Yini Na Sha Bakwai
Washegari kafin Malam Kunkuru ya fito, daliban da suka zo jin karatun sun fara sa-in-sa tsakaninsu. Domin manyan dabbobin can suna zuwa suka kara yi wa Zomo gargadi, cewa su fa ba sa son wargi, don haka in zai shiga taitayinsa gara ya shiga. Maimakon kuma ya yi shiru, kamar yadda ‘yan’uwan nasa suka nema, sai da ya tanka musu. Aka kuma yi ta musayar kananan maganganu kasa-kasa, wadanda fitowar Malamin ce kawai ta kawo karshensu.
Da ya fito, da yake ya lura da canjin tun a jiyan, sai da ya fara bude karatun da jan hankalin daliban, cewa:
“Ita fa wannan makaranta ba wurin fada ba ce. Wanda duk ya san ba zai jure yanayin karatunmu ba, to kamata ya yi ya dena zuwa ma, kawai ya huta. Ya kamata ku sani cewa, shi fa karatu zai iya biyowa ta kan kowa. Kuma duk lokacin da ya biyo sai an yi shi. Wannan shi ne tsarin karatu dama a kowace makaranta. Ba za a dai zagi kowa ba, kuma ba za a aibata kowa ba, amma fa tabbas duk dabi’ar dabbar da aka nemi karin bayani a kan ta, za mu yi. Wannan kuma dama shi ne al’adar karatu.”
Da Zomo ya ji haka, sai ya cika da alfahari yana cewa. “A to, mu ai mun saba zuwa makaranta. Bakinta ne kullum in an yi magana sai su rika ganin kamar wani sabo aka yi.”
Biri ya yi sauri ya kwabe shi, tare da yi masa isharar ya yi shiru. Aka kuma yi sa’a ya yi din. Sannan Malamin ya dora:
“Yana da kyau dai kowa ya sani, komai yana da al’ada, kuma al’adar karatu ita ce juriya: Karatu ba ya taba samuwa sai an sha wuya an jure, kuma sai an hadu da bacin rai an jure. Amma fa idan an yi juriyar karshe ba a taba yin nadama. Kamar yadda a hannu guda, idan aka gaza juriyar kuma nadama ce take biyo baya, maras lokacin karewa. Zabi dai ya rage ga mai shiga rijiya.”
Wani sashe na dabbobin suka ce. “Wannan gaskiya ne Malam.”
Ya kara cewa. “Yanzu ba don albarkacin ilimin ba, ni na isa duk ku zo ku sa ni a gaba kuna sauraro na, kuma komai na fada ku amince?”
“Ina fa.” In ji mafiya yawansu.
Sannan ya ce. “To ina fata wannan bayani zai zama jagora ko alkiblar dukkanmu yayin da muke mu’amula da makarantu a duk inda suke, ba ma iya wannan ba.”
Bayan dukkan dabbobin sun nuna gamsuwarsu da bayanan da Malamin ya yi, sai kuma ya yi sallama da su, ya nufi gida. Su ma a hankali suka nufi gidaje da masaukansu.