Yini Na Sha Tara
A can kuwa kololuwar daji, bayan waccan runduna ta biyu ta wuce dukkan wani bigire da take tsammanin kara haduwa da wata dabba. Ba su yi aunai ba suka hangi irin wancan duhu da rindina ta farko ta hanga. Hankalinsu ya tashi kwarai, suka dauka yanzu tabbas sun gamu da abokan gaba. Sai aka fara shirin gagaga, ba kama hannun yaro. Sai bayan kowa ya kammala daura damararsan ne aka fara tunanin yadda za a afka wa rindunar. A nan sai aka samu rabuwar kai; yayin da tsageru irin su Dan Mitsu da Beguwa. . .