Yini Na Arba’in Da Daya
Sabanin dukkanin yinin da suka shude tun bayan darewarsa karagar mulkin dajin, cikin matukar sanyin jiki, da gayar rashin walwala ya shigo fadar! Wanda duk ya san shi kuma a kallon farko zai iya fahimtar cewa lallai wani abu yana faruwa. Kodayake, dayake ba a yi wa Saraki shisshigi, haka kowa ya yi shiru bayan kammala gaisuwa, aka shiga jiran umarnin da zai bayar, sawa’un da furuci ko da ishara, kamar yadda ya saba. Sai dai a kusan sa’a guda da ya kwashe bai yi daya daga cikin biyun ba.
Abin mamaki, shi ma Shehin Malamin wanda a yanzu shi ne dan gaban goshin fadar bai ce ko uhm ba! Karasowar Dila fadar, shi ya katse shirun da aka yin a tsawon lokaci, “Anya kuwa Rankashidade lafiya kake?”
Zakin ya girgiza kai a hankali, ba tare da furta komai ba. Sai ya kara ce masa. “Ba ka koma ciki ka dan kwanta ka hut aba?” Zakin ya kara girgiza kai irin yadda ya yi a farko. A wannan gabar ne kuma Malamin ya magantu: “Ku kam kuna wuce gona da iri. Ban taba jin inda talaka zai ba wa Sarkinsa shawara wai ya sauka daga kan karaga, ya koma gida ba. To a yi yaya da ragamar garin kenan?”
Zakin ya waiwayo ya kalli Malam Kunkuru kamar zai yi wata magana, sai kawai wani amai ya fara tunkuda daga bakinsa! Nan da nan fada ta ciki da firgici, ba shiri kuma aka daddafe Sarki aka mayar da shi cikin gida. Fada kuma ta tashi daga nan, kowa ya kama gabansa, ya nufi gida cikin mawuyacin hali!
Daga wannan rana dai kullum jikin Barasaken nan kara tsanani kawai yake yi. Wani lokaci sai a ga yana ta faman dafe cikinsa, idan kuma aka durfafi maganin ciwon ciki, sai a ga koma rike kansa. Idan aka mayar da hankali da maganin ciwon kan, sai waccan haraswa ta kara uzzura masa! Kafatanin wani mai magani da suka sani a ciki da wajen dajin sai da suka kirawo shi, amma dukkansu da suka yi babu ko alamun jikin ya san ana yi.
Don haka batun fitowar Sarki fada ma sam babu shi. Da dabbobi suka ga abin ya tsawaita, sai suka hadu suka samu Dila suka ce masa: “Yallabai, ka ga dai duk da ba ambatawa ake yi ba, kowa ya san kai ne wazirin Sarki. Don haka, tun da yanzu ba shi da lafiya kamata ya yi kai ka zo ka ci gaba da zama a mazauninsa kana jan ragamarmu. Bai kamata mu rika zama ba shugabanci ba.”
Dila ya ce da su. “Na ji, kuma na gode da wannan tayi naku, amma ku yi hakuri ba zan iya ba gaskiya.” Da ya lura da tsananin lamun mamaki a tattare da su, da kuma yadda wasu suka fara maganganu irin na ganin baike game da amsar tasa, sai ya kara cewa. “Ba wai mulkin ne ba zan iya ba, ba kuma kwata-kwata ba na so ba ne. Amma kun sani, mu abin da muka gada a gidanmu ita ce hikima. Shi kuwa mai hikima duk inda za ka same shi ba ruwansa da kankanba da cusa kai inda ba a maraba da shi. Domin a can cikin ransa yana jin yana da wata baiwa ta musamman da Ubangiji Ya ba shi, wadda ba za ta taba tabewa ba. Idan an rufe masa kofa a nan, in ya yi gaba zai taras da wasu budaddun kofofin suna yi masa magiyar ya shigo.”
Wani Sashe na dabbobin suka ce, “Haka ne.”
Sannan ya dora: “Da a ce kafin wannan bakon Malamain ya zo ne, ko kuma da a ce Sarki bai dauke shi ya fifita shi a kanmu ba, kamar yadda duk kuka gani, da babu abin da zai sa in karbi wannan aiki ko da ba ku shawarce ni ba. Domin kamar hakki ne a kaina.”
Aka kara cewa, “Haka ne.
Ya ce, “To yanzu wa yake da tabbacin idan da zai iya budar baki ya yi magana, ba Kunkurun zai ce ya rike masa kujerar ba?”
“Babu kam.” Suka fada cikin wata murya mai kalar kuka.
Ya ce, “To daga mafi girman abin ki a gidanmu, shi ne ka yi wa wanda ba ya nan ko mai barci wani abu kana tsammanin gwaninta kake yi masa, shi kuma ya farka ya gwasale ka. Idan irin wannan ta faru da mu, sai mun shafe a kalla yini sittin da daya muna cikin kunci, kuma ba mu kara gwada wani aiki na hikima da zai amfane mu ko wasunmu a cikin wannan yinnan ba!”
Da suka ji wannan sai suka yarda cewa lallai ya kamata su yi masa uzuri. Sannan suka tambaye shi, “Amma kai mene shawararka? Mu kam ba ma son zama babu jagora.”
Ya ce, “Kuna da zabi a cikin ko dai ku yi abin da Sarki yake so, ko ku yi wanda ya dace. Amma kar ku yi abin da kuke kokonton ingancinsa.”
Kafin kowa ya bude baki ya juya ya ce, “Ubangiji Ya ba wa Sarki lafiya.” Ya bar wurin.
Daga nan da suka rasa matsaya, sai suka kara dunguma suka tafi gidan Kahuhu. Shi ma bayan sun sanar da shi bukatarsu, bai bata lokaci ba ya sanar da su cewa. “Ni fa dama can ba abin da ya hada ni da fada. An gayyace ni ne saboda idan an samu wata sarkakkiya wadda ilimi ne zai warware ta, in bayar da gudonmawa daidai abin da Ubangiji Al Alim Ya fahimtar da ni. Yanzu kuwa tun da aka samu wani Malami da zai yi wancan aiki, nauyi ya saraya daga kaina. Kuma shi ya sa ma kuka ga na dena zuwa ai. Don haka a nemi jinin saruta, ni kam zaman fada dama ba nawa ba ne. Zan rika zuwa dubiya dai domin ita hakki ce a kaina.”
Har ya juya zai koma gida, sai kuma ya kara waiwyowa ya ce da su. “Amma idan kun tashi tura jakada wanda yake magana a madadin muryoyinku, kada ku kuskura ku tura wanda kullum aibata jama’a ne kawai a bakinsa. Wanda sharrin jama’a kawai ya sani bai san alkhairinsu ba. Domin wanda duk zuciyarsa ta yumke ba ta ganin komai sai sharri, ba zai taba ganin alkhairi ba, balle ya gayyato muku shi.” Ya shige gida abinsa.
Haka shi ma suka hakura suka bar shi, suka koma cikin rashin sanin takamaimiyar madafa.
Cikin wannan hali kuma ran Sarki kwakwai mutuwarsa kwakwai sai da aka kwashe yini goma sha bakwai, ba tare da kuma sun samu matsaya guda takamaimya ba.
Allah yakyauta
Comment