Yini Na Ashirin Da Uku
A can tsangaya Malam Kunkuru yana tsakiyar dalibai yana ta faman bayar da karatu, dalibai suna gyada kai har yamma ta yi. A lokacin ne kuma waccan runduna ta kananan kwari ta isa makarantar. Wadanda isar tasu ta sa kallo ya koma sama.
Bayan sallama, sai suka sanar da Malamin cewa Sarki yana nemansa cikin gaggawa. Malamin ya yi murmushi ya ce, “To Sarki karatu zai yi, ko kuwa haraji zai karba daga wurina?”
Kwarin nan suka ce. “Ba mu da tabbaci game da wannan.”
Sai ya ce da su, “To ku koma ku ce da Sarki idan jangali yake so, ni ba ni da kudi kuma ba ni da kiwo. Idan kuwa karatu yake bukata, to a ce masa ya zo makaranta. Domin shi ilimi zuwa masa ake yi, ba ya zuwa wa kowa.”
Dabbobin da suka san izzar Sarkin suka rike baki cikin tsananin mamakin kalaman na Kunkuru, shi kuwa gogan ko a jikinsa.
Sai Zomo ya mike tsaye, ya ce, “Malam ka san Sarki kuwa?”
Malam Kunkuru ya yi dariya: “Wato ku dai na fuskanci har yanzu ba ku san me ne ne ainishin abin da ake cewa daraja ko girma na ilimi ba. Ai idan aka ambaci ilimi an kai karshen zance kenan.”
Zomon nan ya ce, “Uhm uhm fa Malam, ni ina jiye maka tsoro, ka san fa sarauta ba wasa ba ce.”
Malam Kunkuru ya kara dariya, “Koda yake kai dama na san tsagera ne ba ladabi ne gare ka ba. Amma duk da haka bari in yi maka tambaya. Shin ba ka sani ba ne cewa sarauta nadi ce, idan aka nada ka kwanaki kadan za ka goge, ka iya aiwatar da ita? Amma shi kuma ilimi in ba ka da shi kawai ba ka da shi, babu wata rana da za a ce kawai ka goge ka zama mai ilimi?”
Zomo ya ce, “Haka ne kam, ba yadda za a yi wani ya rikide daga maras ilimi zuwa mai ilimi duk damar da ya samu, har sai ya yi karatu. Amma haka kuma wata masarautar ce kowa aka nada zai iya gogewa ya zama sarki, ya kuma iya rike ta, wata kam ko da wuta za a goge shi ta fi karfinsa kawai.”
Yayin da ya kawo wannan gabar sai ya fara jin gurnani ya yawaita a bayansa. Don haka ya yi shiru tare da waiwayawa cikin firgici. Ya lura ashe wasu daga daliban ne tuni suka harzuka, suka fara tunanin yin lauma guda da shi. Kunkuru ya dubi sauran dabbobi masu wannan yunkuri ya ce, “Kar wanda ya kara yi mana haka a makaranta. Mu ai a tsarinmu ba a hana kowa magana, abin da muke bukata kawai hujja, duk mai hujja a bar shi ya yi magana ba tare da wata barazana ba.”
Da zomo ya ji haka sai ya kara kaimi, ya ci gaba da maganganunsa. Har kuma zuwa lokacin da makarantar za ta tashi bai nuna ya gamsu da hujjojin Malamin na bijirewa umarnin wancan Sarki ba. A hannu guda wadannan jakadu da suka isar da sakon na Sarki Malamin bai kara ce musu ko uhm ba, har sai lokacin da ya mike da nufin tafiya gida. Sannan ne cikin wata gadara ya ce da su.
“Shawara daya kawai nake so in ba ku, wadda kuma ita za ta fi taimakonku a rayuwa – Ku tsaya ku saurari karatu gobe, in ya so in ma komawa za ku yi sai ku koma.” Ya juya ya yi tafiyarsa abinsa.