Skip to content
Part 26 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Ashirin Da Shida

Kamar yadda suka yi a yinin jiya, haka yau ma suka hallara da wurwuri, suna faman jiran ganin isowar waccan runduna da kuma wannan takadarin Malami da ake ta faman Ambato. Sai dai sabanin yadda suka zata, jakadun ba su karaso fadar ba sai bayan rana ta yi garji, tuni Sarkin ya dade yana tattauna wasu batutuwan da suka shafi wasu lammuran.

Hangen wannan runduna ya sa har wasu daga dabbobin wurin suka mike tsaye, cikin tsananin zakuwa, ba tare da tuna hakan ya saba wa ka’idojin zaman fadar ba. Da karasowar rundunar sai suka jeho Kunkuru tsakiyar da’irar, kuma gaban Sarki, tim. Sarki ya yi kawai yana dubansa zuwa wani lokaci ba tare da furta komai ba. Shi ma Kunkuru dake cukuikuye a cikin igiya babu abin da yake yi sai faman muzurai. Bayan daukar wani dan lokaci kicin wannan yanayi sai Zomo ya yi farat ya ce.

“Ranka yadade ba ka yi mamakin tsagerancinsa ba?  Ga shi gurfane a gabanka cikin sasari, amma tsabar girman kai ya hana shi neman afuwarka.”

Zaki ya girgiza kai, har yanzu bai ce komai ba. Sannan Damisar can da ta jagoranci kawo shin ta kara mayar da zance irin wanda Kudan Zuman nan ya yi wa Sarki dangane da tsagerancinsa. Har yanzu kuwa bai yi ko uhm ba, balle ya musa wancan batu, ko don ya samu sassaucin Basaraken.

Zaki ya yi wani murmushi, wanda da yawa daga dabbobin wurin sun san bai kai har zuci ba, sannan ya kara duban sa ya ce.

“Kai kuwa wane ne kai?”

Kunkurun nan ya ce, “Ni bawa ne daga cikin bayin Allah.”

Ya kara murtuke fuska. 

Nan take kuwa mafiya yawan dabbobin da ke wurin suka tunzura, suka shiga neman izinin Sarkin, “Ka ba ni dama in hadiye shi ba tare da tauna ba.” In ji Dorunar Ruwa. “Ka ban izini in sa shi ya wulakanta ya yi rawa har da haushin Kare a bainar al’umar nan.” In ji Maciji. Yayin da mafi yawan manyan maciya naman tsabar harzuka ta hana su magana sai faman haki da karkarwa da suke yi.

Da Kunkurun nan ya dan karkata kansa da kyar, ya dubi masu maganar nan, sai ya ce. “Duk iya izayarku, ba ku kai zabaniyawan Fir’auna ba, kamar yadda duk izzar Sarkin naku bai kai ya shi ba.  Amma duk da haka, da aka gurfanar da masu gaskiya a gabansa ba su karaya ba. Suka ma ce masa duk abin da zai yi ya yi, tunda dai sun san karshen dai abin da zai iya shi ne ya kashe su”

Zaki ya ce da shi, “Yanzu kana nufin ba ka tsoro a kashe ka din?”

Ya ce, “Eh,  kawai irin maganar da mafi alkhairi daga cikin ‘ya’yan Annabi Adamun nan biyu ya yi ni ma zan fada maka.”

Zakin ya ce, “Wai me kenan.”

Ya ce. “Idan ka sa a kashe ni, ni ko ina da ikon kashe ka ma ba zan aikata ba. Gara kai din ka kashe ni, in ya so ka hada zunubaina da naka, ka dauka. Ka ga in ka je lahira sai ka kasance daga cikin ‘yan’uwata.”

Zakin nan ya dan yi kasake, alamun dai wasu sake-sake sun fara mamayar zuciyarsa. Sannan kuma ya tuna ai a gaban al’umarsa yake. Ya kara zaburowa ya ce. “To yanzu ka shirya in kashe ka?”

Ya ce, “Eh, shirina daya kawai, zan nemi irin alfarmar da Juraiju ya nema kafin a kashe shi .”

Zaki ya ce, “Wace alfarka kenan?”

Ya ce, “Ta in yi salla raka’a biyu cikin takaitacciyar dakika.”

Zaki ya ce, “Wa ne Juraiju?”

Kunkuru ya kau da kai daga inda Zakin yake, ya ce. “A haba, wannan kuma ai karatu ne.”

“In karatu ne shi kuma ba a fadarsa kenan?” Zakin ya tambaye shi.

Ya ce, “A haba, ai ko Sarki Bitubitu dan Rabi’atu bai taba daure Malami kuma ya ce ya yi karatu a daure ba.”

Da Zakin nan ya fahimci tsawon lokacin da suka dauka suna magana da shi, kusan kowace gaba aka taba sai ya ji akwai wani abu da yake son jin karin bayani daga bakin Kunkurun, sai ya fara tunanin ai kuwa ko da zai kashe shi, to kamata ya yi ya bari sai ya labarta masa dukkan wadancan mutane da abubuwa da yake ta ambata. Sai kawai ya dubi Dan Mitsu ya ce da shi. “Kwance shi, ka tafi da shi gidanka, gobe ka dawo mana da shi fada.”  Har kuma ya kwance shi, za su kama hanya Zakin ya kara cewa. “Babu laifi in an kyautata masa.” Dan Mitsu ya risina tare da cewa. “An gama Rankayadade.”

Kafatanin mazauna fadar suka cika da sake-sake da mamakin yadda al’amarin ya kasance, da ma fargabar yadda zai ci gaba da kasancewar a gaba. Haka dai har fadar ta kai lokacin da ta saba tashi, jikin kusan dukkanninsu lakwas, kamar wadanda aka zare wa laka.  

<< Yini Sittin Da Daya 25 Yini Sittin Da Daya 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×