Yini Na Talatin Da Takwas
Kamar sauran labarai, labarin jawaban Kunkuru na jiya da kuma yadda suka kayatar da Sarkin da alama sun karade dajin. Don haka yau fadar ta cika da ‘yan Jari hujja-irin su Babba Da Jaka, da ‘yan sa ido, irin su Kururu, da ‘yan guntsi-fesar, irin su Shaya da Carki, da ‘yan barbada irin su Yanyawa, da dai sauran rukunan dabbobi da tsintsayen da a baya ba su ma damu da zuwa fadar ba. Kuma ba sa yi mata biyayya irin ta sau-da-kafa. Wadanda kuma ganin su a fadar ya. . .
Awesome