Skip to content
Part 3 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Uku

Da sassafe kananan dabbobin nan kuwa suka yi wa fadar tsinke, cike da annashuwa. Kai ka ce su suka zabi wannan tsarin. Zuwa wani dan lokaci Zaki ya fito bisa rakiyar Barewa da Gada, sabanin yadda aka saba gani. Kammala gaisuwarsu  ke da wuya kuma sai ga Dila tare da Kahuhu. Da zuwa su ma suka gurfana, suka kwashi gaisuwa. Zaki ya dube shi ya ce:

“Alaramma me ya sa ba ka son zuwa fada ne?”

Kahuhu ya dan risina: “Rankayadade, ba son zuwa ne ba na yi ba. Wasu ayyukan fadar ne suke tsare ni a lokutan.”

“Ban gane ba.” in ji Zaki.

Kahuhu  ya ce. “Duk lokacin da ban zo ba, ko dai ina koyar da wata jama’a daga cikin jama’arka, ko kuma na tafi siyaha don bunkasa ilimi. Ilimin da ba ni da wani buri da shi face hidimtawa wannan al’uma taka.”

Zaki ya yi murmushi, ya kalli Dila yana cewa: “Wai kuwa ka taba ganin lokacin da hujja ta kure wa Malam Kahuhu?”

Dila ya risina tare da cewa: “E to, ba dai ni na gani ba, amma Kakana ya fada min cewa an taba kure shi. Kuma shi ne ma sanadiyyar cire shi daga Sarkin Malamain Dawa, kafin daga baya da ka mayar musu da rawaninsu.” 

Zaki ya ce. “Amma fa batun nan ya isa abin mamaki. Ko za ka sanar da mu yadda abin  ya faru?”

Cikin turbune fuska, Kahuhu ya ce. “Rankashidade, ko dai dama Dila ya yi shirin tozarta ni a gaban al’umar dawa ne, shi ya sa ya yo min wannan hilar?”

Zaki ya ce: “Ko daya, da gaske ne mu muke neman ka.” Sannanan ya dubi Dila ya ce: “A bar wannan zance haka, mu fuskanci damuwar da take gabanmu.” 

Dila ya dan kara risinawa lokacin da yake cewa: “An gama Rankashidade.” Kodayake bai fidda ran cewa wataran sai ya bi ba’asin labarin, in suka kadaita ba. 

Zaki ya dawo da ganinsa zuwa kan Kahuhu, yayin da yake cewa: “Ina kyautata zaton dai Dila ya yi maka bayanin kalubalen da yake tunkaro mu.” Kahuhu ya gyada kai. “Haka ne”. Sannan Zakin ya kara cewa: “To babban dalilin zaman fadar na wannan lokutan  shi ne samo mafita gare mu baki daya.” Sannan ya fadada kallonsa, yayin da yake cewa: “Wannan kuma kofa ce a bude ga dukkanmu, kowa yana iya ba mu shawarar abin da yake ganin shi ya fi dacewa da mu.” Sannan ya ci gaba da bin su da ido daya bayan daya.

Nan da nan kuwa aka fara daga hannaye. Zaki ya dubi masu daga hannayen nan, sannan ya juyo ya dubi Dila. Nan take Dila ya kara duban hannayen sosai, sannan ya nuna Tururuwa ya ce. “Bisimillah.”

Tururuwar nan ta dan kara matsowa gaba tana mai bayyana cikakken ladabi: “Ubangiji Ya kara wa Manyan dawa yawan rai. Daga abubuwan da na haddace daga zantukan Kakata, takan ce wai, ‘Matsoraci yana mutuwa sau dubu kafin ainishin lokacin mutuwarsa, amma jarumi ba ya mutuwa face sau daya tak.’ Don haka, tabbas maimakon mu tsaya fargaba ta hana mu sakat, gara mun tunkare su, mun gama da su, mu dawo rayuwarmu cikin aminci.” Ta dan tsahirta, don karanta yanayin da Basaraken yake ciki. Da ta lura da cewa lallai motsinsa yana alamta gamsuwa da batutuwanta, sai ta dora: “Kuma ina tabbatar wa fada cewa duk lokacin da aka tashi wannan tafiya, ni ma ina da rawar takawa. Don haka ba za a bar ni a baya ba.”

Dila ya ce. “Ko wace irin gudunmawa kike ganin za ki iya bayarwa a wannan tafiya?” Tururuwa ta ce. “Dukkan rundunar yaki tana bukatar abubuwa uku; abinci  da masana taswira da kuma ‘yan leken-asiri. Don haka, ina mai ba wa fada tabbacin cewa, ni kuma zan bayar da gagrumar gudunmawa a wadannan bangarori. Na farko, duk inda dakarunmu suka yi zango, ni zan lalubo masu inda taskar abinci mafi kusa da su take. Tare da debo musu bakin gwargwado. Na biyu, ina da ilimin sanin taswira, kuma duk rintsi kaina ba juye wa. Sannan idan na so, akwai sinadari da nake digawa a duk hanyar da na bi, ta yadda  duk wanda ya kiyaye da kamshin wannan sinadarin zai iya bibiyar sawuna, har inda na tsaya. Don haka, ina ganin idan har an ba ni dama, ina tabbatarwa da fada cewa komai nisan tafiya da shataletale da rarrabuwa da dakarun za su iya yi, idan daga ta kai daga, ni zan jagoranci kara tattara su wuri guda, sannan in shiryar da su hanyar gida. Abu na karshe kuma, ni gwana ce a leken-asiri. Domin ina sajewa da duhun dare, in kutsa cikin dabbobi da dama ba tare da sun gan ni ko sun ji sautin sawuna ba. Idan kuwa na ji tsoron dabbobi masu karfin jin kamshi, ina iya haka in shige ta karkashin kasa, in gama bincikena, ba tare da an ji ni ba. Haka kuma in na ji tsoron masu iya haka ko tona kasa, sai in zaro fuffukena, in tashi sama, har sai na kammala aikina!”

Zaki da Dila suka kalli juna cikin mamaki da kayatuwa da bayanan Tururuwa. Sannan Dila ya ce mata: “Hakika ke abokiyar tafiya ce. Kuma fada tana maraba da  wannan gagarumar gudunmawa taki.”  Tururuwa ta kara risinawa gami da yin  godiya, sannan ta ja baya.

Daga nan Dila ya kara nuna Biri, tare da cewa: “Bisimillah.” Birin nan ya yi sauri ya furzar da furkakin dirimin da ke bakinsa, gami da zakudowa gaba cikin ladabi: “Rankashidade, ni ina ganin wannan labari an kambama shi ne kawai fiye da kima, amma bai kai yadda muke tsammaninsa ba. Kuma idan ma ya kai, to ni na yi wa fada alwashinn cewa, mu kadai kabilun birai za mu kawo karshen balahirar.”

Dukkan dabbobin nan suka saki baki, suna kallon Birin nan cikin mamaki. Dila ya ce da shi. “Shin ko za ka yi wa fada bayanan da za ta iya gamsuwa?”

“Madalla,” in ji Biri: “Na tabbata fada tana sane da cewa muna cikin dabbobi mafiya yawan kabilu a wannan dajin, idan ba mu fi kowa ba ma. Kuma kowace kabila daga cikinmu tana da wata bajinta da ta shahara da ita. Don haka, idan an ba mu dama, muna da hanyoyi har uku daya bayan daya, wadanda za mu iya amfani da su don kawo karshen wannan razani.”

“Muna jin ka.” In ji Dila.

“Na farko, za mu bi hanyar sulhu. Domin muna da wasu manyan bakaken birai a yammacin Da’ifa. Wadanda suke da kyakkyawar alaka da karnuna. Don har sukan dauki ‘yan kwikwiyo su raine su, su tashi a cikin garkensu. Kai ka ce ‘ya’yansu ne! wadannan biran duk inda suka hadu da wata kabila ta karnuka, nan da nan suke samun kyakkyawar fahimta da jituwa. Don haka, idan fada ta so ta ba wa wannan kabila tamu dama, muna sa ran za su iya samun daidaito da waccan runduna. Ba tare da zubar da jinni ba.

“Idan kuwa hakan ba ta samu ba, muna da wata kabilar biri masu abin mamaki, a dajin Sampolo. ‘Yan mitsi-mitsi ne kwarai, shi ya sa ma muke  ce musu Namamatse. Domin idan a cikin duhu suka wuce, sai ka zata berayen dinka ne! Suna da matukar gudu da zafin nama, kuma sun kware matuka a fannin yaki. Domin idan wata dabba ta zo kusa da su, suna iya tayar da kura cikin gaggawa, nan da nan kura ta bule idanun dabbar. Ko ma su tsokane mata idanun da kansu, ta hanyar amfani da dogayen faratansu. Sannan suna yin wani fitsari mai tsananin doyi, in sun so. Wanda duk dabbar da ta shake shi, nan take za ta dena jin kamshin komai. Wasu ma har maye sukan yi, tamkar sun sha banju!

“Wannan ya sa sau da dama idan za a yi wata fafatawa tsakanin birrai da wasu dabbobi, to Namamatse akan fara turawa gaba. Sau da dama kafin ma wasu masu nauyin jiki su karaso filin dagar mun ci karimin abokan gabarmu, sakamakon illar da suke yi musu cikin gaggawa. 

“Idan kuwa abin ya ci tura, to muna da wata kabilar goggon biri a kudancin Zanzibar, da muke ce musu Banu-Dungazau. Birai ne masu tsananin girman jiki da karfi, kuma fatarsu tana da matukar tauri. Zai yi wuya su hadu da wata dabba komai girmanta gabansu ya fadi. Kodayake ba su cika tsokana ba, amma idan an tabo su, suna iya fafatawa da kowace irin dabba a dawa. Kuma samun galaba a kansu ba karamin aiki ba ne. Saboda sun kware a kusan dukkanin wani salo ko dabaru na fada irin na bil’adama. Duk girman wata kabila daga kabilun kare, ba na ko raba daya biyu Banu-Dungazau za su jure cizonsu na farko. Kuma da zarar sun daga su sama sun fyada da kasa sau daya, to fa zai yi wuya su shura.”

Zaki ya gyada kai cikin alamun kayatuwa da bayanan. Sannan Dila ya kara duban sauran dabbobi da ke daga hannaye, ya ci gaba da ba su umarni. Sannu-sannu sai da aka ba wa duk wanda ya nema dama, ya fadi abin da duk ya so fada. Sannan kuma fada ta yi kawai, hankali ya koma kan basarake.

Zaki, wanda sabbin alamun kuzari suka kara bayyana a tare da shi, ya fara bayani: “Wato, ba ma son matsala, amma abin da ba ma lura shi ne, matsala tana da matukar muhimmanci a rayuwa. Domin sai da matsala kake iya fahimtar dinbun baiwar da Ubangiji  Ya yi maka. Kafin wannan lokaci, ni kaina da nake jagorancin al’umar wannan daji shekara da shekaru, ban taba sanin ku da kuke gabana kullum kuna da wannan tarin darajoji da basira da karfi da dabaru iri-iri haka ba!”

Kahuhu da Dila wadanda su ne ke daf da shi, su ka hada baki: “Ubangiji Ya kara maka nasara.” Sannan ya ci gaba: “Abin mamaki ne kwarai kuma abin alfahari, a ce wadanda muke ganin kamar raunana ne a cikinmu, ashe su ma suna da abubuwan da za su iya taimakon mu da su, ko da a rayuwarmu ta yau da kullum. Kafin wannan lokaci wane ya yi tunanin Mahauniya ma za ta iya taimakon Damisa, ko Kiyashi zai iya taimakon Bauna?” 

Kafatanin jama’ar fadar suka hada baki, suna cewa: “Babu kam!”

Ya ce: “To don haka, daga yau, mun zabi rana irin ta yau a kowace shekara ta zama Ranar Godiya! Wadda za mu rika haduwa mu jiyar da junanmu irin baiwace-baiwace da Ubangiji Al Karim  Ya yi mana. Daga nan mu ci mu sha, mu yi nishadi, kamar yadda muka saba yi a sauran ranakun bukukuwanmu!”

Nan take kuwa fada ta cika da murna, masu rungumar juna na ranguma, masu alkafura ma na yi. Dila ya ce. “Rankashidade, hakika wannan tsari ya yi kyau matuka, kuma bayan kasancewarsa abin farin ciki, zai zama wani babban taimako a gare mu, mu masu nazarin dabi’un al’uma. Domin daga abubuwan da Kakana yake fada min wataran ya taba ce min. ‘Babu wani mai rai face yana da wani bangare wanda baiwarsa ta girmama a cikinta. Wanda Ubangiji Ya tawaya ta wani wuri, to kuma Yana karfafarsa ta wani bangaren da ba lallai ne wasu su sani ba. Shi ya sa babu wani banza a duniya, kuma babu wanda ya cancanci raini ko kaskanci.’ To wannan ranar ta tabbatar min da waccan magana tasa. Kuma ina sa ran sai ma nan gaba.”

Bayan wannan lokaci ne kuma haunawan suka bukaci dukkan mai wani abin cewa ya yi hakuri sai gobe. Kasancewar da maraice ma fada za ta kara zama da manyan dabbobin dawa. A lokacin da zakin ya yi bankwana da su ya koma gida tuni rana ta fara zafi.

Da la’asar kuwa bayan rana ta fara sanyi, manyan dawa suka hallara a fada. Jim kadan Zakin ya bayyana, bisa rakiyar Damisa da Giye a dama da hauninsa.  Bayan dukkan mazauna fadar sun yi gaisuwa, Dila ya fara da cewa.

“Kamar yadda fada ta yi alwashin ba ku dama a matsayinku na manya, na-jika,  wadanda kuma ku ne alfaharin wannan fada. Ga shi Ubangiji Al Karim Ya ara mana rana da lokaci. Da safe Sarki ya gana da kananan dabbobi, kamar yadda ku ka sani. Mun ji ta bakinsu game da wannan balahira da take tunkaro mu. Yanzu kuma dama lokaci ne da fada take sa ran jin ta bakinku. Musamman kasancewarku masu gayya, masu aiki.”

Kafin rufe bakinsa kuwa hannayensu suka  yi wa saman fadar tsinke, kowannensu yana hankoron ya zama shi ne wanda zai fara magana. Dila ya fara nuna wani Toron Giwa mai tsananin girman halitta. Wanda kuma sanennen sadauki ne a cikin dajin, tsawon lokaci. Yana mai cewa . “Misimillah.”

“Ni ina ganin daukan wani lokaci na musamman ana ta tattaunawa a kan wata halitta, wadda kuma ana da tabbacin kabilu ne daga kabilun Kare, to abin kunya ne a gare mu!” Sannan ya dan risina, yana cewa “A gafarce ni, amma tabbas mun yi sakaci, kuma in ba mu dauki matakin da ya kamata wurin farfado da kanmu da tuna wa junanmu mu su wa ne ba. To ba mamaki nan gaba shantakewarmu ta kai ko bakuwar Gafiya ce ta doso mu, sai mun shiga tararddadi.”

Nan da nan kuwa muryoyi a fadar suka rika bayyana sama-sama; “Kwarai” “Tabbas”  “Gaskiya” da ire-irensu. Wadanda dukkansu ke alamta ra’ayi irin na mai maganar. Bayan kammalawarsa ne kuma aka ba wa Bauna dama. Wadda ta mike ita ma cikin takama tana cewa:

“Idan har yanzu fada tana ganin wadancan dabbobi da ake zance barazana ne gare mu, to ina rokon ta ba mu dama, mu kadai, kabilun Bakane. Za mu lalubo su a dajin mu gama da su!”  Ta juya ta bi dabbobin da suke zagaye da fadar da ido.  Sannan ta kawa cewa: “Mu da tun lokacin da aka haife mu ake koya mana jarumta. Domin bayan Bauna babu wata uwa da in ta haifi jariri ta ga ya fara yunkurin tashi sai ta tunkuye shi, ya fadi! Haka za tai ta yi masa na wani lokaci, ba tare da tausayi ba. Don kawai ya fahimci ya zo duniya mai cike da kalubale!”

Kafin ta idar Karkanda ya sako baki, yana fadar tasa gwanintar. Sai ga Kura ma, har daga karshe dai aka rasa wanda za a saurara. 

Dila ya rada wa Zaki. “Sai hakuri fa Rankashidadde, ka san girma da wauta dai tamkar hanta da jinni suke.”

Da Zaki ya lura tamkar sun ma manta a fada suke, sai ya yi wata kara. Sai da dukkansu suka yi shiru, suka nutsu, shi kuma sai ya kama hanya, ya fice daga fadar, cikin tsananin daure fuska!

Nan kuma su ka tsaya cirko-cirko, cike da zullumi. Lokaci mai tsayi suna kallon-kallo a junansu. Sannan daga baya wasu suka fara zarginn wasu, cewa su suka janyo harzikar basaraken. Yayin da daga baya kuma wasu su ka fara zargin Zakin bisa nuna rashin juriya irin ta masu mulki:

“Haka ake jagorancin jama’a?  Ai dama shi babba juji ne, don haka ko da zagin sa aka yi bai kamata ya fusata haka ya bar mu cikin hayaniya ba.” Inji Mugundawa.

Nan da nan Giyen nan da ya fara Magana ya ce. “To ga shi nan dai, yau ku ma kun gani. Yanzu  ya tafi ya bar mu a haka, har mun dawo muna musu da juna. Yanzu kenan in ma fada ne ya barke a tsakaninmu, sai dai mu kashe kanmu. Babu mai tsawatar mana?”

“Kuma na tabbata in da iyalinsa ne ai ba zai tafi ya bar su a cikin wannan yanayin ba.” Inji Kura.

Ai kafin wani lokaci sama da rabin dabbobin wurin babu abin da suke yi sai sukan lamirin Zakin.  Har sai da Dila ya ce da su:

“Tabbas Zaki ya nuna rauni, bai kamata shugaba ya zama haka ba!”

Nan da nan kuwa hankalin dabbobin ya dawo kan sa. Ya kara cewa. “Ina ma laifin in ma ba zai tsawatar ba, ya zauna a wurin dai, watakila ganin idonsan  zai iya sa wasu su ji nauyi, su yi shiru.”

Bauna ta ce. “Madalla, yanzu kai ma ka fara fahimtar rashin cancantarsa kenan? Yanzu kai kana ganin haka ya kamata shugaba ya yi wa jama’arsa?”

“Ina fa….” Inji Dila. “ai da ya yi haka  gara ma ya sa a ladabtar da duk wadanda suka saba doka. To amma shi kullum in abu ya zo wanda ya kamata ya yi zazzafan horo, sai ya ce wai so ba zai bar shi ya azabtar da jikinsa ba.”

Suka hada baki su kusan bakwai: “Ba mu gane ba.” 

“Duk lokacin wani abu ya samu wani daga manyan dabbobi irinku,” Inji Dila. “ya rika bakin ciki kenan. Cewa yake wai ku tamkar wani bangare ne na jikinsa. Shi ya sa duk irin laifin da ku ka yi ma ba ya so a yi muku horo. Domin har shi ake jin zafin. To ya za a yi kuwa mulki ya yiwu da haka?”

Damisa ta karkatar da kai, ta ce. “Au haka ne?’’

Giyen nan ya ce. “Allah sarki!”

Kura ta ce. “Sai kuma na ji ina jin tausayin sa. Ai ni ban san haka yake ji da mu ba sam.”

Nan da nan kuwa duk jikinsu ya yi sanyi, kuma kalaman kusan kowannenu ya sauya daga kaushi zuwa taushi. Shi kuwa Dila bai gushe ba yana  sukar Zaki ta hanyoyin da suke bayyana tsananin damuwarsa ga wadannan dabbobi, har sai da ya lura sun fara galla masa harara. Can ya koma gefe guda ya bata rai. Su kuwa su ka yi ta tafiya daya bayan daya cikin sanyin jiki, har dai fada ta rage Dila da Kahuhu.

Kahuhu ya dubi Dila ya ce. “Wato tabbas na kara yaba kokari da hikimrka yau!” Dila ya yi murmushi sannan ya mayar masa. “Ai zama da ku ne, ka san an ce zama da madaukin kanwa…”  Ya yi dariya sannan ya ce. “To na ji, ka rama.” Bayan wani dan lokaci ya kara cewa. “Amma fa lallai ka ba shi shawara ya dena gangancin barin fada a lokacin da take cike da manya.”  Dila ya ce. “Sa munjaye dai Aalaramma, in ba shi shawara ko mu ba shi?’ Dukkansu su yi dariya.

<< Yini Sittin Da Daya 2Yini Sittin Da Daya 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×