Yini Na Sha Biyar
Da gari ya waye, da sassafe wasu kananan dabbobi karkashin kulawar Gada suka zo suka share fadar da geffanta tas. Sannan zuwa wani lokaci sauran dabbobi mazauna fada suka hallara, kafin daga bisani shi ma Zakin ya fito. Sai bayan kuma ya fito din ne rundunar suka rika jerowa sahu-sahu suna tahowa, bisa wani tsari mai kayatarwa.
Da suka gama hallara, sai suka kara yin wani dan fareti na musamman, don nuna wa fadar karin tabbacin yadda suke da karfin gwiwa. Dila da Kahuhu suka yi musu jawabai takaitattu, sannan shi ma Sarki ya mike tsaye, ya yi musu kalaman bankwana. Daga nan iyalan dabbobin da ke cikin rindunar suka kara yin bankwana na karshe. Ayari ya kama hanya ya yi gabas, kamar yadda na farko ya yi. Suka kuma tsaya su ma suna ta kallonsu suna addu’o’i har zuwa lokacin da suka kule, aka dena hango ko duhunsu.
Bayan wannan lokaci sai Sarkin ya kara jan hankalin kafatanin dabbobin da ke wurin cewa a dage kwarai wurin ci gaba da yi wa rindunonin biyu addu’ar samun nasara da kuma dawowarsu gida cikin iyalansu lafiya. Daga nan ya yi sallama da su, ya koma gida. Bayan wani dan gajeren lokaci su ma suka kama tirbobin nasu gidaddajin.