka, ta yi tagumi cikin hawaye tana kallon sa.
Tsawon lokaci suna cikin wannan halin kafin Allah ya dawo da mijinta Malam Idi – Ya shigo rataye da fartanya a kafada ransa a bace, ko sallama bai mata ba, ya shigo yana kallon Sule, kamar ya fizgo shi ya buga da kasa.
“Shi kuma wannan kukan uban me yake yi?”
Tsahare ta dube shi cikin mamakin tambayar da ya yi ta ce, “Ai ka sani. Yunwa yake ji, kai muke jira ka dawo, ka kawo abin da ka samo ko yaron nan ya ci, ya daina kuka.”
Malam Idi ya harare ta “To ban samo komai ba, sai ya mutu!”
“Kamar yaya, ya mutu? Yaro ne fa.”
Malam Idi ya yi tsaki, “Yaron bai san babu ba ne? Tun safe nake yawon neman kwadago ban samu ba, sai tarin bacin rai da me zan ji?”
Tsahare ta ce “Ta ina wannan yaron zai san ba ka samo komai ba?”
Sule sai kallon ubansa yake yi, yana wage baki cikin kuka.
“To kar ya sani din.” Ya fada kamar ya mare shi, “Wallahi binni zan kai shi bara, don ubansa ya je can ya karata.”
Tsahare ta saki baki, “Wai me yake damunka ne? Binni fa ka ce za kai shi, talauci hauka ne?”
“Ai kuwa zan nuna miki talaucin ma ya fi hauka, don sai na kai shi binnin.” Ya yi gaba a fusace, ya shiga daki, yana zage-zage.
BIRNI/RIJIYAR LEMO
Malam Idi rike da hannun Sule a tsakiyar birni sai kalle-kallen gine-gine da motoci yake yi. Kamar yadda yake kalle-kalle haka mutane ke kallon shi, saboda ganin yadda yake janye da dan karamin yaro ba tare da kula ba.
Daf da wajen wani mutum mai siyar da lemon bawo, Malam Idi ya tsaya, yana kokarin yin magana, mai lemon ya riga shi da cewa.
“Malam na ga kana ta dube-dube ko yaron bata ya yi ne a kwatanta maka ofishin ‘yansanda?”
Malam Idi ya zaro idanu, “Aniyarka ta bi ka, Allah ya raba mu da ofishin ‘yansanda. Ba bata ya yi ba, dana ne, ina neman inda makarantar allo take ne.”
Sule kuwa sai kallon lemon yake, kamar ya dauka, kamar kar ya dauka.
Mai lemo ya yi dariya, “Ai makarantun allo suna da yawa a unguwar nan, ta wanne malami kake nema?”
Malam Idi ya yi tsaki, “Kowacce ma ina nema.”
Mamaki ya kama mai lemon, ya nuna masa gaba, ya ce “To ka yi can za ka same su da yawa sai wadda ka zaba.”
Malam Idi ya yi godiya, kana ya ce “Ba za ka dan ba yaron ko rabin lemon ba, ka ga sai kallon ka yake yi?”
Mailemo ya ce, “Ina kudin?”
Malam Idi ya ce “Au! Ba za ka ba shi don Allah ba? Wallahi ba ni da ko ranyo bare sisin kobo.”
“Ni ma sai da na ba da kudi aka ba ni.” Cewar Mailemo.
Malam Idi ya ce, “Ai shi kenan tun da ba ka yi don Allah sai don kudi.” Ya ja Sule suka kara gaba yana mita. Mailemo ya bi shi da kallo yana mamaki.
*****
Daga inda Mailemo yake, layi hudu Malam Idi ya wuce, ya sami makarantar allo a layi na biyar daga farko, ya isa, yana murna.
Makarantar babba ce, kuma dadaddiya, domin rumfar kwano ta mamaye kofar wani gida, cike da almajirai da alluna da jakunkunansu birjik.
Malam Idi ya karasa, ya tafi gaba-gadi zuwa wajen Malam Mai’almajirai don isar da dalilin zuwansa. Malam Mai’almajirai ya dakatar da shi, alamun ya dan jira shi yana wani abu.
Sai bayan da Malam Mai’almajirai ya sallami almajirai guda uku da ya biya wa karatu, sannan ya saurari Malam Idi.
“Ina sauraron ka Malam me ke tafe da kai?”
Malam Idi ya gyara zama, ya ce “Yauwa Malam, yaro na kawo bara tun daga karkararmu. Ga shi nan.” Ya nuna Sule.
Malam Mai’almajirai ya kalli Sule, sannan ya dubi Malam Idi.
“Na ji ka ce bara.”
“E. Bara na kawo shi.”
“Ba a kawo yaro bara wannan makarantar, sai dai karatu.”
“To karatu malam, na dauka duk daya ne?”
“Ba daya ba ne.” Cewar Malam, ya sake duban Sule. “Sannan wannan yaron ya yi kankantar da za a kawo shi karatu. Kuma a ka’idarmu duk yaron da za a kawo karatu ana hado shi da da kayayyakinsa na sawa da abinci da su sabulai da sauransu. Don haka mu a nan ba za mu karbi wannan yaron ba, ka mai da shi gida sai ya kara girma tukun, wannan ba zai fahimci komai ba.”
Malam Idi ya fara zazzare idanu ya kasa magana, sai daga bisani ya ce, “To na gode Malam. Amma ina son zan bar shi a nan, zan dan zagaya in yi fitsari sai in zo mu tafi.”
“Wannan ba matsala.” Cewar Malam, ya juya, ya kwalla wa wani yaro kira. “Kai Tala, zo, yi sauri raka wannan malamin makewayi zai kama ruwa. Ga buta can.” Ya nuna masa butar.
Malam Idi ya mike, ya nufi wajen butar. Sule ya so, ya ki zama, sai da Malam ya lallaba shi. Malam Idi ya dauki butar, Tala ya wuce gaba, ya bi shi.
Tala da Malam Idi suka karasa wajen makewayi, Malam Idi ya nufi kofa don shiga, Tala ya sami wuri guda ya tsaya don ya jira shi. Malam Idi ya juyo, ya dube shi.
“Ka tafi mana, ai zan iya komawa. Ko tsayawa za ka yi sai na gama?”
Tala ya girgiza kai, ya ce, “A’a ai sha nake sai ka gama sai mu koma, tun da za ka koma kai kadai, shi kenan.” Ya juya, ya tafi.
Jim kadan da tafiyar Tala, Malam Idi ya dudduba, ya ga babu wanda yake kallon sa, sai ya ajiye butar, ya zagaya ta baya, ya gudu. Wannan shi ne yadda mahaifin Sule ya bar shi a birni ya gudu.
Sule bai yi karatu ba, don ba karatun aka kawo shi ba, sai ya zama rikakken dan iskan gari, ya gagari malam da duk sauran ‘yan makaranta har da hukuma sai da ya shigar musu hanci.
*****
“Kai banza ne, ai idan ba ka sha ba, to ba za ka yi zazu ba, ba za ka samu da yawa ba.” Lalo yake gaya wa Dan’amadu, idan yana so ya zuki sigarin.
Haka shi ma Sule yakan dora, ya nuna lallai Dan’amadu bai waye ba.
Dan’amadu a farko ya ce, “Ni dai Babana nake tsoro.”
Lalo ya yi dariya, ya ce, “To Baban naka ganin ka yake yi, ko kuma a gida kake sha? Ai ka sha kawai, ka yi kitimirmira, sai ka cika buhu da jari-bola da wuri.”
Tun Dan’amadu ba ya yarda, har ya fara amincewa, domin wani lokacin yana lura da idan Lalo ko Sule suka sha sholisho ko taba ko wiwi sukan fi shi samun jarin bola. Don idan suka bugu ko ina maka kafafunsu suke yi, su samo abin da za su samo. Haka nan sukan iya dadewa suna tono kasa ko bola ko rami. To a haka Dan’amadu ya fara gwada shan kayan maye don caja kwakwalwarsa da daukar zafi.
“Dan’adam inji ne sai da daukar zafi. Ita kuwa kwakwalwa batur ce sai da daukar caji, yayin da hanci kuma ya zamo salansa sai da fitar da hayaki.” In ji Lalo da Sule.
Tuni suka kware wajen shaye-shaye, sannan sun koyi yawo da makami kamar ‘yar karamar wuka, a jikinsu. Wani lokacin sukan hada daba, wadda suke zama, kuma har wasu yaran sukan taya su zaman. Sai ka ga suna ta wasan karen itatuwa ko kara ko kuma sanduna, wasu lokutan kuma wasanni na banza masu muni.
*
Watarana mahaifin wani yaro mai suna Ididiya, ya kamo shi daga dabar su Dan’amadu saboda bai je makaranta ba, ya zane shi, kana ya kawo shi kofar gida, ya zare masa idanu ya ce “Ididiya me ya sa ba ka je makaranta ba?”
Ididiya yana ciccije baki cikin bacin rai, ya ce “Wallahi na je Baba.”
“Da ka je ai ba zan ganka a wajen shaidanun yaran nan ba.” Cewar mahaifin.
Ididiya ya kuma dagewa yana cewa “Baba wallahi na je.” Yana kuka. Amma sam mahaifinsa bai yarda ba, ya sake cula masa bulala a gadon baya domin ya sami tabbacin ya je din ko bai je ba.
“Kana can wajen yawon banza, ta ya zan yarda ka je makaranta.”
Abin ya ishi Ididiya, ya ce, “Baba a tsine uwar mai karya idan ban je makarantar ba?”
Mamaki ya kama mahaifin Ididiya, me yake ji haka, da shi za a tsine uwar mai karyar da dansa ko kuwa yaya aka fara? Ya sami bakinsa na cewa.
“A’a, ba sai ka tsine ba, je ka.” Ya sallami yaro, a ransa yana fatan Allah ya sa kar yaron ya rike shi a matsayin mai karyar, don ya ji tsoron kar a tsine din.
Ididiya, ya tashi, ya kara gaba, a ransa yana farin ciki ya samu nasara. Komawa dabar su Dan’amadu ya yi.
*****
‘Yan shekarun da suka karu a kan rayuwar su Dan’amadu ba su da yawa, don haka har yanzu suna nan a matsayin yara.
Dan’amadu da Sule sun dade da sauya sana’a daga ta baban-bola sun zama manyan dilolin tabar wiwi.
Abokinsa Lalo kuwa, wanda ya taso da zafin kai, kuma tuburarre ya tubure a harkar bangar siyasa, ya zama rikakken dan jagaliyar siyasa, dan sari-ka-noke, kuma dan-kashe-in-biya ka.
A wani kududdufi dake bayan unguwar Hayin Talaka, a nan su Dan’amadu suke harkar sayar da tabar wiwi, kuma suna samun kasuwa, domin a kalla sun cike sharuddan da ya kamata su cike. Duk sati biyu shi da abokan sana’arsa suna aikawa ‘yansandan da ke dibishin din unguwar kudin Laraba; wato kudin toshiyar baki, haka ma suna aikawa ma’aikatan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na shiyyar su irin wadannan kudade.
Don haka, in har za a zo kame, to ba a tarar da su a gurin, sai mai tsautsayi, shi ma mai tsautsayin idan an kama shi, ba ya wuce awoyi kadan za ka ga an sako shi.
Lokaci-lokaci, Lalo yakan kai wa su Dan’amadu ziyara. Lalo ya sauya sosai, ya yi kudi. Haka suke zama kowa yana kurin irin abubuwan da yake samu da irin gararanba ko kitimurmurar da yake yi. Suna hirar, suna shan kayan maye.
“Ku fa wahala kawai kuke yi?” Lalo ya ce da Dan’amadu., “Ga inda ake samun kudi a banza, kawai taku za ku sauya, ku zama manyan jajayen wuya.”
“Ka yi mana bayani a bude mana, ka tsaya kana ja mana rai.”
Lalo ya yi dariya, “To wanne irin bayani da ya wuce wannan. Mutum daya kawai za ku sankame sai ku samu kudin sama da shekara biyu a wannan harkar da kuke yi.”
“Sankamewa? Kana nufin sace mutane, kidinafin?”
“Harkar da ta ke ja kenan.” Ya ci gaba da dariya. “A nan dai wahalar da kanku kawai kuke yi, ni ma ina kawo muku ziyara ne don mun saba.”
Suka dan yi shiru na lokaci. Kana Dan’amadu ya jinjina kansa.
“Tuntuni na yi wannan tunanin, da za ka bude mana yadda aikin yake da mun fantsama ciki.”
“Haka ne. Za ku bar harkar wuka, ku koma bindiga da kwanan daji a wasu lokutan.” Cewar Lalo.
“To, me za a fasa. Kawai ka dora mu a hanya.”
Lalo ya mike, ya kama hannun Dan’amadu, ya ja shi, suka bar wurin.
Wannan tafiya, ita ce silar komawar Dan’amadu da wasu abokansa harkar sace mutane da karbar kudin fansa. Wasu lokutan akan ba su kwangilar kashe mutum a biya su.
Da yake su Dan’amadu, sun faro iskancinsu tun suna kanana, kuma sam ba su san tarbiyya ba, ba su san mutunci ko darajar mutane ba, nan da nan suka zamo manyan masu satar mutune a daji da kashe-in-biya ka.
Da tafiya ta yi tafiya, Dan’amadu da Lalo suka ja tawagarsu, suka ware, suka sami yaran da suke kamo musu mutane, a zo a biya kudin fansa. Haka nan idan wata kwangilar kisa ce suka samu, sai su yi da kansu ko su ba yaransu su yi. Suka zama gagarumai ‘yan ta’adda.
*****
Yau da gobe, rana dubu ta barawo, rana guda ta mai kaya.
Wata ranar Laraba, hukumar ‘yansanda karkashin jagorancin ASP Habu Sarki, suka shirya wani sumame saboda yawan sace-sace da kashe mutane da ake yi a titunan da su Dan’amadun suke kai wa farmaki.
Kare na yawo, kere na yawo wata rana za a hadu, su Dan’amadu da Lalo da sauran abokan ta’addancinsu sun fito, suka yi kicibis da ASP Habu da tawagarsa, nan suka shiga dauki ba dadi.
Tun da farko, su ASP Habu sun yi musu kwantan bauna, suka samu nasarar cim musu. Sai da suka fara yin musayar wuta, suka kashe wasu daga cikin abokan Dan’amadu, sannan suka jiggita wasu.
A hannu ASP Habu ya kama Dan’amadu. Ya damka shi ga yaransa. Cikin wannan hali, Dan’amadu ya dauka abin na wasa ne, amma daga bisani ya tabbatar lallai ya shiga hannu, za a tafi da shi, sai ya yi yunkurin kwacewa don ya gudu.
“Haba yaro, a rike kake.” Cewar Sergent Miko.
Dan’amadu ya sake yin kici-kicin don kwacewa, amma ya kasa. Saboda tabbas ya riku sosai, “Yaro bai san wuta ba, sai da ya taka.” Sergent ya maimaita masa.
Wannan magana ta bai wa Dan’amadu haushi, ya shammace shi, ya zaro guntuwar wukar da ke daure a kugunsa, ya caka masa a hannu. Babu shiri Sergent Miko ya sake shi, ya dafe hannunsa. Kafin ragowar ‘yansandan su farga Dan’amadu ya ranta a na kare, ya gudu.
Suka dawo gare shi, don ba shi agajin gaggawa ga mummunan raunin da Dan’amadu ya yi masa.
Shi kuma Sule a wajen guduwa, ya fada wani kududdufi da ke gefen hanya, kafin a kai masa daukin gaggawa, ya mutu, sai fito da gawar shi aka yi, suka kai shi asibiti.
*****
Tun da Dan’amadu ya gudu, sai yaran ASP Habu suka shiga binciken inda za su gan shi. A irin hakan ne, suka fuskanci iyayen yaran suna daure musu gindi, kuma suka yi zargin ko su suka boye su, suna boye musu.
Sun yi kokari da dabaru irin nasu na ma’aikata, amma suka samu tirjiya daga gare su da nuna rashin gaskiya, a haka, a binciken suka gano wasu makamai na su Dan’amadu a gidan iyayen shi, suka karfafa zargi a kansu, don haka suka kamo Malam Kasimu, suka tunkuda keyarsa cikin sel, ya fada can gefe, kuka yake yi, kamar karamin yaro, ga shi tsoho. Cike yake da bakin cikin abin da dansa ya jawo masa. Ya mike a hankali, ya dawo bakin kofar sel din mai sanda-sandar karafuna, yana magana da muryar kuka.
“Yallabai, ba zan iya kwana a dakin nan mai doyi da zarni da kunci da tsanani ba.” Ya fadi haka.
Wani dansanda ya harare shi.
“Malam ka yi hakuri, ka yi shiru da bakinka, tun da kun ki fadar gaskiya, har aka ga wasu makaman yaran a gidajenku, ai sai kun amsa tambayoyi.”
Malam Kasimu yana shirin bayar da amsa ya ji an dafa kafadarsa ta baya, bai yi niyyar juyawa ba, amma dai ya juya din. Wanda ya gani a wurin ya ba shi mamaki, Malam Garba ne mahaifin Lalo. Ya kasa magana, sai kallon shi da yake yi.
Malam Garba ya ce, “Kai ma danka ya yi sanadiyyar kawo ka nan kenan?”
“Kamar yadda naka ya yi silar kawo ka ke nan?” Malam Kasimu ya fada saboda tabbacin hakan.
Malam Garba ya yi murmushin takaici.
Malam Kasimu ya yi kwafa, ya ce, “Allah ya tsine wa yaran nan sun cuce mu wallahi, Allah ya isa…”
“A’a.” Malam Garba ya katse shi “Ba haka ya kamata ka fara fada ba, domin kai ka fara cutar danka kafin shi ma ya saka maka.”
“Ban gane ba?” Da mamaki Malam Kasimu ya fada, ya juya, ya fuskance shi sosai.
Malam Garba ya kama hannunsa suka sami wuri, suka zauna, “Idan Allah ya hore maka da, to yana nufin ya ba ka kiwo ne na musamman da yake son ka kula da shi yadda ya kamata. Kiwon da ya fi kiwon kowacce dabba. Amma a sani na da kai ko kadan ba ka yi kiwon da aka dora maka yadda ya kamata ba, ka yi sakaci, ko ba haka ba?”
Kallon shi kawai Malam Kasimu ya yi.
“Misali, ka siyo tunkiya ko akuya daga kasuwa, na san kana zuwa gida madauri da ma’ajiya za ka fara samar musu, sannan kuma abincin da abin sha su biyo baya. Daga haka kuma kullum, na san za ka rinka samo mata abinci da ruwan sha, idan ka gaza za ka ba ta damar zuwa ta nema kana sanye da idonka a kanta, ga duk inda za ta je din. Sannan kuma kana tabbatarwa da ta kwana a inda ka tanadar mata, kuma ba za ka bari wani abin cutarwa ya same ta ba.
“Wannan dan misali, ya isa a ce ka dora rayuwar ‘ya’yanka gabadaya ba wai Dan’amadu kawai ba, amma ba ka yi ba, ko ka yi?” Ya ba shi damar ya amsa.
Malam Kasimu ya girgiza kai alamun bai yi ba.
“To ka dora rayuwar ‘ya’yanka a bisa hanya ta cutarwa. Ilimi, shi ne ginshikin rayuwa da zai taimaka wa ‘ya’yanka don su san kansu, su san wane ne ya halicce su, su gane me suka zo yi duniya? Tarbiyya, ibada da sauran irinsu duk ba ka ba su ba. Kiwon lafiyarsu, tsare musu mutunci, duk ka gaza samar musu, ka ga, ka cuce su kenan, don haka idan har su ma a yanzu suka cuce ka, to sun rama wa kura aniyarta, kuma idan aka bi ta barawo ya kamata a bi ta ma bi sawu.”
Da Malam Garba ya yi shiru, duk cikin dakin sel din ma sai ya yi tsit, har sauran mutanen ciki sun yi mukus, sauraron sa kawai suke yi.
Malam Kasimu ya nisa, yana kallon Malam Garba, ya ce “To kai ka san da haka, me ya sa ba ka dora dan naka a kan turba irin wadda kake fada ba? Kuma ta yaya danka ya ja maka shigowa nan?”
Malam Garba ya yi murmushin karfin hali, ya ce, “Ni da kai duk kanwar ja ce, kamar yadda ake neman danka saboda satar mutane da karbar kudin fansa, da zargin kisa, haka shi ma dan nawa, a wajen bangar siyasa ne ya yi kisa, ya gudu. Kuma sun yi zargin ni nake daure masa gindi, na boye shi. Sai kuma tsautsayin da ya hau kaina, aka samu makamai a gida…”
Ya dan yi shiru, kafin ya dora da fadin “Sannan gaskiya ne abin da ka fada, duk wadancan abubuwan da na fada maka na san da su, na ki bi ne, na toge da uzirin talauci, wai rashin abin hannu a gani na shi ya hana ni aiwatar da abin da ya dace na kula da tarbiyyar ‘ya’yana.”
Ya dan yi shiru cikin damuwa, kafin ya ci gaba “A iya sanina, mutumin da bai kai ni samu da faraga ba ma zai iya, amma na kasa, ni da kaina ma wasu ayyukan ibada ba na yi, wai a gani na ni talaka ne ina fafutikar neman na sa wa a baki, maimakon na gode wa Allah da ya yi ni da rai da lafiya, ya yo ni dan’adam ba tsutsa ko dabba ba.” A yanzu idanunsa sun fara fitar da hawaye, duk da dakiyarsa. “Na gode Allah da ban mutu ba tare da na gane irin wautar da na yi ba, Allah ina rokonka da alfarmarka ka yafe min, kafin in mutu ko a kashe ni, Allah ya sa yarona ya yafe min, ya ji kaina, Allah ya dawo da hankalinsa kan mafificiyar hanya.”
Ya yi dif, haka su ma ragowar. Sun tausaya masa yadda ya kamata.
*****
Bayan kwana biyu, wani dansanda ya bude kofar sel din, ya dubi su Malam Kasimu “Kwa iya fitowa. Da alama zamanku a nan ya kare.”
Gabansu ya fadi, suna tunanin ko yana nufin kashe su za a yi! Malam Garba ya kasa jurewa, ya ce “Me kake nufi?”
“An kamo ‘ya’yan ku. Daya tun jiya, daya kuma dazu da safe. Kuma bincike ya tabbatar ba ku aikata laifin da ake zargin da su ba.”
A tare suka yi ajiyar zuciya.
*****
A wani daki na tuhumar masu laifi, suka hadu da ‘ya’yan nasu. Sannan kuma akwai ‘yansanda a tare da su. Suna daddaure cikin ankwa. Wani dansanda ne ya fara magana.
“Baba Allah ga ‘ya’yanku nan, kuna da ‘yan mintuna na tattaunawa kafin a tafi da su.” Daga haka bai kara cewa komai ba.
Malam Kasimu da Malam Garba suka kalli juna. Kana suka kalli yaran. Malam Garba ne ya so ya fara yin magana, sai ya kasa. To shi ma Malam Kasimun kasa yin maganar ya yi, yana kuka da hawaye. Dole dai Malam Garban ne ya yi maganar.
“Lalo an samu matsala, an yi kuskure da ya kamata a manta da su. A matsayina na mahaifinka ina roko ka yafe min duk wani laifi da na yi maka.”
Lalo, da ganin shi ka san a cikin maye yake, yana magana irin ta ‘yan kashe-in-biya-ka, “Na san kowane laifi ne, ko ma ba ka fada ba, kuma ba zan yafe ba!”
Kowa ya yi mamakin maganar Lalo, har ‘yansandan. Daga haka babu wanda ya sake yin magana, har aka ingiza su Dan’amadu cikin sel din. Iyayen kuwa suke je inda ya dace, don a sallame su.
A cikin sel Dan’amadu ya dubi Lalo, ya ce “Me ya sa ka yi wa mahaifinka haka?”
“Saboda, ya cancanci hakan ne.”
Dan’amadu ya ce, “Me ya sa ka fadi haka?”
Lalo ya dube shi “Ni da kai mun sha ganin wasu yara tun muna kanana suna tafiya makaranta, iyayensu sun sa su sun kuma tura su, shin kai mahaifinka ya taba sa ka a makaranta don ka yi karatu?”
Dan’amadu ya girgiza kai alamun a’a.
Lalo ya cije baki, “To ni ma haka. Sannan me mahaifan naka suka yi maka na inganta rayuwarka da ba ka tarbiyya? Misali, abincinka, abin shanka, suturarka, tsaftarka, tsaro da lafiyarka, haka shi kansa iliminka da duk wani abu da iyaye ya kamata su yi wa ‘ya’yansu. Me suka yi maka a ciki?”
“Gaskiya ban samu ko daya ba, mahaifana ba su san ci na da sha na ba, ba su san makwancina ba, ba su dora ni a kan turbar neman ilimi ba, ba su nuna min ga abu mai kyau da ya kamata in yi ba, ko wani abu mara kyau da ya kamata in gujewa ba. Lissafin babu-babu din da na samu daga iyayena suna da yawa.” In ji Dan’amadu.
Lalo ya girgiza kai cikin nadama, “To wadannan abubuwan duk Allah ya hori iyayenmu su yi mana amma ba su yi ba, suka mayar da mu ‘ya’yan haifi ka yasar. Don haka wanda ya ki bin Allah da Manzonsa (S.A.W.) dole ya fuskanci kin yafiya da kin biyayya daga dansa. Duk da muna yara, kuma mun rasa ilimi da abin da ya kamata, amma mun san yadda ya kamata rayuwa ta kasance, don muna gani da idanunmu. Sanin kanka ne, kowa ya san daidai kuma ya san ba daidai ba. Ko in ce na yafe ko in ce ban yafe ba, to Allah ma sai ya tambayi mahaifina. Sakamako kuma tun a duniya ka ga sun fara gani, kalli yadda aka kamo su a madadinmu, aka kulle su a kuntace.”
Suka kalli juna, Dan’amadu ya kasa magana.
“A yanzu, da muke cikin wannan gidan muke jiran hukuncin da babu wani dan’adam da zai bude baki ya ce yana so, kamata ya yi a ce muna can, muna neman ilimi don taimakon kai da kasarmu da al’ummarmu, ko muna can muna gwagwarmaya don aiki ga kasa da al’ummarmu da kanmu cikin farin ciki. Amma kalle mu fa.”
Bayan shiru na dan lokaci Lalo ya dora da cewa, “Idan ka manta bari in tuna maka rayuwar Aminu. Ai na san ba ka manta Aminu Yaro ba, sa’anmu, dan Malam Mamuda? Mahaifin shi bai fi mahaifanmu komai ba, shi ma talaka ne wanda har iyayenmu sun fi shi samu idan aka duba. To amma me ya faru? Yaya Malam Mamuda ya gudanar da rayuwarsa da ta ‘ya’yansa? Ai kai ma ka sani, ka san irin jajircewar da ya yi, da irin kokarinsa wajen ganin ya bibiyi rayuwar ‘ya’yan nasa, da make-maken nasa yake sa su a makaranta, yake dauke musu nauyin ci da sha da sutura gwargwadon kokarin sa.
“Idan ba ka manta ba, hatta tallan nan ta wulakanci, bai yarda ‘ya’yansa sun yi ba, ya yi kokarin kai su inda za a koya musu sana’a da kasuwanci. Bai yarda ya watsar ko ya wulakantar ko ya banzatar da rayuwarsu ba. A karshe me ya faru?” Ya dan yi shiru, kafin ya dora da cewa, “Kwanaki muna saman motar zagayen siyasa, ina busa kaho, mun tafi kamfen na yi kicibis da Aminun a cikin karamar motar shi yana tukawa, ashe ya zama babban ma’aikaci a makarantar jami’a. Har gaisawa muka yi da shi, ya kira sunana, wallahi sai da na ji wani abu a raina. Haka muna taren hanya, na gan shi, na basar, na sa aka kyale shi, ba a sace shi ba.”
Dif wajen ya yi cikin jimami.
*****
A kotu an sami su Dan’amadu da Lalo da abokan harkarsu da aka kamo da manyan laifuka, ciki har da kisan kai, alkali ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai sun daina numfashi.
Allah ya raba mu da rayuwar haifi-ka-yasar, amin.
“Wannan labarin ya tsuma mu, su kuma yara masu talla fa?”
Na yi murmushin takaici, “Ai nan ma akwai munanan abubuwa masu yawa, akwai kaico, bari ku ji labarin Harira ‘yar talla.”
Thanks