Yini Na Sha Biyu
Jin yadda karatun ya yi musu dadi, ya sa suka fara halartar wurin kafin ma lokacin da daliban suka saba fitowa. Bayan sun kama wuri sun zauna ya su ya su din ne kuma suka fara yi wa kansu tambayoyin, shin wannan zaman da suka fara yi a majalisar Malam Kunkurun ya dace da su? Kuma bai saba wa abin da aka aiko su yi ba? Inda mafiya yawansu suka tafi a kan cewa zaman nasu bai wani saba wa ka’idojin fitowar tasu ba. Domin ta hakan suna sa ran samun dabarun yaki da dama, wadanda za su taimaka musu wurin cimma waccan manufa da suka fito a kanta. A bisa wannan hujja da mafiya yawanu suka bayar, tsirarin ma suka dogara. Don haka suka sa sabuwar niyyar zama a makarantar Malam Kunkuru ba ma tare da kayyade lokaci ko ranar tafiyarsu daga wurin ba.
Da malamin ya fito, suna kan gaba wurin tambaya yau. Zomo wanda yake gaba daf da Malamin ya ce.
“Malam wace dabba ce ta fi kowa zafin cizo?”
Ilahirin dabbobin da suke cikin waccan runduna suka bayyana alamun farin ciki da tambayar da ya yi a fuskokinsu, ta hanyoyi da dama. Domin tambayar tasa ta shafi yaki, irin abubuwan da suka aminta ya dace su rika tambaya, a matsayinsu na wadanda yaki ya fito da su.
Malam Kunkuru ya ce. “Daga cikin abubuwan da cizonsu yake da dan Karen zafi akwai Kura. Idan da dama kar ka taba yarda Kura ta cije ka. Kodayake duk zafin cizon Kura kuma bai kai na Kada ba. Domin ya fi ta yawan hakora da karfin tsokokin da suke rike hakorin. Karairaya kashi a wurinsa ba a bakin komai yake ba. Don haka ka kiyaye inda duk ka ji ana labarin akwai fusatacce ko mayunwacen Kada a wurin. Ko da kuwa nan ne kadai hanya.”
Zomo ya ce. “Na gane, wato dai shi ne karshe a cizo?”
Malam Kunkuru ya ce. “Ni kam ban ce ba.”
Zomon ma ya kwata, yayin da kaso mafi tsoka na dabbobin wurin suka yi musu rakiya, dariyar ta karade wurin.
Daga can gefe Kurege ya ce. “To ita ma Kadar akwai wanda ya fi ta ne?”
Malam kunkuru ya ce. “Kwarai ma kuwa, domin akwai Kifin Okara: Wani katon kifi ne a cikin teku, wanda tsayinsa ya kai takun kafar bil’adama talatin da daya. Kuma bakinsa yana dauke da wasu manya-manyan hakora a kalla hamsin. Sanan yana da karkarfar tsokar baki, wadda take rike da hakorin. Kifayen Okara suna tafiya farauta ayari guda ne a cikin ruwa. Don haka idan ma abin farautarsu ya yi rashin sa’a, ba rukunin hakora daya ko baki daya ne zai cije shi ba. Wannan Kifin idan ka sake ya yi arangama da kai, kuma ya ayyana cinye ka, to ka yi tsalle ka fada can cikin makogoronsa kawai shi ne abin da zai fi maka sauki. Domin idan ka tsaya sai ya tattauna ka, to ban san wata adda ko gatari da zan iya kwatanta saransa da it aba.”
Da yawa daga mazauna majalisar suke ce. “To Ubangiji Ya yi mana tsari sa afkawa tarkonsa.”
Tsirarin da suka rage ba su yi waccan addu’ar ba suka hada baki da Kunkurun wurin amsawa: “Amin summa amin”
Tururuwa ta ce. “Malam to wace dabba ce kuma take da kyakkyar tsarin koyar da karatu.”
Malam Kunkuru ya ce. “Kaso mafi yawa na dabbobi ne suke da tsarin koyar da ‘ya’ya ko kananansu dabaru iri-iri na yadda za su zama daidai da kalubalen rayuwa. Amma daga cikin mafi kyan tsarin koyarwa akwai Kuregen Mika.”
Tururuwar ta ce. “Bayan wannan Kuregen namu ?”
Ya ce. “Iy fa.”
Ta ce. “To shi kuma ya tsarin karatun nasa yake?”
Malam Kunkuru ya ce. “Shi Kuregen Mika mafarauci ne, kuma daga cikin abubuwan da yakan yawan kamawa akwai Kunama. To idan ya tashi kafin ya bar ‘ya’yansa su fara kama Kunama kai tsaye, sai ya fara koyar da su yadda za su rika tinkarar ta. Domin idan ta yi musu wani harbin zai iya kai wa ga halakar su. Yakan kuma yi koyarwar ne ta hanyar bin matakai har guda uku: Da farko zai ba wa ‘ya’yan nasa matacciyar Kunama wadda aka cire wa kari. Idan ya lura sun iya bin duk inda nama yake a jikinta su kwakule, su cinye. Sai ya yarda sun cancanci a kai su aji na biyu kenan. A aji na biyu kuma, sai ya ba su Kunamar matacciya, amma da karinta a jiki. Idan ya lura sun iya cire karin su yar, sannan su cinye naman jiki, sai kuma ya kai su ga aji na uku, kuma na karshe. A wannan ajin ne kuma yake ba su gudar Kunamar, da ranta kuma da karinta a jiki, ya ga yadda za su yi da ita. Da zarar ya ga sun san yadda za su yi dabarar cire karin, su cinye naman, to dalibai sun samu kenan. Sai a yaye su, sun isa fita farauta, ba tare da wata fargaba ba.”
Tsawon lokacin da ya dauka yana wannan bayanin, ilahirin dabbobin sun yi fakare suna ta saurarensa, cikin wani yanayi da yake nuna tsabar kayatuwarsu da bayanan.
Kafin karatun na wannan yinin ya tashi, dukkanin dakarun da suke cikin wancan ayari da Sarkin ya aiko sun sa a ransu cewa ba su da ranar barin wannan majalisa. Domin ko waccan fafatawa ba ta kai wannan ilimin da za su samu a wannan makaranta muhimmanci ba.
Haka suka yi ta tambaya Malamin yana amsawa har yamma likis. Lokacin da Malamin ya tashi, dukkan dabbobi suka tarwatse. Su ma dakaru suka koma masaukinsu, kamar yadda suka yi a jiya.