Skip to content
Part 27 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Ashirin Da Bakwai

Tamkar yini biyu da suka gabace shi, wannan yinin ma tun da sanyin safiya fadar ta dau harami. Wannan hakan kuma, kamar sauran dalilan baya, ba zai taba rasa nasaba da burin bin diddigi da son ganin kwakwaf din yadda za a haife a ragaya ba. Daga cikin abubuwa biyu da suka saba da ranakun da suka gabata kuma, akwai fitowar ‘yan lelen fadar a kan kari, gabanin lokacin da suka zo a sauran ranekun. Sai kuma abu mafi girma, zuwan shi kansa mai gayya da aikin shi ma a irin wannan yanayi, kasa da lokutan da ya saba bayyana.

Bayan gama karbar gaisuwa, sai ya dubi Kahuhu ya ce, “Me za ka ce game da kalaman wannan Malami?”

“Cike suke da rashin da’a. Kuma kamata ya yi ma a ce an ladabtar da shi, don a toshe kofar kar wani ma ya yi kwadayin yi a gaba.” In ji Kahuhun.

“Ko?” In ji Zakin.

“Kwarai kuwa,” In ji Kahuhu; “domin akwai wuraren da dole sai shugaba ya rufe ido ya yi wa Maiwa’azi wa’azi. Kamar yadda Halifa Haruna Rashid ya yi.”

Ya ce, “Ya ya Haruna Rashid din ya yi ne?”

Kahuhu ya ce. “Watarana wani tsageran Maiwa’azi ya zo kofar fadar Halifa Haruna Rashid, ya saki baki ya rika caccakar sa, yana danganta gwamnatinsa da rashin adalci. Da ya ji abin da yake yi, sai ya sa aka kamo shi, aka saka shi a cikin shingen wani masifaffen Doki. Dokin nan kuwa ya samu Malam ya tumurmusa shi sosai. Sannan daga bisani Halifa ya sa aka fito da shi, y ace masa ‘Na tabbata duk nagartarka ba ka kai ya Annabi Musa alaihis salam ba. Haka ni ma duk zalumcina ban kai ya Fir’auna ba. Amma duk da haka Ubangiji cewa Annabi Musan ya yi ya gaya masa magana mai taushi.’ Daga nan da aka salami Malamin sai ya gane ashe shi ne bai iya wa’azin ba. Ka ga wannan ya zama wani babban wa’azi gare shi.”

Dila ya yi farat ya ce, “Kuma a lokaci guda an kare martabar masarautar ba.”

Zakin ya yi dariya, kamar  zai ci gaba da magana game da batun, amma da ya bude baki sai ya kara ce masa: “Amma me ne gaskiyar wadancan kalamai da yake yi, da mutanen da yake ambata?”

“Dukka abubuwa ne da aka saba ambata a tarihin bil’adama. Kuma mafi yawa sun inganta.” In ji Kahuhu.

Ya ce, “To wane ne suka inganta, wannen kuma ba su inganta ba?”

Kahuhu ya ce, “Mutanen can da ya ambata na lokacin Fir’auna da ‘yayan Annabi Adamu da kuma Juraiju duk kissoshinsu sun inganta. Amma batun su Sarki Bitubitu dan Rabi’atu da Sharfu Karrabiy duk sakakkun labarai ne.”

Da mamakinsa sai ya ji Zakin ya ce, “Wato dai na gaskiyar sun fi na kayar yawa?”

Cikin sanyin jiki ya ce masa, “Haka ne, Rankayadade.”

Suna cikin haka sai ga Dan Mitsu ya tiso keyar Kunkuru sun karaso. Da isowarsu kuma dukkansu suka gurfana suka yi gaisuwa. A wannan karon sai Zaki ya yi mamakin yadda ya nutsu ya kuma risina matuka cikin nuna girmmawa gare shi. Har sai da ya tambaye shi.

“Shin me ya sauya tunanin Malamin ne?”

Kunkuru ya ce, “Adalci.”

Zaki ya ce, “Ban gane ba.”

Ya ce, “Adalcinka da na gani kiri-kiri jiya, sabanin yadda ake labarta mana halinka, shi ya kashe min jiki. Ya kuma cusa min girma da kaunarka a raina.”

Zaki ya ce, “Iye?”

Ya ce, “Iy Rankashidade, domin a lokacin da na zo gabanka ban taba tsammanin zan kara taka doron kasa da kafafuna ba. Shi ya sa ma na ce gara in yi kausasan kalamai, tun da tausasan ma ba amfana ta za su yi ba. Domin an ce ba sa tasiri a wurinka in ka so azabtarwa.”

Zaki ya ce, “Wato ni shaidar da ake yi min kenan?”

Ya ce, “Tabbas shi ne abin da muka saba ji game da kai.”

Ya dan yi jim, ya juya dama da hauninsa ya dubi Dila da Kahuhu. Sannan ya juyo da Kunkurun, “Kuma ku duk abin da aka fada muku kawai yarda kuke yi ko?”

Kunkurun ya dan kara dukar da kai, “Ran Sarki ya dade, a yi mini rai. Amma abin da ya sa muke yarda mu ba sanin ka muka yi ba ai. Kuma ana tabbatar mana cewa labaran da muke samu daga makusanta kuma amintattunka suke fita. To idan kuwa sun yi maka wannan shaidar ai dole wanda bai san ka ba ya yarda.”

Tsananin mamaki ya sa fadar ta kara yin tsit, babu wanda yake ko motsin kirki, idan ka dauke jujjuyawar kawuna da idanunsu yayin musayar kallon juna da suke yi irin na mamaki. Zomo ne ya yi karfin hali ya ce, “Malam ka ji tsoron Allah.”

Kunkuru bai ko kalle shi ba, ya ci gaba da maganarsa.

Zaki ya kara tambayarsa, “To su wane wadannan makusanta kuwa?”

Kunkuru ya ce, “Ni kam ba zan iya gane su ba a yanzu, tun da masu bayar da labarin ba su cika kama suna ba in sun tashi fadar abin da wani babba ya fada. Sai dai su fadi kamanni da dabi’unsu.”

Malam Kahuhu ya magantu a daidai wannan gabar: “Ina kyautata zaton  daga jin wadannan kalaman Sarki zai fahimci wannan sam ba malami ba ne, kawai mai yada  fasadi da hada husuma ne a bayan kasa.”

Daga rufe bakinsa Dila ma ya ce, “Haka nan kuma za a fahimci tsananin rashin azancinsa, ta yadda batutuwan ma ba a iya tsara su daidai da yadda hankali zai iya dauka ba.”

Da Kunkuru y agama jin su, sai ya yi dariya. Ya fara kallon Kahuhu ya ce, “A yafe ni Akaramakallahu. Na san kai damuwarka ta kar a cewa wani malami ce, in ka kwantar da hankalinka ni ba zama na zo yi ba,” Sannan ya juya ya dubi Dila: “Rankayadade Sarkin Azanci, a yi hakuri. Na san hikima gadonka ce, kuma wanda ya ga za a ci masa gado sai inda karfinsa ya kare. Kodayake ya kmata kuma kar a rika mantawa cewa Ubangiji Al Karimu yana rarraba baiwarSa duk inda ya so.”

Zakin ya yi murmushi yana mai juya maganansa tsakanin Kahuhun da Dila, a lokacin da yake cewa, “Zan yi mamaki idan kuka yi zaton zan iya aminta da zantukan wani, alhali ku kun karyata su.  Ko in iya aminta da wani, alhali ku kuna inkarin halayyarsa. Saboda in wani bai san ku su wane a wurina ba, ai ku kun sani.”

Suka gyada kai, cikin wani yanayi mai bayyana gamsuwa da maganganun nasa. Wannan kuma shi ya sa kusan dukkan mazauna fadar a wannan lokacin suka saki ransu, wancan yanayin damuwar da fuskokinsu suka bayyana a farko ya gushe.

Bayan wadannan kalaman fadar ba ta tattauna wasu muhimman batutuwa ba har zuwa lokacin tashinta. A wannan karo ma Zakin ya yi wa Dan Mitsu umarnin tafiya da Kunkuru gida da kuma kyautata masa, harwayau zai ci gaba da zuwa da shi fada kullum zai taho. Sannan ya koma gida. wadanda za su tsaya su yi dan kus-kus dinsu duk suka tsaya suka yi, su ma suka tarwatse.

Ana haka dai, a zo da Kunkuru fada a yi zama a tashi, har sai da aka kwashe yini goma, Sarki bai yanke masu wani hukuncu ba! Kodayake ba wannan ne ma ya fi damun dabbobin da ke zuwa fadar kamar maganganun da a kullum yake yi ba. Musamman kuma da aka yi rashin sa’a Sarkin yana matukar son saurarensa, kasancewarsa mai yawan bayar da labarai irin na tarihi da kuma kokarin zakulo wani fanni na ilimi da ya zama bako a wurin Sarkin. Tare da cewa bai cika samun daidaituwar fahimta a matsaya daya da manyan masanan fadar ba. 

<< Yini Sittin Da Daya 26Yini Sittin Da Daya 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×