Yini Na Sha Takwas
Bayan turo rinduna ta biyu, kusan babu wani babban aiki a fadar Zaki, don haka a wannin yinin da ya fito, ya taras fadar a cike makil. Sai ya dubi Dila ya ce. “Ina ganin ai ma iya ci gaba da sauraren labaranmu ko?”
Dila ya dan gyada kai cikin rashin kuzari, tare da cewa. “Haka ne Rankayadade.”
Sarkin ya dube shi cikin shakku ya ce. “Amma da alama akwai wani hanzari ko?”
Dila ya ce. “To idan ma dai da shi bai fi jan kunne wa dukkan masu bayar da labarin cewa kowa. . .